Skip to content

Dinya

    Aika

    Ɗinya itaciya ce wadda ta samo asali daga nahiyar Afirka, musamman a yankunan da ake samun ruwan sama. Sunanta na kimiyya shi ne Vitex doniana, tana daga cikin dangin Lamiaceae. A harshen Turanci ana kiranta da black plum ko African olive, amma a Hausance ta fi shahara da suna ɗinya. A wasu yankuna kuma tana da sunaye daban-daban, misali, a Yarbanci ana ce mata òori-nla, yayin da a wasu ƙasashen Afirka take da sunayen da suka dace da harsunan mutanen wurin.

    15664838382506758066294231569338
    Ɗinya itaciya mai dimbin alfanu.

    Ɗinya na daga cikin muhimman itatuwa da aka daɗe ana cin gajiyarsu tun zamanin kaka da kakanni. Ana cin ’ya’yanta kai tsaye a matsayin kayan marmari saboda ɗanɗanonsu mai daɗi, kuma suna da laushi da santsi a baki. Baya ga haka, ɗinya na ɗauke da yalwar sinadaran gina jiki, tana kuma bayar da maiƙo, furotin, da minerals. Wannan ya sa take da tasiri wajen inganta lafiyar al’umma musamman a yankunan karkara inda ake samun ta cikin daji.

    Baya ga cin ’ya’yanta, ana amfani da ganyayyaki da ɓawonta a matsayin magungunan gargajiya. Bincike daga masana sun nuna cewa ganyen ɗinya na da amfani wajen maganin zazzaɓin cizon sauro da gudawa, yayin da ɓawonta ke da tasirin kariya ga hanta da kuma kashe ƙwayoyin cuta. A al’adance, a wasu ƙauyuka ana amfani da ɓawon ɗinya wajen sarrafa ruwan magani don warkar da cututtuka iri-iri.

    Saboda wadannan dalilai, ɗinya na daga cikin itatuwan da ke da babbar rawar takawa wajen abinci, magani da kuma tattalin arzikin al’umma.

    Siffar bishiyar ɗinya

    Ɗinya (Vitex doniana) itaciya ce mai juriya wadda take daga cikin manyan itatuwa ‘yan asalin Afirka. Ita ce itaciya mai rassan da ke yaɗuwa a sama suna ba da inuwa mai yawa. A matsakaicin girma, tana iya kaiwa tsayin mita 20 zuwa 25, yayin da faɗinta zai iya kaiwa mita 1 a wuraren da take girma sosai.

    • Ganyaye: Ganyen ɗinya suna da launin kore mai ƙyalli, suna fitowa a cikin rukuni-rukuni kamar guda biyar. Sun kasance masu faɗi kuma suna da santsi, suna da ban sha’awa da kyan gani a lokacin damina.
    • Fure: Ɗinya na fitar da ƙananan furanni masu launin fari ko ruwan ƙasa waɗanda ke fitowa a gungu. Furannin suna jan hankalin ƙwari musamman zuma da tsuntsaye waɗanda ke taimakawa wajen ɗaukar ƙurar furanni (pollination).
    • ’Ya’yan ɗinya: ’Ya’yan ɗinya su ne nau’in drupes masu zagaye ko ɗan tsawo da tsawon santimita 2 zuwa 3. A lokacin da ba su nuna ba, suna da launin kore mai ɗan duhu, amma idan sun nuna sai su koma baƙi mai duhu ko shuɗi mai duhu. Suna da ɗanɗano mai zaƙi, ɗan kauri, kuma suna da laushi a baki. Ana iya cin su kai tsaye, ko a busar da su a ci daga baya.
    • Tsaba: A cikin kowace ɗinya akwai ƙwallo guda ɗaya ko fiye da ke da ƙarfi da tauri. Wannan ƙwallo yawanci ana yar da shi a ƙasa, amma bincike ya nuna yana ɗauke da maiƙo da furotin masu yawa, tare da wasu sinadaran masu amfani.
    • Jijiya: Bishiyar ɗinya na da jijiyar da ke shiga ƙasa sosai, abin da ke ba ta damar jure fari da kuma tsayuwa tsayin daka a kan ƙasa mai rauni.

    Ɗinya tana ɗaya daga cikin itatuwan da ke ba da kariya ga muhalli saboda bishiyoyinta suna iya hana asarar ƙasa ta hanyar rufe ƙasa da ganye da kuma tsayar da ruwa. Wannan ya ƙara mata muhimmanci a tsarin kiyayewa da inganta noma.

    Amfanin ɗinya

    Ɗinya na ɗaya daga cikin itatuwan da al’umma da dama a Afirka ke amfani da su tun zamanin kaka da kakanni. Amfaninta ya shafi fannoni da yawa, kama daga abinci zuwa magungunan gargajiya, da kuma masana’antu.

    1. Amfani a matsayin Abinci

    • ’Ya’yan ɗinya: Ana cin su kai tsaye a matsayin kayan marmari. Yawanci ana cin su idan sun nuna saboda ɗanɗanon su mai zaƙi ne. Haka kuma ana iya busar da su a adana su domin amfani a lokuta masu zuwa.
    • Ganye: A wasu yankuna, ganyen ɗinya ana tafasa su ana sha a matsayin abin sha mai amfani ga lafiya. Ana kuma iya haɗa su da abinci a matsayin mahadi.
    • Ƙwallo: Duk da cewa a baya ana yawan yar da ƙwallon, bincike ya nuna cewa suna da yalwar sinadarin maiƙo da furotin, tare da sinadaran gina jiki masu muhimmanci. Wannan na nuna tabbacin amfani da su wajen abinci a nan gaba, musamman a matsayin tushen maiƙo da furotin.
    • Man ɗinya: Daga ƙwallon ɗinya ana iya tace mai wanda za a iya amfani da shi wajen dafa abinci ko kuma a yi amfani da shi a masana’antu.

    2. Amfani a matsayin magungunan gargajiya

    • Ganye: Ana amfani da ganyen wajen maganin zazzaɓin cizon sauro da ciwon gudawa. Ana tafasa ganyen ana sha a matsayin magani.
    • Ɓawo ko sassaƙe: Sassaƙen itaciyar dinya na da tasirin kariya ga hanta (anti-hepatotoxic) da kuma kashe ƙwayoyin cuta (antibacterial). A wasu ƙauyuka, ana shan ruwan ɓawon ɗinya don rage ciwon ciki ko matsalolin narkewar abinci.
    • ’Ya’yan ɗinya: Ana ɗaukar su a matsayin tushen kuzari ga jiki saboda sinadaran da suke ɗauke da su, musamman ga yara da tsofaffi.
    • Ƙwallo: Sabbin bincike na nuni da cewa ƙwallon ɗinya na ɗauke da sinadaran antioxidants da ke iya kare jiki daga cututtuka masu alaƙa da ƙwayoyin free radicals, kamar su ciwon daji.

    3. Amfani ga Masana’antu

    • Man ɗinya: Za a iya amfani da shi wajen sarrafa man shafawa, sabulu, da kayan kwalliya.
    • Sinadarai: Wasu sinadarai da ke cikin ƙwallon suna da amfani wajen haɗa magungunan zamani, musamman saboda ƙarfinsu a matsayin antioxidant, antibacterial da anticancer.
    • Itace: Ana amfani da itacen ɗinya wajen gini, ƙera kayan ɗaki da kuma samar da makamashin girki (charcoal).

    Ɗinya, saboda wannan yalwar amfaninta, ta kasance muhimmiyar itaciya a tsakanin al’ummomin Afirka. Ita ce itacen da ke samar da abinci, lafiya da tattalin arziki.

    Wuraren da ɗinya take fitowa

    Ɗinya tana daga cikin manyan itatuwa masu yaɗuwa a nahiyar Afirka. An fi samun ta a yankin Afirka ta Yamma, ciki har da Najeriya, Ghana, Burkina Faso, Togo, Benin, da Nijar. Haka kuma tana bazuwa zuwa Afirka ta Gabas, a ƙasashen Uganda, Kenya da Tanzania, da wasu sassa na Afirka ta Tsakiya.

    A Najeriya, ɗinya tana da yawa a jihohin da ke da yanayin savanna da kuma yankunan da ake samun ruwan sama sosai. Akwai ɗinya sosai a jihar Ebonyi, tana fitowa ne a daji ba tare da shuka ta musamman ba. Haka ma a wasu sassan Arewa da Kudu, ɗinya tana fitowa a daji, ko kuma a cikin gonaki da ke kusa da gidaje inda ake amfani da ita don inuwa da kuma ’ya’yan itace.

    Ɗinya tana da juriya ga yanayi. Za ta iya rayuwa a wuraren da ake samun ruwan sama mai yawa, haka nan kuma tana iya jure fari saboda jijiyoyinta masu tsawo wanda ke samun ruwa daga ƙasa mai zurfi. Wannan juriya ta sa tana iya bunƙasa a wurare masu ƙasa marar ƙarfi, har ma a wuraren da ake sare gandun daji ko zaizayar ƙasa.

    A gefe guda kuma, ɗinya ta fi bunƙasa a wuraren da ƙasa ke da yalwar sinadarai da kuma ƙasa mai ɗan danshi. Itaciyar tana iya fitowa a wuraren da ba a kula da su, amma tana iya ba da amfanin ’ya’yan itace da yawa idan aka shuka ta da kulawa.

    file
    Ƙwallon ɗinya yana ƙunshe da muhimman sinadarai masu amfani a fannoni daban-daban.

    Saboda irin yaɗuwar ta a fadin Afirka, ɗinya ta zama itace da ta dace da muhalli daban-daban, daga yankin savanna har zuwa dazuzzukan da ke da ruwan sama mai yawa. Wannan ya sa take da matuƙar muhimmanci wajen kiyayewa da kuma amfani a fannoni daban-daban na rayuwa.

    Sinadaran da ke cikin ɗinya

    Ɗinya na ɗauke da sinadaran gina jiki masu matuƙar amfani ga lafiyar ɗan’adam. Bincike daban-daban ya tabbatar da cewa duka ’ya’yan ɗinya, ganye da ƙwallon ɗinyar suna da yalwar sinadaran da ke samar wa jiki kuzari da kuma kare shi daga cututtuka.

    • Bitamin C – wanda ke ƙarfafa garkuwar jiki, yana kuma taimakawa wajen warkar da raunuka.
    • Bitamin A – wanda ke da muhimmanci ga lafiyar ido da fata.
    • Minerals: Kamar calcium, magnesium, potassium da iron, waɗanda ke taimaka wa jiki wajen gina ƙashi, jini da kuma daidaita aikin tsoka.
    • Kitse kashi (36.5%) – wanda wannan kashi ya fi yawa idan aka kwatanta da yawancin ‘ya’yan tsirran da ke samar da wannan sinadarin, kamar su soyabean da ƙwallon auduga.
    • Furotin kashi (27.6%) – adadin ya fi yawa idan aka kwatanta da wake. Wannan ya nuna ƙwallo ɗinya na iya zama kyakkyawan tushen furotin samun sinadarin furotin.
    • Carbohydrate kashi (17.6%) – wanda ke ƙara kuzari.
    • Ash kashi (5.2%) – abin da ke nuna akwai minerals masu yawa a ciki.
    • Fiber (4.8%) – sai dai ba shi da yawa, amma yana da amfani wajen inganta narkewar abinci.
    • Threonine (7.6%) da Methionine (6.2%) – waɗanda suke daga cikin kyawawan nau’ikan amino acids da jiki ke bukata.
    • Amino acids a cikin ƙwallon ɗinya ya kai kusan kashi 37%, abin da ya sa ta zama tushen furotin mai kyau.
    • Phenolic compounds (170 mg/100g) – suna da ƙarfi wajen aikin antioxidant, suna kuma daƙile lalacewar ƙwayoyin halitta.
    • Alkaloids (11.4 mg/100g) – suna da amfani wajen maganin ciwo da kuma daƙile ƙwayoyin cuta.
    • Flavonoids (3.8 mg/100g) – suna taimakawa wajen rage haɗarin cutar daji da kuma kare jiki daga lalacewa sanadiyyar ‘free radicals’.

    Saboda waɗannan sinadarai, ɗinya na daga cikin itatuwan da ke haɗa abinci mai gina jiki da kuma sinadaran kariya ga lafiyar jiki.

    Muhimmancin tattalin arziki

    Ɗinya ba itaciya ce da ke bayar da abinci da magani ba kawai, har ila yau tana da muhimmanci sosai wajen tattalin arziki a al’ummomin Afirka.

    Kayan sayarwa

    ’Ya’yan ɗinya ana sayar da su a kasuwanni, musamman a lokacin damina da bazara, inda suke samun kasuwa sosai saboda ɗanɗanon su mai zaƙi. A wasu yankuna, ana busar da ’ya’yan domin ajiya da sayarwa a lokacin da ba a samun sabbin ’ya’yan. Wannan sana’a na taimakawa mata da matasa a ƙauyuka wajen samun kuɗaɗen shiga.

    Man ƙwallon ɗinya

    Ƙwallon ɗinya na ɗauke da mai mai yawa (kusai kashi 36%). Wannan mai yana iya amfani a matsayin man girki, idan aka tace shi yadda ya dace. Haka kuma masana’antu kan yi amfani da man wajen yin sabulai, man shafawa, da wasu kayan kwalliya. Idan aka ci gaba da tacewa da kasuwanci, man ƙwallon ɗinya zai iya maye gurbin man da ake shigo da shi daga ƙasashen waje.

    Magungunan gargajiya da na zamani

    Ganyen da ɓawon ɗinya suna da muhimmanci ga masu sayar da ganyayyaki da masu sana’ar gargajiya. A kasuwanni, ana samun su ana sayarwa a matsayin magunguna. Hakan na nuni da yiwuwar su zama tushen samar da magungunan zamani idan aka gudanar da bincike sosai.

    Itace da gawayi

    Itacen ɗinya yana da juriya sosai, yana da ƙarfi da ƙwari dalilin da yasa ake amfani da shi wajen gini da ƙera kayan aiki. Baya ga haka, yana samar da gawayi mai kyau, wanda ake amfani da shi a gida da kuma wajen kasuwanci.

    Gina arzikin karkara

    Ɗinya tana taka muhimmiyar rawa wajen inganta arzikin al’umma a yankunan karkara. Tana samar da abinci ga al’umma. Tana samar da abin kasuwanci ga mata da matasa. Har ila yau, tana taimakawa wajen samar da aikin yi ga masu noma, masu busarwa da masu sayarwa.

    Ƙalubale da matsaloli samuwar ɗinya

    Duk da muhimmancin ɗinya ga abinci, lafiya da tattalin arziki, akwai wasu matsaloli da ƙalubale da ke hana a ci gajiyar ta yadda ya kamata. Waɗannan ƙalubale sun haɗa da:

    Rashin noman zamani

    Yawancin bishiyoyin ɗinya suna fitowa ne a tsarin ɗabi’a (natural) a daji ba tare da an shuka ta tsarin noman zamani ba. Saboda haka, ’ya’yan ba su da yawa kamar yadda ake buƙata a kasuwanni. Rashin noman zamani ya rage yawan amfanin gonar da kuma yuwuwar kasuwanci mai faɗi.

    Sare bishiyoyin ɗinya

    A wasu yankuna, ana yawan sare itacen ɗinya don samar da gawayi ko kuma aikin gini. Wannan yana rage adadin bishiyoyin da ake da su, yana kuma haifar da haɗarin ɓacewar wannan muhimmin tsiro.

    Rashin wayar da kan jama’a

    Mutane da dama ba su san amfanin ƙwallon ɗinya ba. Yawanci bayan an cin sashen da ake iya ci, ƙwallon ana yarwa a matsayin shara. Wannan rashin sani ne ya hana a yi amfani da ƙwallon wajen samar da mai da kuma sinadarin furotin.

    Ƙarancin bincike

    Binciken kimiyya kan ɗinya bai yi yawa ba idan aka kwatanta da sauran ’ya’yan itatuwa na duniya. Rashin wadataccen bincike yana hana a gano sabbin hanyoyin amfani da ɗinya a masana’antu da fannin kiwon lafiya.

    Sauyin yanayi

    Sauyin yanayi da ƙarancin ruwan sama a wasu yankuna na iya yin tasiri kan yawan ’ya’yan ɗinyar da ake samu. Duk da cewa tana da juriya ga fari, matsanancin canjin yanayi zai iya rage yawan ‘ya’yan da ake samu.

    Inganta samarwa da sarrafawa

    Domin tabbatar da dorewar ɗinya da kuma inganta amfaninta ga al’umma, akwai buƙatar a ɗauki matakai na kiyayewa da kuma bunƙasa noman zamani.

    • Noman zamani: Akwai buƙatar a shigar da ɗinya cikin tsarin noma na zamani kamar yadda ake yi da mangwaro da kankana. Hakan zai tabbatar da samun ’ya’ya da yawa da kuma ingantattun tsaba.
    • Dasa sabbin tsirrai: Gwamnati da ƙungiyoyin al’umma za su iya ƙaddamar da shirin reforestation, inda za a dasa sabbin bishiyoyin ɗinya a dazuzzuka da kuma gonaki.
    • Hana sare bishiyoyi ba bisa tsari ba: Akwai buƙatar a samar da dokoki da za su taƙaita sare itatuwa ba bisa ka’ida ba, tare da wayar da kan jama’a kan illar wannan aiki ga muhalli.
    • Tace man ƙwallon ɗinya: A samar da ƙananan masana’antu na cikin gida da za su tace man ƙwallon ɗinya domin amfani a abinci da kuma masana’antu.
    • Magungunan zamani: Bincike kan sinadaran phytochemicals da ke cikin ɗinya zai iya kaiwa ga ƙirƙirar sabbin magunguna masu ƙarfi, musamman a fannin antioxidant, antibacterial da anticancer.
    • Kayan kwalliya da sabulai: Man da ake samu daga ƙwallon ɗinya har ila yau zai iya zama muhimmin sinadari wajen haɗa sabulan, man shafawa da sauran kayayyakin kwalliya.
    • Wayar da kan jama’a: A ƙarfafa ilimantar da jama’a kan amfanin ɗinya, musamman ƙwallonta, domin daƙile zubar da shi a matsayin shara. Wannan zai ƙara buƙata da kuma darajar kasuwancin abubuwan da ake samarwa daga ƙwallon.
    • Bincike da haɓakawa: A ƙara gudanar da bincike na kimiyya kan ɗinya a fannoni daban-daban, ciki har da abinci, magani da kuma amfanin masana’antu. Jami’o’i da cibiyoyin bincike su haɗa kai da manoma wajen ƙirƙirar sabbin irin noma, yadda ake sarrafawa da kiyayewa.

    Ɗinya na ɗaya daga cikin manyan itatuwan ‘yan asalin Afirka da suka daɗe suna taka muhimmiyar rawa wajen inganta rayuwar al’umma. Ɗinya itaciya ce mai yalwar amfani ta fuskar abinci, magani da kuma tattalin arziki. ’Ya’yan ɗinya suna da ɗanɗano mai zaƙi kuma suna cike da bitamin, minerals da fiber. Ganyayyakinta da ɓawonta kuma suna da amfani a fannin magungunan gargajiya, musamman wajen magance zazzaɓin cizon sauro, gudawa da matsalolin hanta.

    Sabbin bincike sun kuma nuna cewa, ƙwallon ɗinya wadda ake watsi da shi a baya, na ɗauke da yalwar kitse, furotin da sinadaran phytochemicals masu ƙarfi. Wannan ya tabbatar da yiwuwar amfani da ƙwallon ɗinya wajen samar da abinci, magani, abubuwa sarrafawa a masana’antu kamar sabulai da man shafawa, da kuma sinadaran da za su iya taka rawa a wajen haɗa magungunan zamani.

    Duk da wannan muhimmanci, akwai ƙalubale irin su rashin noman zamani, yawan sare itatuwa, ƙarancin bincike da rashin wayar da kan jama’a kan amfanin ɗinya. Saboda haka, akwai buƙatar a ɗauki matakan kiyayewa da bunƙasa noman ɗinya, tare da ƙara bincike kan amfaninta. Idan aka inganta amfani da ɗinya da hanyoyin sarrafa abubuwan da ake samu daga gare ta, ba kawai za ta ci gaba da kasancewa abinci da magani ga al’umma ba, har ila yau za ta kasance muhimmin ginshiƙi wajen ƙarfafa tattalin arzikin karkara da samar da aikin yi.

    Manazarta

    Irampagarikiye, R., Diouara, A. A. M., Thiam, F., Nguer, C. M., et al. (2025). Vitex doniana Sweet, applications and therapeutic potential: A scoping review. Discover Applied Sciences, 7, 139.

    Wikiwand. (n.d.). Ɗinya.

    Alummar Hausa. (2019, August). Afanin ɗinya baka. 

    *** Tarihin Wallafa Maƙalar ***

    An kuma sabunta ta 18 September, 2025

    *** Sharuɗɗan Editoci ***

    Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.

    Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.

    Maƙalar ta amfanar?
    EAa

    You cannot copy content of this page

    ×