Skip to content

Lookman Ademola

Ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne ɗan asalin Najeriya, Ademola Lookman ya kafa tarihi a fannin ƙwallon kafa, inda ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasan Afrika na shekarar 2024. Babbar lambar yabo ce wacce aka gabatar masa a wurin bikin karramawa da hukumar CAF ta shirya a Marrakech a ƙasar Maroko. Hukumar ta amince da ƙwazon da Lookman ya yi a kulob ɗinsa na Atalanta da kuma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Najeriya a shekarar 2024.

Ademola Lookman ke nan, yake ɗaukar hoton selfie riƙe da kambun karramawa.

 

Lookman a yanzu ya bi sahun ɗan wasa Victor Osimhen, wanda shi ma ya lashe irin wannan kyautar a shekarar 2023. Haka kuma, cin ƙwallaye uku a wasa ɗaya wato (hat-trick) da ya yi a gasar UEFA (Europa League) da kuma gagarumar gudunmawar da ya bayar a gasar cin kofin Afrika ga Najeriya ta shekarar 2023 (AFCON) ya ƙara nuna irin rawar da ɗan wasan ya taka.

Haihuwar Ademola

An haifi Ademola Lookman a ranar 20 ga Oktoba, shekarar 1997, a Wandsworth, da ke birnin Landan. Ya taso a cikin gida mai arzikin kula da al’adu, Lookman bai watsar da al’adunsa na gargajiya ba, duk da kasancewar ya tashi a Turai, ya rungumi al’adun gida Najeriya, wanda ke ci gaba da tasiri a matsayinsa da aikinsa. Lookman ya kasance mabiyin addinin Kiristanci ne. Mahaifin Lookman mai sha’awar ƙwallon ƙafa ne, ya taka muhimmiyar rawa a cigaban ɗan nasa a wasannin kwallon kafa. Ƙarfafawa da goyon bayan mahaifinsa sun yi tasiri a shaharar Lookman a fagen tamaula.

Ademola Lookman sanye da rigar gida Najeriya, a ɗaya daga cikin wasannin da ya bugawa ƙasar.

 

Ɗaukakar Ademola a Peckham

Kafin ya shiga harkar wasan ƙwallon kafa, Lookman ya yi fice a fannin ilimi a makarantar St. Thomas the Apostle College da ke Peckham. Ya sami kyakkyawan sakamakonsa na GCSEs, hakan ya ba shi damar daidaita ilimi tare da bunƙasa a fagen ƙwallon ƙafa.

Harkar ƙwallon ƙafar Lookman ta fara ne a filin wasa na Peckham. A lokacin da yake da shekaru 11, ya shiga ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Waterloo FC academy, inda ya inganta ƙwarewarsa na tsawon shekaru biyar. Ba da daɗewa ba, sadaukarwarsa da cancantarsa suka ba shi damar zuwa Charlton Athletic academy a cikin shekarar 2013.

A cikin watan Nuwamba 2015, Lookman ya fara buga wasan ajin ƙwararru a matsayin ƙwararren ɗan wasa a Charlton Athletic. Bayan wata ɗaya, ya ci kwallonsa ta farko a kan Brighton da Hove Albion. Ƙwazonsa da sauri ya sa shi zama tauraro mai tasowa da haskawa a harkar ƙwallon ƙafa a Ingila.

Zuwan Lookman kulob ɗin Everton

Hazakar Lookman ta ɗauki hankalin Everton, wanda ta kai shi ga sanya hannu a kwantaragi a kan fam miliyan 11 a watan Janairun 2017. Ya buga wasan da ba za a manta da shi ba, inda ya ci ƙwallon a kan Manchester City.

Zuwan shi RB Leipzig a matsayin aro

Bayan nasarar kwantaragin aro, Lookman ya shiga ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta RB Leipzig a cikin 2019. Kodayake zamansa a Jamus ya ba da gudummawa a mahimman lokuta ga  Borussia Mönchengladbach. Haka nan aron da Fulham da Leicester City suka nema ga ɗan wasan sun biyo baya wannan, ya nuna juriyarsa duk da rashin daidaito da aka samu.

Nasararsa a kungiyar Atalanta a gasar Serie A

Salon taka ledar Lookman ya ɗauki babban sauyi a cikin shekarar 2022 lokacin da ya shiga ƙungiyar Atalanta  kan yarjejeniyar shekaru huɗu. Shekararsa ta farko ta kasance mai ban mamaki, a wasannin da suka gwabza da Salernitana, Spezia, da Juventus. Ya ƙare kakar wasanni ta 2022/23 da ƙwallaye 15, inda ya sami kyautar Gwarzon Ɗan wasan Atalanta.

Ademola, ɗan wasan gaba ne mai ƙwazo da sa’ar zura ƙwallo a raga.

 

A ranar 22 ga Mayu, 2024, Lookman ya yi wata muhimmiyar bajinta, inda ya ci hat-trick (ƙwallaye uku a jeri cikin wasa ɗaya) a wasan da Atalanta ta doke Bayer Leverkusen da ci 3-0 a wasan ƙarshe na UEFA Europa League. Wannan ɗaukaka ce ta farko da Atalanta ta samu a Turai kuma babban kofi na biyu a cikin shekaru 61.

Wasanninsa a Ingila zuwa Najeriya

Lookman ya fara balaguro a tsakanin ƙasa da ƙasa da ƙungiyoyin matasan ‘yan wasan Ingila, ciki har da 2017 FIFA U-20 da suka lashe gasar cin kofin duniya. A shekarar 2020, ya sauya sheka zuwa Najeriya, ƙasarsa ta gado, inda ya buga wasansa na farko a Super Eagles a shekarar 2022. Ya taka rawar gani a fafatawar da Najeriya ta yi a wasan ƙarshe na cin kofin nahiyar Afirka na 2023.

Wasan ƙarshe na gasar Europa League na Lookman ya ƙara masa ɗaukaka, inda ya samu jinjinar 10/10 daga L’Équipe. Wannan wani yabo ne da ba kasafai ake samun shi ba ya sanya shi cikin rukunin jarumai kamar Lionel Messi, Neymar, da Erling Haaland, wanda hakan ke nuna ƙwarewarsa da tasirinsa a wasannin ƙwallon ƙafa.

Lookman ke nan yake murnar zura ƙwallo a raga a cikin wasannin ya taka leda a kulob ɗinsa.

 

Cigaban Ademola Lookman daga filayen gida na Peckham zuwa kungiyoyin kwallon kafa na Afirka shaida ce ga basirarsa da aiki tuƙuru da kuma juriya. A matsayinsa na Gwarzon ɗan wasan Afrika na shekarar 2024, ya ci gaba da zaburar da wasu ‘yan wasan ƙwallon ƙafar masu kishin ƙasa a faɗin nahiyar.

An zabi Lookman a cikin tawagar ‘yan ƙasa da shekara 20 ta Ingila don buga gasar cin kofin duniya ta FIFA U-20 na 2017. Ya zura ƙwallaye uku a gasar, biyu a kan Costa Rica a zagaye na 16 na ƙarshe da ƙwallo ɗaya a ragar Italiya a wasan kusa da na ƙarshe. Ingila ta doke Venezuela 1–0 a wasan ƙarshe, don samun nasarar farko a gasar cin kofin duniya tun bayan gasar cin kofin duniya ta 1966.

Lookman ya samu kiransa na farko don buga wa Ingila ‘yan kasa da shekara 21 don neman cancantar shiga gasar cin kofin Turai da ta Netherlands ta ‘yan ƙasa da shekara 21 da kuma Latvia ‘yan ƙasa da shekara 21 a watan Satumba 2017.

Lookman ya ƙi amincewa da tayin Najeriya a farkon shekarar 2018 bayan ya gana da shugaban hukumar ƙwallon ƙafar ta Najeriya. Daga baya ya yi watsi da buƙatun Najeriya a karo na uku a watan Satumbar 2018, bayan da babban manajan Ingila, Gareth Southgate ya tabbatar masa da cewa yana cikin yarjejeniyarsa.

Duk da nasarar da ya samu a Ingila a matakin matasa, kuma a baya ya yi watsi da tayin Najeriya, a watan Janairun 2020 hukumar ƙwallon ƙafa ta Najeriya ta sanar da cewa Lookman zai sauya sheka zuwa Najeriya. A ranar 10 ga Fabrairu 2022, FIFA ta amince da buƙatar Lookman na wakiltar tawagar Najeriya. Lookman ya fara bugawa Najeriya wasa ne a ranar 25 ga Maris, 2022, a wasan da suka tashi babu ci da Ghana a wani ɓangare na zagaye na uku na matakin cancantar shiga gasar cin kofin duniya ta FIFA 2022.

Lookman shi ne gwarzon ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Afrika na shekarar 2024 CAF.

 

Lookman ya kasance cikin ‘yan wasan Najeriya da za su buga gasar cin kofin Afirka ta 2023 da aka gudanarwa a Ivory Coast. Ya zura wa Najeriya ƙwallayen biyu a wasan da suka doke Kamaru da ci 2-0 a zagayen ƙungiyoyi 16, kafin su ci ƙwallo ɗaya tilo a wasan da suka doke Angola da ci 1-0 a wasan kusa da na ƙarshe. Najeriya ta sha kashi a wasan ƙarshe da Ivory Coast 1-2. Lookman da sauran tawagar Najeriya an karrama su domin nuna kwazonsu.

Salon taka ledar Lookman

Lookman ƙwararren ɗan wasan gaba ne, yana da gudu sosai, yana kai hari sosai kuma mai cin ƙwallo ne, yana haifar da matsala ga abokan karawa saboda saurin ƙafarsa da kuma kula. Yana da ƙwazo wajen zura ƙwallo a raga kuma yana da damar aiki da kafafunsa biyu, da kuma kansa. Lookman ɗan wasa ne mai ƙirƙira, wanda zai iya banƙara tsaron abokan karawa tare da dabarar wucewarsa da wayo.

Karammawa

Ya samu karramawa a ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa daban-daban a wasannin da ya taka leda a ciki;

  • Atalanta: UEFA Europa League: 2023–24
  • England U20: FIFA U-20 World Cup: 2017
  • Nigeria :Africa Cup of Nations runner-up: 2023

A matsayinsa na ɗan wasa ma ya samu lambobin yabo da dama da suka haɗa da;

  • LFE Apprentice of the Year (Championship): 2015–16
  • Atalanta Player of the Season: 2022–23, 2023–24
  • Africa Cup of Nations Team of the Tournament: 2023
  • UEFA Europa League Team of the Season: 2023–24
  • African Footballer of the Year: 2024
  • CAF Team of the Year: 2024

Ƙungiyoyin ƙwallon ƙafar Lookman

Ga jerin ƙungiyoyin da Lookman ya bugawa leda da adadin shekarun da ya kwashe har da adadin ƙwallayen da ya zura a raga tun lokacin da ya tsinci kansa a duniyar tamaula;

ShekaraKulob Adadin ƙwallaye
2008–2013Waterloo
2013–2015Charlton Athletic
2015–2017Charlton Athletic10
2017–2019Everton 1
2018RB Leipzig (a matsayin aro) 5
2019 – 2022RB Leipzig(0)
2020–2021Fulham (a matsayin aro)(4)
2021–2022Leicester City (a matsayin aro)6
2022Atalanta33

Ga kuma jerin ƙungiyoyin da Lookman ya bugawa leda na ƙasa da ƙasa,

ShekaraƘasaAdadin ƙwallaye
2016     England U190
2016–2017England U204
2017–2019England U211
2017–2019Nigeria27

Manazarta

FotMob (n.d.): Ademola Lookman – stats, career and market value. FotMob 

My Nigeria (n.d.): Ademola Lookman, Biography. My Nigeria. 

Nlebem, A. (2024, December 17). Ademola Lookman: 10 interesting facts about the African Player Of the Year – Businessday NG. Businessday NG. 

Was this article helpful?
YesNo

You cannot copy content of this page

×