Madubin mata a gwagwarmaya da siyasar Nigeria. An haifi Hajiya Gambo Sawaba a ranar Lahadi, 15 ga watan February na shekarar 1933, a garin Zaria da ke jihar Kaduna.
Sunan mahaifinta Isa Amartey Amarteifio (Christened Theophilus Wilcox,) dan asalin kasar Ghana ne. Ya kammala karatunsa a makarantar Ghana School of Survey. Ya yo hijira zuwa Nigeria ne a shekarar 1910, ya zo ne don neman aiki a Nigerian Railway Corporation, daga nan kuma sai ya yanke shawarar yin zama na dindindin.
Aiki ya kawo shi garin Zaria, inda a nan Christened Theophilus ya karbi addinin Musulunci, ya sauya suna zuwa Isa. A nan kuma ya hadu da Fatima, wadda take Banufiya ce ‘yar asalin karamar hukumar Lavun da ke jihar Niger. Kakanta makeri ne, jajirtaccen namijin da baya juya baya ga abinda ya sanya a gaba. Shi ne ya haifi mahaifinta (wato kakan Gambo Sawaba, Mamman Dazu).
A lokacin da suka hadu, Fatima ta kasance Bazawara, tana da ‘ya’yanta uku da suka haifa tare da tsohon mijinta mai suna Muhammad Alao, wanda ya rasu.
Bayan ‘yan shekaru da haduwarsu sai suka yi aure, wanda a cikin auren nasu sun samu ‘ya’ya shida, Gambo ita ce ‘ya ta biyar. Asalin sunanta shi ne Hajaratu, ana kiranta da sunan Gambo ne saboda an haifeta bayan an haifi ‘yan biyu kafin ita. Bisa al’adar Hausawa ana kiran wanda aka haifa bayan an haifi ‘yan biyu da sunan Gambo, don haka ake kiran Hajara da sunan Gambo.
Karatu da rayuwa
Gambo ta yi karatu a makarantar Native Authority Primaary School da ke Tudun wada Zaria. Daga nan karatunta ya tsaya, bayan rasuwar mahaifinta a shekarar 1943, wanda ya rasu sakamakon matsanancin ciwon kai. Shekaru uku bayan rasuwar mahaifinta, mahaifiyarta ma ta rasu.
Gambo tana ‘yar shekaru goma sha-uku a duniya ta auri wani tsohon soja mai suna Abubakar Garba Bello, wanda ya samu kwarewar aiki, kuma ya yi ritaya bayan an gama yakin duniya na biyu. Mijin Gambo Sawaba ya tafi ya barta a lokacin da ta samu cikin farko, kuma bai sake waiwayarta ba, har ta haifi ‘yarta mai suna Bilkisu. Bayan wasu ‘yan shekaru, sai Gambo ta sake yin wani auren, inda ta auri wani mutum mai suna Hamidu Gusau. Mutum mai tsaurin ra’ayi da saurin fushi da tsangwama, wanda shi ma zaman nasu bai dau lokaci mai tsawo ba suka rabu. An ce bayan wannan auren ma ta sake yin wasu auren har sau biyu.
Gwagwarmaya da siyasa
Gambo, tun a lokacin kuruciyarta mace ce mai tsayuwar daka a kan duk abinda ta sanya a gaba, tare da watsar da komai don ganin ta cimma gacin abin. Kuma da wuya a kayar da ita a magana ko musu a kan abu, matukar tana da gaskiya, bata yarda ta sarayar da hakkinta. Bata da kwauron-baki. Ta taso da tausayin mutane masu tabin hankali, tana zama da su, ta yi hira da su. Tana taimaka musu da abubuwan bukata kamar su abinci, sutura da ‘yan kudi idan tana da su. Har ma a kan yi fada da ita don kare hakkinsu.
Gambo ta fara fuskantar wahala a sha’anin siyasar Nigeria tun tana da shekaru sha-bakwai a duniya. A wancan lokacin a Arewacin Nigeria jam’aiyyar da take da karfi ita ce N.P.C wato Northen People’s Congress, wacce ta ke da goyon bayan sarakuna da kuma turawan mulkin mallaka. Amma a tare da hakan, sai Gambo ta zabi ta shiga jam’iyyar adawa ta malam Aminu Kano, wato Northern Element Progressive Union, NEPU. Jam’iyya ce ta talakawa, wadda talakawan ne ke dawainiya da ita, ta hanyar sadaukarwa da kuma karo-karo, har ta yi karfi.
Babbar manufar jam’iayyar NEPU ita ce; yaki da turawan mulkin mallaka, ba wa mata cikakkiyar damar fitowa a dama da su a harkokin karatun addini da na zamani, da harkar tattalin arziki da kuma yaki da cin hanci da rashawa.
Gambo ta shiga Jam’iyyar ne a lokacin da aka bude karamin ofishin jam’iyyar a garin Zaria. A lokacin jam’iyyar na yin tarukanta a boye, tare da boyewa hukumomi duk wasu aikace-aikacenta. (kila saboda gudun fushin sarakunan lokacin)
Kalmar ‘Sawaba’ ba ya daga cikin sunan Gambo na yanka, ko na dangi. Suna ne da ke nufin ‘Yanci, ko kuma kubuta daga cikin wani hali na matsin-lamba. A wata majiyar an ce Malam Aminu Kano ne ya sa mata sunan bayan an zabeta a matsayin shugabar matan jam’iyyar. Yayin da a wata majiyar kuma aka ce; ta samu sunan ne a yayin gudanar da wani taron siyasa a garin Zariya, yayin da wani mutum, daya daga cikin jiga-jigan jam’iyyar mai suna Alh. Gambo Sawaba, wanda kuma shi ne babban mai jawabi a taron, cikin barkwanci ya kirata da suna “Hajiya Gambo Sawabiya!”
Ta samu damar zuwa garin Abeokuta, inda ta ziyarci fitacciyar mai fafutukar kwatar ‘yancin matan nan, wato Funmi-Layo Ramsome Kuti. Gambo Sawaba ta samu ilimi a kan hanyoyin da Funmi-layo ta bi ta samu nasara a zanga-zangar da ta shirya ta dakatar da harajin da matan garin Egba ke biya. Ta kuma samun karin ilimi da dabarun zama ‘yar gwagwarmaya. Ta fara da fafutukar yaki da auren wuri da ake yiwa kananan yara mata, da bautar da su da ake yi, da kuma hana su damar yin karatu mai zurfi a Arewacin Nigeria.
Cikin ‘yan watanni kadan, Sawaba ta samarwa kanta matsayi da suna a siyasar Nigeria. A wani jawabi da ta yi a wani taron siyasa da aka yi a Zaria, inda ta mike a cikin dakin taron cike da maza, cikin kwarin gwaiwa, ta gabatar da jawabin da mutanen wajen kowa ya ji shakkar bude baki ya kalubalanceta.
Gambo Sawaba ta ci gaba da daga darajarta ta hanyar bi gida-gida, inda take tattaunawa da matan da ke da ra’ayin siyasa amma suna tsoron fitowa a dama da su, kawai saboda kasancewarsu mata, tana karfafa musu gwiwa, da ba su shawarwari.
Dangin mijinta basa jin dadin irin rawar da take takawa a siyasance, saboda wannan dalilin uwar mijinta ta dauke ‘yarta. Amma duk da haka ta ci gaba da jan hankulan matan Arewa a kan fitowa a dama da su a harkokin rayuwa.
A shekarar 1952, wata kotu ta daure Gambo Sawab a gidan yari na tsawon watanni uku, bisa zarginta da ake yi na cewa tana hurewa mata kunne, suna cire lillibi, kuma suna hada kafada da kafada da maza wajen gudanar da harkokin rayuwa. Shekara guda bayan ta gama wa’adin zaman gidan yarinta, hukumomi a Kano suka haramta mata zaman garin, inda aka hada ta da dogarai suka mayar da ita Zaria. Duk da haka ta ci gaba da harkokin siyasarta a garin na Zaria. An sake daureta a gidan yarin Kaduna, da kuma Jos.
Jaridar Daily Trust ta ce, “A duk lokacin da aka gurfanar da Gambo Sawaba a gaban kotu, to kotun tana kasancewa ne a cike da magoya bayanta.”
Ba zaman gidan yari ne kawai ke cutar da ita ba. Domin Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa; “A shiga biyu da ta yi gidan yarin Central Prison a garin Zaria, an yayyaga mata kaya, an aske mata gashin kanta, an keta mata haddi, wanda hakan ya jefa rayuwarta cikin matsananciyar damuwa da jin kunyar mutane.”
A shekarar 1990, a yayin gabatar da wata hira a game da tsangwamar da mata ‘yan siyasa ke fuskanta, Malama Ladi Shehu ta fadawa jaridar First Nation Magazine cewa; “Gambo da wasu daga cikin matan jam’iyyar NEPU, mafi yawancinsu an kullesu a gidan yari, an aske musu gashin kansu, an daddake su, wasu ma daga cikinsu an kashe su.”
Dukkan gwagwarmayar da Gambo Sawaba ta yi a kan a bawa matan Arewa damar su zaba kuma a zabesu a sha’anin siyasa, bata yi nasara ba, hakazalika bata taba samun nasarar cin zabe a jam’iyyarta ta NEPU, da kuma wasu jam’iyyu biyu da ta taba yi a rayuwarta ba.
A shekarar 1998, ta sanar da dakatar da dukkan harkokin siyasarta, a wata hira da ta yi da jaridar New Nigerian ta ce; “Siyasa a kasar nan ta rasa dandano, kuma ta rasa mutane masu akida, yanzu sai siyasar ubangida, da kuma neman kudi ko mukami.”
Sau goma sha shida Gambo Sawaba tana shiga gidan yari a rayuwarta. An ce akwai wani bargo da take yafawa, wanda a jiki ta rubuta ‘Bargon gidan yari.’
Ga wasu daga cikin maganganun Gambo Sawaba a lokacin gwagwarmayarta;
“Babu wasu kofofi da zasu bude a jikina; baki, hanci, idanu, da ma kowane waje da jini zai bulbulo saboda azabtarwa.”
“Hakorana na gaba gabadayansu ba na ainahi ba ne. Na ainahin duk sun karye kuma sun fice daga bakina, saboda gallazawa.”
A sakamakon azabtarwarwar da aka yi mata a gidan yari a 1957, sai da ta bukaci ayi mata tiyata don a ceto rayuwarta daga larurar mafitsara da ta samu.
Gambo Sawaba ta rasu a watan October na shekarar 2001. Ta rasu tana da shekaru 71 a duniya. Ta bar ‘ya daya.
Tarihi ba zai taba mantawa da Hajiya Gambo sawaba ba, saboda tasirin da take da shi a Nigeria, akwai katafaren Asibiti a garin Zaria mai suna Hajiya Gambo Sawaba General Hospital. Sannan akwai dakin kwanan dalibai mata a jami’ar Bayero dake Kano, da aka sanyawa sunan Gambo Sawaba Hall.
Sharuɗɗan Editoci
Duk maƙalun da ku ka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta tare da sa idon kwamitin ba da shawara na ƙwararru. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.
Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.