Skip to content

Fabrois

Fibrois wata tsoka ce da ke fito wa mace kan mahaifarta. Wani ƙiyasi ya nuna cewa, kaso 70 zuwa 80 na mata za su kamu da fibroids a rayuwarsu. Amma duk da haka ba kowa ba ne zai bayyana alamomin cutar ta ba ko kuma ya buƙaci kulawar likitoci.

Abu mafi muhimmanci game da Fibroid shi ne kusan yawanci benign ne (non-cancerous) Wasu fibroids ɗin suna farawa ne daga ciwon kansa, amma benign fibroids ba sa taɓa zama cancer.

Ba a fiye samun cancerous fibroid ba, saboda haka, zai fi ga matan da ba sa bayyana alamomin da su fi mayar da hankali a kan kulawa maimakon yin magani.

Fibroid cuta ce dake jikin mahaifa.

Bincike ya nuna Fibroids tana ƙara girma da kaɗan-kaɗan. Wasu za su fara daga girman kamar gyaɗa zuwa girman ƙanƙana. Hakan bai fiye faruwa ba. Ko da ta yi girman haka, akwai maganin da ake ba mace domin samun sauƙi da rage raɗaɗi.

Ire-iren fibroids.

Fibroids un rabu kashi-kashi kuma sunansu ya danganta da inda suka fitowa uterus.

1- Intramural Fibroid: Wannan ita ce wadda aka fi sani. Tana fitowa a kan muscular wall na uterus.

2- Subserosal Fibroid: Wannan na fitowa daga wajen mahaifa, kuma tana ƙara girma sosai yadda za a ga ta ƙara wa mahaifar girma sosai.

3- Submucosal Fibroids: Wannan tana fitowa cikin Uterine Cavity (wato sararin da ke cikin mahaifa).

4- Pedunculated Fibroid: Wannan kuma a manne take da Uterine wall.

Alamomin fibroids

Yawancin matan da ke da fibroid ba sa fuskantar wasu alamomi, amma ga waɗanda suke fuskanta:

1- Zubar jini mai yawa lokacin al’ada.

2- Lokacin al’ada ya wuce sati ɗaya

3- Raɗaɗin pelvic

4- Yawan fitsari.

5- Constipation.

6- Ciwon baya ko ƙafufu.

7- Jin zafi lokacin jima’i

8- Rashin samun juna-biyu.

Abubuwan da ke haifar da fibroids

Har yanzu babu tabbas a kan abin da yake kawo tsirowar fibroids. Wataƙila ya danganta da matakin Estrogen na mata. Estrogen sex hormone ne. Shi yake da haƙƙin wajen girman: nono, ƙugu, jinin al’ada, fata, fitowar gashi ga mata, da sauran su. Ga maza kuma, girman gaɓɓai, lafiyar ƙashi, da emotions.

Ana ganin Fibroid na samuwa ne ta dalilin matakin estrogen. Lokacin da mace take matashiya, matakin estrogen da progesterone (shi ma wannan hormone ne.)

Duk da haka bayan wannan, akwai genetic factors. Da yawan fibroids suna ɗauke da abubuwan da suke iya canza genes ɗin mahaifa.

Mutanen da ake tunanin za su fi saurin kamuwa da fibroids

1- Hereditary: idan uwa ko ‘yar uwar mace tana ko ta taɓa kamuwa da fibroids, ana kyautata zaton ita ma za ta iya kamuwa da ita. Hakan ba ya nufin tabbas za ta kamu da ita.

2- Launin fata: baƙaƙen fata sun fi saurin kamuwa da Fibroids.

3- Obesity (kiba): mace mai ƙiba sai ta fi mara ƙiba saurin kamuwa.

4- Nau’in cima: Yawan cin jan nama da rashin cin isassun ganyayyaki kan iya haifar da fibroids cikin sauri.

Hanyar magance fibroids

Hanyoyin magance fibroids sun danganta da girma da kuma inda fibroid ɗin take da alamominta, sannan ana duba idan mace tana da niyyar sake haihuwa ko ba ta da niyya.

1. Amfani da magunguna

Gonadotropin-releasing hormone (GnRH): wannan maganin yana sa fibroid ta yamushe sakamakon yana sa matakin estrogen ya yi ƙasa.

Progestin-releasing intrauterine device (IUD): yana rage zubar jini, amma ba ya ragewa fibroids girma.

Bayan waɗannan, ana amfani da birth control pills domin rage wasu alamomin, kamar zubar jin da raɗaɗi.

Akwai hanyoyi nonsurgical da ake bi wajen maganin fibroids su ne

Uterine Artery Embolization: ana rufe hanyoyin da fibroids suke samun jini (abincinsa), saboda haka zai fara loƙumewa.

MRI-guided focused ultrasoumd surgery: Ana amfani da high frequency na sound waves domin a ragargaza fibroid.

Hanyoyin surgical

Myomectomy: Ana yanke Fibroid a bar uterus. Ana yin wannan surgery ɗin ne idan mace tana son ta ƙara haihuwa.

Hysterectomy: Ana cire uterus ɗin gabaɗaya. Wannan ita ce hanyar da aka tabbatar fibroid ba za ta taɓa dawowa ba.

Wani lokacin mutum tsarin rayuwa da cimaka kawai zai canza domin samun sauƙi ko kuma kariya. Misali, mace ta dinga yawan motsa jiki. Motsa jiki yana rage ƙiba sannan yana sa estrogen ya yi ƙasa. Ko mace ta dinga yawan cin kayan marmari da kuma kayan da ba sa kara ƙiba sosai. Idan mace ta rage damuwa, wannan ma hanya ce ta guje wa cutar da kuma maganinta. Saboda fibroids yakan iya haifar da yawan zubar jini, matsaloli dangane da juna biyu, da kuma rashin haihuwa gabaɗaya.

Manazarta

Allan Warshowsky. (2002). Healing Fibroids: A Doctor’s Guide to a Natural Cure. Simon & Schuster

Johanna Skilling. (2002). Fibroids: The Complete Guide to Taking Charge of Your Physical, Emotional, and Sexual Well-Being. Penguin Books.

Lloyd B. Greig. (2008) 100 Questions & Answers About Uterine Fibroids. Jones & Bartlett Learning.

M. Sara Rosenthal. (2001) Uterine Fibroids: The Complete Guide. Avery.

Was this article helpful?
YesNo

You cannot copy content of this page

×