Shi kalmar force a fannin ilimin lissafi da fasaha, wato physics, na iya daukar ma’anar duk wani abu da ke iya sa wani abun ya tafi ko ya tsaya guri guda. Force, vector quantity ne domin yana da magnitude and direction. A Turance zamu iya cewa, ‘force is the push or pull or is that which changes or tends to change the state of rest or a uniform motion of a body. Unit na force shi ne:
NEWTON (N)
Rabe-raben force
Force iri biyu ne, ko ya kasance; contact force ko kuma field force. Contact force shi ne force dake existing, wato kasancewa, tsakanin bodies guda biyu da suke manne. Misalan sa sune friction, upthrust, reactional force, thrust, tension da sauransu.
Field force shi ma force ne dake existing sakanin bodies guda biyu amma wadanda basu manne ba ko basu tare. Misalansu su ne, electric force, magnetic force, gravitational force da nuclear force.
Friction: Force ne dake opposing relative motion kuma yana faruwa tsakanin bodies ko abu guda biyu dake tare ko manne. Friction can be defined as the force that opposes the relative motion between any two bodies or surfaces in contact.
Shi ma friction ya rabu gida biyu, akwai dynamics friction da static ko limiting friction.
Static friction shi ne frictional force dake existing tsakanin surfaces guda biyu kafun su fara tafiya ko kuma lokacin da zasu fara tafiya. Amma shi Dynamics frition, frictional force ne dake faruwa yayin da surfaces guda biyu suke cikin tafiya.
Laws of solid friction da kuma calculation akan friction
Laws of friction: Friction yana da laws guda biyar kamar yadda zamu gan su:
Na farko: friction is always opposing motion.
Na biyu: Friction depends on the nature of surfaces in contact. Abunda ake magana anan shi ne friction between two rough surfaces is greater than the frictional force between smooth surfaces.
Na uku: It does not depend on relative speed between the surfaces.
Na hudu: Friction does not depend on the area of the surfaces in contact. Sai kuma na karshe
Na biyar: Frictional force is directly proportional to the normal reaction(R) between the two surfaces in contact. A nan zamu iya rubuta shi mathematically kamar haka
F α R 1
F = µR 2
Ta yadda F = Frictional force, R= Normal reaction da µ ana kiransa coefficient of friction wannda constant ne.
Sannan ana iya rubuta R = mg 3
Ta yadda m = mass na body, g = acceleration due to gravity.
Kafin ku yi exercise din idan kuna so kuna iya duba makalarmu da ta yi bayani akan banbancin dake tsakanin mass and weight, dimension, position, distance and displacement.
*** Tarihin Wallafa Maƙalar ***
An wallafa maƙalar 19 July, 2025
An kuma sabunta ta 19 July, 2025
*** Sharuɗɗan Editoci ***
Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.
Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.