Skip to content

Jemage

Jemagu yawanci suna da matsakaicin tsawon rayuwa har zuwa shekaru 30 a cikin daji. Yayin da yawancin nau’in jemagu ke da tsawon rayuwa a kasa da shekaru 20, binciken kimiyya ya tabbatar da cewa nau’in-nau’i shida na iya rayuwa fiye da shekaru 30.

Matsakaicin lokacin da jemagu kan ɗauka suna rayuwa yakan kai har zuwa shekaru 20.

Nau’ikan jemagu

Akwai kusan nau’ikan jemagu har kusan guda 1,400 da ake samu a duk faɗin duniya. Ban da sashen hamada mai tsananin da kuma wuraren da ke da iyaka da hamadar, ana iya samun jemagu kusan a ko’ina a duniya. An kasa jemagu zuwa rukuni biyu: Megachiroptera (wato manyan jemagu na ‘ya’yan itace na Tsohuwar Duniya) da Microchiroptera (kananan jemagu na ‘ya’yan Old World).

Bayyanar jemagu

Shaidu sun tabbatar da dabbobi masu shayarwa masu tashi kamar jemagu sun bayyana tun a zamanin Eocene Epoch, kimanin shekaru miliyan 50 da suka wuce; an samu tarihin burbushin halittar jemage. Ta yin la’akari da kamanceceniyar ƙasusuwa da hakora, yawancin masana sun yarda cewa kakannin jemagu watakila ƙwari da ke cin dabbobi masu shayarwa, suna kuma zaune a cikin kogunan bishiyoyi. Jemagu ba ɓeraye ba ne kuma ba su da alaƙa da su.

Yadda jemagu suke tashi

Jemage na musamman ne, duk da cewa suna da alaƙa da halayen dukkan dabbobi masu shayarwa, kamar gashi, tsarin zafin jiki, damar ɗaukar ‘ya’yansu da shayar da su. Jemagu ne kawai dabbobi masu shayarwa da ke iya tashi sama.

Tsarin tantanin fuka-fukai da tsarin ƙasusuwa da daidaituwar tsokoki suna ba wa jemagu kuzarin da ake bukata don kama ƙwari, suna shawagi a sama da sauka a kan furanni, ko kuma guje wa hadari cikin sauri. Fita daga sassan jiki da haɗa hannuwa, ƙafafu, da wutsiya su ne siraran tantanin fata guda biyu masu ɗauke da hanyoyin jini da jijiyoyi, waɗanda ke ba wa fuka-fukan kuzari.

Kasusuwan hannu da na yatsu huɗu ba du da nauyi, sirara ne masu tsayi suna tallafawa, bazawa, da sarrafa tantanin fuka-fukan. Ba kamar sauran dabbobi masu shayarwa ba, gaɓoɓin baya suna a matsayin gwiwoyi, yayin da ƙasan ƙafafun suke fuskantar gaba. Yatsunsu suna da faratu waɗanda ke taimakawa wajen kamawa da kuma rataye kai ƙasa a wajen hutawa na jemage na yau da kullun.

Yawancin tsokokin jemagu da ke sarrafa kadawar fuka-fukai suna makale ne a kafada, ba kamar tsuntsaye ba, wadanda tsokarsu ke ɗaure da ƙashin hakarkarin. A jikin jemagu, tsoka ɗaya ce kawai ke manne da ƙashin ƙirji, kasusuwan hakarkari kuma suna baje.

Shin jemage zai iya iyo a ruwa?

Akwai bayanan kimiyya ƙalilan game da wannan batu, la’akari da masana dabi’ar halittu a wannan fanni da alama ya goyi bayan gaskiyar cewa wasu jemagu na yin iyo a cikin yanayi mai ma’ana amma ba ya cikin yanayin halayensu na yau da kullun. Misali, dawakai masu tashi, galibi mazauna tsibirin, na iya yin tafiya mai nisa don samun abinci. Saukowa tilas ko faɗuwar ruwa don tattara ‘ya’yan itace waɗanda suka faɗo kuma suka sha iyo a can na iya buƙatar yin iyo ba zato ba tsammani.

Salon rayuwar jemagu

Ga mutane, lokacin yini shi ne lokacin aiki, neman abinci da sauran su. Ga jemagu kuwa, wannan lokaci ne da suke barci da hutawa a wani ɓoyayyen waje. Idan dare ya gabato, aikin jemagu yana farawa; sai shiga yawo a cikin kogunan nasu daga ƙarshe fito don neman abinci. Bayan sun ci tsawon awa daya ko biyu za su iya sake hutawa, sannan su ci abinci a karo na biyu kafin gari ya waye.

A cikin nau’ika da yawa, maza da mata suna tasowa tare su rabu amma ban da lokacin da barbara. A cikin nau’i masu yin ƙaura daga waje zuwa waje, barbarar tana faruwa a lokacin kaka da hunturu. Mace tana adana maniyyi har zuwa bazara lokacin da ƙwai ya samu a jikinta. A watan Mayu ko Yuni, mata suna taruwa a manyan wurare domin haihuwa. Yawancin nau’ikan suna ɗaukar cikin ɗa guda ɗaya a kowace, amma wasu na iya samun biyu, uku, ko ma huɗu. Macen takan rataye kanta a sama yayin haihuwa, ƙafafu ne farkon gaɓar da ke fara fitowa. Bayan ta haihu sai ta ɗauke jariri don sauya masa wajen da ya dace. Jaririn zai fara girma, yana rarrafe zuwa ga nonon uwa, ya manne da kansa yana sha. Da maraice lokacin da uwa ke neman abinci, tana iyawa a cikin ‘yan kwanaki na farko, ta ɗauki jaririn su fita tare. Daga baya jaririn zai riƙa zama a kogo, yana manne da bango ko rufin kogon. Mahaifiyar na iya komawa sau da yawa a cikin dare don ciyar da shi.

Tsawon lokacin rayuwar jemagu

Matsakaicin lokacin da jemage kan ɗauka suna rayuwa yakan kai har zuwa shekaru 20, amma wasu nau’ikan jemagu guda shida na iya rayuwa har tsawon shekaru 30.

Rayuwar jemagu yawanci ta kai shekaru 30 amma idan a cikin daji suke, kasancewar babu takurawa idan aka kwatanta da cikin mutane. Duk da cewa yawancin nau’in jemagu ba su wuce shekaru 20 ba, amma masana kimiyya sun tabbatar da nau’ika guda shida a cikin jemagun da ke rayuwa fiye da shekaru 30. Wata ƙaramar jemagiya daga yankin Siberiya ta kafa tarihi a duniya a shekarar 2006, ta kasance tana da shekaru 41.

A cewar wani binciken da aka yi a cikin mujallar FASEB, “Jemagu (nau’in Chiroptera) suna da ban sha’awa musamman daga mahangar nazarin halittu, bayan tasirin girman jiki, jemagu su ne rukunin dabbobi mafi daɗewa.” Saboda haka, jemagu sun ci gaba da rayuwa har ninki goma fiye da yadda aka tsara girman jikinsu, kuma suna da nagartattun siffofi kamar; ƙarfin hali, juriyar tashi, ƙwaƙwalwa, da kuma cikakken kuzarin jikin da ake buƙata don guje wa mafarauta, matsalolin yanayi, yunwa, da rashin lafiya.

Masana kimiyya suna nazarin juriya ga iskar oxygen da furotin homeostasis a matsayin dalilin da yasa jemagu ke iya rayuwa na dogon lokaci idan aka kwatanta da sauran dabbobin da ke tashi kuma masu shayarwa.

Tsarin rayuwar jemage

Rayuwar jemagu kamar sauran dabbobi da halittu tana wanzuwa ne a bisa wasu matakai da kan fara tun daga barbara, tsarin rayuwar jemagu ta ƙunshi matakai kamar

Ɗaukar ciki da haihuwa

Yawancin nau’in jemage suna da tsarin (polygynous), ma’ana maza suna saduwa da mata da yawa. Jemagu yawanci suna haihuwa tsakanin watan Mayu da Yuli lokacin da suke zaune a wurare masu zafi. Jemage a yanayi daban-daban na iya haihuwa aƙalla sau biyu ko fiye a kowace shekara. Ciki zai iya wucewa ko’ina daga makonni shida zuwa watanni shida, dangane da nau’in da jemagen ya faɗa.

Jarirai (Pups)

Jaririn jemage na iya kaiwa kashi 40% na nauyin mahaifiyarsa a lokacin da aka haife shi. Ana kiran jemagu jarirai da suna pups a Turance. Mata a yawancin nau’in jemagu suna ɗaukar ciki kuma suna haifar ɗa ɗaya. Uwar tana ba da mafi yawan kulawa ga jaririn. Shi ma uban yana da mahimmanci a cikin nau’in jinsin ɗaya. Yawancin nau’ikan suna shayarwa ga dukkan jarirai, wanda wata macen takan shayar da ‘ya’yan wata. A cikin nau’ikan da matansu suka koma yankinsu na asali don yin aure, hakan na iya taimakawa wajen ƙara adadin mazauna yankin.

Matasa (Adults)

Damar jemagu ta tashi ta dogara ne da girman jikinsu yayin da suka girma da kuma tsayin fuka-fukansu. Yawancin jemagu suna yaye ‘ya’yansu a cikin ƙasa da watanni uku. Bayan haka, jemagun da ake kira vampire (wato nau’o’in jemagu ne masu zuƙar jinin tsuntsaye da sauran dabbobi a matsayin abinci), suna ci gaba da kula da jariransu, kuma matasansu suna samun ‘yancin kai daga baya a rayuwa fiye da sauran nau’ikan jemagu. Haka tana faruwa saboda jinin da ke a matsayin abinci gare su, wanda ke da wahalar samu a cikin yanayin dare. Da zarar sun girma, yawanci jemagu suna yini barci, sai dare su tashi su fara farautar abinci.

Dalilan da ke sa jemage tsawon rayuwa

Jemage suna da ƙarancin masu farautar su daga cikin sauran halitta. Masana kimiyya sun tabbatar da cewa wannan wani ɓangare na baiwar da suke da ita  na kasancewa halittun da ke walwala a lokacin dare kuma suna iya tashi. Tun da a lokacin dare kawai suke farkawa daga barci har ma su fita, hakan yana rage musu haɗarin zama ganima, sannan tashi sama da suke yi yana ba su damar tsira daga hari. Yawancin jemagu, haɗari mafi muni da suke fuskanta shi ne faɗowa ƙasa da suke dalilin rashin lafiya.

Mujiya, shaho, da macizai su ne ke cin jemagu, amma wannan ba shi da tasiri idan aka kwatanta da miliyoyin jemagu da cutar (white nose disease) farin hanci ke kashewa. Cutar, da ake kira da (white fungus) da ake gani a kan muzzles da fuka-fukansu, tana shafar jemagu masu sanyin jiki

A daya ɓangaren kuma, mutane na ɗaya daga cikin maharan jemagu masu hatsarin gaske. Yawancin mutane suna tsoron jemagu kuma suna ɗaukar su a matsayin wani nau’in ɓeraye. Lokacin da mutane suka fahimci jemagu suna zaune a cikin sorayen gidajensu ko kuma wasu wurare, za su fara yunƙurin kashe da kawar da su.

Tasirin jemagu ga rayuwar jama’a

Kimanin magunguna 80 sun samu daga tsire-tsire waɗanda ke dogara ga jemagu don yin barbara da haihuwarsu. Duk da yake jemagu ba makafi ba ne, nazarin yadda jemagu ke amfani da ecolocation (fasahar gano waje ko kuma wani ba tare da ganin ido ba) ya taimaka wa masana kimiyya wajen inganta kayan aikin kewayawa ga makafi. Bincike kan jemagu kuma ya haifar da ci gaba a cikin alluran rigakafi.

Ana kallon jemagu a matsayin abin ban tsoro, amma duk da kasancewar su a matsayin halittu masu ban tsoro, amma a haƙiƙa suna taimakawa wajen haɗa ƙwayar tsiron shuka mace da namiji domin su girma har su kai ga matakin amfani. Har ila yau jemagu ke cinye ƙwari masu wahalar da amfanin gona da ma mutane. Saboda haka idan babu jemagu, duniyar ɗan’adam za ta galafaita sosai.

Jemage suna iya haɗa barbarar tsirran ‘ya’yan itatuwa daban-daban har sama da guda 300, wanda suka haɗa da ayaba, mangwaro, da avocados. Haka nan za su iya cin sauro har guda 1,200 a cikin sa’a guda.

Cututtukan da jemagu ke yaɗawa

Jemagu na yaɗa cututtuka da yawa masu haɗari da barazana ga rayuwar mutane, ga wasu muhimmai daga ciki waɗanda ya kamata a kula kuma a kiyaye;

Histoplasmosis

Histoplasmosis wata cuta mai kama hunhu. Tana faruwa ta hanyar shakar ƙwayar cutar da ake kira (Histoplasma capsulatum fungal spores). Ana samun waɗannan ƙwayar cutar a cikin ƙasa mai wadatar yawu da fitsarin jemagu da tsuntsaye waɗanda suka wuce shekaru 3. Wannan ƙasa za ta iya kasancewa a kusa da tsofaffin gidajen kaji, kusa da gidan tururuwa ko a cikin ruɓaɓɓun bishiyoyi, ko a cikin koguna, da sauran wuraren da jemagu ke zaune, ciki har da cikin gidaje da cikin ɗakuna.

Rabies

Rabies cuta ce mai saurin kisa daga kwayar cutar rabies. Mutane na iya kamuwa da cutar idan jemagu masu ɗauke da cutar suka cije su, ko kuma lokacin da fitsari da yawun jemagu ya shiga cikin idanu, hanci, baki ko rauni.

Manazarta

Harper, R. (2024, September 4). Why do bats fly? An evolutionary journey. Bat Conservation International.

UCMP Berkeley (n.d).  Life history and ecology of the chiroptera UCMP Berkeley

Sadier, A., Urban, D. J., Anthwal, N., Howenstine, A. O., Sinha, I., & Sears, K. E. (2020). Making a bat: The developmental basis of bat evolution. Genetics and Molecular Biology, 43(1 suppl 2).

Institution, S. (n.d.). BAT Facts | Smithsonian Institution. Smithsonian Institution.

Was this article helpful?
YesNo

You cannot copy content of this page