Skip to content

Hukunce-hukuncen ittikafi

Ma’anar ittikafi: Ittikafi shine lizimtar masallaci don bautawa Allah Madaukakin Sarki.

Hukuncinsa: Sunnah ne, ba ya wajaba sai ga wanda ya yi bakance akansa. Dalilin haka ya tabbata daga Al-Kur’ani da Hadisai da ijma’in malamai.

Dalili daga Al-Kur’ani

Allah Ya ce: “Kuma mun yi wasiyya ga Ibrahim da Isma’il cewa su tsarkake daki na, saboda masu dawafi da masu ittikafi da masu ruku’i da sujjada” (Suratul Bakara, aya ta 125). Allah Ya kuma cewa: “Kuma kada ku rungume su alhali kuna masu ittikafi a cikin masallatai” (Suratul Bakara, aya ta 187).

Dalili daga Hadisi

An karbo daga Nana Aisha (Allah Ya yarda da ita), ta ce: “Lallai Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya kasance yana yin ittikafin kwanaki goman karshe na Ramadan, har Allah ya karbi rayuwarsa. Sa’an nan matansa suka yi ittikafi bayansa“. Buhari da Muslim ne suka rawaito wannan hadisi.

Ijma’in malamai

Imamun Nawawi yace: “Ittikafi sunnah ne, baya wajaba sai da bakance da ijma’i”. Ittikafi sunnah ne ga maza da mata, saboda matan Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi)  sun yi ittikafi tare da shi a rayuwarsa, kuma sun yi bayan mutuwarsa.

Shin a watan Ramadan ne kadai ake yin Ittikafi?

Ittikafi sunnah ne a kowani lokaci, amma tattaran maluma sun tafi akan yin ittikafi a watan Ramadan ya fi lada da falala. Haka nan falalar ta fi yawa a kwana goman karshe na Ramadan. Saboda Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya dawwama akan yin ittikafin kwanaki goman karshe na Ramadan, har Allah ya karbi rayuwarsa, kamar yadda Nana Aisha (Allah Ya yarda da ita) ta rawaito.

Karancin lokacin yin ittikafi

Malamai sun yi sabani dangane da karancin lokacin yin ittikafi. Amma magana mafi rinjaye ita ce, karanci lokacin ittikafi shine wuni da dare, saboda babu dalilin da ya iyakance yawan kwanakin yin ittikafi.

Yaushe ake shiga ittikafi, kuma yaushe ake fita?

Idan mutum ya yi niyyar yin ittikafi na kwanaki goman karshen Ramadan, to magana ma fi rinjaye ta malamai ita ce; zai shiga kafin faduwar rana na wunin ashirin na watan Ramadan.  Kuma zai fito daga Ittikafinsa ne da zaran rana ta fadi a wunin karshe na watan Ramadan. Amma wasu malamai sun so ga mai ittikafi ya fita lokacin fita zuwa idi ranar sallah.

Sharuddan ittikafi:

  1. Musulunci: Dole mai ittikafi ya zama musulmi, saboda Allah ba ya karban ibadar kafuri.
  2. Hankali: Dole mai ittikafi ya zama mai hankali, saboda mahaukaci babu taklifi a kansa.
  3. Balaga: dole mai ittikafi ya zama baligi, saboda yaro babu taklifi akansa. An karbo daga Aliyu Bin Abi Dalib (Allah Ya yarda da shi), Lalle Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “An dauke alkalami akan mutane uku; daga mai bacci har sai ya farka, da mahaukaci har sai ya warke, da kuma karamin yaro har sai ya balaga“. Imam Ahmad da Abu Dawud da Tirmizi da Nisa’I da Ibn Majah ne suka rawaito hadisin.
  4. Niyya: Mai ittikafi zai yi niyyar lizimtar masallaci don yin ibada. Niyya sharadi ne a kowace ibada. Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Lallai ayyuka (suna karbuwa ne) da niyya, kuma lallai kowani mutum yana samun sakamakon abinda yayi niyya“. Buhari da muslim ne suka rawaito shi.
  5. Ya kasance a masallaci: Wasu malamai sun shardanta ya zama a masallacin juma’a, in ya zama ranar juma’a zata shiga cikin kwanakin ittikafin.

Sharhi:

Malamai sun yi sabani kan shardanta azumi ga mai yi ittikafi. Amma magana mafi rinjaye ita ce: mustahabbi ne yin azumi ga mai ittikafi, sai dai in ya zama a cikin watan Ramadan ne yake yin ittikafinsa, to nan kam wajibi ne yayi azumi.

Abubuwan da suke bata ittikafi:

  1. Jima’i: Malamai sun hadu akan idan mai ittikafi yayi jima’i, to ittikafinsa ya lalace. Saboda fadin Allah Madaukakin Sarki: “Kuma kada kuyi jima’i da su, alhali kuna masu ittikafi a cikin masallatai” (Suratul Bakara, aya ta 187). Ibn Abbas (Allah Ya yarda shi) ya ce: “Idan mai ittikafi ya yi jima’i, to ittikafinsa ya lalace, sai ya sake“. Ibn Abi Shaibah ne ya rawaito shi.
  2. Rungunar mace ta hanyar sha’awa.
  3. Fitowar maniyyi ta hanyar rungumar mace, ko ta hanyar maimaita kallonta, ko ta hanyar wasa da al’aura.
  4. Zuwan jinin haila da na biki (na haihuwa)
  5. Gushewar hankali ta hanyar shan abin maye
  6. Ridda, wato barin Musulunci
  7. Yin niyyar yanke ittikafin.
  8. Fita daga masallaci ba don bukatar hakan ba.

Laduban mai ittikafi:

  1. Tsarkake niyya. Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Allah ba ya karban wani aiki, sai wanda aka tsarkake niyya, kuma aka nemi yardan Allah da shi“. Nisa’i ne ya rawito shi.
  2. Mai ittikafi ya yi kokarin wajen yin ayyukan ibada a cikin wadannan darerrakin goman karshe na Ramadan. Saboda a cikinsu akwai daren lailatul kadiri wanda ya fi dare dubu falala.
  3. Mai ittikafi ya yi kokarin kauracewa abinda ba zai amfane shi ba, ya shagalta da abinda ya kawo shi.
  4. Ya yi kokari ya kauracewa sabo, kuma ya nesanci jayayya da gulma da rada da sauran ayyukan sabo.
  5. Kada ittikafin mai ittikafi ya zama wata dama ce ta haduwa da abokai a masallaci don hirar duniya. Saboda manufar ittikafi ita ce barin shagulgular duniya, da kuma lizimtar masallaci don bautawa Allah Madaukakin Sarki.
  6. Ya halatta mai ittikafi ya ci abinci ko abin sha a cikin masallaci.
  7. Ya halatta mai ittikafi yayi bacci a cikin masallaci.
  8. Ya halatta mai ittikafi ya ware wurin da zai yi ittikafinsa a cikin masallaci.
  9. Saka tufafi mai kyau, da kuma saka turare.
  10. Wanke kai da kuma gyara gashi, da aske farshe, da aske gashin gaba da na hammata da sauran abubuwan tsabtace jiki.
  11. Zuwa duba mara lafiya da kuma sallar jana’iza in ya kasance a cikin masallacin da yake yin ittikafi ne.
  12. Ya halatta dangin mai ittikafi su ziyarce shi a masallacin da yake yin ittikafinsa, saboda matan Manzon Allah S.A.W sun kasance suna ziyartarsa a masallaci.
  13. Ya halatta a daura wa mai ittikafi aure a cikin masallaci, ko ya halarci auren wani, ko kiran sallah ko tada ikama, ko yi wa wani ta’aziyya ko taya murna, duk in a cikin masallacin da yake yin ittikafi ne.

Wasu daga kurakuran masu ittikafi:

  1. Yawan bacci safe da rana a lokacin ittikafi.
  2. Yawan fita daga masallaci ba tare da bukatar hakan ba.
  3. Yawan amfani da waya, da kuma shagaltuwa da kafofin sada zumunta.
  4. Yawan ziyarce-ziyance tsakanin masu ittikafi, ko kuma daga mutane wasu daban.
  5. Wuce gona da irin wajen kawo nau’uka na abinci masu yawa.
  6. Yawan hira mara amfani.
  7. Wasu daga cikin masu ittikafi na zaton cewa ittikafi na nufin lizimtar masallaci ne kawai, ba tare da yawaita yin ayyukan ibada ba.
  8. Wasu masu ittikafi na zaton cewa baya halatta ga mai ittikafi ya kula da tsabta.
  9. Akwai wasu suna ittikafi, alhali iyalansu na tsananin bukatar su, watakila bai bar musu abinda zasu ci ba, ko ya zama bai nemi izinin iyayensu.

Allah Ya bamu ladan ayyukanmu kuma Ya yafe mana kura-kuranmu, amin.

Was this article helpful?
YesNo

You cannot copy content of this page

×