Skip to content

Laser

Fasahar laser na ɗaya daga cikin muhimman cigaban kimiyya da fasaha a zamanin yau. Wannan fasaha ta shafi amfani da haske mai ƙarfi, daidaitacce, kuma mai tafiya a madaidaiciyar hanya domin yin ayyuka daban-daban a fannoni kamar likitanci, masana’antu, sadarwa, kimiyya, da rayuwar yau da kullum. Wannan fasaha ta sauya yadda ake gudanar da ayyuka masu buƙatar daidaito da sauri a duniya.

Fasahar laser na nufin amfani da haske na musamman da ake samarwa ta hanyar ƙara ƙarfin hasken a cikin tsari mai sarrafuwa. Wannan haske yana da siffofi na musamman, domin yana tafiya a bigire ɗaya kawai, kuma yana da ƙarfi sosai idan aka kwatanta da hasken fitila na yau da kullum. Ana amfani da wannan haske wajen yankawa, aunawa, bincike, da kuma magance cuta a fannoni daban-daban.

Asalin kalmar LASER

Kalmar LASER ta samo asali ne daga jimla ta Turanci wadda ke nufin Light Amplification by Stimulated Emission of Radiation. Idan aka fassara ta zuwa Hausa, tana nufin ƙara ƙarfin haske ta hanyar fitar da radiation cikin tsari mai motsawa. Wannan suna yana bayyana yadda fasahar ke aiki, wato ƙara ƙarfin haske ta hanyar motsa ƙwayoyin sinadarai su fitar da makamashi a sigar haske mai ƙarfi da tsari.

Hasken laser
Fasahar laser ta shahara sosai musamman a wannan zamani da fasahohi.

Fasahar laser tana da matuƙar muhimmanci a rayuwar zamani saboda tana sauƙaƙa ayyuka da dama tare da ƙara inganci da sauri. A fannin likitanci, ana amfani da ita wajen yin tiyata cikin da daidaito, musamman a aikin ido da fata. A masana’antu kuwa, tana taimakawa wajen yankan ƙarfe da ƙera kayayyaki cikin inganci mai yawa.

A fannin sadarwa, fasahar laser na taka muhimmiyar rawa a tsarin fiber optic wanda ke ba da damar watsa bayanai cikin sauri ta intanet da hanyoyin sadarwa. Haka kuma a kimiyya, tana taimakawa wajen gudanar da bincike mai zurfi da aune-aune cikin daidaito. A rayuwar yau da kullum, ana amfani da ita a na’urori kamar printer, barcode scanner, da DVD player.

Tarihin fasahar laser

Tarihin fasahar laser ya samo asali ne daga binciken kimiyya na shekaru da dama da suka gabata, inda masana kimiyya suka fara fahimtar yadda haske da makamashi ke mu’amala da ƙwayoyin halitta. Wannan fasaha ta cigaba a hankali har ta kai ga ƙirƙirar na’urar laser ta farko a ƙarni na 20, kuma daga nan ta zama ɗaya daga cikin manyan cigaban kimiyya a duniya.

Aikin Einstein (stimulated emission)

Asalin fasahar laser ya dogara ne da aikin fitaccen masanin kimiyyar nan Albert Einstein a shekarar 1917. Shi ne ya gabatar da hasashen da ake kira stimulated emission of radiation. Wannan hasahe yana bayyana cewa idan atom ko ƙwayar halitta ta samu kuzari, za ta iya fitar da haske (photon), kuma idan aka sake motsa ta da haske mai irin wannan kuzari, za ta iya fitar da karin haske mai kama da na farko. Wannan hasahe ne ya zama ginshiƙin da aka gina fasahar laser a kai, kodayake a wancan lokaci babu kayan aiki ko fasaha da za ta aiwatar da shi kai tsaye.

Ƙirƙirar laser ta farko a 1960

Bayan shekaru masu yawa na bincike, a shekarar 1960, masanin kimiyya Theodore H. Maiman ya ƙirƙiri laser ta farko a duniya. Wannan laser ta yi amfani da kristal na ruby don samar da haske mai ƙarfi da tsari. Wannan ƙirƙira ta zama babbar nasara a tarihin kimiyya, domin ita ce ta fara tabbatar da cewa hasashen Einstein zai iya zama gaskiya a aikace. Laser ta farko ta buɗe ƙofa ga sabon zamani na fasaha, inda aka fara amfani da laser a gwaje-gwaje da bincike na kimiyya.

Gudummawar masana ga cigaban fasahar laser

Fasahar laser ba ta wanzu daga aiki na mutum guda ba, ta samu sakamakon bincike da gudummawar manyan masana kimiyya daga sassa daban-daban na duniya. Waɗannan masana sun yi aiki a matakai daban-daban, wasu sun kafa ginshiƙin ka’idar kimiyya, wasu kuma sun tabbatar da ita a aikace, yayin da wasu suka inganta ta har ta zama fasaha mai amfani a rayuwa. Ga irin rawar da suka taka:

Albert Einstein

Albert Einstein ya kasance tushen farko na hasashen kimiyyar da ya haifar da laser. A shekarar 1917, ya gabatar da ka’idar da ake kira stimulated emission of radiation. Wannan ka’ida ta bayyana yadda atom ke iya fitar da haske idan aka motsa shi da makamashi na waje. Kodayake Einstein bai ƙirƙiri laser kai tsaye ba, amma hasashensa ya zama ginshiƙi na duk fasahar laser. Ba don wannan ka’ida ba, da ba za a iya fahimtar yadda laser ke aiki ba.

Charles H. Townes

Charles Hard Townes ya taka muhimmiyar rawa wajen juya hasashen Einstein zuwa aiki. A shekarar 1950s, shi ne ya yi aiki kan fasahar da ake kira MASER (Microwave Amplification by Stimulated Emission of Radiation), wadda ita ce tushen laser. Townes ya nuna cewa ana iya amfani da stimulated emission ba kawai a hasken microwave ba, har ma a haske na gani (light). Wannan tunani ya buɗe ƙofa ga ƙirƙirar laser ta zamani. Saboda wannan gudummawa, ya samu lambar yabo ta Nobel a fannin Physics.

Fasahar laser wajen yin tiyata
Fasahar laser ta taimaka matuka a fannin kiwon lafiya, likitoci ƙwararru na amfani da fasahar wajen yin tiyata.

Arthur L. Schawlow

Arthur Leonard Schawlow ya yi aiki tare da Charles Townes wajen ƙara zurfafa bincike kan yadda za a iya amfani da stimulated emission a hasken gani. Shi ne ya taimaka wajen haɓaka ƙa’idojin kimiyya da suka sa aka fahimci yadda laser za ta iya aiki a aikace. Ayyukansa sun taimaka wajen tsara hanyar gina na’urar laser mai amfani a rayuwa, ba kawai a ƙa’idar bincike ba.

Theodore H. Maiman

Theodore Harold Maiman shi ne masanin da ya ƙirƙiri laser ta farko a duniya a shekarar 1960. Ya yi amfani da kristal na ruby don samar da haske mai ƙarfi da tsari wanda ya tabbatar da dukkan ƙa’idojin da aka yi shekaru ana nazari a kansu. Ƙirƙirarsa ta zama babbar nasara a tarihin kimiyya, domin ita ce ta fara juyar da laser daga ka’idar bincike zuwa fasahar da ake iya amfani da ita a aikace.

Nikolay Basov da Aleksandr Prokhorov

Waɗannan masana biyu daga ƙasar Rasha sun taka muhimmiyar rawa wajen haɓaka ka’idar quantum electronics, wadda ita ma ginshiƙi ce a fasahar laser. Sun yi bayani kan yadda ake sarrafa makamashi a matakin ƙwayoyin zarra (atoms da molecules), wanda ya taimaka wajen fahimtar yadda laser ke samar da haske mai tsari. Saboda gudummawarsu, tare da Townes, sun samu lambar yabo ta Nobel a Physics.

Yadda fasahar laser ke aiki

Fasahar laser tana aiki ne bisa ƙa’idojin quantum physics, inda ake sarrafa makamashi da haske a matakin ƙwayoyin zarra (atoms da electrons). Aikin laser yana gudana ne ta matakai da ke a jere har sai an samu haske mai ƙarfi da tsari na musamman.

Stimulated emission ofradiation

Wannan shi ne tushen aikin laser gabaɗaya. A wannan mataki, atom da ke cikin yanayin kuzari ana motsa shi da haske mai makamashi iri ɗaya, wanda ke sa atom ɗin ya fitar da wani haske mai kama da na farko. Waɗannan haske biyu suna da irin launi, ƙarfi da kuma tafiya a hanya guda. Wannan tsarin shi ne ya sa laser ke samar da haske mai tsari sosai.

Ƙara kuzarin ƙwayoyin atoms

Domin laser ta fara aiki, dole ne a fara ƙara kuzari ga atoms a cikin wani abu da ake kira active medium. Ana yin wannan ta hanyar wutar lantarki, haske mai ƙarfi ko wasu hanyoyin makamashi. Lokacin da atoms suka karɓi wannan kuzari, electrons dinsu suna hawa zuwa mataki mafi girma na makamashi, inda suke zama a yanayin da ba su da kwanciyar hankali. Wannan yanayi shi ake kira excited state.

Fitar da haske

Lokacin da atoms suka fara komawa daga yanayin kuzari zuwa yanayin kwanciyar hankali, suna fitar da makamashi a sigar haske wato photon. Wannan fitarwa na iya faruwa ta hanyar halitta ko kuma ta hanyar stimulatio, inda hasken waje ke tilasta atom ya saki makamashi. A cikin laser, yawancin hasken da ake samu suna fitowa ne cikin tsari mai kama da juna, wanda ke ƙara ingancin hasken.

Haɗuwar haske wuri guda

Bayan fitar haske da yawa, ana samun haɗuwar su cikin tsari guda ɗaya wanda ake kira coherent beam. A wannan yanayi, dukkan hasken yana tafiya a hanya ɗaya, yana da launi iri ɗaya, kuma yana cikin lokaci ɗaya. Wannan shi ne abin da ke sa laser ta bambanta da sauran haske, domin haskenta ba ya tarwatsewa, yana ci gaba da tafiya a madaidaicin bigire kuma da ƙarfi.

Bambanci tsakanin laser da haske na al’ada

Laser da haske na yau da kullum sun bambanta sosai a tsarinsu da yadda suke aiki. Hasken yau da kullum yana fitowa ne ta hanyoyi daban-daban kuma yana watsuwa a kowane ɓangare, yayin da laser ke tafiya amadaidaicin bigire guda ɗaya. Hasken yau da kullum ba shi da tsari mai kyau na lokaci da launi, amma laser tana da cikakken tsari. Haka kuma, laser tana da ƙarfi sosai kuma ana iya amfani da ita wajen aikin da ke buƙatar daidaito mai yawa, yayin da hasken yau da kullum ake amfani da shi ne wajen haskakawa kawai.

Abubuwan da ke cikin na’urar laser

Na’urar laser tana aiki ne ta hanyar haɗin gwiwar sassa masu muhimmanci da ke sarrafa makamashi da haske har sai an samar da haske mai tsari da ƙarfi. Kowanne ɓangare yana da rawar da yake takawa, kuma rashin ɗaya daga cikinsu na iya hana na’urar yin aiki yadda ya kamata.

Active medium

Active medium shi ne ainihin abin da ke samar da hasken laser. Shi ne wurin da atoms ko molecules ke samun kuzari sannan su fitar da haske. Wannan abu na iya kasancewa sinadaran iska kamar helium da carbon dioxide, ko sandararrun kamar crystal na ruby ko Nd:YAG, ko kuma ruwa-ruwa. Muhimmancin active medium shi ne ƙayyade irin laser ɗin ɗin da za a samu, da kuma ƙarfinta da launin hasken da za ta fitar. Idan atoms na cikin wannan abu suka sami kuzari mai yawa, suna shiga yanayin da ake kira population inversion, wanda ke ba da damar samar da laser mai ƙarfi.

Energy source

Energy source ko pump source shi ne tushen makamashi da ke cusa kuzari cikin active medium. Wannan makamashi na iya fitowa daga wutar lantarki, haske mai ƙarfi, ko wani nau’in sinadari. Aikin wannan sashi shi ne ya tayar da electrons daga ƙasa zuwa matakin kuzari mafi girma. Idan babu wannan mataki, atoms ba za su iya shiga yanayin da zai ba da damar fitar da hasken laser ba. Saboda haka, energy source shi ne injin motsa dukkan tsarin laser.

Optical cavity

Optical cavity shi ne tsarin madubai biyu da ke kewaye da active medium. Madubi ɗaya yana nuna haske gabaɗaya, yayin da ɗayan ke bari wani ɓangare ya fita a matsayin laser beam. Aikin wannan sashi shi ne ya sa haske ya ci gaba da motsawa a tsakanin madubai, yana ƙara ƙarfi a kowane zagaye. Wannan maimaituwar tafiyar haske tana ƙara yawan hasken har sai sun kai matakin da za su fita a matsayin haske mai ƙarfi da tsari.

Output beam

Output beam shi ne hasken laser da ke fita daga na’urar. Wannan haske shi ne samfurin ƙarshe na dukkan aikin da aka yi a cikin na’urar. Output beam yana da siffofi na musamman kamar tafiya a madaidaicin bigire, ƙarfi mai yawa, da tsari mai kyau. Wannan shi ne ake amfani da shi a aikace-aikacen likitanci, masana’antu, sadarwa da kimiyya.

Fasahar laser a fannin sadarwa
Fannin sadarwa ba zai yi aiki ba idan babu fasahar laser. Na’urori da dama na aiki da fasahar laser wajen aika bayanai cikin sauri.

Nau’o’in hasken laser

Laser suna da nau’o’i daban-daban bisa ga abin da ake amfani da ita wajen samar da active medium da kuma yadda suke aiki. Kowane nau’i yana da siffofi da amfani na musamman a fannoni daban-daban.

Gas laser

Gas laser tana amfani da iskar gas a matsayin active medium. A cikin wannan nau’i, ana cusa wutar lantarki cikin gas domin tayar da ƙwayoyin atoms ɗinsa su fara fitar da haske. Misalan gas laser sun haɗa da Helium-Neon laser da CO₂ laser. Helium-Neon laser ana yawan amfani da ita a na’urorin aune-aune da gwaje-gwaje da bincike saboda tana samar da haske mai launin ja mai tsabta. CO₂ laser kuwa tana da ƙarfi sosai, kuma ana amfani da ita a masana’antu wajen yankan ƙarfe da kuma a fannin likitanci. Gas laser na da fa’ida saboda suna samar da haske mai tsabta da tsari, amma suna buƙatar tsarin sarrafawa mai kyau da kayan aiki na musamman.

Solid-state laser

Solid-state laser tana amfani da daskararrun abubuwa kamar crystal ko glass a matsayin active medium. A cikin wannan nau’i, ƙwayoyin atoms da aka saka cikin crystal suna samun kuzari ta hanyar haske ko wutar lantarki. Misalai sun haɗa da Ruby laser da Nd:YAG laser. Ruby laser ita ce laser ta farko da aka ƙirƙira a duniya, kuma tana samar da haske mai launin ja. Nd:YAG laser kuwa tana da amfani sosai a likitanci da masana’antu saboda ƙarfinta da ingancinta. Wannan nau’i na laser yana da ƙarfi sosai kuma ana iya amfani da shi a ayyuka masu buƙatar daidaito da tsauri.

Liquid dye laser

Liquid dye laser tana amfani da sinadarai masu ruwa-ruwa da ke iya canja launin haske. Wannan nau’i yana da sauƙi sosai domin ana iya daidaita launin hasken da yake fitarwa. A cikin wannan laser, ana cusa makamashi cikin dye molecules domin su fitar da haske. Muhimmin fasalinta shi ne cewa ana iya canja  launin haske cikin sauƙi, wanda ya sa ta zama mai amfani a bincike na kimiyya da gwaje-gwaje. Duk da fa’idarta, tana buƙatar kulawa mai yawa saboda sinadaranta na iya lalacewa cikin lokaci.

Semiconductor laser

Semiconductor laser tana amfani da sinadaran lantarki kamar silicon ko gallium arsenide. Ita ce laser mafi ƙanƙanta kuma mafi amfani a na’urorin zamani. Ana amfani da ita sosai a electronics da fiber optics. Misali, tana cikin CD/DVD players, barcode scanners, da kuma tsarin intanet na fiber optic. Wannan nau’i na laser yana da fa’ida saboda tana da ƙanƙanta, tana anfani da wuta kaɗan, kuma tana da sauƙin haɗawa cikin na’urori daban-daban. Saboda haka, ita ce mafi yawan laser da ake amfani da ita a rayuwar yau da kullum.

Nau’o’in fasahar laser bisa aiki

Ana rarraba fasahar laser bisa yadda take fitar da haskenta da kuma ƙarfin aikinta. Wannan rabe-rabe yana taimakawa wajen fahimtar yadda ake amfani da kowane nau’i a fannoni daban-daban kamar likitanci, masana’antu, da kimiyya.

Continuous wave laser

Continuous wave laser ita ce wadda ke fitar da haske ta kuma ci gaba ba tare da katsewa ba. Wannan yana nufin cewa idan an kunna ta, tana ci gaba da fitar da hasken laser har sai an kashe ta. Wannan nau’i na laser yana da amfani a wuraren da ake buƙatar haske mai ɗorewa da daidaito, kamar a fiber optic communication da wasu nau’o’in gwaje-gwaje na kimiyya. Saboda ci gaba da fitar da haske, CW laser tana da matuƙar amfani wajen aikace-aikacen da ke buƙatar haske mai kwanciyar hankali.

Pulsed laser

Pulsed laser ita ce wadda ke fitar da haske a tsarin dabara-dabara, maimakon ci gaba. Wato tana fitar da haske na ɗan lokaci kaɗan, sannan ta tsaya, sannan ta sake fitarwa. Wannan tsarin yana ba da damar samun haske mai matuƙar ƙarfi a cikin ɗan gajeren lokaci. Saboda haka ana amfani da pulsed laser a aikace-aikacen da ke buƙatar ƙarfi mai yawa cikin lokaci kaɗan, kamar a aikin tiyata ƙarama, yankan abubuwa masu tauri, da kuma binciken kimiyya mai zurfi.

High-power laser

High-power laser ita ce laser mai matuƙar ƙarfi wadda ke fitar da makamashi mai yawa. Wannan nau’i yana iya yankawa, narkarwa ko canja tsarin kayan aiki cikin sauƙi saboda ƙarfin haskenta. Ana yawan amfani da high-power laser a masana’antu wajen yankan ƙarfe mai kauri, walda, da kuma sarrafa manyan kayan aiki. Haka kuma ana amfani da ita a wasu aikace-aikacen soja da bincike na kimiyya da ke buƙatar makamashi mai yawa.

Low-power laser

Low-power laser ita ce laser mai ƙaramin ƙarfi wadda ba ta da haɗari sosai ga kayan aiki ko jikin ɗan Adam idan aka yi amfani da ita daidai. Ana amfani da ita a na’urori kamar barcode scanners, laser printers, da na’urorin aune-aune. Haka nan ana amfani da ita a likitanci a wasu ƙananan ayyuka da ba sa buƙatar ƙarfi mai yawa. Saboda ƙarancin ƙarfinta, low-power laser tana da aminci sosai kuma tana dacewa da na’urorin yau da kullum da mutane ke amfani da su a gida ko ofis.

Fasahar laser a masana'antu
A masana’antu ma fasahar laser na taka muhimmiyar rawa wajen yanka ƙarafa, yin zane-zane ko rubutu a jikin ƙarafa da robobi.

Amfanin fasahar Laser

Fasahar laser tana daga cikin manyan fasahohin zamani da suka sauya yadda ake gudanar da ayyuka a fannoni daban-daban. Muhimmancinta ya fito ne daga damarta ta samar da haske mai tsari, ƙarfi da daidaito, wanda ke ba da damar yin aiki cikin sauri da ƙanƙantar kuskure.

A fannin likitanci

A fannin likitanci, fasahar laser ta kawo babban sauyi wajen yadda ake yin tiyata da magance cututtuka. Ana amfani da laser wajen yin ayyuka masu buƙatar daidaito sosai, domin tana iya aiki a kan ƙaramin yanki ba tare da lalata sauran sassan jiki ba.

  • A tiyata (surgery), ana amfani da laser wajen yankawa ko gyara sassan jiki daidai da buƙata. Wannan yana rage zubar jini sosai kuma yana hanzarta warkewar majiyyaci.
  • A maganin ido (LASIK), laser tana taimakawa wajen gyara matsalolin gani kamar short-sightedness da long-sightedness. Ana sake fasalin cornea domin mutum ya samu ingantaccen gani ba tare da amfani da tabarau ba.
  • Haka kuma, a cire fata ko gashi, ana amfani da laser wajen cire gashi marar amfani ko gyara fata mai tabo ko ƙuraje. Wannan yana ba da sakamako mai kyau da ɗorewa fiye da hanyoyin gargajiya.

A fannin masana’antu

A masana’antu, fasahar laser tana taka muhimmiyar rawa wajen ƙara inganci da rage ɓata lokaci da kayan aiki.

  • A yankan ƙarfe da roba, ana amfani da laser saboda tana iya yanka kayan aiki masu tauri cikin daidaito sosai ba tare da lalata gefensu ba. Wannan yana da amfani sosai a masana’antar mota da jiragen sama.
  • A ɓangaren walda, laser tana haɗa sassan ƙarfe ko kayan aiki cikin inganci da matuƙar ƙarfi da tsafta. Wannan hanyar walda tana da sauri kuma tana rage lahani ga kayan aiki.
  • A yayin zane-zane a jikin kayayyaki, ana amfani da laser wajen rubutu ko yin alamomi a ƙarfe, robobi da wasu abubuwa. Wannan yana da amfani a branding da tsaron kayayyaki

A fannin sadarwa

Fasahar laser ta zama ginshiƙi na musamman a tsarin sadarwar zamani, musamman ta hanyar fiber optic internet.

  • A fiber optic internet, ana amfani da hasken laser wajen tura bayanai cikin sauri ta cikin optical fibers. Wannan yana ba da damar samun ayyukan intanet mai sauri sosai tare da ƙarancin asarar bayanai.
  • A watsa bayanai mai sauri, laser tana ba da damar tura bayanai daga nesa sosai cikin lokaci kaɗan. Wannan ya sa duniya ta zama kamar ƙaramin ƙauye a fannin sadarwa, inda bayanai ke tafiya cikin sakanni.

A fannin kimiyya da bincike

A fannin kimiyya, fasahar laser tana da muhimmiyar rawar takawa wajen gudanar da bincike mai zurfi da aune-aune masu inganci.

  • A yayin auna abubuwa, ana amfani da laser wajen auna nisa, girma da motsi cikin daidaito sosai. Wannan yana da amfani ga fannin injiniyanci, sararin samaniya da geophysics.
  • A ɗakunan gwaje-gwaje, laser tana taimakawa wajen nazarin siffofin abubuwa a matakin ƙwayoyin halitta. Ana amfani da ita wajen gwaje-gwajen da ke buƙatar haske mai tsari.
  • A yayin amfani da spectroscopy, laser tana taimakawa wajen nazarin sinadarai ta hanyar duba yadda suke hulɗa da haske. Wannan yana taimakawa wajen gano sinadarai da fahimtar tsarinsu.

A rayuwar yau da kullum

Fasahar laser ta shiga rayuwar yau da kullum ta hanyoyi da dama, ko da mutane ba su lura da ita kai tsaye.

  • A laser printer, ana amfani da hasken laser wajen buga takardu cikin sauri da inganci. Wannan yana ba da rubutu mai tsafta da daidaito.
  • A barcode scanner, laser tana karanta lambobin sirri na kayayyaki a shaguna da manyan kantuna, wanda ke hanzarta saye da sayarwa.
  • A DVD/Blu-ray player, laser tana karanta bayanan da ke cikin kaset domin nuna fina-finai ko kunna sauti. Wannan ya kasance muhimmin ɓangare na nishaɗi kafin zuwan streaming.

Illoli da haɗura

Duk da fa’idojin fasahar laser masu yawa, tana da wasu illoli da haɗura idan ba a yi amfani da ita yadda ya kamata ba. Wannan ya sa ake buƙatar kulawa da bin ƙa’idojin tsaro sosai yayin amfani da ita.

Cutar da ido

Ɗaya daga cikin manyan haɗuran laser shi ne takan iya cutar da ido. Idan hasken laser mai ƙarfi ya shiga ido kai tsaye, zai iya lalata retina, wanda hakan zai iya haifar da raguwar gani ko ma makanta gabaɗaya. Saboda haka, ido yana daga cikin sassan jiki mafi rauni ga hasken laser, kuma yana buƙatar kariya ta musamman.

Ƙona fata

Laser mai ƙarfi na iya haifar da ƙonewa a fata idan ta shafe ta kai tsaye. Wannan na faruwa ne musamman a high-power lasers da ake amfani da su a masana’antu ko likitanci. Ƙonewar na iya zama mai sauƙi ko mai tsanani dangane da ƙarfin laser ɗin da lokacin da ta shafi fata.

Hasken laser a ido
Hasken laser kai tsaye na iya yin illa ga ido ko fata, don haka ana buƙatar ƙwarewa da kayan kariya yayin sarrafa wannan fasaha.

Amfani ba tare da horo ba

Amfani da fasahar laser ba tare da horo ba na iya haifar da manyan haɗura. Mutanen da ba su da ilimi kan yadda ake sarrafa laser za su iya yin kuskure wanda zai iya jawo rauni ko lalata kayan aiki. Saboda haka, ana buƙatar ƙwararru masu horo su ne kawai ke amfani da na’urorin laser a fannoni masu haɗari.

Hanyoyin kariya

Saboda haɗarin da ke tattare da laser, ana buƙatar amfani da kayan kariya kamar gilashin kariya (safety goggles) da sauran kayan tsaro. Waɗannan kayan suna kare ido da fata daga hasken laser mai haɗari. Haka kuma, ana amfani da tsarin tsaro a wuraren aiki domin tabbatar da cewa laser ba ta cutar da masu aiki ko muhalli ba.

Kalubalen fasahar laser

Duk da cewa fasahar laser tana da matuƙar amfani a fannoni da dama na rayuwa, akwai wasu manyan kalubale da ke hana ta yaɗuwa ko sauƙin amfani a wasu wurare. Waɗannan ƙalubale sun shafi farashi, fasaha, da kuma yanayin amfani da ita.

Tsadar haɗawa

Ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen fasahar laser shi ne tsadar ƙera ta da kuma kula da ita. Na’urorin laser suna buƙatar kayan aiki na musamman kamar madubai masu inganci, active medium mai tsari, da tsarin sarrafa makamashi mai kyau. Haka kuma, bincike da haɓaka sabbin fasahohin laser na buƙatar kuɗi masu yawa. Saboda haka, ba kowace ƙasa ko kamfani ba ne ke iya mallaka ko samar da na’urorin laser cikin sauƙi.

Wutar lantarki mai ƙarfi

Yawancin na’urorin laser, musamman masu ƙarfi (high-power lasers), suna buƙatar wutar lantarki mai yawa don yin aiki yadda ya kamata. Wannan na iya zama matsala a wuraren da wutar lantarki ba ta da tabbas ko kuma ba ta da ƙarfi. Idan babu isasshiyar wuta, laser ba za ta iya samar da haske mai tsari da ƙarfi kamar yadda ake buƙata ba.

Ƙwarewar mutum

Fasahar laser tana buƙatar ƙwararrun masu amfani da suka samu horo na musamman. Wannan saboda sarrafa laser ba abu ne mai sauƙi ba, kuma kuskure na iya haifar da haɗari ga ido, fata ko kayan aiki. Saboda haka, a yawancin lokuta, ana buƙatar injiniyoyi, likitoci ko masana kimiyya masu ilimi na musamman su yi amfani da ita.

Iyaka ga amfani

Duk da cewa fasahar laser tana da amfani sosai, amma ba a iya amfani da ita a kowane yanayi ko wuri. Wasu yanayi kamar wurare masu ƙura, hayaki mai yawa ko yanayi mai zafi na iya rage ingancin aikin laser. Haka kuma, a wasu yankuna masu ƙarancin kayan aiki da fasaha, amfani da laser na iya zama da wahala ko ba zai yiwu ba gabaɗaya.

Manazarta

Hocker, G. B. (2010). Laser technology and applications. In E. L. Wolf (Ed.), Progress in optics (Vol. 55, pp. 1–78). Elsevier.

National Institute of Standards and Technology (NIST). (2022). Laser technology and measurement applications.

Silfvast, W. T. (2004). Laser fundamentals (2nd ed.). Cambridge University Press.

Svelto, O. (2010). Principles of lasers (5th ed.). Springer.

U.S. Department of Energy. (2020). Lasers and their applications in science and industry.

Sharuɗɗan Editoci

Duk maƙalun da ku ka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta tare da sa idon kwamitin ba da shawara na ƙwararru. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.

Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.

Maƙalar ta amfanar?
EAa

You cannot copy content of this page

×