Garkuwar jiki, wadda ake kira immune system a turance, shi ne tsarin halitta na musamman da ke kare jiki daga cututtuka, kwayoyin cuta (bacteria, virus, fungi), da wasu abubuwa masu guba da ke iya kawo rashin lafiya ga jiki. Wannan tsarin yana da ƙarfin gano abubuwa masu illa ga lafiya da kuma lalata su kafin su jawo matsala ga jiki.
A ilimin kimiyya, garkuwar jiki ba wani sashi guda ba ne, hadin kai ne na gaɓoɓi, ƙwayoyin jini, tsokoki, da hanyoyin jini da ke aiki tare. Wannan haɗin kai ya haɗa da gaɓoɓin da ake kira spleen, thymus, da lymph nodes, wanda kowanne ke da rawar takawa da ba za a iya maye gurbinsa da wani ba.
Spleen yana tace jini, lalata tsofaffin kwayoyin jini, da kuma taimakawa wajen gano kwayoyin cuta. Thymus wuri ne da T cells suke girma da kuma koyon yadda za su gane kwayoyin cuta. Yayin da lymph nodes su ne wuraren da kwayoyin garkuwa ke taruwa, suna tace jini da gano abubuwan da ba su dace ba.

Garkuwar jiki na aiki ne a matakai daban-daban: daga garkuwar jiki ta farko wadda ake kira innate immunity, har zuwa garkuwar jiki ta musamman wadda ake kira adaptive immunity, wadda ke iya tuna ƙwayoyin cuta domin kare jiki daga kamuwa da su nan gaba.
Muhimmancin garkuwar jiki
Garkuwar jiki na taka muhimmiyar rawa wajen kare lafiyar jiki gabaɗaya. Ta hanyar gano abubuwa masu cutarwa da lalata su, garkuwar jiki na hana yaɗuwar ƙwayoyin cuta, kuma tana taimakawa wajen gyara sassan jiki da suka lalace. Idan garkuwar jiki ta yi rauni ko ba ta aiki yadda ya kamata, jiki zai fi kamuwa da cututtuka, kuma warkewa daga cuta zai zama da wahala. Wannan yana nuna cewa garkuwar jiki ginshiƙi ne na rayuwa mai lafiya. Ga wasu misalai:
- Mutanen da ke fama da cutar HIV/AIDS suna da raunin garkuwar jiki, wanda hakan ke sa su fi sauƙin kamuwa da cututtuka kamar pneumonia, tuberculosis, da cututtukan fata.
- Yaran da ba a yi musu rigakafin ƙwayoyin cuta ba na iya kamuwa da measles ko polio, saboda jikinsu ba shi da isasshen tsarin antibodies domin ya yaƙi cuta.
Garkuwar jiki ba kare jiki daga cuta kawai take ba, har ma tana kula da lafiyar jiki a dukkan matakai. Misali, tana taimakawa wajen cire ƙwayoyin jini da suka lalace, gyara ƙwayoyin halitta (cells) da suka lalace, da kuma rage tasirin gubar da ta shiga jiki. Wannan yana nuna cewa garkuwar jiki wani tsarin aiki wanda ba ya tsayawa, tun daga haihuwa har zuwa tsufa.
Sassan garkuwar jiki
Garkuwar jiki tsarin ne mai haɗakar aiki wanda ke ƙunshe da sassa daban-daban da suke aikin tare domin kare jiki daga cututtuka da abubuwa masu guba. Kowanne sashi yana da rawar takawa da ba za a iya maye gurbinsa sa wani ba, kuma suna aiki ne a cikin matakai daban-daban domin tabbatar da ingantaccen tsaro ga jiki.
Kwayoyin jini
Kwayoyin jini wato white blood cells, ko leukocytes, su ne manyan dakarun garkuwar jiki. Su ne ke gano abubuwan da ba su dace ba, su lalata ƙwayoyin cuta, kuma su taimaka wajen gyara ƙwayoyin halittar da suka lalace. Akwai nau’o’in ƙwayoyin jini da dama, amma manyan su sun hada da:
B Cells (B lymphocytes)
Waɗannan ƙwayoyin jini na samar da antibodies, wato sinadaran da ke gano ƙwayoyin cuta da kuma hana su yaɗuwa a jiki. Antibodies suna kama ƙwayoyin cuta kai tsaye ko kuma suna sa sauran ƙwayoyin garkuwar jiki su lalata su. Misali: Lokacin da mutum ya kamu da cutar ƙyanda ko ya samu rigakafin cutar, B cells suna samar da antibodies da ke kare jiki daga cutar a nan gaba.
T Cells (T lymphocytes)
T cells suna da rawar takawa ta kai hari kai tsaye ga ƙwayoyin cuta ko kuma taimakawa B cells wajen aiki. Akwai nau’ikan T cells da dama:
- Helper T cells: Suna taimakawa B cells da sauran ƙwayoyin jini wajen aiki.
- Cytotoxic T cells: Su na lalata kwayoyin cuta ko ƙwayoyin halitta da suka kamu da virus kai tsaye.
Phagocytes
Phagocytes su ne ƙwayoyin da ke cinye kwayoyin bakteriya masu cutarwa kai tsaye, suna narkar da su, sannan suna tsarkake jiki daga abubuwan guba. Misali: Macrophages suna cinye bakteriya da datti a jiki, suna taimakawa wajen hana yaɗuwar cuta.
Gaɓoɓin lymphatic
Gaɓoɓin lymphatic suna taka muhimmiyar rawa wajen tara kwayoyin garkuwar jiki, tace jini, da gano abubuwan da ba su dace ba. Manyan gabobin sun hada da:
Lymph nodes
Su ne wuraren da ƙwayoyin garkuwa ke taruwa, suna tace lymph (jini mai ɗauke da sinadaran garkuwar jiki) daga sassan jiki daban-daban. Suna taimakawa wajen gano ƙwayoyin cuta da samar da antibodies. Misali: Idan mutum yana fama da cutar mura ko infection, lymph nodes suna kumbura saboda ƙarin kwayoyin garkuwa da ke aiki a ciki.
Spleen
Spleen yana tace jini, lalata tsofaffin kwayoyin jini, da kuma kashe kwayoyin cuta. Haka kuma, yana samar da wani adadin lymphocytes da antibodies.
Thymus
Thymus shi ne wurin da T cells ke girma da koyon yadda za su gane kwayoyin cuta. Wannan yana tabbatar da cewa garkuwar jiki na da karfin gane kwayoyin cuta da kuma kawar da su.
Sinadaran garkuwar jiki
Sinadaran da jiki ke samarwa suna taka rawa mai mahimmanci wajen yaƙi da cuta. Wadannan sun hada da:
- Antibodies: Suna kama ƙwayoyin cuta da kuma hana su yaɗuwa.
- Cytokines: Suna aika saƙonni tsakanin ƙwayoyin garkuwa domin su yi aiki tare.
- Interferons: Suna taimakawa wajen daƙile yaɗuwar virus a cikin ƙwayar halitta.

Misali: Idan mutum ya kamu da cutar influenza, sinadaran cytokines da interferons suna taimaka wa ƙwayoyin garkuwa su gano ƙwayoyin cuta, su kai hari, sannan su hana su yaɗuwa cikin sauri a jiki.
Nau’o’in garkuwar jiki
Garkuwar jiki ta asali (innate immunity)
Garkuwar jiki ta asali ita ce tsarin kariya na farko da jiki ke da shi tun daga haihuwa. Ba ta bukatar sanin ko wace ƙwayar cuta kafin ta fara aiki. Wannan garkuwa tana aiki a matsayin shinge na farko, tana hana ƙwayoyin cuta shiga jiki ko yaɗuwa a ciki.
Wasu daga cikin hanyoyin da wannan garkuwa ke aiki sun hada da fata, wadda ke hana shigar ƙwayoyin cuta, hanci da gashin cikin hancin (cilia) wanda ke tace iska ya riƙe ƙura da ƙwayoyin cuta, ya hana su kaiwa ga huhu, da sinadaran acid a ciki (stomach acid) da ke kashe kwayoyin cuta da suka shiga ta baki. Haka nan, fatar baki da hanci da kuma hawaye suna ɗauke da sinadaran yaƙi da bakteriya, wanda da suke taimakawa wajen daƙile cuta.
Misali, idan mutum ya shaki iska mai ɗauke da ƙwayoyin cuta, garkuwar jiki ta asali tana hana yawancinsu shiga huhu ko kuma tana kashe su kafin su jawo cuta, ta haka tana kiyaye lafiyar jiki tun kafin cuta ta fara kamuwa.
Garkuwar jiki ta musamman (adaptive immunity)
Garkuwar jiki ta musamman tana aiki ne idan ƙwayar cuta ta wuce shinge na farko na garkuwar jiki. Wannan garkuwa tana da ikon gano kwayar cuta ta musamman, ta samar da antibodies da T cells don yaƙar ta, sannan ta tuna ƙwayar cutar domin kare jiki a gaba.
Siffofin garkuwar jiki ta musamman sun haɗa da tabbacin damar tuna cuta. Misali, idan mutum ya taɓa kamuwa da farankama, B cells da T cells da suka yi aiki a farko za su tuna ƙwayar cutar. Saboda haka idan ƙwayar cutar ta sake shiga jiki, antibodies suna yin aiki cikin sauri, don haka ba zai sake kamuwa da cutar ba. Wannan yana nuna yadda garkuwar jiki ta musamman ke inganta kariya mai dorewa ga jiki.
Cututtuka da matsalolin garkuwar jiki
Raunin garkuwar jiki
Raunin garkuwar jiki yana faruwa idan tsarin kariya na jiki ba ya aiki yadda ya kamata. Wannan na iya faruwa saboda cuta kamar HIV/AIDS, wanda ke lalata T cells, ko kuma wasu matsaloli kamar rashin abinci mai gina jiki ko wasu cututtuka masu tsanani da ke rage yawan ƙwayoyin garkuwar jiki.
Sakamakon raunin garkuwar jiki shi ne mutum zai zama mai sauƙin kamuwa da cututtuka. Misali, yaro mai raunin garkuwar jiki na iya kamuwa da cututtuka da yawa a lokaci guda saboda jikinsa ba zai iya yaƙar su ba. Mutanen da ke da raunin garkuwar jiki na iya kamuwa da pneumonia, tarin fuka, da cututtukan fata cikin sauƙi.
Cututtukan autoimmune
Cututtukan autoimmune suna faruwa ne idan garkuwar jiki ta kai hari ga sassan jiki da kanta, tana ganin sassan jiki kamar ƙwayoyin cuta. Wannan na jawo kumburi, zafi, da matsaloli ga gaɓoɓin da abin ya shafa.
Misali, a Rheumatoid arthritis, garkuwar jiki na kai hari ga gwiwowin mutum, ta haifar da kumburi da zafi. A cutar lupus, garkuwar jiki na kai hari ga fata, gaɓoɓin ciki, da wasu sassa na jiki. Haka kuma, a cutar Type 1 diabetes, garkuwar jiki na lalata ƙwayar halittar da ke samar da sinadarin insulin a cikin hanta, wanda hakan ke jawo matsala wajen sarrafa sinadarin glucose a jiki.

Allergies
Allergies suna faruwa ne idan garkuwar jiki ta yi tsanani wajen karɓar abubuwa marasa cutarwa kamar pollen, abinci. Wannan tsanani yana haifar da alamomi kamar tari, atishawa, kumburin fata, ko matsalar numfashi a lokuta masu tsanani.
Misali, mutumin da ke da allergy ga pollen na iya jin atishawa, tari, da zufa yayin bazara lokacin da furannin itatuwa ke girma. Wannan yana nuna cewa koda abubuwa marasa cutarwa suna iya rikitar da garkuwar jiki idan ba ta daidaita yadda ya kamata.
Hanyoyin kula da lafiyar garkuwar jiki
Abinci mai gina jiki
Abinci na ɗaya daga cikin abubuwan da suka fi tasiri wajen ƙarfafa garkuwar jiki. Cin abinci mai ɗauke da sinadaran gina jiki kamar bitamin C, bitamin D, da zinc yana taimakawa wajen kara yawan ƙwayoyin garkuwa da inganta aikinsu. Misali, ‘ya’yan itatuwa kamar lemu da kankana, kayan marmari kamar karas da broccoli, kifi mai maiƙo, da wake suna taimakawa garkuwar jiki wajen aiki yadda ya kamata. Waɗannan abinci suna taimakawa wajen samar da antibodies da sauran sinadaran garkuwar jiki masu kare jiki daga cututtuka.
Motsa jiki
Motsa jiki na taimakawa wajen karfafa garkuwar jiki ta hanyoyi daban-daban. Yana kara yawan ƙwayoyin jini masu kare jiki, inganta zagayawar jini, da kuma taimaka wa sinadaran garkuwar jiki su isa sassan jiki cikin sauri. Haka kuma, motsa jiki na rage damuwa, wanda ke da alaƙa da ƙarfafa garkuwar jiki. Misali, mutane da ke yin tafiya ko wasu nau’ikan motsa jiki na yau da kullum suna da karfin garkuwar jiki fiye da waɗanda ba sa motsa jiki.

Barci isasshe
Barci mai kyau yana taka muhimmiyar rawa wajen kula da garkuwar jiki. Yana taimakawa wajen sabunta ƙwayoyin jini da sauran sassan garkuwar jiki, sannan yana rage yawan sinadaran damuwa a jiki da ke rage karfin garkuwar jiki. Rashin barci na iya sa mutum ya fi kamuwa da cututtuka saboda garkuwar jiki ba ta samun lokaci na sabuntuwa.
Rigakafi
Alluran rigakafi suna koyar da garkuwar jiki yadda za ta gane wasu ƙwayoyin cuta kafin su jawo matsala. Wannan yana rage yiwuwar kamuwa da cututtuka kamar measles, polio, da hepatitis. Rigakafi yana aiki ne ta hanyar samar da antibodies da memory cells a jiki, don haka idan mutum ya sake haɗuwar da cutar, garkuwar jiki za ta karɓa cikin sauri, ta kare lafiya.
Guje wa hayaƙi da guba
Gurbatacciyar iska, taba sigari, da wasu sinadarai masu guba na rage ƙarfin garkuwar jiki. Guje wa shan hayaki, zama a wuraren da iska ba ta gurbata, da kuma rage amfani da sinadarai masu guba na taimakawa wajen kare garkuwar jiki da lafiyar jiki gabaɗaya. Misali, mutane masu nisantar hayaki suna da ƙarfin garkuwar jiki fiye da waɗanda ke shan taba ko zama a wuraren da iska ta gurbata sosai.
Manazarta
Department of Health & Human Services. (n.d.). Immune system explained. Better Health Channel.
KidsHealth (n.d.). All about the immune system. Nemours KidsHealth.
Professional, C. C. M. (2025, December 22). Immune system. Cleveland Clinic.
Sabir, S., & Jan, A. (2025, December 1). Physiology, immune response. StatPearls – NCBI Bookshelf.
Sharuɗɗan Editoci
Duk maƙalun da ku ka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta tare da sa idon kwamitin ba da shawara na ƙwararru. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.
Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.
