Skip to content

Diphtheria

    Aika

    Diphtheria cuta ce mai saurin yaɗuwa wadda ake iya riga-kafinta, wadda bakteriya mai suna Corynebacterium diphtheriae ke haddasawa. Cutar na iya hallaka kashi 5 zuwa 10 cikin 100 na waɗanda suka kamu, kuma ƙananan yara na cikin haɗari sosai. Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta tabbatar da cewa barazanar cutar a Najeriya na da yawa a matakin ƙasa, amma akwai ƙarancin haɗari a matakin yanki na duniya.

    Diphtheria cuta ce mai saurin yaɗuwa da bakteriya masu haifar da guba ke haddasawa. Ana iya kamuwa da ita ta hanyar shaƙar tiririn atishawa ko tari daga wanda ke ɗauke da cutar. Wasu mutanen ba sa nuna alamomin cutar amma za su iya yaɗa ta. Wasu sukan sami ƙananan alamomi ne, yayin da wasu kuma za su iya fuskantar mummunar matakim cutar, rikice-rikicen lafiya da ma mutuwa.

    Kowa zai iya kamuwa da diphtheria, amma cutar ta fi yawaita a cikin yaran da ba a yi wa riga-kafi ba. Cutar diphtheria na haifar da lalacewar hanyoyin numfashi kuma tana iya bazuwa a cikin jiki gabaɗaya. Manyan alamominta sun haɗa da zazzabi, ciwon maƙogwaro da kumburin gaɓar wuya.

    diphtheria0
    Cutar diphtheria ta fi kama ƙananan yara kuma ta fi yi musu illa.

    Hanyar kariya mafi kyau ita ce yin riga-kafi. Riga-kafin yana da aminci kuma yana taimaka wa jiki ya yaƙi cutar. Kafin samuwar riga-kafin diphtheria da yawaitar yin riga-kafin a shekarun 1930, ana samun cutar a ko’ina a duniya. A cikin shekarun nan, yawaitar cutar na ƙaruwa saboda ƙarancin riga-kafi, duk da cewa riga-kafin yana nan kuma yana da inganci.

    Tasirin annobar COVID-19

    Annobar COVID-19 ta shafi samar da riga-kafin yara da kuma ayyukan lura da cutuka. Waɗannan matsaloli sun sa yara da dama suka zama masu raunin kariya daga cutukan da riga-kafi ke hana yaɗuwar su, ciki har da diphtheria.

    Babu wani yanki na duniya da ya tsira gabaɗaya daga cutar diphtheria, kuma wuraren da ba su da isasshen riga-kafi na barin cutar ta bazu, wanda hakan ke ƙara yawan yaɗuwa da haifar da haɗari ga duk wanda bai  sami cikakken riga-kafi ba.

    Dole ne a ƙarfafa shirin riga-kafi da lura da cutuka a matakin lafiya na farko, kuma a tabbatar an kai riga-kafi ga dukkan yara a lokacin jarirantaka, yarintaka da balaga. Yana da kyau kuma ƙasashe su kafa ƙaƙƙarfan tsarin kula da cutuka don gano su da gaggawa da ɗaukar matakan kariya.

    Alamomi gane cutar diphtheria

    Alamomin diphtheria na bayyana cikin kwanaki 2 zuwa 5 bayan kamuwa da ƙwayar bakteriyar. Alamomin sun haɗa da ciwon maƙogwaro, zazzaɓi, kumburin gaɓar wuya da jin kasala. Cikin kwana 2 zuwa 3 bayan kamuwa, ƙwayar cutar na haddasa samuwar wani tantani mai launin toka a hanyar numfashi wanda ke rufe hanci, tonsils da maƙogwaro, yana hana numfashi da haɗiya abinci.

    Mafi yawan munanan rikice-rikice da mutuwa daga cutar diphtheria na faruwa ne saboda gubar da take haifarwa. Matsalolin da ka iya tasowa sun haɗa da kumburin zuciya da jijiyoyi. Idan ba a yi wa wanda ba shi da riga-kafi magani da wuri ba, kusan 30% na masu cutar na mutuwa, kuma yara ƙasa da shekara 5 na cikin haɗari sosai.

    Waɗanda ke cikin haɗarin kamuwa

    Duk wanda ba shi da cikakken riga-kafi yana cikin haɗarin kamuwa da cutar.

    Diphtheria na dawowa a duk lokacin da riga-kafin ya ragu. Lalacewar tsarin kula da lafiya a ƙasashe da ke fama da rikici ko bala’i kamar girgizar ƙasa kan hana ci gaba da riga-kafin. Cunkoso a sansanonin ‘yan gudun hijira na ƙara haɗarin yaɗuwar cutar.

    Maganin cutar diphtheria

    Tarar cutar da magani da wuri na rage haɗarin rikice-rikicen lafiya ko mutuwa. Saboda haka, idan an yi zargin kamuwa da cutar diphtheria, ya kamata a yi gwaji nan da nan kuma a fara magani da wuri-wuri.

    Ana warkar da diphtheria da maganin antitoxin da kuma antibiotics. Antitoxin na kashe gubar da ke cikin jini, yayin da antibiotics ke hana yawaitar ƙwayoyin bakteriya, rage yawan gubar da ke samuwa, da hana bazuwar cutar ga wasu. Sai dai, yawancin ƙwayoyin cutar a yanzu suna nuna juriya da bijirewa ga wasu daga cikin magungunan antimicrobial na yau da kullum. Duk wanda ya kamu da cutar ya kamata a yi masa riga-kafi bayan cutar ta wuce.

    Dukkan waɗanda suka yi mu’amala da masu cutar diphtheria ya kamata a ba su antibiotics a matsayin kariya. Ya kamata a duba matsayin riga-kafinsu, idan ba su da cikakken riga-kafi a ba su.

    Riga-kafin cutar diphtheria

    Ana iya daƙile cutar diphtheria ta hanyar riga-kafin da ake haɗawa da na tetanus, pertussis da sauran cutuka. WHO na ba da shawarar cewa a yi riga-kafi har sau 6 tun daga makonni 6 na haihuwa har zuwa lokacin balaga domin samun kariya mai ɗorewa.

    Yin riga-kafi ga al’umma gaba ɗaya tare da wadatar masu riga-kafi a matsayin ɓangare na shirin lafiya a matakin farko ita ce hanya mafi inganci ta kawar da cutar. Duk yara su sami riga-kafi na farko da kuma ƙarin allurai 3 don kariya ta dogon lokaci. Riga-kafin lafiyayye ne kuma yana da inganci. An fi bayar da riga-kafin diphtheria tare da na wasu cutukan irin su tetanus, pertussis, Hemophilus influenzae, hepatitis B da poliomyelitis.

    A shekarar 2023, kashi 84% na yara sun karɓi dukkan allurai 3 na riga-kafinsu farko. Sai dai akwai bambanci mai yawa a cikin ƙasashe da ma tsakanin yankuna. Raguwar yin rigakafi a tsakanin ƙananun yara na iya haifar da sabbin rahotannin bullar cutar diphtheria.

    Tarihin ɓullar cutar diphtheria a Najeriya

    Najeriya ta fuskantar bullar cutar a shekarar 2011 da kuma 2022. A shekarar 2023, daga Janairu zuwa Afrilu, bullar cutar ta shafi jihohi 21 da Babban Birnin Tarayya (FCT).

    Tun daga mako na 26 na kididdigar cututtuka (wanda ya ƙare a ranar 2 ga Yuli, 2023), Najeriya ta fara fuskantar ƙaruwar da ba ta saba gani ba na bullar cutar diphtheria a jihohi da dama. Daga 30 ga Yuni zuwa 31 ga Agusta, 2023, an samu jimillar 5898 da ake zargin sun kamu da cutar a cikin ƙananan hukumomi 59 da ke cikin jihohi 11. A mako na 34 (wanda ya ƙare 27 ga Agusta), an samu rahoton mutane 234 da ake zargi daga ƙananan hukumomi 20 a cikin jihohi 5. An tabbatar da guda ɗaya ta hanyar dakin gwaje-gwaje daga samfurori 22 da aka tattara. Guda 18 daga cikin waɗannan an danganta su ta fuskar hanyar yaɗuwa (epidemiologically linked), yayin da guda 141 suka dace da alamomin likitanci (clinically compatible).

    Daga 30 ga Yuni zuwa 31 ga Agusta, 2023, an sami ƙaruwar da ba a saba gani ba na yawan adadin da ake zargin sun kamu. A wancan lokacin, an sami rahoton mutane 5898 da ake zargi da cutar a ƙananan hukumomi 59 da ke jihohi 11. Mafi yawan waɗanda ake zargi sun fito daga:

    • Kano: 1816
    • Katsina: 234
    • Yobe: 158
    • Bauchi: 79
    • Kaduna: 45
    • Borno: 33

    Adadin waɗanda aka tabbatar sun kamu

    • Daga cikin jimillar 8353 da aka yi zargin sun kamu tun bayan bullar cutar a shekarar 2022 akwai mutane 4717, kwatankwacin kashi (56.5%) da aka tabbatar da sun kamu da cutar.
    • Adadin mace-mace ya ragu daga 6.7% zuwa 6.1%. Daga cikin 4717 da aka tabbatar, 3466 (73.5%) yara ne ‘yan shekaru 1 zuwa 14. Fiye da rabin waɗanda suka kamu mata ne (2656; 56.3%).

    Ƙoƙarin Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO)

    Shirin riga-kafi na duniya ya fara a shekarar 1974. Riga-kafin da ke yaƙar diphtheria an haɗa shi da wannan shiri tun daga farko, kuma tsakanin 1980 zuwa 2000, riga-kafin ya daƙile fiye da kaso 90% na yaɗuwar cutar.

    A cikin shekarun baya-bayan nan, ana fuskantar bullar diphtheria sakamakon ƙarancin riga-kafi. Don shawo kan hakan, WHO na aiki da ƙasashe membobinta wajen daƙile bullar cutar da kuma ƙarfafa shirin riga-kafi na yau da kullum don hana kamuwa da cutar diphtheria mai kaiwa ga mutuwa.

    Shawarwarin hukumar lafiya WHO

    • A tabbatar da an yi riga-kafi mai yawa don gina garkuwar al’umma.
    • A riƙa bin diddigin waɗanda suka yi mu’amala da masu cutar da kuma ba su magani nan da nan.
    • A yawaita ɗakunan gwaje-gwaje don gano ƙwayar cutar cikin hanzari.
    • A samar da wadataccen maganin DAT a kowace ƙasa ko yanki domin saurin bayarwa ga marasa lafiya.
    • A riƙa ware masu alamomin cutar daga sauran marasa lafiya a asibitoci.
    • A riƙa kula da tsafta da nisantar juna a cibiyoyin kiwon lafiya.
    • A ba da riga-kafi ga duk wanda ke cikin haɗarin kamuwa kamar yara ‘yan ƙasa da shekara 5, malaman makaranta, ma’aikatan kiwon lafiya da masu kula da masu cuta.
    • A ba da antibiotics na kariya (penicillin ko erythromycin) ga masu kula da masu cuta har tsawon kwanaki 7.
    • A ƙara wayar da kai ga matafiya da za su je wuraren da ake da rahoton ɓullar cutar cewa su tabbatar da an yi musu riga-kafi kafin tafiya.

    Muhimman bayanai a takaice

    • Diphtheria cuta ce da ƙwayar bacteria ke haifarwa wadda ke shafar manyan sassan numfashi, kuma a wasu lokuta ƙananan sassa na fata. Cutar na haifar da guba (toxin) da ke iya lalata zuciya da jijiyoyin jiki.
    • Diphtheria cuta ce da riga-kafi ke hana yaɗuwar ta, sai dai ana buƙatar riga-kafi mai yawa da kuma ƙarin alluran (booster doses) don ƙarfafa garkuwar jiki.
    • Mutanen da ba su sami riga-kafi ba ko waɗanda riga-kafinsu bai cika ba suna cikin haɗarin kamuwa da cutar.
    • Ga waɗanda ba su da riga-kafin kuma ba su sami kulawa ta gaggawa ba, diphtheria na iya hallaka kusan 30% na waɗanda suka kamu da ita, musamman ƙananan yara da ke cikin haɗari sosai.
    • Ƙaruwar yaɗuwar cutar diphtheria a ‘yan shekarun nan na ƙara jaddada muhimmancin tabbatar da cewa an ci gaba da yi wa al’umma riga-kafi da yawa a duk matakan rayuwa.
    • A shekarar 2023, kimanin kashi 84% na yara a duniya sun karɓi allurai 3 na riga-kafin diphtheria a lokacin jarirantaka, yayin da kashi 16% ba su karɓi cikakken riga-kafin ba. Bambance-bambancen adadin riga-kafin ya sha bamban a ƙasashe da ma cikin ƙasa guda.

    Manazarta

    Dateline Health Africa. (2025, March 3). Diphtheria cases rise in Nigeria as Lagos becomes worst-hit state. Dateline Health Africa.

    Infectious Diseases – Emerging Africa (ID-EA). (2024, December 30). Diphtheria’s global resurgence – A preventable crisis demanding renewed and continuous vigilance. Infectious Diseases – Emerging Africa.

    Nigeria Centre for Disease Control (NCDC). (2025). Diphtheria situation report: Week 4, 2025. NCDC

    World Health Organization (WHO). (2025, July 15). Global childhood vaccination coverage holds steady, yet over 14 million infants remain unvaccinated.  WHO

    *** Tarihin Wallafa Maƙalar ***

    An kuma sabunta ta 25 July, 2025

    *** Sharuɗɗan Editoci ***

    Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.

    Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.

    Maƙalar ta amfanar?
    EAa

    You cannot copy content of this page

    ×