Skip to content

Kerkeci

Kerkeci dabba ce mai tsarin shayarwa wadda take daga cikin dabbobin jeji masu matuƙar muhimmanci a tsarin halittu. Ita ce asalin karnukan gida, kuma tana daga cikin dabbobin da suka fi nuna basira, haɗin kai da dabarar rayuwa a cikin jeji. Kerkeci ya shahara sosai a tarihi, al’adu, tatsuniyoyi da kuma binciken kimiyya, inda ake kallon shi a lokaci guda a matsayin dabba mai ban tsoro da kuma alamar jarumtaka da tsari.

IMG 20260110 WA0010
Kerkeci dabba ce mai matuƙar basira da juriya ga yanayi daban-daban.

A ilimin kimiyya, kerkeci na da matsayi na musamman saboda rawar da yake takawa wajen daidaita yawan dabbobi a muhalli, abin da ke taimakawa kare daidaiton tsarin halittu gabaɗaya. Duk da cewa a wasu wurare an yi ƙoƙarin kawar da dabbar, masana sun tabbatar da cewa ɓacewar kerkeci na iya haifar da mummunar matsala ga yanayi.

Tarihin samuwar kerkeci

Kerkeci yana daga cikin tsofaffin dabbobin farauta da suka bayyana a doron ƙasa tun zamanin da. Tarihinsa yana da alaƙa kai tsaye da juyin halittar dabbobin dangin kare, musamman a cikin jinsin canis lupus. Binciken ɓirɓishin halittu da na ƙwayoyin halitta ya nuna cewa kerkeci ya taka muhimmiyar rawa wajen samuwar wasu dabbobi irin su karnuka da jakai.

Asalin kerkeci a juyin halitta

Masana ilimin halittu sun nuna cewa asalin kerkeci ya samo tushe ne daga wasu tsofaffin dabbobin farauta masu kama da kare da suka rayu miliyoyin shekaru da suka wuce. Waɗannan dabbobin sun bunƙasa ne a yankin Arewacin Amurka da Eurasia, inda yanayi mai sanyi da faɗaɗɗun dazuzzuka suka ba su damar bunƙasa.

A tsawon lokaci, canjin yanayi, motsin nahiyoyi, da ƙaruwa ko raguwa abinci sun tilasta wa waɗannan dabbobi yin sauye-sauye a siffa da halayya. Daga nan ne aka samu rarrabuwa zuwa nau’o’i daban-daban, wanda daga cikinsu kerkeci ya zama mafi girma da ƙarfi.

Samuwar dabbobi rukunin canis lupus

Nau’in canis lupus ya fara bayyana kimanin shekaru dubu ɗari zuwa dubu ɗari biyu da suka wuce. Wannan nau’in ya fi sauran ‘yan uwansa ƙarfi da daidaituwa da muhalli iri-iri. Saboda haka, ya iya yaɗuwa daga Asiya zuwa Turai da Arewacin Amurka ta hanyar tsohuwar hanyar ƙasa da ta haɗa nahiyoyin biyu. Kerkeci ya nuna kwarewa ta musamman wajen daidaituwa da muhalli, inda ya iya rayuwa a dazuzzuka, tsaunuka, da hamada. Wannan iya daidaituwa ce ta sa ya zama ɗaya daga cikin dabbobin farauta mafi nasara a duniya.

Yaɗuwar kerkeci a duniya

Bayan samuwarsa, kerkeci ya yaɗu sosai a faɗin nahiyoyi uku. A Turai da Asiya, ya zama babban dabbar farauta a cikin dazuzzuka da filayen ciyayi. A Arewacin Amurka kuma, ya zama muhimmin ɓangare na tsarin halittu, inda yake taka rawa wajen daidaita yawan dabbobin ciyawa.

Kerkeci a dazukan Afirka

A Afirka ana samun wani nau’in kerkeci, wanda masana suka fi danganta shi da nau’in canis lupus a matsayin ƙaramin reshe mai suna canis lupus lupaster. A da ana rikide shi da jackal saboda kamanninsa, amma binciken ƙwayoyin halitta ya tabbatar da cewa kerkeci ne na gaskiya. Ana samun wannan kerkeci ne musamman a:

  • Arewacin Afirka, kamar Masar, Sudan, Libya, da Habasha
  • Wasu sassan Gabashin Afirka.

Yana rayuwa a yankunan busassu, hamada, da filayen savanna. Jikinsa ya fi ƙanƙanta idan aka kwatanta da kerkecin Turai, gashinsa kuma ba ya da kauri sosai, domin yanayin zafin Afirka. Yawanci yana cin ƙananan dabbobi, tsuntsaye, da kuma ragowar abubuwan ganima.

Kerkecin Habasha

Akwai kuma wani nau’i na musamman a Afirka mai suna Ethiopian worlf, wanda ake kira kerkecin Habasha. Wannan nau’in ba reshe ne na Canis lupus kai tsaye ba, amma yana daga cikin dangin kerkeci gabaɗaya. Ana samunsa ne kawai a tsaunukan Habasha, kuma yana ɗaya daga cikin dabbobin da ke fuskantar barazanar ɓacewa. Yana rayuwa ne a saman tsaunuka, yana cin ƙananan ɓeraye da sauran dabbobin ƙasa. Wannan nau’in yana da muhimmanci sosai a fannin nazarin juyin halittar kerkeci a Afirka.

Alaƙar kerkeci da kare

Daya daga cikin muhimman abubuwa a tarihin kerkeci shi ne alaƙarsa da kare. Masana sun amince cewa kare ya samo asali ne daga wani reshe na kerkeci, bayan ɗan Adam ya fara hulɗa da su a zamanin da. A hankali, wasu kerkeci suka saba da zama kusa da mutane, lamarin da ya kai ga samuwar karnuka ta hanyar zaɓin dabi’a ta mutum. Wannan alaƙa ta sa kerkeci ya zama ginshiƙi a fahimtar tarihin hulɗar ɗan Adam da dabbobi, musamman wajen farauta, tsaro, da zamantakewa.

Kerkeci a zamanin yau

A yau kuma, kerkeci yana fuskantar ƙalubale da dama sakamakon ayyukan ɗan Adam kamar sare dazuzzuka, faɗaɗa birane, da farautarsa saboda tsoron cutar da dabbobin gida. Duk da haka, har yanzu yana nan a sassa da dama na duniya, kuma ana ɗaukar shi a matsayin muhimmiyar dabba a tsarin halittu.

Tarihin samuwar kerkeci ya nuna doguwar tafiya ta juyin halitta, daidaituwa, da gwagwarmaya, abin da ya sanya shi ɗaya daga cikin dabbobin da suka fi jan hankali a ilimin halittu.

Kerkeci a kimiyyance

Sunan kimiyya na kerkeci shi ne Canis lupus, wannan suna yana nuna matsayin kerkeci a cikin tsarin rarraba halittu a kimiyyance, inda yake cikin jinsin Canis da kuma dangin Canidae. Wannan rukuni ya haɗa da wasu sanannun dabbobi masu kama da juna ta fuskar halitta da ɗabi’a, kamar karnukan gida, jakunan dawa da fox. Matsayinsa a cikin wannan dangi yana nuna kusancin alaƙarsa da kare, har ma masana kimiyya ke ganin cewa karnukan gida sun samo asali ne daga tsohuwar hallitar kerkeci na jeji ta hanyar daɗaɗɗen tsarin daidaituwa da ɗan Adam.

Nau’ikan kerkeci

A cikin nau’in canis lupus, akwai rassa ko ƙananan nau’o’i da dama da suka samo asali sakamakon bambancin muhalli, yanayin ƙasa, da yanayin sauyin yanayi a sassa daban-daban na duniya. Waɗannan bambance-bambancen sun shafi launin gashi, girman jiki, kaurin fata, halayen rayuwa, da dabarun farauta. Daga cikin fitattun nau’ikan da aka fi sani akwai kamar haka:

Kerkeci mai launin toka

Kerkeci mai launin toka shi ne mafi yawan yaɗuwa kuma mafi shahara a cikin dukan nau’ikan kerkeci. Ana samun shi a yankuna da dama na duniya, musamman a Turai, Arewacin Amurka, da sassan Asiya. Launin gashinsa yana bambanta daga toka mai haske zuwa toka mai duhu, wani lokaci har yana haɗuwa da ruwan kasa ko baƙi, gwargwadon yankin da yake rayuwa.

Wannan nau’in kerkeci yana da ƙarfi sosai a jiki, yana da dogayen ƙafa da faffaɗan ƙirji, abin da ke ba shi damar yin doguwar tafiya da sauri yayin farauta. Yawanci yana rayuwa ne cikin rukuni, inda suke aiki tare wajen kama ganima kamar barewa, dawakan jeji, ko wasu manyan dabbobi. Hakan yana nuna irin tsarin zamantakewa da haɗin kai da ke tattare da wannan nau’in.

Kerkecin yankin Arctic

Kerkecin Arctic nau’i ne na kerkeci da ya dace da tsananin sanyi da ƙanƙara a yankunan arewacin duniya. Ana samun shi musamman a yankunan Arctic, inda yanayin sanyi yake da tsanani kuma abinci ba ya samuwa a sauƙaƙe. Saboda haka, wannan kerkeci ya samu canje-canje na musamman da suka ba shi damar rayuwa a irin wannan muhalli.

Gashinsa yana da matuƙar kauri kuma yawanci fari ne, abin da ke taimaka masa wajen ɓoye kansa a cikin ƙanƙara da kuma kare jikinsa daga tsananin sanyi. Ƙananan kunnuwansa da kaurin fatar jikinsa suna rage asarar zafi. Kerkecin Arctic yana da haƙuri sosai wajen jure yunwa, domin sau da yawa yana rayuwa a wuraren da dabbobi ke da ƙaranci.

Kerkecin yankin Asiya

Kerkecin Asiya nau’i ne da ya saba da yanayin busasshiyar ƙasa, hamada, da tsaunuka a sassan Asiya. Wannan nau’in yana rayuwa ne a wuraren da yanayin zafi da fari ke yawan faruwa, don haka jikinsa da halayensa sun dace da irin waɗannan ƙalubale.

Yawanci kerkecin Asiya yana da jiki siriri fiye da kerkeci mai launin toka, tare da gashi marar kauri sosai. Wannan yana taimaka masa wajen jure zafi da rage nauyin jiki yayin motsi a yankunan tsaunuka da hamada. Hanyoyin farautarsa sun fi dogaro da sauri da dabara, inda yake kama ƙananan dabbobi ko ragowar abin ganima, bisa la’akari da ƙarancin abinci a muhalli.

Waɗannan bambance-bambancen suna bayyana ne a launi, girman jiki da kaurin gashi, amma ba su canja ainihin halayen asali na kerkeci ba.

Duk da wannan bambancin na zahiri, dukkan nau’o’in kerkeci suna da siffofi iri ɗaya a halayya da tsarin rayuwa. Suna rayuwa ne cikin rukuni mai tsari, suna amfani da haɗin kai wajen farauta da kare yankinsu, kuma suna da matuƙar basira wajen sadarwa da juna. Wannan daidaiton halayya tsakanin nau’o’in ya nuna cewa, duk inda kerkeci yake a duniya, yana riƙe da asalin dabi’arsa ta dabbar farauta mai tsari da haɗin kai.

Tsarin muhallin kerkeci

Kerkeci na daga cikin dabbobin jeji da suka fi iya daidaituwa da yanayi iri-iri a duniya. Ana samun shi a yankuna da dama na Arewacin Amurka, Turai da Asiya, har ma da wasu sassan Gabas ta Tsakiya. Wannan yaɗuwa ta nuna ƙarfin juriya da sauƙin daidaituwarsa da yanayi, domin yana iya rayuwa a dazuzzuka masu duhu, filayen ciyawa masu faɗi, tsaunuka masu tsayi, har ma da yankunan sanyi masu cike da ƙanƙara.

A yankuna masu sanyi, kerkeci kan bunƙasa da gashi mai kauri da jiki mai ƙarfi domin kare kansa daga tsananin sanyi, yayin da a wuraren da ke da zafi ko bushewar yanayi yake samun launin gashi da ya dace da muhalli domin ɓoye kansa daga bayyana. Wannan damar da yake da ita na sauya siffofi bisa yanayin muhalli ya sanya ya zama ɗaya daga cikin dabbobin jeji mafiya juriya da tabbata.

Yawanci kerkeci yana guje wa wuraren da mutane ke da yawa, domin yana buƙatar faffaɗan fili don farauta, kiwo da watayawa. Yana zaɓar yankuna masu nisa da hayaniya, inda zai iya watayawa cikin ’yanci ba tare da tsangwama ba. Sai dai a cikin ƙarnuka na baya-bayan nan, faɗaɗar birane, noma da sare dazuzzuka sun rage wuraren da kerkeci ke rayuwa sosai. Wannan raguwar muhalli ta haifar da ƙalubale ga rayuwarsa, ta kuma jefa wasu nau’o’insa cikin barazanar raguwa ko ɓacewa a wasu yankuna. Duk da haka, har yanzu kerkeci na ci gaba da nuna juriya da ƙoƙarin dacewa da sabbin yanayi, abin da ke nuna ƙarfinsa a matsayin ɗaya daga cikin manyan dabbobin jeji na duniya.

Tsarin halayyar kerkeci

Ɗaya daga cikin manyan siffofin da suka fi bayyana halayen kerkeci shi ne yadda yake rayuwa cikin rukuni. Wannan rukuni ba kawai tarin dabbobi ba ne, illa tsari ne mai ƙa’ida da tsattsauran tsarin zamantakewa. Rukunin yawanci na ƙunshe da shugabanni da sauran mambobi, inda ake samun tsari na bin umarni da ɗaukar nauyi. Shugabannin rukuni su ne ke jagorantar sauran, musamman wajen yanke shawara kan lokacin farauta, inda za a nufa, da kuma yadda za a kare yankin da suke rayuwa a cikinsa daga mamayar wasu.

Kowane mamba a cikin rukuni yana da rawar da yake takawa, wanda hakan ke ƙarfafa haɗin kai da jituwa. Wasu na da ƙwarewa wajen farauta, wasu kuma wajen lura da tsaro ko kula da ’ya’ya. Wannan tsarin ya sa kerkeci ya fi sauran dabbobin farauta nasara, domin yana amfani da ƙarfi da basirar rukuni gabaɗaya maimakon dogaro da ƙarfi na kai tsaye. Rayuwar rukuni kuma tana taimaka musu wajen tsira a mawuyacin yanayi, musamman lokacin ƙarancin abinci ko tsananin sanyi.

Kerkeci dabba ce mai matuƙar basira da tsarin sadarwa mai zurfi. Suna fahimtar juna ta hanyoyi da dama, ciki har da sautin murya, motsin jiki da kuma ƙamshi. Kukan kerkeci, wanda aka fi sani da howling a turance, ba wai kawai kukan ban tsoro ba ne, illa wata muhimmiyar hanya ce ta sadarwa. Ta hanyar wannan kuka, mambobin rukuni kan sanar da juna wurinsu, su haɗu bayan sun watse, ko kuma su yi gargadi ga wasu kerkeci da ke kusa cewa wannan yanki na su ne.

Baya ga kuka, kerkeci na amfani da motsin jiki kamar girgiza wutsiya, karkatar da kai ko nuna haƙora domin isar da saƙo. Haka kuma, tana amfani da hanci wajen nuna iyakar yankinsa da kuma gane sauran mambobin rukuni. Wannan cikakken tsarin sadarwa yana taimaka musu wajen guje wa rikici a cikin rukuni da kuma samun nasara a yayin farauta, domin dukkan mambobi suna aiki ne bisa fahimtar juna.

Tsarin abincin kerkeci

Kerkeci dabba ce mai cin nama gabaɗaya, wato carnivore a kimiyyance, kuma tsarin jikinsa da halayyarsa sun dace da wannan irin abinci. Yana farautar manyan dabbobi kamar barewa da rakumin dawa, haka kuma yana cin ƙananan dabbobi kamar zomo da wasu nau’ikan ɓeraye, gwargwadon abin da muhalli ya tanadar masa. Wannan sassauci a zaɓin abinci yana ba shi damar rayuwa a wurare daban-daban na duniya.

Abin da ya bambanta kerkeci da yawancin dabbobin farauta shi ne dabarar haɗin kai da yake amfani da ita wajen kamo ganima. Maimakon kai hari kai tsaye, mambobin rukuni kan bi dabbar da suke farauta na dogon lokaci, suna gajiyarta har ta rasa ƙarfi. Daga nan ne sukan kai hari cikin tsari da haɗin kai, abin da ke rage musu haɗari tare da ƙara yiwuwar samun nasara.

Ta wannan hanyar farauta, kerkeci na taka muhimmiyar rawa wajen daidaita yawan dabbobi a jeji. Ya fi kama tsofaffi, marasa lafiya ko marasa ƙarfi, wanda hakan ke taimakawa wajen kiyaye lafiyar sauran dabbobin da ke cikin muhallin. Wannan rawar da yake takawa ta sa masana ilimin muhalli ke kallon kerkeci a matsayin dabba mai matuƙar muhimmanci ga daidaiton tsarin halittu, domin yana hana taruwar dabbobi fiye da kima da lalacewar ciyayi da muhalli gabaɗaya.

Tsarin haihuwa da renon ’ya’ya

Kerkeci na bin tsarin haihuwa mai ƙa’ida, inda yake haihuwa sau ɗaya kacal a cikin shekara, yawanci a lokacin bazara ko farkon damina, lokacin da yanayi ke da sauƙi kuma abinci yake samuwa. Macen kerkeci ɗaya ce kaɗai daga cikin rukuni, wadda yawanci take shugabanci, ke haihuwa. Wannan tsari ne da ke taimakawa wajen rage rikici da kuma tabbatar da cewa ana da isasshen abinci da kulawa ga ’ya’yan da aka haifa. Yawan ’ya’yan da take haifa kan bambanta, amma galibi suna kasancewa da dama, kuma ana haifar su ne makafi da rauni, suna buƙatar cikakkiyar kulawa daga manya.

IMG 20260110 WA0009
Kerkecin da ke rayuwa a yankuna masu bushewar yanayi yana juriyar yunwa.

Kiwon ’ya’yan kerkeci ba nauyin uwa kaɗai ba ne, illa aikin dukkan rukuni gabaɗaya. Maza da mata na taimakawa wajen kawo abinci, kare ’ya’yan daga haɗari, da kuma koya musu dabarun rayuwa. Wannan haɗin kai wajen renon ’ya’ya na ƙara ƙarfafa alaƙar zumunci a cikin rukuni, yana kuma ba ƙananan damar koyon dabarun farauta, sadarwa da bin tsari tun suna ƙanana. Ta wannan hanya, kerkeci na tabbatar da cewa ’ya’yansa sun tashi cikin tsari mai ƙarfi, suna da basira da ƙwarewar da za su ba su damar rayuwa a jeji.

Kerkeci a cikin al’adu

Kerkeci ya taka muhimmiyar rawa a al’adu da tarihin al’ummomi daban-daban na duniya, inda aka dinga kallon shi ta hanyoyi mabambanta bisa ga yanayin zamantakewa da tunanin jama’a. A wasu al’adu, musamman a tsakanin wasu ƙabilun Asiya da Turai, ana ɗaukar kerkeci a matsayin alamar jarumtaka, hikima da aminci, saboda tsarin rayuwarsu a rukuni da jajircewarsu wajen kare juna. A irin waɗannan al’adu, ana ganin kerkeci a matsayin dabbar da ke koyar da darusan haɗin kai da biyayya.

Sai dai a wasu al’ummomi, musamman waɗanda ke dogaro da kiwo, kerkeci ya zama abin tsoro da barazana, domin yana iya kai hari ga dabbobin gida. Wannan fahimta ta sa aka gina tatsuniyoyi da labarai da ke nuna kerkeci a matsayin dabba mai haɗari ko mugunta. A cikin tatsuniyoyi da labaran gargajiya na Turai, ana yawan bayyana kerkeci a matsayin dabbar da ke wakiltar ƙarfi, yaudara ko barazana, yayin da a wasu labarai na zamani ake nuna ta a matsayin alamar ’yanci da rayuwa ba tare da takura ba.

A duk waɗannan ra’ayoyi, kerkeci ya ci gaba da zama muhimmiyar alama a tunanin ɗan Adam, yana bayyana alaƙar da ke tsakanin mutum da jeji, da kuma tsoron abin da ba a iya sarrafawa ba a cikin yanayi.

Muhimmancin kerkeci ga tsarin halittu

A fannin ilimin muhalli, kerkeci na daga cikin dabbobin da ake kira keystone species, wato dabbobin da tasirinsu a cikin tsarin halittu ya fi girman yawansu. Rashin kerkeci a wani muhalli na iya jawo babban sauyi, wanda zai lalata daidaiton yanayi baki ɗaya. Kasancewar shi a jeji na taimakawa wajen sarrafa yawan dabbobin da yake farauta, musamman waɗanda suka yi yawa fiye da kima, abin da ke hana lalacewar ciyayi da ƙasa.

Ta hanyar rage yawan barewa da makamantansu, kerkeci na ba ciyayi damar farfaɗowa, hakan kuma yana taimakawa sauran halittu kamar tsuntsaye da ƙananan dabbobi. Wannan tasiri yana bayyana yadda dabba ɗaya kaɗai za ta iya sauya yanayin muhalli gabaɗaya. Saboda haka, masana ilimin muhalli suna ganin kare kerkeci da wuraren da yake rayuwa ba kawai kariya ce ga dabba ɗaya ba, illa kariya ce ga cikakken tsarin halittu. Kare kerkeci yana nufin kare dazuzzuka, filayen ciyawa da dukkan halittun da ke rayuwa a cikinsu, wanda hakan ke da matuƙar muhimmanci ga ɗorewar yanayi a duniya.

Kerkeci ba a matsayin dabbar jeji kawai yake ba, dabba ce da ke da dogon tasiri a kimiyya, al’adu da tsarin halittu. Duk da fuskantar barazana daga ayyukan ɗan Adam, har yanzu tana kasancewa alamar ƙarfi, basira da haɗin kai. Fahimtar rayuwar kerkeci da muhimmancinta na taimakawa wajen girmama yanayi da kuma kare dabbobin da Allah Ya halitta domin daidaiton duniya.

Manazarta

Exposed Wildlife Conservancy. (n.d.). A wolf’s diet and ecological role. 

LibGuides at International Environment Library Consortium. (n.d.). Behavior & ecology – Gray wolf (Canis lupus) Fact sheet.

National Institutes of Health. (n.d.). Perception toward wolves are driven by economic status and religion across their distribution range.

National Park Service. (2025, January 12). Wolf ecology – Yellowstone National Park. U.S. Department of the Interior.

Sharuɗɗan Editoci

Duk maƙalun da ku ka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta tare da sa idon kwamitin ba da shawara na ƙwararru. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.

Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.

Maƙalar ta amfanar?
EAa

You cannot copy content of this page

×