Farfesa Jibril Aminu, na ɗaya daga cikin fitattun haziƙan malaman jami’o’i kuma jajirtaccen ma’aikacin gwamnati wanda ya sadaukar da rayuwarsa kacokan ga cigaban ƙasa. Sanannen farfesa ne a fannin ilimin zuciya, kuma fitaccen ɗan siyasa, kana kuma mai ba da shawara. Babu shakka farfesa Jibril Aminu ya bar gado mai ɗorewa a fannin likitanci, ilimi, da ma’aikatun gwamnati.

Haihuwarsa
An haifi farfesa Jibril Aminu a ranar 25 ga Agustan shekarar 1939, a garin Song, yankin Adamawa, a lokacin mulkin mallaka. Aminu ya rasa mahaifinsa tun yana ƙarami, mahaifiyarsa da kawunsa ne suka kula da shi, wanda a ɗaya daga cikin hirarrakin da aka yi da shi ta ƙarshe da aka buga a jaridar Aminiya a shekarar 2016 ya bayyana hakan.
Karatunsa
Farfesa Jibril Aminu ya halarci makarantar Elementary School a garin Song, daga baya kuma ya halarci makarantar Middle Yola. Haka zalika ya kasance tsohon ɗalibin kwalejin Barewa. Ya yi karatun digirinsa farko a fannin likitanci daga Jami’ar Ibadan a shekara ta 1965 kuma ya ci gaba inda ya kai ga samun digirin digirgir (Ph.D) a fannin kimiyyar magunguna (wato Medicine) a Turance daga babbar makarantar likitancin ta Royal Post-Graduate da ke birnin London.
Hazaƙarsa ta bayyana tun shekarunsa na farko, ya kasance koyaushe mafi ƙwazo a aji. Bayan ya fita da sakamako na daban a dukkan darussan da ya rubuta jarrabawar kammala makarantar sakandare ta Afirka ta Yamma (WASCE) a 1957, kuma ya kammala digirinsa a jami’ar Ibadan, wato digirinsa na farko a shekarar 1965.
Gwagwarmayar aiki da siyasa
Farfesa Jibril Aminu ya yi ayyuka da dama a tsawo shekaru da yawa da kuma jagoranci a manyan makarantu a fannonin likitanci da asibitocin koyarwa. Bayyanarsa a fagen siyasa kamar sauran takwarorinsa, ya faro ne da gwagwarmayar ƙungiyar ɗalibai wanda har ya kai ga kafa ƙungiyar ‘yan Arewa, wadda ta haɗa kai da marigayi Abubakar Tafawa Ɓalewa da marigayi Sardauna.
An nada shi Ministan Ilimi, daga baya kuma ya zama Ministan Man Fetur da Ma’adinai tsakanin 1989 zuwa 1992. A lokacin da yake rike da mukamin a fannin mai, ya jagoranci kungiyar masu samar da man fetur ta Afrika da kuma taron OPEC.
Aikin ilimi na Aminu ya shahara kuma ya faɗaɗa. Ya yi aiki a matsayin Babban Sakatare na Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa (1975-1979), Mataimakin Shugaban Jami’ar Maiduguri (1980-1985), da kuma Farfesan Likitanci a Jami’ar Howard da ke Washington, D.C. Ya kasance likita mai ba da shawara kuma ya riƙe manyan ayyuka na koyarwa da gudanarwa a jami’o’in Najeriya.
Farfesa Jibril Aminu yana daga cikin waɗanda suka jagoranci samar da tsarin ilimi na 6-3-3-4. Ya ba da gudummawa wajen samar da ƙarin jami’o’i guda bakwai, wanda hakan na nuna gudummawarsa mai ɗorewa ce a fagen ilimi a Najeriya. Ya taka muhimmiyar rawa wajen tsara manufofin ilimi a Najeriya a matsayinsa na Babban Sakatare na Hukumar Kula da Jami’o’i ta ƙasa (NUC) daga shekarar 1975 zuwa 1979.
Jibrin Aminu ya kuma kafa hukumar kula da kwalejojin ilimi ta ƙasa (NCCE) da kuma hukumar kula da ilimin makiyaya ta ƙasa (NCNE) a lokacin da yake rike da muƙamin ministan ilimi.
Bayan ya kammala aikinsa na NUC a matsayin magatakarda na Hukumar, ya koma asalin aikinsa a matsayin likitan zuciya kuma visiting professor a Kwalejin Kimiyya ta Jami’ar Howard da ke Washington DC, daga nan ne aka naɗa shi Mataimakin Shugaban Jami’ar Maiduguri.
A bangaren man fetur, jagorancin haziƙin mai hangen nesa, ya inganta tsarin gaskiya da kuma kuɗaɗen shiga na ƙasa, musamman faɗaɗa hanyoyin sadarwa na bututun mai a faɗin Nijeriya da kuma samar da ƙarin gidajen man a faɗin kasar nan.
A sashen asibitin koyarwa na Jami’ar Ibadan, ya yi aiki a ɓangarori da dama kamar haka;ya yi aiki a matsayin mai ba da shawara, Babban Malami, kuma Babban Shugaban Nazarin Clinical Studies daga 1973 zuwa 1975.
Ya kuma kasance Farfesa a sashen koyar da ilimin Likitanci a Jami’ar Howard da ke Amurka tsakanin 1979 zuwa 1980.
An zaɓe Farfesa Aminu a matsayin Sanata mai wakiltar Adamawa ta tsakiya a shekarar 2003 kuma an sake zaɓen shi a shekarar 2007, inda ya yi aiki har zuwa 2011.
A fannin diflomasiyya, Aminu ya taba zama jakadan Najeriya a Amurka daga 1999 zuwa 2003. Daga baya ya wakilci Adamawa ta tsakiya a majalisar dattawan Najeriya daga shekarar 2003 zuwa 2011, inda ya kasance mamba a kwamitocin harkokin ƙasashen waje, ilimi, sojojin sama, da lafiya.
Ya kuma kasance wakili a tarukan ƙasa da dama da suka haɗa da taron ƙasa na shekarar 2014, wanda a ƙarshe ya goyi bayan ya nuna damuwa game da taron.
A cikin jerin lakcocin jaridun gasar Champion Newspaper karo na 4 a shekara ta 2001, Aminu a matsayin bako mai jawabi, ya nuna shakku kan sha’awar tsarin tarayya a matsayin tsarin gwamnati.
A tsawon shekarun nan, tasirin Farfesa Aminu ya yawaita, ya zaburar da wasu mutane da yawa, abin da ya gadar sun haɗa da; hazaƙa, hidima, da sadaukarwa ga al’ummarsa. Ya horar da ɗalibai da dama da suka hada da Dr. Aliyu Idi Hong, tsohon ƙaramin ministan lafiya da harkokin waje.
Lambobin yabo
- Farfesa Aminu dai ya samu lambar yabo ta (CON) ta ƙasa a shekarar 2002.
- Ya kuma samu digirin girmamawa na Dakta a fannin Kimiyya daga Jami’ar Ahmadu Bello a shekarar 1988, da sauran yabo da dama.
- Ooni na Ife ne ya karrama shi a shekarar 2010 da laƙabin gargajiya “Bobaselu of the Source,” wanda ke nuna matsayinsa a fagen siyasa da al’adu.
- Hukumar kula da jami’o’i ta kasa, NUC, ta kaddamar da karramawa ga babban sakataren hukumar Farfesa Jibril Aminu, yayin da yake cika shekaru 85 a duniya.
Iyalai
Allah ya albarkaci Aminu da yara tara – mata huɗu da maza biyar. Daya daga cikin ‘ya’yansa, Murtala, a wata hira da ya yi da jaridar Punch a shekarar 2018, ya bayyana shi a matsayin uba mai zuciya, wanda ya yi tafiye-tafiye da yawa saboda aikinsa.
Mutuwarsa
Marigayi farfesa Jibrin Aminu ya rasu ne a ranar Alhamis 5 ga watan Yuni, 2025, a Abuja bayan ya sha fama da rashin lafiya. An yi jana’izarsa a babban masallacin ƙasa da ke Abuja.
Manazarta
Ande, E. (2025, June 5). Ex-petroleum minister, Jibrin Aminu, dies at 85. Punch Newspapers.
Hammangabdo, J. K., & Hammangabdo, J. K. (2025, June 6). Jibril Aminu (August 1939- June 2025). Leadership News.
Nigeria: Updated – Jibril Aminu, former education minister, dies at 85. (2025, June 6). allAfrica.com.
*****
Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.
Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.