Skip to content

Kabeji (cabbage)

Kabeji yana ɗaya daga cikin waɗansu nau’ikan abincin kayan lambu da ba sosai ake nazari a kansu ba. Ainihin kabeji mamba ne na rukunin kayan lambu da ake kira “cruciferous” wanda ya hada da broccoli, Kale, radishes, Brussel sprouts, da sauran su. Kabeji yakan zo a cikin launuka iri-iri kamar kore, fari, purple da ja. Ya wanzu a duniya na tsawon dubban shekaru kuma abu ne na kowa da kowa.

An noma kabeji a matsayin kayan lambu da tun zamanin tsohuwar ƙasar Girka kimanin shekaru 2600 da suka gabata, kuma yana da dogon tarihin amfani da shi a matsayin magani. Akwai bayanai da yawa game da amfani da shi don dalilai daban-daban kamar riga-kafin buguwa, ciwon kai, ciwon ciki, har ma da cutar kansa. An daɗe ana amfani da ganyen Kabeji a matsayin kayan girki, da kuma shafawa ga cutukan daji, har ma a zamanin yau, an gudanar da bincike a kansa a matsayin hanyar yin riga-kafi ko magance ciwon nono ga iyaye mata masu shayarwa.

Dukkan kabeji suna da kawunan da suka tsiro daga ganyen da ya kewaye su. Akwai nau’ikan ƙwallon kabeji da yawa daban-daban, da launuka su ma daban-daban. Kabeji yana da mahimmanci a matsayin kayan amfanin gona don kasuwanci da ake sarrafawa a mafi yawan sassan duniya kuma yana da matsayi a cikin manyan kayan lambu.

Sinadaran abinci a cikin kabeji

Kabeji, kamar sauran kayan lambu na rukunin cruciferous, yana cike da bitamin da minerals waɗanda jikin ɗan’adam ke muradin samu, yayin da ya rage ƙarancin kuzari. Idan aka yi la’akari da bayanin sinadiran da ya ƙunsa, tabbas ya cancanci zama babban abinci, amma galibi ana watsi da shi saboda wasu kayan zamani kamar su berries acai. Idan aka bayyana bayanin sinadaran  abinci da suke cikin kabeji, lallai zai kasance mai ban sha’awa sosai ga al’umma. A cewar kafar Livestrong, kofi ɗaya na yankakken kabeji ya ƙunshi:

  • Calories: 22
  • Sinadarin kitse ko maiƙo: gram 0.1
  • Cholesterol: microgram 0
  • Sodium: micrograms 16 MG
  • Carbohydrates: grams 5.2
  • Sinadarin fiber: grams 2.2
  • Sinadarin sukari: grams 2.8
  • Sinadarin furotin: grams 1.1

Tare da ƙarancin adadin kuzari, gishiri, da sukari, yana ba da wasu sinadarin fiber da furotin har ila yau. Abincin da ya ƙunshi sinadarin fiber, sashe ne mai mahimmanci na daidaitaccen tsarin abinci kuma yana tallafawa tsarin narkewar abinci mai kyau. Haka nan, ana ɗaukar furotin daga shuka a madadin furotin daga nama.

cabbage
Kabeji daɗaɗɗen kayan lambu ne mai matuƙar alfanu ga lafiyar ɗan’adam.

A ƙarshe, kabeji babban tushen wani sinadari ne da ake kira antioxidants. Waɗannan sinadarai suna taimaka wa jiki yaƙar abin da ake kira free radicals – abubuwa masu lalata ƙwayoyin halitta. Ana tsammanin waɗannan radicals suna taimakawa wajen haɓaka cututtuka kamar ciwon daji, cututtukan zuciya, da ciwon sukari. Antioxidants suna taimakawa wajen rage yaɗuwar radicals a cikin jiki kuma suna tallafawa wajen inganta tsarin garkuwar jiki da yaƙar kumburin da zai iya cutar da jiki.

Sinadaran bitamin da minerals

Kabeji kuma yana ƙunshe da wani ƙarin alfanu idan ana batun samar da bitamin da minerals da jiki ke buƙata. A jikin kabeji guda ɗaya cikakke akwai bitamin da minerals kamar haka:

  • Bitamin K
  • Bitamin C
  • Folate (B9)
  • Manganese
  • Bitamin B6
  • Thiamin (B1)
  • Pantothenic Acid (B5)
  • Calcium
  • Magnesium
  • Potassium
  • Riboflavin (B2)
  • Bitamin A (IU)

Amfanin kabeji ga lafiya

Waɗannan bitamin da minerals da ke ƙunshe cikin kabeji suna da tasiri mai yawa a jiki wanda zai iya inganta lafiyar jiki gabaɗaya. Wasu daga cikin muhimman amfanin kabeji ga lafiya sun haɗa da:

Rage tsananin kumburi

Kumburi na daga cikin hanyoyin da jiki ke taimakawa wajen yaƙi da kamuwa da cuta. Sai dai kumburi na yau da kullun zai ba da gudummawa ga cutuka kamar cutukan zuciya da ciwon daji. Sinadaran da ake samu a cikin kabeji da sauran ‘ya’yan itatuwa da kayan marmari na iya taimakawa wajen rage kumburi.

Inganta narkewar abinci

Sinadarin fiber da ake samu a cikin kabeji na iya taimakawa wajen inganta tsarin narkewar abinci da haɓaka motsin hanji na yau da kullun.

Daƙile cutukan zuciya da bugun jini

Sinadaran antioxidants a cikin kabeji suna taimakawa wajen rage kumburi, wanda ke da alaƙa da cutukan zuciya. Kabeji ya ƙunshi wani abu da ake kira anthocyanins. Yawancin nazari sun gano waɗannan sinadarai na iya rage haɗarin hawan jini da bugun zuciya har ma da bugun jini. A ƙarshe, yayin da yawancin sinadarin sodium a cikin abinci ke da alaƙa da cutukan zuciya, shi kuwa sinadarin potassium a cikin kabeji yana taimaka wa jiki rage sodium ta hanyar fitsari.

Inganta garkuwar jiki

Bitamin C da ake samu a cikin kabeji yana da amfani ga dukkan jiki. Ba wai kawai maganin antioxidant ba ne wanda ke yaƙar ‘free radicals’, yana taimakawa wajen yaƙi da cututtukan zuciya, ciwon daji, har ma da mura. Bitamin C har ila yau yana taimakavwa jiki wajen karɓa da sarrafa sinadarin ƙarfe da jikin yake buƙata.

Ƙara ƙarfin ƙashi

Kabeji yana cike da bitamin K. Wannan muhimmin bitamin yana taimaka wa jiki yaƙar karyewar ƙashi kuma yana inganta ƙarfin ƙashi. An yi imani da cewa rashin bitamin K na iya taimakawa wajen ci gaban osteoporosis da ƙara haɗarin karaya, musamman a cikin tsofaffi.

Daƙile ciwon sukari

Kasancewar kabeji yana da ƙarancin sinadarin carbohydrates kuma yana da yawaitar sinadarin fiber, don haka babban zaɓi ne ga waɗanda ke rayuwa da ciwon sukari domin yana iya taimakawa wajen rage matakan sukarin jini ba tare da wata matsala mai haɗari ba.

Inganta lafiyar zuciya

An bayyana anthocyanins a matsayin sinadarin da ke ba da kariya daga cutar kansar da ke hana kumburin da zai iya haifar da cutukan zuciya. Wani rahoto na baya-bayan nan a cikin Mujallar American Journal of Clinical Nutrition ya danganta cin abinci mai arzikin sinadarin flavonoid da ƙarancin haɗarin mutuwa daga cutukan zuciya kuma ya bayyana cewa ko da ƙaramin adadin abinci mai yawaitar flavonoid ɗin na iya zama da fa’ida. Babban sinadarin polyphenol a cikin kabeji na iya daƙile haɗarin cutukan zuciya ta hanyar hana haɓakar platelet da rage hawan jini.

Illolin cin kabeji

Duk da yake kabeji yana samar da yawancin bitamin da minerals da jiki ke buƙata, za a iya samun wasu lahani a dalilin yawaita cin kabeji.

Kayan lambu nau’in ‘cruciferous’ kamar kabeji na iya haifar da gas, kumburi da gudawa. Zai fi kyau a sannu a hankali a riƙa amfani da waɗannan kayan lambu a cikin tsarin abinci. Mutanen da ke da matsalar narkewar abinci na iya iyakance adadin kabeji da za su ci ko kuma su nemi shawarar likitocin abinci (nutritionists).

Manazarta

Clinic, C. (2025, April 22). 8 Health benefits of cabbage. Cleveland Clinic.

O’Neill, M. (2024, December 19). 8 Health benefits of cabbage. Health.

*****

Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.

Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.

Maƙalar ta amfanar?
EAa

You cannot copy content of this page

×