Skip to content

Karancin abinci

Ƙaranci abinci shi ne rashin samun abinci mai gina jiki ko rashin daidaituwa tsakanin sinadaran gina jiki da jikin ɗan’adam ke buƙatar aiki da su domin ginawa da haɓaka jikin. Ƙarancin abinci na iya zama rashin abinci mai gina jiki ko wuce ƙa’ida ko adadin wani nau’in abinci guda ɗayab’ ya yi yawa a jiki. Ƙarancin abinci abinci na samuwa saboda ƙarancin adadin sinadaran kuzari (carbohydrates), ko kuma rashin furotin ko bitamin ko mineral.

Ƙarancin abinci mai gina jiki ya fi yi wa ƙananan yara illa.

Jikin ɗan’adam yana buƙatar nau’ikan sinadaran gina jiki, kuma a wani adadi, domin kula da sassan jiki da ayyukansu. Rashin abinci mai gina jiki yana faruwa ne lokacin da sinadaran gina jiki da ake samu ba su kai adadin waɗanda jikin ke bukata ba. Ƙarancin abinci na iya kasancewa ko dai ta hanyar rasa abinci mai gina jiki gabaɗaya, ko kuma a samun wadataccen nau’in sinadarin gina jiki amma a rasa sauran nau’ikan sinadaran. Misali rashin bitamin ko mineral ɗaya na iya haifar da mummunan sakamako ga lafiyar jiki. A gefe guda kuma, yawan abubuwan gina jiki na iya haifar da matsala har ila yau.

Manyan rukunan abinci

1. Macronutrient

Macronutrients su ne manyan tubalan samar da abinci, su ne sinadaran carbohydrates da fats, ( wato kuzari da maiƙo). Su ne sinadaran gina jiki waɗanda jikin ɗan’adam ya dogara da su don samar da kuzari da karfi. Idan ba tare da su ba, ko ma ɗaya daga cikinsu, to babu shakka jiki zai raunan matuƙa, ya rushe tare da dakatar da ayyukan sassan jiki.

2. Micronutrients

Micronutrients su ne sinadaran bitamin da minerals. Jikin ɗana’dam yana buƙatar waɗannan a cikin madaidaitan adadi, yana buƙatar su don aiwatar da kowane nau’in ayyuka. Mutane da yawa suna da ƙarancin wasu bitamin da minerals iri-iri a cikin abincinsu. Wataƙila ba za a lura da ƙarancin bitamin da ke shafar jiki ba, amma yayin da rashin abinci mai gina jiki na micronutrient ya ƙara tsananta, za a iya fara samun tasiri mai ɗorewa.

Lokacin da jiki yake da adadin furotin, carbohydrate da mai (kitse) don amfani da shi, yana adana su a matsayin ƙwayoyin mai (kitse) a cikin nama. Amma lokacin da jiki ya ƙare don adanawa, ƙwayoyin mai da kansu dole ne su girma.

Waɗanda ƙarancin abinci yake shafa

A zance mafi inganci, rashin abinci mai gina jiki na iya shafar kowa. Rashin sanin abinci mai gina jiki, rashin samun abinci iri-iri, tsarin zamantakewa na yau da kullun da kuma tasirin tattalin arziki duk su ne ke haifar da ƙarancin abinci, wanda shi kuma yake haifar rashin abinci mai gina jiki. Wasu mutanen sun fi wasu fuskantar haɗarin rashin wasu nau’ikan abinci masu gina jiki. Mutanen da ke cikin haɗarin rashin abinci mai gina jiki sun haɗa da:

• Talakawa

Al’ummomin da ke fama da talauci galibi suna samun abinci mai sinadaran kuzari, amma suna da ƙarancin abinci mai gina jiki. Ko a cikin ƙasashen da suka ci gaba kamar Amurka, ko a ƙasashe masu tasowa waɗanda ke da ƙarancin albarkatu, al’ummominsu matalauta ba su da isasshen abinci mai gina jiki.

• Yara

Yara suna da buƙatar abinci mai gina jiki fiye da manya don girmansu. Yara musamman marasa galihu, suna cikin haɗarin kamuwa da cutar ƙarancin abinci mai gina jiki.

• Marasa lafiya

Yawancin cututtuka na yau da kullun da ke addabar wasu mutane, na iya shafar sha’awar ci ko sha kai tsaye. Mutane da yawa idan suna fama da wasu cutukan ba za su iya ci ko shan wasu nau’ikan abinci ba, ko ma gabaɗaya ba sa iya cin abincin, to wannan babu shakka zai haifar da cutar ƙarancin abinci.

• Tsofaffi

Yayin da manya ke ci gaba da girma, abinci mai gina jiki na iya lalacewa saboda dalilai da yawa, wanda suka haɗa da rage motsi, rage sha’awar abin ci da abin sha na sinadaran gina jiki.

Sakamakon ƙarancin abinci mai gina jiki

– Rashin abinci mai gina jiki na Macronutrient (wato rashin gina jiki na sinadarin furotin) yana hana jiki kuzarin samar wa da kansa kariya. Hakan na dakatar da ayyukan sassan.

– Mutanen da ke fama da ƙarancin abinci mai gina jiki, sau da yawa ba su da ƙarfi sosai. Idan yara ne wataƙila jikinsu ya kasa girma.

– Hakazalika wata matsalar da ƙarancin abinci kan haifar ita ce rasa riga-kafin kariya daga cututtuka. Wannan yana sa mutanen da ba su da abinci sosai su kamu da rashin lafiya. Idan suka samu rauni kuma, yana ɗaukar lokaci mai tsayi kafin warkewa.

– Haka nan aikin da zuciya take yi yana raguwa, yana haifar da ƙarancin bugun zuciyar, ƙarancin jini da ƙarancin ɗumin jiki.

Lokacin da aka rasa adadin kuzari gabaɗaya, hakan yana shafar matakan bitamin da minerals ma. Wasu daga cikin cututtukan da rashin abinci mai gina jiki ke haifarwa sun haɗa da marasmus da kwashiorkor, suna kuma haifar da ƙarancin bitamin. Alal misali, rashin bitamin A, na iya haifar da matsalolin gani, haka nan rashin bitamin D, zai iya haifar da ƙasusuwa marasa ƙwari.

Wasu mutane na iya cin adadin sinadaran kuzari da jiki ke bukata, amma ba su da isasshen bitamin da minerals. A irin waɗannan lokuta, tasirin ƙarancin abinci mai gina jiki na iya bayyana. Mutane na iya rasa ƙiba daga rashin abinci mai gina jiki na macronutrients, kuma suna iya samun alamun cutar anemia – rauni, rashin ƙarfi da gajiya – sakamakon rashin minerals ko bitamin.

Alamomi ƙarancin abinci mai gina jiki

Rashin abinci mai gina jiki na iya haifar da alamomi kamar haka:

• Ƙarancin nauyin jiki, bayyanar ƙasusuwa da ƙarancin maiƙo da tsoka a jiki.

• Siraran hannaye da ƙafafu tare da ƙumburin ciki da kai.

• Rashin girma da bunƙasar tunani ga yara.

• Rauni, kasala da gajiya.

• Bushewar fata, fitowar ƙuraje da raunuka.

• Karyewar gashi da zubewar shi.

Manazarta

Ld, L. S. M. R. (2023, July 14). Malnutrition: Definition, symptoms and treatment.Healthline. 

Professional, C. C. M. (n.d.-a). Malnutrition. Cleveland Clinic. 

Shashidhar, H. R., MD. (n.d.). Malnutrition: practice essentials, background, pathophysiology

World Health Organization: WHO. (2019, November 14). Malnutrition. WHO.

Was this article helpful?
YesNo

You cannot copy content of this page

×