Skip to content

Kaciyar mata

  • Wallafawa:
  • Rukuni: Lafiya, Al'ada
Aika |

Kaciyar mata (Female Genital Mutilation – FGM) wata tsohuwar al’ada ce da ake gudanarwa a wasu al’ummomi musamman a ƙasashen Afirka, Gabas ta Tsakiya da wasu sassan Asiya. Ana aiwatar da ita ta hanyar yanke wani ɓangare na farjin mace ba tare da wani dalilin kimiyya ko na lafiya ba. A wasu wuraren, ana yin wannan aiki ne tun yarinya na ƙarama. Wani lokaci kafin ta kai shekaru goma, bisa zato ko hasashen cewa hakan zai sa ta zama mai kunya, mai tsafta ko kuma ta samu karɓuwa a cikin al’umma.

Duk da cewa wasu al’adu suna ganin wannan aiki a matsayin hanya ta tabbatar da halin kirki, gaskiyar magana ita ce kaciyar mata tana janyo rauni, zubar jini, cututtuka, da matsaloli masu tsanani ga lafiyar mace. Hakan ne ya sa Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana kaciyar mata a matsayin cin zarafi da tauye haƙƙin ɗan Adam, musamman ga mata da ’yanmata. Haka kuma, wasu hukumomin duniya irin su Majalisar Ɗinkin Duniya (UN) da Asusun Tallafa wa Ƙananan Yara (UNICEF) sun bayyana wannan aiki a matsayin abin da ya saɓa wa mutunci da martabar mace, domin yana hana ta ’yancin jiki da lafiya.

images 34
Kaciyar mata na wacce ta samo asali daga al’ada, na jefa dubban mata cikin gararin rayuwa.

Kaciyar mata ba illa ta jiki kawai take ba, har ma tana barazana ga tunani da ƙwaƙwalwar mata. Mata da ’yanmatan da aka yi wa irin wannan aiki sukan fuskanci tsoro, damuwa, da ƙuncin tunani, wanda hakan yakan shafi rayuwarsu gabaɗaya. Wannan dalili ya sa, ƙasashe da dama suke ƙoƙarin kawar da wannan al’ada ta hanyar ilimi, doka, da wayar da kai, domin kare lafiyar mata da haƙƙinsu.

Ma’anar kaciyar mata

A cewar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), kaciyar mata na nufin “duk wata hanya da ake cire wani ɓangare ko dukkan farjin mace, ko kuma a raunata wajen don dalilan da ba na lafiya ba.” Wannan ma’anar ta haɗa da duk wani aiki da ke lalata ko rage siffar asalin jikin mace a wajen haihuwa, ba tare da wani dalilin likitanci ba.

A wasu al’ummomin, ana ba wa wannan aiki suna daban-daban kamar “kaciya,” “tsaftacewa,” ko “gyaran mace.” Amma a zahiri, duk waɗannan sunaye suna nufin abu guda ne, wato raunin da ake yi wa mace ta hanyar yanke wani ɓangare na jikinta.

Wannan kaciyar tana da dogon tarihi a cikin wasu al’ummomi, inda ake ganin tana da alaƙa da tarbiyya, aure, ko ibada. Sai dai, binciken masana ya tabbatar da cewa ba a sami wata fa’ida ta lafiyar mace da ke tattare da kaciyar ba. Maimakon haka, tana haifar da cututtuka, rauni, da matsalolin haihuwa.

Haka kuma, babu wata hujja daga addinin Musulunci ko Kiristanci da ta amince da irin wannan aiki. Malamai da masana addini da dama sun bayyana cewa kaciyar mata ba wajibi ba ce kuma ba ta cikin koyarwar addini.

Saboda haka, kaciyar mata al’ada ce da ta samo asali daga tunanin jama’a da tsarin zamantakewa na da, ba daga addini ko kimiyya ba. Don haka, ya zama wajibi a fassara ta a matsayin mummunar al’ada da ya kamata a kawar da ita ta hanyar ilmantar da al’umma da kare haƙƙin ’yanmata.

Nau’ikan kaciyar mata

Dangane da fahimtar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), kaciyar mata ta kasu kamar haka:

Nau’i na ɗaya (Clitoridectomy)

Wannan nau’in kaciyar mata shi ne wanda ake cire gabaɗaya ko wani ɓangare na ƙaramar tsoka da ke saman farjin mace. Wannan tsoka tana ɗaya daga cikin manyan wuraren jin daɗi a jikin mace, kuma cire ta na iya haifar da rauni, zubar jini, da ciwo mai tsanani. A lokuta da dama, wannan nau’i yana rage wa mace damar jin daɗin jima’i gabaɗaya, tare da jawo matsalolin haihuwa ko ciwon yoyon fitsari saboda lalacewar jijiyoyi da tantanin fata.

Nau’i na biyu (Excision)

A wannan nau’i, ana cire (clitoris) gabaɗaya tare da (labia minora), kuma a wasu lokutan ma har da (labia majora). Wannan nau’in kaciyar ya fi tsanani fiye da na farko saboda yana ƙara yawan fatar da ake cirewa. Yana haifar da zubar jini mai yawa, kamuwa da cuta, da yiwuwar samun toshewar hanyoyin fitsari. Bugu da ƙari, mace mai irin wannan kaciya na iya fama da ciwon al’aura da matsalolin saduwa bayan aure.

Nau’i na uku (Infibulation)

Wannan shi ne mafi tsanani cikin nau’o’in kaciyar mata. Ana yin shi ta hanyar rage bakin farji, inda ake ɗaure ko haɗe labia minora domin samar da ƙaramin bakin da zai bar ƙofa ɗaya kawai don fitar fitsari da jinin al’ada. Ana rufe farji gabaɗaya har sai lokacin aure, inda mijin ko likita zai buɗe wajen kafin saduwa ko haihuwa. Wannan nau’i na iya haifar da matsanancin rauni, kumburi, rashin iya yin fitsari da kyau, ciwon jiki mai tsanani, da kuma toshewar hanyoyin haihuwa. Sau da yawa ana buƙatar sake tiyata domin buɗe wajen yayin haihuwa, sannan wani lokacin a sake rufe shi bayan haihuwar.

Nau’i na hudu

Wannan nau’i ya haɗa da duk wasu nau’o’in gyaran al’aura da ba su da dalilin likitanci ko na magani. Yana iya haɗawa da sokewa, hudawa, murɗewa, ƙonewa, yankewa, ko yin wasu ƙananan canje-canje a farjin mace da ba su da wata fa’ida ta lafiya. A mafi yawan lokuta, waɗannan hanyoyi suna jawo matsalolin lafiyar jini, kamuwa da cututtuka, rauni mai tsanani, da tabon da ba ya warkewa. Haka kuma suna iya haifar da matsaloli na tunani da jin tsoro ko fargaba ga mace da aka yi wa irin wannan kaciya.

Dalilan yin kaciyar mata

  • Al’ada

A yawancin al’ummomi, ana ɗaukar kaciya a matsayin wani ɓangare na al’ada ko alamar tsarkakewa. Wasu suna ganin cewa macen da aka yi wa kaciya ta fi tsafta, kuma hakan yana nuna ta balaga ko ta kai matsayin da ake ganin ta mace cikakkiya. A wasu wurare, kaciya tana zama muhimmin ɓangare na bukukuwan gargajiya da ake yi domin nuna shiga sabuwar rayuwa. Duk da haka, wannan fahimta ta dogara ne da al’ada, ba tare da wata hujjar kimiyya ko addini ba.

  • Addini

Wasu mutane na yin kaciya bisa tunanin cewa addininsu ya umarta yin hakan. A gaskiya kuwa, babu wata hujja a cikin littattafan addini da ke tabbatar da wajibcin kaciya ga mata. A Musulunci, babu ayar Alƙur’ani ko sahihin hadisi da ke umartar hakan, haka ma a Kiristanci babu nassin da ya kawo ta. Duk da haka, wasu na ci gaba da yin kaciyar bisa dogaro da fahimta ko al’adar yankinsu da suka haɗa da addini.

  • Kariya ga budurci

A wasu al’ummomi, ana ganin yin kaciyar hanya ce ta kare mace daga yin alfasha ko zina. Ana ɗaukar cewa cire ko rage clitoris yana rage sha’awa, don haka zai taimaka wajen kiyaye budurcinta har zuwa aure. Sai dai wannan dalili ba shi da tushe na kimiyya, domin ba kowane lokaci ne kaciya ke hana sha’awa ba, kuma sau da yawa tana jawo matsalolin tunani, ciwo, da tsoro maimakon ladabi ko kunya.

  • Karɓuwa a cikin al’umma

Wani dalili da ake bayarwa shi ne tsoron rashin karɓuwa a tsakanin al’umma. A wasu yankuna, iyaye na yin kaciya domin ‘ya’yansu mata su samu karɓuwa a wajen aure ko jama’a. Ana ɗaukar mace da ba a yi mata kaciya ba a matsayin marar ladabi ko wadda ba ta dace da al’ummarsu ba. Wannan matsin lamba na zamantakewa yana tilasta wa iyaye yarda da yin kaciya ko da kuwa sun san haɗarinta.

  • Ra’ayoyi na zamantakewa

A wasu al’ummomi, ra’ayoyi na gargajiya sun kafa tunanin cewa macen da ba a yi mata kaciya ba tana da rauni, rashin kima, ko ba ta cika matsayin mace ba. Ana danganta kaciya da ladabi, biyayya, da kamun kai, alhali kuwa hakan ra’ayi ne kawai ba tare da hujjar zahiri ba. Wannan fahimta ta nuna cewa kaciyar mata ta samo asali ne daga tsarin al’adu da tunani na zamantakewa, ba daga addini ko kimiyya ba.

Illolin kaciyar mata

Kaciyar mata tana da illoli masu yawa, waɗanda ke shafar lafiyar mace ta jiki da ta tunani. Waɗannan illoli suna iya bayyana nan take bayan aikin, ko kuma su daɗe kafin su bayyana.

Illolin nan take

Nan da nan bayan an yi kaciyar, mace na fuskantar ciwo mai tsanani saboda yankar nama da raunin da ke faruwa a wajen farji. Hakan na jawo zubar jini sosai wanda zai iya kaiwa ga rasa rai idan ba a samu taimakon likita da wuri ba.

Haka kuma, saboda rashin tsafta ko amfani da kayan aikin da ba su da tsabta, mace na iya kamuwa da cututtuka kamar tetanus, ciwon yoyon fitsari, cututtukan jini, ko ma cuta mai sa raunuka su rufta.

A wasu lokuta, ana samun matsalar wahalar yin fitsari saboda kumburi ko toshewar hanyar fitsari, wanda ke haifar da ciwo da wahala. Rashin samun taimako cikin lokaci na iya jawo matsala mai tsanani ga lafiya ko ma mutuwa.

Illolin dogon lokaci

Illolin kaciyar mata ba su tsaya nan take kawai ba. Bayan wani lokaci, mace na iya fama da ciwo mai ɗorewa a wajen farji, musamman lokacin jima’i ko haila. Akwai kuma matsaloli a lokacin haila, saboda toshewar hanyar jini ko kumburi da ya biyo bayan kaciya.

A lokacin haihuwa, matan da aka yi wa kaciya na iya fuskantar wahala mai tsanani, saboda yankan da aka yi yana hana buɗewar farji yadda ya kamata. Wannan na iya jawo zubar da ciki, rauni a mahaifa, ko ma mace ta mutu a lokacin haihuwa.

Haka kuma, kaciya na iya haifar da rashin haihuwa saboda lalacewar sassan da suke da alhakin ɗaukar ciki. Ta fuskar tunani, mace na iya shiga cikin ƙunci, tsoro, damuwa, da rashin jin daɗin jima’i wanda ke shafar dangantaka da mijinta da ma rayuwarta gabaɗaya.

Matsayin doka da haƙƙin ɗan Adam

Kaciyar mata tana cikin ayyukan da duniya ta amince cewa suna tauye haƙƙin ɗan Adam, musamman na mata da ’yanmata. Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), Majalisar Ɗinkin Duniya (UN), da sauran hukumomi na ƙasa da ƙasa sun bayyana cewa kaciya cin zarafi ce da take haƙƙin mutum.

An bayyana hakan a cikin manyan dokokin duniya kamar:

  • Universal Declaration of Human Rights (1948), wadda ta tabbatar da haƙƙin kowane ɗan Adam na mutunci da ’yanci.
  • Convention on the Rights of the Child (CRC), wadda ke kare haƙƙin yara daga duk wani aiki da zai cutar da su.
  • Convention on the Elimination of All Forms of Discrimination Against Women (CEDAW), wadda ta haramta duk wata hanyar wariya ga mata, ciki har da kaciya.

A Najeriya, an ɗauki mataki mai ƙarfi ta hanyar Violence Against Persons (Prohibition) Act, 2015 (VAPP Act), wadda ta bayyana kaciyar mata a matsayin laifi. Bisa wannan doka, duk wanda ya aikata irin wannan aiki, ko ya taimaka wajen aikatawa, na iya fuskantar hukunci da ɗaurin kurkuku. Wannan mataki yana nufin kare mata da ’yanmata daga irin wannan cin zarafi da cutarwa ta jiki da ta tunani.

Yaɗuwar kaciyar mata a duniya

Kaciyar mata na daga cikin matsalolin da suka shafi lafiyar jama’a da haƙƙin ɗan Adam a duniya baki ɗaya. Rahotanni daga ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa, musamman Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da UNICEF, sun nuna cewa fiye da mata da ’yanmata miliyan 200 a duniya sun taɓa fuskantar kaciya. Wannan adadi yana wakiltar babban kaso na mata a ƙasashe da dama, musamman a yankunan da al’adar ta yi karfi.

Kaciyar mata ta fi yawa a ƙasashen Afirka, Gabas ta Tsakiya, da kuma wasu sassan Asiya. A irin waɗannan ƙasashe, ana ɗaukar kaciya a matsayin al’ada ko alamar ladabi da tsafta, duk da cewa babu wata hujjar likitanci da ke goyon bayanta.

A Najeriya, wannan al’ada ta fi yawaita ne a wasu yankuna na ƙasar kamar:

  • Yammacin ƙasar, inda take da alaƙa da al’adun Yoruba.
  • Kudancin ƙasa, musamman a tsakanin Inyamurai da wasu ƙabilu na yankin.
  • Wasu sassan Arewa, inda ake aikatawa bisa dalilan al’ada da zamantakewa, kodayake yawanta na ƙara raguwa sakamakon wayar da kai da dokokin hana irin wannan aiki.

A wasu ƙasashen Afirka kamar Somaliya, Sudan, Masar, da Habasha, adadin mata da aka yi wa kaciya ya kai fiye da kashi 80% na al’umma. Wannan ya nuna cewa kaciya ba ta tsaya a ƙasa guda ba, illa ce da ke da tushe a al’adu daban-daban da ke buƙatar haɗin kai wajen magance ta.

Matakan daƙile kaciyar mata

Ƙungiyoyi na cikin gida da na ƙasa da ƙasa suna ɗaukar matakai daban-daban don kawar da al’adar kaciyar mata, ta hanyar haɗa ƙarfi da ƙarfe tsakanin gwamnati, al’umma, da cibiyoyin kiwon lafiya. Wasu daga cikin matakan sun haɗa da:

  • Wayar da kai

Babban mataki shi ne wayar da kai a tsakanin jama’a, ta hanyar ilimantarwa game da illolin da kaciyar mata ke haifarwa. Ana amfani da kafafen yaɗa labarai, makarantu, da wuraren ibada domin sanar da mutane cewa kaciya ba ta da wata fa’ida ta lafiya kuma tana haifar da mummunan sakamako ga rayuwar mace.

  • Ƙarfafa mata da ’yanmata

Ƙoƙari na biyu shi ne ƙarfafa mata da ’yanmata su san haƙƙinsu da damar yanke shawara game da jikinsu. Wannan yana taimakawa wajen rage yarda da al’adar, domin mata su daina karɓar wannan aiki da sunan al’ada ko ladabi.

  • Ƙa’idar doka

Haka kuma, ƙasashe da dama sun kafa dokoki da suka haramta yin kaciyar mata, ciki har da Najeriya, wadda ke da dokar Violence Against Persons (Prohibition) Act, 2015. Ana ƙoƙarin tabbatar da aiwatar da irin waɗannan dokoki domin hukunta masu aikata laifin da kuma kare waɗanda abin ya shafa.

  • Haɗin gwiwar shuwagabanni

Haɗin kai tsakanin malamai, shuwagabannin addini, da na gargajiya yana da matuƙar muhimmanci. Waɗannan shuwagabanni suna da tasiri a cikin al’umma, kuma idan suka fahimci illolin kaciyar mata, suna iya taka rawa wajen canja tunanin jama’a da daƙile wannan aiki gabaɗaya.

  • Tallafi ga waɗanda aka yi wa kaciya

Mataki na ƙarshe shi ne tallafa wa waɗanda aka yi wa kaciya, ta hanyar samar musu da kulawar lafiya, jinya, da shawarwari. Wannan yana taimakawa wajen rage raɗaɗin ciwo da matsalolin tunani da suke fama da su, tare da ba su damar sake samun ƙwarin gwiwa a rayuwa.

Manazarta

World Health Organization. (2020). Female genital mutilation: Key facts. WHO

United Nations Children’s Fund (UNICEF). (2016). Female genital mutilation/cutting: A global concern. UNICEF

United Nations Population Fund (UNFPA). (2018). Eliminating female genital mutilation: An interagency statement. UNFPA

Tarihin Wallafa Maƙalar

Sabuntawa: 15 November, 2025

Sharuɗɗan Editoci

Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.

Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.

Maƙalar ta amfanar?
EAa

You cannot copy content of this page

×