Skip to content

Hankaka

Pied Crow sunan tsuntsun hankaka ke nan da Turanci. Kalmar pied tana nufin launuka biyu ko fiye, ke nan hakan na nuna cewa hankaka yana da launuka biyu wato baƙi da fari kamar yadda ake ganin shi.

Kamar yadda sunan sa ya nuna, yana da launin baƙi mai sheki daga wuyansa baƙin na katsewa da wani babban yanki na farin gashi wanda ya yaɗu ta jikin fuka-fuki daga kafaɗu har zuwa ƙasan ƙirjinsa. Idanuwansa launin maroon ne mai duhu da kuma ƙafafu. Dukkan jinsin biyu, mace da namiji suna kama da juna kuma ba su da bambance-bambance a cikin nau’insu.

Wuraren da tsuntsun ke samuwa

Wannan tsuntsu yana wanzuwa a mafi yawan yankin kudu da hamadar sahara, amma babu shi, ko kuma ba kasafai ba a kan same shi a dazuzzukan tsakiya da yammaci ba. Sun zama mafi yawa, adadin yawansu na ƙaruwa musamman a yankin Karoo na Afirka ta Kudu.

Bambanci tsakanin kasancewar su da yawa a yankin da ake noman alkama a arewacin Cape Town (Swartland) da ƙarancinsu a yankin noman alkama da ke gabashin Cape Town (Overberg) yana da ban mamaki. Ana tsammanin wannan bambanci yana da alaƙa da abinci, amma ba a bayyana hakan. A zahiri gabaɗayan tsarin yaɗuwar tsuntsayen ya kasance abu mai wuyar warwarewa. Awai wuraren da ko wanne ɗaya daga cikin nau’ika biyu ya fi rinjaye, wuraren da suke samuwa, da wuraren da ba a samu.

Muhallin zaman hankaka

Hankaka sun fi son buɗaɗɗen gandun daji na yankin savanna, ciyawar daji, da ciyayi a warwatse da bishiyoyi. Suna ƙara zama ruwan dare a filayen noma, birane, da kewayen birni. Suna daidaituwa sosai da sauye-sauyen yanayi kuma ba sa damuwa da neman abinci a ƙauyuka, garuruwa, da birane, galibi suna ziyartar wuraren sharar gida da kwantena.

Halaye da dabi’un hankaka

Hankaka tsuntsu ne mai cin komai, wato sukan ci nama da tsirrai. Sun fi ci daga kayan shuke-shuke irin su ‘ya’yan itace da iri, amma kuma suna cin dabbobi masu rarrafe (kamar kunkuru), ƙananan dabbobi masu shayarwa, kifi, ƙwari da sauran tsuntsaye. Yawancin lokaci ana ganin hankaka a bibiyu ko ƙananan rukunai, amma suna iya taruwa da yawa a wuraren jama’a ko a wuraren abinci masu kyau, misali, kan juji da manyan gawawwakin dabbobi masu shayarwa.

A lokacin saduwar jima’i, mace da namiji suna gina gida, wanda babbar sheƙa ce da aka yi da tsinkaye, wani lokacin har da guntuwar waya. Sannan suna lulluɓe gidan da gashin dabbobi ko busassun kashinsu ko tsumma.

Hankaka tsuntsaye ne masu yawa kuma yawanci suna cin abinci su bibiyu ko a ƙananan rukunai, amma kuma suna taruwa a cikin manyan garkuna inda abinci ke da yawa. Suna kwana a gidajen jama’a a wuraren shakatawa na birane a cikin manyan bishiyoyi tare da ɗaruruwan wasu tsuntsayen. Wannan tsuntsun an san shi da yin farautar manyan tsuntsaye: ƙananan tsuntsayen ganima har zuwa manyan ungulu. Ƙila ƙanƙan tsuntsaye ne za su yi shi da kansa. Haka nan suna yin fashin tsuntsayen teku don samun abinci. Wannan nau’in galibi suna zaune a cikin babban kewayensu.

Sukan yi ƙaura ko matsawa daga waje zuwa waje a tsarin shekara-shekara, ko a kowane lokaci hakan ya danganta da muhallansu. Wani lokaci kaurar na kasancewa bayan haifuwa. Manyan dai sukan zauna a waje, yayin da matasan ke ƙaura zuwa sabbin yankuna. Hankaka, kamar sauran tsuntsaye da yawa, yana yin sautin “kraaak” na yau da kullun, ko gajerun sautin “krow” ko “rrawrr”. Haka nan yana yin sautukan “tarrrrrh” ko “torrrrrh”. Sauran sautukan da hanci ne, da makogwaro, kuma sau da yawa yakan motsa kai da wutsiya a lokaci guda.

Abincin hankaka

Hankaka tsuntsaye ne masu cin tsirrai da kuma nama, suna cin dabbobi nau’in invertebrates yawa, wato marasa ƙashin baya  kamar ƙwari, gizo-gizo, da kuma ƙananan vertebrates (masu ƙashin baya) ciki har da ɓeraye, tsuntsaye da ƙwai, kadangaru, kwaɗi, da kifaye. Suna iya kama ƙananan tsuntsaye da jemagu a yayin da duke tashi. Har ila yau hankaka na yin sintiri a wuraren da ake zubar da shara da kuma yakan yi rangadi domin tsintar matattun dabbobi a gefen hanya. Suna kuma cin kayan shuke-shuke irin su iri, saiwoyi, ’ya’yan itace, dabino, shinkafa, da dankali.

Tsarin haihuwar hankaka

Suna yin kwarkwasa ko zawarci a farkon lokacin barbara. Namiji yana matsawa kusa da mace, tare da baza gashinsa  na wuya. Sannan ya sunkuya yana yin wani nau’in sauti mai nuna yana kiran macen. A yayin amsa kiran, macen na miƙa kanta, tana tsugunne tare da girgiza fuka-fukanta, wanda hakan wani yanayi ne na kiran namiji ya yi jima’i da ita. Lokacin yin jima’in ya bambanta dangane da iyaka da kuma damina. Waɗannan tsuntsayen suna keɓe a ɗaiɗaiku ne cikin sheƙarsu. Duka manya hankaka suna gina gida, wato wata babbar sheƙa wadda aka gina daga sanduna da saiwoyi. Cikinta mai zurfi wanda aka lailaye tare da laka, taki, gashin dabbobi, ciyawa, kirtani da sauran abubuwa. Sau da yawa suna gidaje masu tsayi a cikin kogunan bishiyoyi, ko saman turken tarho, ko dogon gini, amma da wuya su gina a kan tudu. Suna yin ƙwai 4 zuwa 5 daga watan Satumba zuwa Nuwamba. Dukkan jinsinan biyu suna yin ƙyanƙyasa amma mace tana yin mafi yawa a tsawon kwanaki 18 zuwa 19. Iyaye suna ciyar da kuma kula da jariran, waɗanda ke zama a cikin gida har na kimanin kwanaki 35 zuwa 45.

Barazanar da hankaka ke fuskanta

Hankaka yana da tarin yawa kuma yana iya kasancewa mai yawa a cikin gidajensu. A halin yanzu ba sa fuskantar wata barazana.

Yawan adadin hankaka

A cewar wata hukumar kula da tsuntsaye, hankaka ya yaɗu kuma ya zama gama gari a ko’ina cikin yankin da ya wanzu, amma babu cikakken adadin yawansu da aka samu. A halin yanzu, an bayyana wannan nau’in tsuntsaye a matsayin mafi ƙarancin damuwa kuma alƙaluman yawansu a yau sun tsaya ba sa raguwa.

Hankaka a gonaki

Hankaka suna da mahimmanci kyakkyawa da akasin haka. Saboda nau’in abincin da suke ci, suna iya lalata gonaki da amfanin gona. A gefe guda kuma, suna cin mushen dabbobin da suka mutu, don haka suna taimakawa ba kawai ga mutane ba, har ma da dukkan muhallan da suke rayuwa a ciki.

Abubuwan sha’awa game da hankaka

  • Hankaka halittu ne masu wayo. Alal misali, za su taɓa ƙwan tsuntsaye a kan reshe don su farfashe su. Haka kuma sukan zubar da gyaɗa a kan titi ta yadda motoci za su tattake, su kuma su riƙa ɗaukar ƙwayar gyaɗar suna ci bayan ɓawon ya cire. Haka zalika suna watsa duwatsu a kan ƙwayayen jimina don su fashe.
  • Ƙwararru ne wajen bin gobarar daji don cin kwari, kuma suna bin kunyar gonaki don cin dabbobi masu rarrafe.
  • Hankaka ba su da tsoro sosai, musamman idan suna bin mikiya nau’in golden. Sukan jefa duwatsu, itatuwa, a kan mafarauta ko mutane.
  • Har ila yau, hankaka dabbobi ne masu tada hankali, suna bayyana jin yunwa ta hanyar mamaya tare da kuka mai ƙarfin sauti. Suna nuna farinciki, fushi, da baƙinciki.
  • Kusan dukkan nau’ikan hankaka na gidan suna amfani da wasu abubuwan a matsayin kayan aiki. Hankaka na iya koyan yaren ɗan’adam.
  • Ana ɗaukar hankaka a matsayin tsuntsu mai waƙa kuma yana da tarin waƙoƙin waƙa. Kamar mutane, gwargwadon yadda waƙar take daɗaɗawa, gwargwadon kwantar da hankali da tasirinta. An koyawa wasu hankaka rera wakokin wasan kwaikwayo.
  • Hankaka suna da kyakkyawar ƙwaƙwalwa kuma suna iya ɓoye abinci a wurare da yawa, su motsa abincin sosai, kuma suna iya tuna daidai inda yake. Saboda girmansa, hankaka yana da mafi girman ƙwaƙwalwar duk tsuntsaye baya ga wasu nau’ikan aku ba su da ita. Rabon ƙwaƙwalwa da  gangar jiki iri daya ne da na gwaggon biri haka zalika da na mutane.

Manazarta

Amar, A., & Cunningham, S. (n.d.). How climate change is causing pied crow numbers to soar. The Conversation.

Biodiversity and Development Institute. (2024, June 5). Pied Crow (Corvus albus). BDI.

Britannica Kids (n.d).  pied crow. Britannica Kids.

*****

Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.

Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.

Maƙalar ta amfanar?
EAa

You cannot copy content of this page

×