Cutar hawan jini dai wata cuta ce da ta zama annoba cikin al’umma kula da yadda ta yawaita da kuma illolinta ga rayuwa wadda ya kamu da ita. cutar hawan jini dai kamar yadda masana suka tabbatar cuta ce da ke da matukar wuyar sha’ani ganin yanayinta da kuma hanyoyin magance ta.
Ana iya sanin ko ana dauke da cutar hawan jini ne ko sabanin haka yayin da aka ziyararci asibiti don gwajin cutar. Alamomin cutar hawan jini sun hada da; yawan ciwon kai, yawan faduwar gaba ko tsinkewar zuciya, raguwar gani ko gani garara-garara. Illolin cutar hawan jini sun hada da:
- Tana iya kawo shanyewar sassan jiki
- Tana iya haifar da ciwon koda wanda zai iya janyowa ta daina aiki kwata-kwata
- Takan iya haddasa makantar Ido har abada.
- Takan haifar da ciwon zuciya, da dai sauransu.
Abubuwan da suke iya haddasa cutar hawan jini:
- Rashin motsa jiki
- Yawan cin gishiri a abinci ko abin sha
- Yawan cin kitse
- Shan giya ko wacce iri
- Yawan kiba
Abubuwan dake rage barazanar kamuwa da cutar hawan jini:
- Yawaita cin kayan marmari irin su; kankana, ayaba, gwanda, abarba, lemu, yalo, karas, alayyahu, zogale, rama, da sauran danginsu.
- Daina cin gishiri
- Daina shan giya
- Yawaita motsa jiki
- Rage cin kitse
- Ziyarar asibiti lokaci zuwa lokaci don duba lafiya