Skip to content

Google Drive

Google Drive manhaja ce ta kyauta daga kamfanin Google, wacce ke ba da damar adana fayil-fayil a yanar gizo da samun damar bincikar su ko amfani da su a ko’ina mutum ya kasance. Google Drive tana ba da damar yin amfani da aikace-aikace da manhajojin yanar gizo kyauta don ƙirƙirar rubutu ko lissafi ko tsara lakcoci da sauran su.

Babban aikin wannan manhaja shi ne ɗaukar wasu fayil-fayil ko bayanai daga rumbun kwamfuta zuwa can ma’ajiyar ta yanar gizo. Ma’ajiyar wacce ake kira da (cloud storage), tana aiki ne ta hanyar loda fayil-fayil zuwa sararin gajimaren. Wannan na taimakawa ma’ajiyar kwamfuta ta samu sukuni da sarari.

Babu shakka ma’ajiyar yanar gizo ta sararin gajimare tana da alfanu mai yawa fiye da ma’ajiya ta kwamfuta ko kuma ta memory. Lokacin da fayil-fayil ke cikin sararin gajimare, ana iya bincikar su ko yin amfani da su daga duk inda aka kasance tare da kowace na’ura mai hawa intanet. Bugu da ƙari, ana iya tura su zuwa ga wasu mutane.

Tambarin Google Drive daga Gaurav kachariya a shafin Medium

Idan mutum yana da asusun Google, to kai tsaye yana da ma’ajiyar Google Drive, ma. Yin rajista kawai don mallakar asusun yana ba wa mutum damar samun ma’ajiya mai zurfin 15GB don yin ajiya kyauta.

Baya ga adadin ma’ajiyar da ake samu a kyauta, akwai kuma tsarin da ake biyan kuɗi don samun wadataccen sarari. Abin burgewar ma shi ne, farashin Google Drive yana da sauƙi, kuma yana iya ɗaukar duk wani abin da ake buƙatar ajiyewa. Idan akwai buƙatar ƙara zurfin sararin ma’ajiyar, za a iya samun 100GB a kan dala 1.99 kawai a tsawon wata guda. Idan buƙatar ta fi haka ma, ana  iya mallakar sarari mai zurfin 2TB a kan farashi dala 9.99 duk wata.

Kamfanin Google ya kirkiri manhajar Google Drive ne don ma’ajiyar hotuna da kuma adana abubuwan da aka turo ta saƙon imel daga Gmail da ayyukan da ake yi a Google Workspace, waɗanda za su iya ɗaukar sarari da yawa.

Dalilan amfani da Google Drive

Google Drive ita ce manhaja ɗaya tilo kuma shahararriya da ke samar da sararin ajiye-ajiyen fayil-fayil ta amfani da fasahar ma’ajiyar yanar gizo wato (cloud storage). Idan har mutum bai taɓa amfani da ma’ajiyar yanar gizo ba, misali Google Drive a baya ba, to wannan maƙalar za ta fayyace masa fa’idojin adana fayil-fayil a wannan nutsattsiyar ma’ajiya. Saboda akwai damar bincika tare da amfani da fayil-fayil daga kowace kwamfuta matuƙar tana iya hawa intanet.

Ƙirƙirar fayil-fayil a Google Drive

Manhajar Google Drive, baya ga adana fayil-fayil kawai; tana kuma ba da damar ƙirƙira da rabawa da  sarrafa bayanai tare da kayan aikin ƙirkira. Misali, nau’ikan fayil-fayil da za a iya ƙirƙira suna kama da fayil-fayil da ake ƙirƙira da manhajojin kudin Microsoft Office daban-daban, kamar Microsoft Word ko Excel da sauran su. Ga jerin nau’ikan fayil-fayil da za a iya ƙirƙira a kan Google Drive kuma a tura su zuwa inda ake so:

Document

Don tsara rubutu kowane iri ne misali, wasiƙu da kasidu da sauran fayil-fayil na rubutu da ake yi da manhajar rubutu kamar Microsoft Word.

Spreadsheet

Don adanawa da tsara bayanai da ma yin lissafi, wadanda ake iya yi da taimakon manhaja kamar  Microsoft Excel.

Presentation

Don ƙirƙirar faya-fayan lakcoci ko tallace-tallace da ake amfani da manhajar  Microsoft PowerPoint.

Forms

Don ƙirƙirar fom da ake amfani da shi wajen tattarawa da tsara bayanan mutane

Drawing

Don ƙirƙirar zane-zane kowane iri ta amfani da kowane irin shapes

Yadda Google drive ke aiki

Wani masani na’urori da fasaha mai suna Kochovski, A. (2024), ya bayyana yadda manhajar Google drive take a aiki, a wata kafar yanar gizo ta Cloudwards. Babbar manufar Google Drive ita ce adana fayil-fayil da daidaita su zuwa kwamfuta. Ana iya amfani da shafin yanar gizon Drive don loda fayil-fayil da shirya su a yanar gizo. Bugu da ƙari, idan aka sauke manhajar Google Drive ta na’ura mai ƙwaƙwalwa ta kan tebur, za a iya amfani da babban fayil ɗin Drive a kan kwamfutar don ci gaba da daidaita mahimman fayil-fayil zuwa sararin gajimare da kuma tabbatar da an sabunta su yayin da ake aiki a kansu.

Google Drive ba kawai yana taimakawa don adana fayil-fayil ba ne, yana aiki a matsayin wata cibiya don sarrafa dukkan ayyukan da ake yi da manhajojin Google. Drive yana aiki tare da duk tsarin ƙa’idod’jin Google, kamar Google Workspace don aikace-aikacen ofis. Wannan yana nufin za a iya amfani da shi don ƙirƙirar fayil-fayil na Google Docs ko Google Forms ko Google Sheets (spreadsheet) don adana bayanai ko shirya lakcoci don gabatarwa ta amfani da Slides na Google.

Haka nan tana ɗaya daga cikin ma’ajiyar sararin gajimare mafi girman sarari da ke ba da damar tura kowane irin fayil, abin sha’awa shi ne damar turawar ta musamman ce, wato lokacin da ake tura fayil-fayil a Google Drive, za a iya ba da izini ga kowane mutumin da aka turawa da shi. Haka nan ana iya ba wa sauran masu amfani damar yin gyara (ƙari ko ragi) a fayil-fayil ɗin Google Docs, akwai kuma damar yin aiki tare da mutane sama da mutum 100 a kan kowane aiki ɗaya a Google Workspace.

Wannan yana nufin cewa idan aikin yana buƙatar haɗin gwiwar ta yanar gizo mai yawa, hakan na tabbata ta yin amfani da Google Drive, musamman idan ana buƙatar yin aiki tare a kan fayil-fayil na Google Docs da yawa.

Haka nan za a iya amfani da ma’ajiyar Google Drive don loda hotuna da bidiyo ta tsarin atomatik kamar yadda ake yi da manhajar Google photos.

Alaƙar Google Drive da Gmail

Asusun Gmail da Drive suna da alaƙa sosai ta tsarin karba da kuma baydrwa. Gmail yana amfani da Drive don adana abubuwan da aka turo cikin imel kamar hotuna da sauti har ma da da bidiyo. Haka nan, Drive yana amfani da Gmail don raba fayil-fayil.

Google drive da Gmail suna da alaƙa ta kusa. Hoto: Zapier

Gmail kuma yana ba da zaɓin ɗauko abubuwan da suke cikin ma’ajiyar  Google Drive zuwa cikin akwatin rubuta sakon imel.

Tsaron sirrin

Sai dai wani ƙalubalen wannan ma’ajiya shi ne ba ta cikakken amincin sirri ga abubuwan da ake adanawa. Domin kuwa Google yana iya bincika fayil-fayil da aka adana don samun bayanai, waɗanda yake amfani da su don ƙirƙirar bayanan tallace-tallace a shafukan masu amfani da shi.

Siffofin Google Drive

Wannan ma’ajiya tana da sauƙi kuma cike take da kayan aiki masu nagarta, hakan ya sanya ta zama ɗaya daga cikin manhajojin Google da aka fi amfani da su. Daga cikin manyan siffofin wannan manhaja a cewar, Urrutia, D. (2023) daga shafin Arimetrics, akwai:

File Storage

Akwai sarari mai zurfin 15GB na ajiya kyauta, kuma za a iya faɗaɗa shi har zuwa 200TB a kan farashi daban-daban. Tana ba da damar ɗaukar kowane nau’in fayil-fayil: hotuna ko bidiyo ko saƙonnin rubutu da sauransu. Haka nan tana ba da damar haɗa waɗannan fayil-fayil gabaɗaya tare da wasu manhajojin Google kyauta kamar Gmail, Google photos ko Chromebook.

Document creation

Tare da zaɓin Google Docs, da ya kasance a cikin manhajar Drive, za a iya ƙirƙirar fayil-fayil na rubutu, lakcoci da spreadsheet (don adana bayanai da yin lissafi). Haka nan ta haɗa da kayan aiki don ƙirƙira fom ɗin yanar gizo da sauran su.

Connectivity

An tsara Google Drive ta yadda za a iya raba fayil-fayil cikin sauƙi ga duk wanda ake so, ba da damar gyara rubutu tsakanin mutane da yawa da samun damar buɗe bayanan a kan kowace na’ura da ke hawa intanet, ko  kwamfutar kan tebur ko wayar hannu ko kwamfutar tafi-da-gidanka.

Integrated apps

Baya ga kayan aikin da aka samar don ƙirƙirar rubutu da bayanai, wannan manhaja tana da ɗaruruwan kayan aikace-aikace iri-iri masu sauƙi, waɗanda za a iya samu a shafin yanar gizon Chrome.

Fa’idojin amfani da Google Drive

Ogla Weis (2024) ta zayyana muhimmanci da matsalolin ma’ajiyar Google drive shafin CloudMounter.

  • Ana amfani da manhajar a na’urori daban-daban
  • Manhajar na ba da damar ƙirƙira da tsara fayil-fayil iri-iri
  • Damar bincika da duba abubuwan da aka ajiye cikin sauri
  • Sauƙin tura abubuwa zuwa ga abokan hulɗa
  • Wurin ajiya na kyauta mai zurfin sararin 15 GB

Matsalolin amfani da Google Drive

  • Ƙalubalen tsaro ga bayanai da abubuwan da ake ajiyewa
  • Manhajar tana buƙatar fasahar sadarwa ta intanet kafin ta yi amfani
  • Tana da iyakacin girman fayil din da za a iya lodawa a rana ɗaya
  • Ƙayyade girma ko nauyin fayil ɗin da za a iya ɗorawa
  • Matsololin ɗorawa da sauke fayil-fayil
  • Google yana binciken bayanan da aka adana a cikin ma’ajiyar.

Manazarta

Weis, O. (2024, April 4). Pros and Cons of Google Drive – Everything you need to know. CloudMounter

Urrutia, D. (2023, October 24). What is Google Drive – Definition, meaning and examples. Arimetrics.

Kochovski, A. (2024, August 2). What Is Google Drive and How Does it Work? A 2024 Step-by-Step Guide. Cloudwards.

Was this article helpful?
YesNo

You cannot copy content of this page

×