Skip to content

Lambar IMEI

Lambar IMEI tana da matukar mahimmanci, saboda tana iya bincikawa da kuma bayar rahoton ko an saci wayar, tabbatar da halaccinta lokacin saye ko sayarwa, da sauransu.

Mece ce lambar IMEI?

Lambar IMEI na nufin “International Mobile Equipment Identity”, lamba ce ta musamman da aka liƙa wa kowace na’urar wayar hannu don bambance na’urori daban-daban. Lambar IMEI ta ƙunshi lambobi 15 kuma yawanci ana iya samun ta a bayan wayar hannu, ko kuma ana iya samun ta cikin saiti ko ta hanyar shigar da lambar musamman a wayar (USSD code).

Ana amfani da wannan lamba ta musamman don bambanta kowace na’urar wayar hannu daga wata. Ana adana lambobin IMEI a cikin EIR (Equipment Identity Register), rumbun adana bayanai da ke ɗauke da bayanai game da duk ingantattun wayoyi.

Lambar IMEI tana ba mutum damar samun cikakkun bayanai game da wayar ba tare da samun damar shiga ta jiki ba, kamar su ƙera wayoyin hannu, sunan ƙira, kwanan wata da aka saki, da wasu bayanai.

Amfani lambar IMEI

Bibiyar wayoyin hannu da aka sace

Ana iya amfani da lambar IMEI don bin diddigin wayoyin hannu da aka sace ko suka ɓace, saboda masu ba da sabis na sadarwa na iya amfani da ita don kashe na’urar da hana amfani da ita a cikin hanyoyin sadarwarsu.

Kunna wayoyin hannu

Haka nan ana amfani da lambar IMEI wajen kunna wayar hannu a kan hanyoyin sadarwa, inda aka tabbatar da ingancin na’urar tare da tabbatar da ingancinta.

Saita bayanan fasaha

Ana iya amfani da lambar IMEI don tabbatar da bayanan fasaha game da wayar hannu, kamar ƙirarta, masana’anta, da sigarta.

Gargaɗi game da lambar IMEI

Kada a bayyana lambar IMEI ta wayoyinku ga kowa sai dai a lokutan da bukatar hakan ta taso kuma bisa amincewarku. Saboda ana iya amfani da ita ta haramtattun hanyoyi, misalin masu ayyukan kutse ko masu satar bayanai.

Binkciko lambar IMEI a kan iPhone

Domin binciko lambar IMEI a waya kirar iPhone, ga hanyoyin da za a bi;

1. Amfani da Dialpad (Allan maɓallai). Mafi sauki daga cikin hanyoyin da za a duba lambar IMEI a kan iPhone shi ne amfani da dialer (Allon maɓallai). A kan dialer iPhone, za a shigar da lambar USSD don nemo lambar IMEI nan take. Ga lambar USSD *#06#. Da zarar an danna waɗannan lambobi na USSD za su nuna lambar IMEI na iPhone nan take.

2. Amfani da manhajar saitin waya. Kodayake akwai wani ƙauli da ke cewa lambar USSD *#06# ba ta aiki a kan wayoyi ƙirar iPhones. Don haka idan lambar USSD ba ta binciko lambar IMEI ba, za a iya nemo lambar ta saitin wayar. Ga yadda ake dubawa;

– A buɗe manhajar saituna akan wayar iPhone

– Idan manhajar ta buɗe, sai a yi ƙasa

– Za a ga About, sai a taɓa shi

– Bayan taba About sai a yi ƙasa za a ga lambar IMEI ta iPhone ta bayyana.

Shi ke nan, wannan ita ce hanyar da za a iya duba lambar IMEI ta iPhone a cikin saitin wayar.

Wasu ƙarin hanyoyi duba lambar IMEI a kan iPhone

Akwai sauran wasu hanyoyin da za a iya ganin lambar IMEI. Za ka iya samun lambar IMEI ta iPhone akan murfin wayar daga ciki.

Hakazalika za a iya duba rasitin da aka sayi wayar.

Haka nan za a iya amfani da ID na Apple don shiga appleid.apple.com.

Yadda ake toshe wayar hannu ta IMEI

A yayin ɓata ko satar wayar hannu, za a iya toshewa ko dakatar da aikin wayar ta hanyar da amfani da lambar IMEI. Abubuwan da ke cikin wayar ba za su ganu ba ga wanda ya sata ko ya tsinta ba, kuma ba za a iya amfani da ita ba tunda an toshe ayyukan watsa bayanai. Amma idan wayar ta dawo hannun mai ita na asali za a iya buɗe ta cikin sauƙi.

Matakin da za a bi domin toshe wayar shi ne, yin korafin da ya dace ga kamfanin samar da sabis, kodayake ba koyaushe hakan ke faruwa ba, amma dai mai waya na iya neman toshe wayar hannu ta hanyar IMEI.

Fa’idojin toshe wayar hannu ta IMEI

1. Idan aka toshe wayar hannu ta amfani da lambar IMEI, shiga da fitar saƙonni, kira da haɗin bayanai za su tsaya cak.

2. Wayar za ta ci gaba da aiki tare da manhajar WiFi, amma wani mahaluki ba zai iya amfani da ita.

3. Toshe wayar hannu ta IMEI ba ya goge bayanan mutum

4. Irin wannan kulle wayar hannu ba ya goge bayanan sirri. Idan akwai wayar hannu wacce ba a sait lambar tsare sirri ba (PIN), duk hotuna, bidiyoyi da sauran su ana iya duba su.

5. Toshe wayar hannu ta IMEI zai taimaka wajen dawo da ita cikin sauri idan an gan ta, kuma hakan zai hana barayi amfani da ita.

Manazarta

Ahmed, M. (2022, October 20). Yadda za a duba lambar IMEI na wani iPhone.. Mekano Tech

Martinez, J. (2022, September 13). Yadda ake toshe wayar hannu ta IMEI. Móvil Forum.

Ruiz, F. (2019, February 13). Yadda ake sanin IMEI na Wayata. Androidsis.

Salama, A. (2024, March 19). Yadda za a nemo lambar IMEI a kan iPhone. تذكرة نت.

Urbina, C. E. R. (2022, December 10). Yadda ake toshe wayar hannu ta IMEI? AndroidAyuda.

Was this article helpful?
YesNo

You cannot copy content of this page

×