Skip to content

Fasahar 6G

  • Wallafawa:
  • Rukuni: Fasaha
Aika |

Fasahar sadarwar 6G, ko Sixth-Generation Network a turance, ita ce fasahar sadarwa ta nan gaba da ake sa ran za ta gaji 5G a ƙarshen shekarun 2030. Ana kallon wannan fasaha a matsayin tsarin sadarwa mai matuƙar sauri, ƙarancin jinkiri, da babban ƙarfin haɗa na’urori fiye da duk wani salo da ya gabata. Babban manufar 6G shi ne haɗa intanet da fasahohi irin su Artificial Intelligence, sarrafa bayanai, tauraron ɗan Adam, da quantum communication domin samar da sadarwa mai kama da tunani; wato tsarin da ke fahimta, nazari, da biyan buƙata cikin gaggawa. Saboda haka, 6G ba kawai sabuwar fasahar intanet ba ce, ta haɗa da wata sabuwar mahangar sadarwa da za ta haɗa mutane, injuna, bayanai, da muhallin rayuwa cikin tsari guda.

Screenshot 20251123 1428492
Fasahar 6G ita ce fashar d ake sa ran za ta maye gurbin 5G a karshen shekarar 2030.

Dalilin samar da sabon tsarin sadarwa

Ƙaruwar yawan amfani da intanet a duniya, haɓakar na’urori masu fasahar intanet, da yawaitar manyan bayanai sun nuna cewa fasahar 5G ba za ta iya ɗaukar dukkan buƙatun nan gaba ba. Ana sa ran nan da ɗan lokaci, biliyoyin injuna za su rika hulɗa da juna ba tare da hannun mutane ba. Motoci masu tuƙi da kansu, masana’antu masu sarrafa kansu, asibitoci na dijital, da birane masu tunani (smart cities). Irin wannan tsarin yana bukatar intanet mai saurin gaske, ingantaccen tsaro, da ƙarancin jinkiri wanda fasahar 6G kaɗai ce za ta iya bayarwa. Haka kuma, sabbin fasahohi irin su hologram communication, real-time robotics gabaɗaya suna buƙatar hanyar sadarwa da ke iya aiki kamar ƙwaƙwalwa; mai nazari, saurin yanke hukunci, da cikakken daidaito. Don haka, 6G ta taso ne domin cike giɓin da ke tsakanin fasahar yau da buƙatun gobe.

Tarihin kafuwar fasahar 6G

Daga 1G zuwa 5G

Cigaban 6G ya samo asali ne daga dogon tarihin sabbin fasahohin sadarwa da aka gina a baya. Fasahar 1G a shekarun 1980 ita ce ta fara ba da damar kiran waya ba tare da igiya ba (wireless), duk da cewa ingancinta ƙalilan ne. 2G ta kawo rubutattun saƙonni, tsaro, da ingancin murya. Zuwan 3G, intanet ya samu gurbi a wayoyin hannu, wanda ya fara sauya yadda mutane ke amfani da fasaha. Fasahar 4G ta buɗe babbar kofa ga bidiyo, kafofin sada zumunta, da aikace-aikacen yanar gizo masu nauyi. Sai kuma fasahar 5G, wadda ta gina duniyar IoT, masana’antu masu tunani, da sadarwa mai ƙarancin jinkiri. Wannan tafiya ta tabbatar da cewa kowane zamani yana buƙatar sabon salo, wanda zai iya ɗaukar nauyin cigaban tattalin arziki, ilimi, kiwon lafiya, da sadarwa. 6G ita ce mataki na gaba a wannan jerin.

Binciken farko kan fasahar 6G

Bincike game da 6G ya fara ne a shekarar 2020, lokacin da ƙasashe da cibiyoyin bincike suka gane cewa 5G ka iya zama ƙaramin mataki kawai a tsarin sadarwa na duniya. Jami’o’i, cibiyoyin fasaha, hukumomin sadarwa, da manyan kamfanonin sadarwa suka fara nazarin yiwuwar samun hanyar da za ta haɗa AI, quantum computing, tauraron ɗan Adam, da terahertz spectrum. Ƙasashe kamar China, Japan, Amurka, Koriya ta Kudu da ƙasashen Turai su suka kafa shirye-shiryen bincike da zuba jari domin tsara yadda fasahar 6G za ta kasance. Ana hasashen cewa samar da ƙa’idojinta ya kammala a ƙarshen shekarun 2020, sannan a fara amfani da ita a duniya a farkon shekarun 2030. Wannan tunani ya nuna cewa 6G ba fasaha ce da za ta zo kwatsam ba, face sakamakon tsari, bincike, da ginin harsashin sadarwa na gaba.

Ƙasashe da cibiyoyin da ke jagoranci

A yau, ƙasashe da dama sun fara zuba jari mai yawa domin gina 6G. China ita ce kan gaba, ta hanyar cibiyoyi kamar China Mobile, Huawei, da ZTE, waɗanda ke gudanar da gwaje-gwajen terahertz, fasahar tauraron ɗan Adam, da haɗin AI. A Amurka, manyan jami’o’i irinsu MIT, tare da kamfanoni kamar Qualcomm, Apple, da Google, suna jagorantar bincike kan sabbin hanyoyin sarrafa bayanai da tsaro. Ƙungiyar Tarayyar Turai (EU) ma ta kafa shirin Hexa-X, wanda Ericsson, Nokia, da wasu cibiyoyi na kimiyya ke jagoranta. Haka kuma ƙasashen Japan, Koriya ta Kudu, da Singapore suna daga cikin ƙasashen da suka fara tsara dokoki, gwaji, da ƙirƙirar kayan aikin fasahar 6G.

Muhimman siffofin fasahar 6G

Fasahar 6G ba kawai matsawa daga 5G ba ne, sabon tsari ne da ke ƙoƙarin haɗa AI, holographic communication, quantum networking, edge computing, da tauraron ɗan Adam a cikin cibiyar sadarwa guda ɗaya. Manufar ita ce samar da hanyar sadarwa da ke da tsaro, sauri, ƙarancin jinkiri, da damar ɗaukar na’urori biliyoyi a lokaci guda. 6G za ta ba da damar sadarwa tsakanin mutane da injina, injina da injina, da tsakanin na’urori masu sarrafa kansu kamar motocin kai tsaye, injinan gona, da sarrafa manyan masana’antu.

  • Saurin sarrafa bayanai

Ana sa ran 6G zai iya kaiwa 1 terabit a cikin sakan ɗaya (1 Tbps); wanda ya fi saurin 5G sau ɗaruruwa. Wannan saurin ya isa sauke fina-finai masu nauyi a cikin ‘yan sakanni kaɗan, ko gudanar da hologram cikin lokaci. Haka kuma zai bai wa masana’antu, asibitoci, makarantu, da gwamnati damar sarrafa manyan bayanai ba tare da tangarɗa ba.

  • Ƙarancin jinkiri

Ƙarancin jinkiri shi ne lokacin da bayanai ke ɗauka kafin su isa wurin da aka aika su. Fasahar 5G tana iya kaiwa 1 millisecond, amma 6G na ƙoƙarin ragewa zuwa 0.1 millisecond. Wannan matuƙar ƙarancin jinkirin zai zama muhimmi wajen aiwatar tiyatar nesa, motoci masu tuƙí’i da kansu, aikin soja ta sarrafa drone, wasannin kai tsaye (VR/AR), da injinan masana’antu masu buƙatar real-time experience.

  • Terahertz spectrum

Ɗaya daga cikin ginshiƙan fasahar 6G shi ne amfani da Terahertz (THz) spectrum, wato nisan zango tsakanin 0.1 zuwa 10 terahertz. Wannan yanki yana ba da damar sufuri mai saurin gaske da ƙaramin jinkiri. Sai dai yana da iyaka wajen nisan isarwa, saboda haka ana buƙatar sabbin na’urori, ƙananan matattarar sigina (small cells), da fasahar tauraron ɗan Adam domin ya yi aiki yadda ya kamata.

  • Yawan haɗin na’urori

Ɗaya daga cikin muhimman ginshiƙan 6G shi ne damar haɗa na’urori biliyoyi a lokaci guda ba tare da illolin cunkoso ba. Wannan ya haɗa da wayoyi, na’urorin IoT, injinan masana’antu, firikwensin gona, hanyoyin sufuri na smart, da cibiyoyin birane masu aiki da fasaha. 6G zai ƙara faɗaɗa ƙarfin network density, har ya wuce abin da 5G ke bayarwa sau da yawa, yana ba da damar sadarwa mai ƙwari, kai tsaye, da ƙarancin amfani da kuzari. Wannan yawan connectivity zai zama tushen samar da smart cities, kiwon lafiya daga nesa, noman zamani, da bayanan tattalin arziki.

  • Ingantaccen tsaro

Sabuwar fasahar 6G tana ɗauke da ƙarin matakan tsaro domin ta kare bayanai a duniya mai cike da haɗuran yanar gizo. Ana sa ran za ta yi amfani da quantum-resistant encryption, wato ɓoyayyun bayanan da ko kwamfutocin quantum ba za su iya karya su cikin sauƙi ba. Haka kuma, 6G za ta haɗa AI cybersecurity, wacce ke gano hare-haren intanet kafin su faru, da blockchain don tabbatar da gaskiya da sahihancin bayanai. Za a samar da matakan kariya ga na’urori masu yawa, domin hana kutsen fasaha, satar bayanai, da karya sirrin jama’a. Wannan zai sa 6G ta zama cibiyar sadarwa mai aminci, ɗorewa, da kariya fiye da dukkan fasahohin da suka gabata.

  • Artificial Intelligence & Machine Learning

AI da ML za su zama zuciyar fasahar 6G, domin su ne ke kula da yadda cibiyar sadarwa ke aiki. A fasahar 6G, AI ba wai kawai za ta sarrafa zirga-zirgar bayanai ba ne, har ma za ta iya hasashen matsaloli kafin su faru, ta daidaita bandwidth ga na’urori masu bukata, ta rage jinkiri, kuma ta inganta tsaro. Wannan yana nuna fasahar sadarwa mai hankali wacce ke koyon dabi’u masu amfani, tana sauya ƙa’idoji kai tsaye, tana kuma tabbatar da ingantaccen haɗi a kowane yanayi; ko a birni mai cunkoso, ko a karkara mai nisa.

  • Edge da cloud computing

Fasahar 6G ba za ta dogara ga manyan cibiyoyin bayanai kaɗai ba, domin ana sa ran bayanai za su rika wanzuwa a kusa da inda ake samar da su, wato a edge computing. Wannan yana rage jinkiri, yana ba da damar ayyuka kamar motoci masu tuƙi da kansu, likitanci daga nesa, da VR/AR mai inganci. Cloud computing kuwa zai ci gaba da taka rawa wajen adanawa, lissafawa, da sarrafa bayanai masu yawa. Haɗa cloud da edge computing zai ƙirƙiri wani tsarin sadarwa mai sauri, kuma mai ƙarancin amfani da makamashi.

  • Quantum communication

Tare da yuwuwar zuwan quantum computers, tsoffin hanyoyin encryption na iya zama masu rauni. Saboda haka fasahar 6G an gina ta da quantum communication, wacce ke amfani da ka’idar quantum physics wajen kare bayanai. Wannan irin sadarwa tana da matuƙar tsaro, domin duk wani yunƙurin sata ko canja bayanai zai iya bayyana nan take. Quantum key distribution zai zama ginshiƙin tabbatar da sirri da amincin bayanai a nan gaba.

  • Satellite-based networks

Fasahar 6G ba za ta takaita ga cibiyoyin hasumiyar ƙasa ba. Za a haɗa ts da tauraron ɗan Adam; musamman manyan gungun taurari masu ƙanƙanta, don samar da intanet a kowane yanki na duniya, ciki har da hamada, dazuka, tekuna, da yankunan da ba su da sabis. Wannan haɗin tauraron ɗan Adam da 6G zai samar da cibiyar sadarwa ta duniya wacce ba ta da iyaka, tare da gudu mai ƙarfi da ƙarancin jinkiri. Wannan yana taimakawa wajen rage giɓin fasaha tsakanin ƙasashe masu cigaba da masu tasowa.

  • Blockchain da data integrity

Sabuwar fasahar 6G za ta samar da bayanai masu yawa, don haka tabbatar da sahihancinsu ya zama dole. Blockchain zai taka rawa wajen tabbatar da gaskiya, kulawa da izinin samun bayanai, da hana canjin da bai dace ba. Duk bayanin da ya shiga fasahar zai zama abin bibiyu, bayyananne, kuma sahihi. Wannan ya dace da aikace-aikacen gwamnati, kasuwanci, kiwon lafiya, da IoT. Saboda haka 6G ba kawai zai zama mai sauri ba, har ma tsarin sadarwa  da ke mutunta amana, kariya, da gaskiya.

Tsarin aikin fasahar 6G

  • Core network

A fasahar 6G, core network shi ne ginshiƙin cibiyar sadarwa wanda ke kula da gudanar da bayanai, sarrafa zirga-zirga, da tabbatar da haɗin kai tsakanin na’urori. Core network yana haɗa edge nodes, satellite links, da manyan data centers domin samar da hanyar sadarwa mai ƙwari, sauri, da ƙarancin jinkiri. Wannan tsarin yana ba da damar gudanar da ayyuka masu rikitarwa kamar holographic communication, telemedicine, da masana’antu masu sarrafa kansu. Core network ne ke ɗaukar nauyin rarraba bayanai, samar da tsaro, da tabbatar da inganci ga duk na’urorin da ke haɗe da fasahar.

  • Distributed networking

Distributed networking a fasahar 6G yana nufin cewa aikin sarrafa bayanai bai dogara ga wuri guda kawai ba, ana rarraba shi zuwa nodes da ke kusa da wurin amfani. Wannan yana rage jinkiri sosai kuma yana ba da damar gudanar da ayyuka a lokaci ɗaya, musamman ga na’urori masu buƙatar real-time communication kamar motoci masu tuƙi da kansu, robots, da drones. Haka kuma, distributed networking yana ƙara ƙarfin resilience, domin idan wuri ɗaya ya samu matsala, sauran nodes za su ci gaba da aiki ba tare da tangarɗa ba.

  • Software-defined networking (SDN)

Software-defined networking (SDN) na ba fasahar sadarwar damar canja hanyoyi da ka’idoji ta hanyar software maimakon hardware kawai. A 6G, SDN zai yi aiki tare da AI domin daidaita bandwidth, sarrafa traffic, da kiyaye tsaro. Wannan yana nufin fasahar sadarwa za ta iya gyara kanta, gano matsaloli, da bayar da ingantattun hanyoyi ga na’urori masu yawa cikin sauri. SDN na da matuƙar muhimmanci domin 6G za ta haɗa na’urori biliyoyi da sabbin fasahohi kamar IoT, smart cities, da holographic communication.

Aikace-aikacen 6G

  • Holographic communication

Fasahar 6G za ta ba da damar holographic communication, wato sadarwa ta hoton mutum ko abubuwa a cikin siffa ta 3D kai tsaye, ba tare da bukatar motsin jiki ko ganewa a fili ba. Wannan zai canja yadda mutane ke taro, yin taron kasuwanci, ko gudanar da karatu, inda za a iya ganin mahalarta kamar suna a cikin daki guda. Holographic communication zai kuma taimaka wajen horar da ma’aikata, yin nuni a fannin kimiyya, da bayar da horo mai inganci daga nesa.

  • Virtual & Augmented Reality

Ta hanyar Virtual Reality (VR) da Augmented Reality (AR), 6G za ta ba da damar kirkirar yanayi mai cike da abubuwa na dijital a duniya. Ɗalibai za su iya yin koyo cikin yanayi mai kama da ainihi, likitoci su gudanar da tiyata daga nesa, kuma injiniyoyi su yi gwaje-gwaje ba tare da haɗari ba. Wannan zai haifar da ingantaccen tsarin koyo, aiki, da jin daɗi a fannoni daban-daban.

  • Smart healthcare

A fannin kiwon lafiya, fasahar 6G za ta sauƙaƙa remote diagnosis, robotic surgery, da wearable medical devices. Likitoci za su iya sa ido kan marasa lafiya daga nesa, yin aikin tiyata da taimakon robots da cikakken daidaito, da kuma amfani da bayanai kai tsaye domin inganta kulawa da lafiya. Wannan zai rage wahala, ɓata lokaci, da kashe kuɗi a asibitoci, musamman a wurare masu nisa ko karkara.

  • Intelligent transport systems

Fasahar 6G za ta canja zirga-zirgar ababen hawa ta hanyar motoci masu tuƙi da kansu, smart traffic lights, da predictive traffic management. Na’urorin IoT za su yi musayar bayanai kai tsaye, inda motocin za su iya guje wa haɗari, rage cunkoso, da kiyaye kuzarin man fetur. Wannan tsarin zai ƙara aminci, rage gurbata muhalli, da inganta tafiye-tafiye.

Smart cities a zamanin 6G

  • Sarrafa ababen more rayuwa ta kwamfuta

Birane za su rika amfani da fasahar 6G wajen sarrafa albarkatu kamar wutar lantarki, ruwa, da sufuri ta hanyar kwamfuta, wanda ke rage ɓata lokaci, kuzari, da lalacewar kayan more rayuwa.

  • Zirga-zirgar ababen hawa

Hanyoyi za su gane motsin ababen hawa da daidaita fitilu ta atomatik domin sauƙaƙa zirga-zirga. Motoci masu tuƙi da kansu za su tattauna da juna da hanyoyi domin gujewa haɗari.

  • Smart surveillance & security

Fasahar 6G za ta ba da damar amfani da AI-powered surveillance a birane, inda kyamara da firikwensin zamani za su gano matsaloli, tsaro, da haɗari cikin lokaci ɗaya, ba tare da dogaro ga mutane ba.

  • Inganta amfani da makamashi da muhalli

Smart meters da sensors za su lura da amfani da makamashi da ruwa a birane, su ba da rahoto kai tsaye, kuma su taimaka wajen rage ɓarna da kiyaye muhalli.

  • E-Governance

Hanyoyin fasahar 6G za su bai wa gwamnati damar gudanar da ayyuka cikin hanzari da gaskiya, kama daga bayar da lasisi, tara kudaden haraji, zuwa tsarin kiwon lafiya da ilimi, wanda ke rage dogaro da takardu da lokaci.

Na’urorin da ke tattaunawa da juna

  • Internet of everything

Fasahar 6G za ta haɗa duk na’urori zuwa internet of everything, inda na’urorin ke fahimtar juna, musayar bayanai, da aiwatar da ayyuka ba tare da kulawar ɗan Adam ba. Wannan yana ba da damar gudanar da ayyuka cikin sauri, daidai, kuma mai aminci.

  • Motoci masu tuƙi da kansu

Motoci za su iya sadarwa da juna da hanyoyi, yin nuni kan cunkoso, haɗari, ko sauyin yanayi, wanda ke rage haɗari da sauri.

  • Na’urorin gida masu tunani (smart homes)

Gidaje za su iya sarrafa kayan lantarki, tsarin tsaro, da na’urorin jin daɗi ta hanyar na’ura ɗaya ko wayar hannu, kuma na’urori za su iya sadarwa da juna domin daidaita ayyuka.

  • Smart agriculture da sensors

Fannin noma zai amfana sosai, inda na’urorin sensors za su lura da ƙasa, ruwa, yanayi, da amfanin gona, su rarraba ruwa da sinadarai yadda ya dace, ta yadda za a samu ingantaccen amfanin gona.

  • Masana’antu masu sarrafa kansu

Masana’antu za su gudanar da aiki ba tare da kulawar kai tsaye daga ɗan Adam ba, inda injuna ke sarrafa juna, lura da kayan aiki, da tattara bayanai domin inganta aiki da rage ɓarna.

Tasirin 6G ga tattalin arziki da aikin yi

  • Sabbin masana’antu da kasuwanni

Fasahar 6G za ta samar da damammaki na ƙirƙirar sabbin masana’antu da kasuwanni waɗanda ba su wanzu a yanzu ba. Aikace-aikacen holographic communication, smart cities, da Internet of Everything za su haifar da bukatar sabbin na’urori, manhajoji, da ayyuka masu alaƙa da sadarwa. Kamfanoni za su iya samar da sabbin kayayyaki da ayyuka, musamman a fannoni irin su kiwon lafiya, ababen hawa, robotics, da virtual reality services. Wannan zai kara haɓaka fannin kasuwanci a matakin gida da na duniya baki ɗaya.

  • Haɓakar digital economy

Haɓakar fasahar 6G zai kawo cigaba mai girma ga digital economy, wato tattalin arzikin da ke dogara da bayanai da intanet. E-commerce, digital marketing, online education, da cloud-based services za su samu cigaba sosai. Bugu da ƙari, 6G za ta ƙara saurin musayar bayanai, rage lokaci da tsadar gudanar da harkoki, kuma ta bai wa ƙananan kamfanoni damar shiga kasuwannin duniya cikin sauƙi. Wannan zai ƙara samun kuɗaɗen shiga, rage giɓin kasuwanci, da samar da ingantaccen yanayi ga masu sha’awar sana’o’in dijital.

  • Sabbin fannonin ƙwarewa da horo

Ma’aikata za su buƙaci sabbin dabarun ƙwarewa da horo domin aiki a duniyar 6G. Fannin software development, cybersecurity, AI, data analytics, cloud computing, da IoT za su zama muhimmai. Haka kuma, horo a kan sarrafa jiragen drones, smart agriculture, da motoci masu tuƙi da kansu zai ƙara yawan ayyukan yi a fannoni daban-daban. Wannan tsarin zai bai wa matasa damar samun sabbin sana’o’i da ƙwarewa, yana kuma haifar da gasa a fannin aiki a matakin duniya.

Tasirin 6G ga tattalin arziki da aikin yi zai zama mai ɗorewa, domin yana haɗa fasaha, kasuwanci, da ƙwarewar ɗan Adam cikin tsarin guda, wanda zai bai wa ƙasashe da kamfanoni damar yin gasa a matakin duniya.

Ƙalubale da barazanar 6G

  • Giɓin fasaha tsakanin ƙasashe

Duk da cewa 6G na da damar kawo ci gaba mai girma, giɓin fasaha tsakanin ƙasashe masu ci gaba da masu tasowa na iya zama babban ƙalubale. Ƙasashe masu ƙarancin kayan aiki ko rashin horar da ƙwararru na iya tsayawa a baya wajen amfani da fasahar. Wannan yana iya ƙara bambanci a fannin tattalin arziki, ilimi, da kimiyya. Ƙasashe da kamfanoni waɗanda suka fara zuba jari cikin 6G za su samu fa’ida fiye da waɗanda ba su da wannan damar.

  • Tsaro da sirrin bayanai

Haɓakar haɗin na’urori da yawaitar bayanai yana ƙara haɗarin hare-haren yanar gizo da satar bayanai. Duk da matakan quantum encryption da AI-powered cybersecurity, barazanar fashin yanar gizo da kutsen sirrin mutane na iya zama babban ƙalubale. Mutane za su buƙaci sanin yadda za su kare bayanansu, yayin da hukumomi da kamfanoni za su ƙara ƙoƙarin samar da tsaro mai ƙarfi.

  • Tsadar gina tsarin sadarwa

Gina fasahar 6G yana buƙatar zuba jari mai yawa a kayan aiki, tauraron ɗan Adam, da cibiyoyin edge. Wannan tsada na iya zama babban cikas ga ƙasashe masu tasowa da kamfanoni masu ƙaramin ƙarfi. Haka kuma, sabbin dokoki da tsarin kulawa za su ƙara tsadar kafawa da gudanar da fasahar sadarwa.

  • Tasirin makamashi damuhalli

Sabuwar fasahar 6G za ta yi amfani da manyan na’urori, tauraron ɗan Adam, da cibiyoyin bayanai, wanda za ta iya ƙara yawan amfani da makamashi da gurɓata muhalli. Haka kuma, tsarin nan na terahertz spectrum da edge computing zai buƙaci ƙarin kayan aiki. Don haka, samar da tsarin da ke ɗorewa, mai amfani da kuzari kaɗan, kuma mai daidaita yanayi zai zama babban ƙalubale ga masana da masu tsara dokoki.

Fasahar 6G a Najeriya da Afirka

A Najeriya da yawancin ƙasashen Afirka, fasahar ICT ta samu cigaba na ɗan gajeren lokaci, duk da kasancewar wasu yankuna ba su da cikakken sabis na intanet mai sauri. A wasu birane kamar Lagos, Abuja, da Cape Town, amfani da fasahar 4G da fara gwaje-gwajen 5G ya fara bai wa mutane damar amfani da fasahar zamani, e-commerce, da ayyukan gwamnati ta yanar gizo. Sai dai a karkara da wasu ƙananan birane, rashin kayan aiki, ƙarancin fiber optic, da ƙarancin horar da ma’aikata na rage yawan amfani da fasaha. Wannan ya nuna cewa Najeriya da wasu ƙasashen Afirka gabaɗaya na da buƙatar ƙarin zuba jari kafin fasahar 6G ta zama mai amfani ga kowa.

Manyan damarmakin kasuwanci

Fasahar 6G za ta samar da sabbin damammaki na kasuwanci a Najeriya da Afirka. A fannin noma, smart agriculture zai taimaka wajen inganta amfanin gona ta hanyar na’urorin sensors da drones. A fannin lafiya, telemedicine da na’urorin likitanci na smart devices za su sauƙaƙa kulawa da marasa lafiya daga nesa. E-commerce da digital finance za su ƙaru, suna bai wa ƙananan kamfanoni damar shiga kasuwanni na duniya. Haka kuma, ƙirƙirar smart cities a manyan birane zai haifar da damarmaki a fannin gine-gine, intelligence transportation, da tsaro. Wannan ya nuna cewa 6G na iya zama babbar hanyar haɓaka tattalin arziki da samar da ayyukan yi a Afirka.

Abubuwan da ake buƙata kafin wanzuwar fasahar 6G

Domin 6G ta yi tasiri sosai a Najeriya da Afirka, akwai bukatar:

  • Zuba jari a kayan aiki da cibiyoyin sadarwa, ciki har da tauraron ɗan Adam da fiber optic, domin rage gibin fasaha.
  • Horon ƙwararru, musamman a fannoni kamar AI, cybersecurity, IoT, da network engineering, domin gudanar da fasahar 6G yadda ya kamata.
  • Dokoki da tsare-tsare na e-governance da tsaro, domin kare bayanai, na’urori, da sirrin jama’a.
  • Shirin dorewar makamashi da muhalli, domin rage tasirin amfani da kayan aiki masu ƙarfi da gurbata muhalli.

Bambanci tsakanin 4G, 5G da 6G

  • Sauri

Fasahar 4G na bayar da gudun sauke bayanai har zuwa 100 Mbps a wurare masu ƙarancin ƙarfi da 1 Gbps a wurare inganci. Wannan ya isa yin mu’amala ta yanar gizo, sauke bidiyo mai kyau, da gudanar e-commerce mai sauƙi.

Fasahar 5G ta kawo saurin da ya kai 10–20 Gbps, wanda ke ba da damar gudanar da aikace-aikacen da ke buƙatar bandwidth mai yawa kamar VR/AR da IoT.

Yayin da a fasahar 6G ana sa ran za ta kai gudun 1 terabit a sakan ɗaya (1 Tbps), wanda ya fi 5G sau ɗaruruwan lokaci. Wannan zai ba da damar gudanar da holographic communication, real-time robotics, da manyan na’urori masu haɗi ba tare da matsalolin cunkoso ba.

  • Jinkiri

Fasahar 4G tana da latency kusan 50–100 milliseconds, wanda ya isa yin kiran bidiyo da wasanni, amma ba ya dacewa da ayyuka masu buƙatar real-time.

Fasahar 5G tana rage jinkirin zuwa 1 millisecond, wanda ke ba da damar ga motoci masu tuƙi da kansu, masana’antu masu sarrafa kansu, da wasannin VR/AR.

Fasahar 6G za ta rage jinkirin zuwa 0.1 millisecond, wanda zai ba da damar real-time communication, tiyata daga nesa, da tsarin masana’antu da ke buƙatar real-time decision-making.

  • Amfani da bandwidth

Fasahar 4G tana amfani da spectrum na MHz, yayin da 5G ta fara amfani da GHz spectrum. 6G za ta yi amfani da Terahertz spectrum (0.1–10 THz), wanda ke ba da damar isar da bayanai cikin sauri mafi girma, ƙarancin jinkiri, da haɗin na’urori masu yawa.

  • Yawan na’urori

Fasahar 4G tana iya ɗaukar na’urori ɗaruruwan ko dubunnai kaɗan a cibiyar sadarwa ɗaya. 5G za ta iya ɗaukar na’urori miliyoyi a kowace km², tana ba da damar IoT da smart cities. Yayin da fasahar 6G za ta ƙara wannan ƙarfin sosai, ta haɗa na’urori biliyoyi a lokaci guda, ciki har da na’urorin gida, motoci, masana’antu, da cibiyoyin birane.

Makomar fasahar 6G

  • Lokacin da ake sa ran fara amfani

Masana suna hasashen cewa fasahar 6G za ta fara amfani daga farkon shekarun 2030, bayan ƙarewar gwaje-gwaje da ƙirƙirar ƙa’idojin fasahar. Ƙasashe da kamfanoni masu jagoranci za su fara amfani da ita a matakin gwaji a wasu birane, kafin ta bazu zuwa ƙasashe masu tasowa.

  • Hasashen masana kan rayuwar dijital

Ana sa ran fasahar 6G za ta canja rayuwar dijital gabaɗaya. Za ta kawo smart cities, smart healthcare, intelligent transport, holographic communication, da Internet of Everything. Rayuwa za ta fi haɗa kai da injuna da na’urori, inda mutane za su iya yin hulɗa da duniya ba tare da ƙuntatawa ba. Haka kuma, 6G za ta ƙara damarmaki a fannin tattalin arziki, aikin yi, da ilimi, yayin da za ta ƙara buƙatar ƙwararrun ma’aikata da sabbin fannoni.

Manazarta

Ericsson. (2021, March). 6G white paper: The next generation of connectivity. 

Huawei Technologies. (2022, July). 6G vision: Towards 2030. 

International Telecommunication Union. (2020, December). IMT-2030: Framework and roadmap for 6G. 

Qualcomm. (2021, November). 6G: The next horizon for wireless technology. 

Zhang, Y., Wang, J., & Li, X. (2022). Terahertz communications for 6G: Opportunities and challenges. IEEE Communications Magazine, 60(5), 50–57.

Sharuɗɗan Editoci

Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.

Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.

Maƙalar ta amfanar?
EAa

You cannot copy content of this page

×