Skip to content

Fas (fax)

Na’urar fax wata na’ura ce da ke ba da damar aika takardu ta amfani da layukan waya. Wannan ita ce hanya ta farko ta aika sakonnin takardu kafin zuwan intanit kuma har yanzu ana amfani da ita sosai a harkokin kasuwanci da yawa a yau. Na’urar fax ta ƙunshi haɗin layin tarho, tiren takarda, na’urar daukar hoton takardu ko wasu hanyoyin shigar da takardu, da faifan fitarwa don tattara takardun da aka aiko. Mai aikawa zai shigar da bayanansa cikin na’urar, ya ɗauki hoton bayanin ko kuma ya shigar da takardar da yake son aikawa, ya buga lambar mai karɓa sannan ya danna “Aikawa”.

Ana amfani da na’urar fax sau da yawa wajen watsa bayanan sirri saboda suna ba da ingantacciyar hanya fiye da imel ko wasu hanyoyin dijital.

Ire-iren na’urar fax

Kamar yadda fasaha ta ci gaba, haka ma na’urar fax, kuma a yanzu akwai nau’ikan na’urorin fax iri-iri da ake samu a kasuwa. Amma yana da mahimmanci a yi la’akari da yanayin muhalli na waɗannan nau’ikan na’urorin fax daban-daban don sayen wanda ya fi dacewa da buƙatun mai saye.

Thermal fax

Wannan nau’in yana amfani da zafi don canja wurin hoton zuwa ga sashen na’urar da ke karɓar bayanai. Na’urorin fax na thermal gabaɗaya sun fi sauran nau’ikan ƙarfi, amma kuma suna amfani da ƙarin wasu na’urorin don samar da bayanan fax ɗin. Bugu da ƙari, suna haifar da zafi mai yawa kuma suna iya haifar da gurɓataccen yanayi.

Inkjet fax

Wannan nau’in yana amfani da tawada don canja wurin hoton zuwa ga sashen karɓar bayanai. Duk da yake waɗannan na’urori gabaɗaya sun fi araha fiye da na’urorin fax na thermal, su ma ba su da inganci kuma suna buƙatar ƙarin wasu na’urorin don samar da bayanan fax. Sannan tawadar da ake amfani da su a cikin waɗannan na’ura na iya gurɓata iska.

Laser fax

Wannan nau’in yana amfani da Laser don canja wurin hoton zuwa ga ɓangaren da ke karɓar bayanai. Na’urorin Laser fax gabaɗaya su ne nau’in fax mafi inganci kuma suna buƙatar mafi ƙarancin ƙarin na’urori don samar da bayanan fax. Duk da haka, suna iya haifar da zafi mai yawa, wanda zai iya gurɓata muhalli.

Ana yawan amfani da na’urorin fax lokacin ƙaddamar da muhimman takardu ga hukumomin gwamnati. Misali, IRS na buƙatar ‘yan kasuwa su aika da bayanan harajinsu ta amfani da na’urar fax.

Yayin da ake la’akari da tasirin muhalli ga na’urorin fax, yana da muhimmanci a lura da makamashi da sauran na’urori ko sinadarai da ake bukata don samar da fax, da kuma yuwuwar gurɓata iska da na’urorin kan haifar. Yana da mahimmanci a bincika nau’ikan na’urorin fax ɗin da ake da su kuma a zaɓi mafi kyau.

Amfanin na’urar fax

Na’urar fax ta kasance wani ɓangare na cigaba da ya wanzu a ofisoshi tun shekaru masu yawa, amma lokacin da fasahar sadarwa ta hanyar dijital ta bayyana, sai na’urar fax take neman ɓacewa. Na’urar dai tana taimakawa wajen aiwatar da ɗimbin ayyukan ofis da duka haɗa da:

1. Aikawa da karɓar takardu

Daya daga cikin muhimman alfanun na’urar fax a wuraren aiki da ofisoshi na zamani shi ne aikawa da karɓar fayil-fayil. Wannan na da tasiri ga takardun da aka rattaba hannu ko waɗanda ke buƙatar a rattaba hannu na zahiri a kansu. Yayin da sa hannu ta hanyar amfani da na’ura yake samun karɓuwa a tsarin dokar wasu ƙasashe da masana’antu, har yanzu akwai wasu wuraren da ake buƙatar sa hannu na zahiri.

A yayin da harkar kasuwanci ke buƙatar samun kwangilar da aka sanya hannu ko yarjejeniya daga abokin ciniki ko mai sayarwa, yana iya zama ƙalubale wajen yin hakan ta hanyar dijital. A irin wannan lokaci, na’urar fax na iya yin amfani don aikawa da daftarin da sauri da karɓar kwafin da aka sa hannu a mayar da shi. Wannan na da amfani saboda takardar fax ɗin ana adana ta a hukuma ce kuma ana iya amfani da ita a matsayin shaidar doka.

2. Isar da bayanai a sirrance

Ana amfani da na’urar fax sau da yawa wajen watsa bayanan sirri saboda suna ba da ingantacciyar hanya fiye da imel ko wasu hanyoyin dijital. Lokacin da aka aika da takarda ta hanyar fax, ana watsa ta ta layin waya a matsayin analog maimakon ta intanet. Wannan yana sa bayanin ya zama mai wahalar samu ga masu kutse. Hakazalika, wannan na’ura musamman na zamani suna da siffofi da ɓangarorin inganta tsaron bayanai.

Waɗannan ɓangarori suna tabbatar da cewa mutane masu izini ne kawai za su iya karɓar takarda. Har ila yau na’urorin fax sun zama gama gari a fannin kiwon lafiya da na shari’a, inda ake keɓancewa da tsare bayanai masu matukar muhimmanci. Haka nan, wasu hukumomin gwamnati da hukumomin gudanarwa na iya buƙatar wasu bayanai da za a watsa ta hanyar fax don tsaro ko dalilai na doka.

3. Aiwatar da cinikayya

‘Yan kasuwa sukan yi amfani da fax don tabbatar da odar kaya, isarwa, da sauran cinikayya tsakanin abokan hulɗa ko abokan ciniki. Lokacin da ɗan kasuwa ya sayi wani abu daga mai sayarwa ko kamfani, yana iya aika odar sayayyar ta fax don tabbatar da cikakkun bayanai. Bayan haka mai sayarwar ya sake duba odar, sannan ya aika fax ɗin baya da tabbacin sayarwa, tare da nuna cewa ya karɓa kuma ya sarrafa shi.

Yin amfani da na’urorin fax don tabbatar da cinikayya na iya taimakawa wajen rage kurakurai da rashin fahimta tsakanin ‘yan kasuwa ko masu saye da sayarwa. Haka nan yana ba da cikakken bayanan cinikayya.

4. Raba manyan fayil-fayil

Ana iya amfani da naurar fax don rabawa ko tura manyan fayil-fayil lokacin da imel ko wasu hanyoyin dijital suka gaza. An tsara na’urorin don aika fayil-fayil ta hanyar layin tarho, don haka za su iya sarrafa manyan fayil-fayil ba tare da buƙatar ayyukan raba fayil na yanar gizo ba. Wannan na’ura ta fax, tare take da na’urar daukar hoto a jikinta don aika babban fayil.

Yan kasuwa sukan yi amfani da fax don tabbatar da odar kaya, isarwa, da sauran cinikayya tsakanin abokan hulɗa ko abokan ciniki.

Da farko ana bincika fayil ɗin da za a aika, sai a canja shi azaman hoto (kamar TIFF ko PDF). Bayan haka, za a iya amfani da na’urar fax ɗin don buga lambar fax ɗin mai karɓa da aika fayil ɗin. Amma akwai iyakoki da sharuɗa. Saurin tafiyar fayil ɗin na iya zama marar sauri idan aka kwatanta da hanyoyin dijital, musamman manyan fayil-fayil. Kuma ingancin hoton zai iya zama marar gamsarwa idan na’urar fax ɗin tana da ƙaramar ƙwaƙwalwa ko karancin tawada ko mara kyau.

5. Sadarwa tare da abokan ciniki

Ga abokan ciniki da abokan haɗin gwiwa ba tare da samun damar yin amfani da intanet ba ko kuma ba masu magana da kayan aikin dijital ba, amfani da na’urorin fax yana tabbatar da cewa mahimman bayanai sun isa ga duk wanda ke da ruwa da tsaki a cikin cinikayya. Wannan yana da mahimmanci yayin gudanar da takardun doka, kwangila, ko wasu takardu. Na’urorin fax sun fi zama abin dogaro fiye da hanyoyin dijital a wasu fannoni.

Saƙonnin imel na iya ɓacewa a cikin spam ko kuma a goge su da gangan, yayin da na’urorin fax ke aika daftarin aiki kai tsaye zuwa ga mai karɓa. Yin amfani da na’urar fax na iya taimaka wajen ɗan kasuwa fita daga cikin waɗanda suka dogara kawai a kan hanyoyin sadarwa na dijital. Ɗan kasuwa na iya saduwa da abokin ciniki na musamman ta hanyoyin sadarwa da yawa.

6. Sadarwa a hukumomin gwamnati

Ana yawan amfani da na’urorin fax lokacin ƙaddamar da muhimman takardu ga hukumomin gwamnati. Misali, IRS na buƙatar ‘yan kasuwa su aika da bayanan harajinsu ta amfani da na’urar fax. Haka nan ya shafi lokacin shigar da takarda tare da wasu hukumomin gwamnati. Baya ga samar da hanyar takarda, aika fax ɗin zuwa hukumomin gwamnati na iya taimakawa wajen tabbatar da cewa an karɓi waɗannan takardun a kan lokaci.

Yawancin hukumomin gwamnati suna da ƙayyadaddun lokuta don ƙaddamar da takarda, kuma wannan hanya ta fax na iya zama amintacciyar hanya don tabbatar da aiki a kan lokaci.

7. Ajiye fayil-fayil

‘Yan kasuwa na iya amfani da na’urorin fax yayin da network ya gurɓace don aikawa da karɓar muhimman takardu ba tare da katsewa ko jinkiri ba. Wannan yana da mahimmanci ga ƙwararru kamar ma’aikatan lafiya ko masu aikin gaggawa.

Idan akwai katsewar wutar lantarki, na’urorin fax na iya aiki idan an haɗa su da janareta ko wata na’urar adana makamashin lantarki. Bugu da ƙari, wasu ‘yan kasuwar na iya ajiye keɓaɓɓiyar na’urar fax a matsayin wajen ajiya don amfanin gaggawa. Wannan yana ba su damar ci gaba da aikawa da karɓar takardu masu mahimmanci, koda kuwa hanyoyin sadarwar dijital ba sa samuwa.

Tasirin fax a yau

Na’urar fax ta kasance muhimmiyar fasaha a yau. Ta hanyar amfani da eFax Mobile App, ɗaya daga cikin mafi kyawun manhajojin fax. Za a iya aika sakonnin fax da yawa ga mutane da yawa a cikin daƙiƙa guda. Sakonnin fax suna wanzuwa kamar fax na zahiri, kuma ana iya bin kowane mataki na tsarin watsawa, da suka haɗa da lokaci da kwanan watan kammalawa.

Samar da na’urar fax ta zamani ya taimaki mutane masu aiki da masu kasuwanci sauya yadda sukke aikawa, karɓa har ma da karanta bayanan fax. A yau, za a iya aika fax cikin sauƙi kamar yadda ake iya aika imel ta hanyar amfani da fax na cikin wayoyin hannu mai amfani da fasahar yanar gizo, kuma ya zama mafi kyawun na’urar fax.

Yadda na’urar fax ke aiki

Na’urorin fax na gargajiya suna aika kwafin hoto ko bayani yadda ya kamata a cikin wayoyi na tarho. A babban matakin, na’urar fax tana aiki cikin matakai uku:

  • Duba daftarin aiki (document)
  • Aika saƙonni zuwa wata na’urar fax ɗin
  • Fax yana buga daftarin aiki (document)

Na’urar zamani ta fax na iya amfani da modem maimakon layin waya don aika fax ta intanet. Wannan yavyi kama da yadda Voice over Internet Protocol (VoIP) ke ba da damar yin kiran waya na gargajiya ko wasu aikace-aikacen yanar gizo kamar WhatsApp ko Facebook Messenger.

Manazarta

Tutor, C. (2023, November 4). ICT devices – Uses of fax machines – ClassNotes.ng.

Tagonline. (2024, August 13). What are the different types of fax machines available in the market? Electronic Office Systems.

Was this article helpful?
YesNo

You cannot copy content of this page

×