Makami mai linzami, wanda ake kira missile a turance, wani nau’in makami ne na zamani da ake harbawa daga wani wuri zuwa wani wuri mai nisa domin kai hari bisa wata manufa ta soja ko ta tsaro. Abin da ya bambanta makami mai linzami da sauran makamai shi ne yana tafiya da kansa bayan an harba shi, ba kamar harsashi ko bam na da, da ake jefa su su faɗi ba. Wannan makami yana amfani da injin motsawa da kuma tsarin jagoranci domin ya bi hanya madaidaiciya zuwa inda aka nufa, koda kuwa wannan wuri yana da nisa sosai ko yana motsi.
Makami mai linzami yana iya ɗaukar abubuwan fashewa iri daban-daban, kama daga bam har zuwa manyan makamai masu ƙarfi kamar na nukiliya, gwargwadon irin aikin da aka tsara masa. A aikace, ana ƙera makami mai linzami ne domin ya iya kauce wa kariyar abokan gaba, ya gano inda aka nufa da shi, sannan ya bugi wurin daidai yadda zai yi tasiri. Wannan ne ya sa ake ɗaukar shi a matsayin ɗaya daga cikin manyan makaman zamani da suka sauya yanayin yaƙe-yaƙe, domin yana ba ƙasa damar kai hari daga nesa ba tare da kusantar maƙiyi ba.
Haka kuma, makami mai linzami yana aiki ne da haɗin gwiwar manyan sassa kamar injin da ke ba shi ƙarfin tashi, tsarin sarrafa hanya wanda ke tabbatar da cewa bai ɓace ba, da kuma na’urar gano manufa wadda ke taimaka masa ya bugi wurin da aka nufa kai tsaye. Saboda wannan haɗakar fasahohi masu rikitarwa, ƙirƙira da sarrafa makami mai linzami na buƙatar ilimin kimiyya da fasaha mai zurfi, musamman a fannoni kamar injiniyanci, lissafi, da ilimin sararin samaniya.
Asalin fasahar makami mai linzami
Asalin fasahar makami mai linzami ta samo tushe ne tun daga tsoffin rokoki da mutane suka fara ƙirƙira ƙarnoni da dama da suka gabata. An fara amfani da irin waɗannan rokoki ne a matsayin kayan yaƙi a wasu sassan duniya, musamman a Asiya, inda aka yi amfani da su domin tsoratar da abokan gaba da kuma jefa abubuwan fashewa daga nesa. Duk da cewa waɗannan tsoffin rokoki ba su da tsarin jagoranci (guided system) ko daidaito, sun zama tushen da ya haifar da bincike da ƙirƙira a fannin makaman da ke tashi da kansu.
A hankali masana kimiyya suka fara fahimtar yadda motsin roka ke aiki, musamman dangane da ƙa’idojin motsi da ƙarfin turawa daga gas mai fita daga injin roka. Wannan fahimta ta haifar da sabbin gwaje-gwaje da suka kai ga samar da rokoki masu ƙarfi da za su iya kai abubuwa nesa sosai, wanda daga baya ya zama tubalin fasahar makami mai linzami na zamani.
Cigaban fasaha a lokacin Yaƙin Duniya na II
Babban cigaba a fasahar makami mai linzami ya faru ne a lokacin Yaƙin Duniya na Biyu, lokacin da ƙasashe masu yaƙi suka fara neman hanyoyin kai hari daga nesa cikin sauri da ƙarfin gaske. A wannan lokaci ne aka zuba jari mai yawa a binciken kimiyya da ƙera makamai masu linzami, domin samun rinjaye a kan abokan gaba. Fasahar roka ta samu cigaba sosai, musamman a Turai, inda aka haɗa ilimin injiniya, lissafi, da kimiyyar makamashi domin ƙirƙirar makamai masu iya kai hari daga nesa mai nisa.
Rokar V-2 da Jamus ta ƙera
Daya daga cikin muhimman nasarorin wannan lokaci akwai ƙirƙirar rokar V-2 da Jamus ta yi. Wannan roka ita ce ta farko a duniya da ta iya tashi zuwa sararin sama sannan ta faɗo kan wurin da aka manufa a nesa sosai da kuma saurin gaske. Rokar V-2 ta nuna cewa ana iya kai hari daga nesa ba tare da amfani da jirgin sama ba, kuma ta zama ginshiƙin fasahar makamai masu linzami da aka haɓaka daga baya.
Masana da suka yi aiki a kan wannan roka sun taka muhimmiyar rawa a ci gaban fasahar sararin samaniya da makamai bayan yaƙin, domin ilimin da aka samu daga wannan shiri ya zama tushen sabbin makamai da rokoki na binciken sararin samaniya.
Cigaban missiles a lokacin Yaƙin Cacar Baki
Bayan Yaƙin Duniya na Biyu, gasa ta siyasa da ta soja tsakanin Amurka da Tarayyar Soviet ta haifar da sabon babi a tarihin makami mai linzami. Wannan lokaci, wanda ake kira Yaƙin Cacar Baki, ya kasance lokacin da kowanne ɓangare ke ƙoƙarin nuna ƙarfi ta hanyar mallakar makamai masu linzami mafi girma da nisa, musamman waɗanda za su iya ɗaukar makaman nukiliya.
An ƙera manyan makamai masu linzami masu iya ketare nahiyoyi, waɗanda ake iya harbawa daga wata ƙasa su kai hari a wata ƙasa mai nisa sosai cikin ɗan lokaci kaɗan. Wannan cigaba ya sauya tsarin tsaron duniya, domin ya sanya yiwuwar yaƙin duniya ya zama barazana mai girma. Haka kuma, binciken da aka yi a wannan lokaci ya taimaka wajen bunƙasa fasahar sararin samaniya, domin irin waɗannan rokoki ne suka zama tushen ƙaddamar da tauraron ɗan Adam da kuma jiragen binciken sararin samaniya.
Sassan makami mai linzami
Makami mai linzami na zamani ba wani abu guda ɗaya ba ne, haɗin manyan sassa ne na fasaha da aka tsara su yi aiki tare cikin daidaito domin tabbatar da cewa makamin ya tashi, ya bi hanyar da aka nufa, sannan ya kai hari yadda aka tsara. Waɗannan sassa sun haɗa da; ilimin injiniyanci, kimiyyar makamashi, sarrafa na’urori, da fasahar kayan aiki masu jure zafi da matsin lamba. Idan wani sashe daga cikin waɗannan ya samu matsala, makamin na iya gaza kaiwa ga manufa ko ma ya lalace kafin ya isa inda aka nufa.
Jikin makamin (airframe)
Jikin makami mai linzami, wanda ake kira airframe, shi ne ginshiƙin da ke riƙe da dukkan sauran sassan makamin. Wannan jiki yana da muhimmanci sosai domin shi ne ke ba makamin siffarsa, ƙarfinsa, da ikon jure matsin iska da zafin da ke tasowa yayin tashi cikin sauri mai tsanani. Ana ƙera shi da kayan da suke da sauƙin nauyi amma masu ƙarfi ƙwarai, kamar wasu nau’ikan ƙarafa na musamman ko kayan haɗe-haɗen sinadarai da aka ƙera domin jure yanayi mai tsauri.
Tsarin jikin makami yana da matuƙar muhimmanci wajen rage gogayya da iska yayin tafiya, domin gogayya mai yawa na iya rage sauri ko ma janyo zafi da zai lalata makamin. Saboda haka, ana tsara shi da siffa mai kaifi a gaba domin ya ratsa iska cikin sauƙi yayin tafiya. Haka kuma, jikin yana ƙunshe da ɗakuna daban-daban da ake saka injin tura makamin, tsarin jagoranci, kayan fashewa, da sauran na’urori.
A wasu nau’o’in makamai masu linzami, jikin na iya rabuwa gida-gida yayin tafiya, musamman a manyan makamai masu nisa, inda wani ɓangare zai ƙare aikinsa ya faɗi yayin da sauran sassan ke ci gaba da tafiya. Wannan tsari yana taimakawa wajen rage nauyi domin ƙara sauri da nisan da makamin zai iya kaiwa.
Injin tura shi (propulsion system)
Injin tura makami mai linzami shi ne abin da ke ba shi ƙarfin motsi domin ya tashi daga wurin da aka harba shi ya kuma ci gaba da tafiya har zuwa inda aka nufa. Wannan tsarin yana aiki ne ta hanyar ƙone wani nau’in mai wanda ke haifar da tururi ko gas mai ƙarfi da ke fita da ƙarfi daga bayan makamin, wanda hakan ke tura shi gaba bisa ƙa’idojin motsi na kimiyya.
Akwai manyan nau’o’i biyu na tsarin tura makami mai linzami, waɗanda suka bambanta da irin man da suke amfani da shi da kuma yadda suke aiki.
Solid fuel
Makami mai linzami mai amfani da solid fuel yana amfani da nau’in mai mai ƙarfi wanda aka riga aka sarrafa shi ya zama kamar wani abu mai kama da roba ko dutse a cikin injin makamin. Wannan nau’in mai yana ƙonewa ne a hankali amma da ƙarfi sosai, yana samar da gas mai zafi da ke tura makamin gaba. Babban amfanin wannan tsari shi ne sauƙin adanawa da kuma shirya makamin domin harbawa cikin gaggawa, domin ba sai an haɗa wani mai kafin amfani ba.
Haka kuma, injin mai ƙarfi yana da sauƙin sarrafawa a fannin tsaro, domin ba ya buƙatar tsarin bututun mai mai rikitarwa. Sai dai, da zarar an kunna shi, ba a iya dakatar da ƙonewar sai ya ƙare gabaɗaya, wanda hakan ke nufin makamin zai ci gaba da tafiya har sai man ya ƙone. Wannan na iya rage ikon sarrafa makamin idan aka kwatanta da wasu nau’o’in injuna.
Liquid fuel
A wannan tsarin kuma, makami mai linzami yana amfani da mai nau’in ruwa-ruwa wanda ake zubawa cikin tankuna daban-daban a cikin jikin makamin. Ana haɗa wannan mai da wani sinadari domin ya ƙone ya samar da ƙarfin turawa. Babbar fa’idar wannan tsari ita ce ana iya sarrafa ƙonewar, a ƙara ko rage ƙarfi, ko ma a dakatar da shi idan akwai buƙata. Wannan yana ba da damar sarrafa tafiyar makamin cikin daidaito sosai.
Sai dai kuma, tsarin mai nau’in ruwa-ruwa yana da rikitarwa sosai, domin yana buƙatar tankuna masu ƙarfi, bututun jigilar mai, da na’urorin sarrafawa. Haka kuma, shirya makamin kafin harbawa na iya ɗaukar lokaci, domin dole ne a cika tankuna da mai kafin amfani. Amma kuma, wannan tsarin yana da amfani sosai a manyan makamai masu linzami da kuma rokoki na sararin samaniya saboda ikon sarrafa tafiya da yake bayarwa.
Tsarin jagoranci (guidance system)
Tsarin jagoranci shi ne zuciyar da ke ba makami mai linzami ikon sanin inda zai tafi da yadda zai isa ga wurin da aka nufa cikin daidaito. Idan har babu wannan tsarin, makamin zai kasance kamar roka ce kawai wadda za ta iya tashi amma ba za ta iya kai hari daidai ba. Tsarin jagoranci yana haɗa na’urori masu auna motsi, kwamfutoci, da na’urorin gano wuraren da aka nufa domin kula da hanyar da makamin ke bi tun daga lokacin da aka harba shi har zuwa lokacin da zai bugi wurin da aka nufa.
Wannan tsarin yana iya aiki ta hanyoyi daban-daban gwargwadon irin fasahar da aka saka a cikin makamin da kuma irin aikin da aka tsara masa. A wasu lokuta makamin yana bin hanyar da aka riga aka tsara masa tun kafin harbawa, yayin da a wasu lokuta kuma yana iya bin abu mai motsi kamar jirgin sama ko jirgin ruwa. Saboda haka, tsarin jagoranci yana ɗaya daga cikin sassan da suka fi rikitarwa a ƙirar makami mai linzami.
Inertial gbuidance
Tsarin inertial guidance yana aiki ne ta amfani da na’urori masu auna motsi da juyawa domin gano yadda makamin ke tafiya a sarari. Wannan tsarin ba ya buƙatar wata sigina daga waje, domin yana lissafa tafiyar makamin ne ta amfani da bayanan da yake samu daga na’urorin da ke ciki. Ana saka na’urori masu auna sauri da karkata a cikin makamin, waɗanda ke ba kwamfuta damar sanin matsayin makamin a kowane lokaci.
Babban amfanin wannan tsari shi ne ba ya dogaro da wani abu daga waje, wanda ke nufin ba za a iya katse shi ta kowace hanya ba. Saboda haka, ana amfani da shi a makamai masu linzami na nesa mai tsawo. Duk da haka, idan tafiya ta yi tsawo sosai, ƙaramin kuskure a lissafi na iya ƙaruwa har ya jawo makamin ya ɗan kauce daga inda aka nufa.
GPS guidance
Tsarin GPS guidance yana amfani da sigina daga tauraron dan Adam domin gano ainihin wurin da makamin yake a duniya. Ta wannan hanya, makamin yana iya sanin matsayinsa da kuma gyara hanyar da yake bi domin ya isa wurin da aka nufa cikin daidaito. Wannan tsari yana ƙara ingancin makamai masu linzami sosai, musamman wajen kai hari kan wuraren da aka riga aka sani a taswira.
Duk da cewa wannan tsari yana da daidaito mai girma, yana dogaro ne da siginar da ke fitowa daga sararin samaniya. Idan aka katse wannan sigina ko aka yi masa katsalandan, makamin na iya rasa daidaitonsa. Saboda haka, a wasu makamai ana haɗa GPS da inertial guidance domin su taimaka wa juna.
Laser guidance
Laser guidance yana aiki ne ta hanyar hasken laser da ake tsara da shi kan wurin da ake so a kai hari. Ana iya haskaka wannan wurin daga ƙasa, daga jirgin sama, ko daga wata na’ura mai sarrafa kanta. Makamin yana bin hasken laser ɗin ne har sai ya kai ga wurin da aka nufa.
Wannan tsari yana da amfani sosai wajen kai hari kan wuri ko abu guda ɗaya da ake gani a fili, kamar tanki ko gini. Yana ba da daidaito sosai, amma yana buƙatar a ci gaba da haskaka wurin har sai makamin ya isa. Idan hasken ya ɓace ko aka katse shi, makamin na iya rasa inda zai tafi.
Radar guidance
Radar guidance tana amfani da radio waves domin gano wuri ko abin da aka nufa da kuma bibiyarsa yayin da makamin ke tafiya. A wasu lokuta makamin da kansa ne ke aika siginar radar, ya kuma karɓi amsar da ta dawo domin sanin inda abu yake. A wasu lokuta kuma ana iya jagorantar makamin daga wata na’ura ta waje wadda ke bibiyar makamin da abin da aka nufa lokaci guda.
Wannan tsari yana da amfani sosai wajen kai hari kan abubuwan da ke motsi, musamman jiragen sama ko jiragen ruwa. Yana iya aiki ko da cikin duhu ko yanayin da ba a iya gani sosai. Sai dai kuma, ana iya yin katsalandan ga radar ta hanyar amfani da wasu na’urori na musamman da ke rikitar da siginar.
Nau’in ababen fashewa (warhead)
Warhead shi ne ɓangaren makami mai linzami da ke ɗauke da abin fashewa ko wani nau’in makami da zai lalata wuri ko abin da aka nufa. Wannan shi ne ainihin dalilin ƙera makamin, domin duk sauran sassa suna aiki ne domin kai wannan ɓangare zuwa inda aka nufa. Nau’in warhead da aka saka a makami yana danganta da irin aikin da aka shirya masa da kuma irin ɓarnar da ake son haifarwa.
Conventional warhead
Conventional warhead yana ɗauke da abubuwan fashewa na asali kamar bam da ake amfani da su a yaƙi. Wannan nau’i yana haifar da lalacewa ta hanyar fashewa mai ƙarfi da tarkace da ke watsuwa a wurin. Ana amfani da shi domin lalata gine-gine, kayan soja, ko taron sojoji. Duk da cewa yana da ƙarfi, tasirinsa yana iyakance ne ga wurin da ya fashe kawai idan aka kwatanta da manyan makamai na musamman.
Nuclear warhead
Nuclear warhead shi ne mafi ƙarfi a cikin nau’o’in warhead, domin yana amfani da makamashin nukiliya wajen haifar da fashewa mai girma ƙwarai. Irin wannan fashewa na iya lalata birni gabaɗaya tare da haifar da zafi, haske, da tiriri mai haɗari. Makamai masu linzami da ke ɗauke da wannan nau’i suna daga cikin manyan makaman da ke barazana ga duniya, saboda ƙarfinsu da kuma tasirin da suke da shi na dogon lokaci ga rayuwa da muhalli.
Chemical ko biological warhead
A wasu lokuta, ana iya saka sinadarai masu guba ko ƙwayoyin cuta a cikin warhead domin su bazu a wurin da aka nufata. Irin wannan makami yana haifar da illa ga mutane ta hanyar guba ko cututtuka maimakon fashewa kawai. Saboda haɗarin da suke da shi ga fararen hula da muhalli, amfani da su yana ƙarƙashin dokoki da yarjejeniyoyin ƙasa da ƙasa.
Nau’o’in makami mai linzami
Makami mai linzami yana da nau’o’i daban-daban waɗanda ake rarrabe su bisa ga yadda suke tafiya, yadda ake harba su, da kuma irin aikin da aka ƙera su domin yi. Wannan rarrabewa tana taimaka wa masana da sojoji su fahimci irin makamin da ya dace da kowace manufa, domin ba duk makamai masu linzami suke aiki iri ɗaya ba. Wasu an ƙera su domin kai hari daga nesa mai tsawo, wasu domin kariyar iska, yayin da wasu kuma aka tsara su domin kai hari kan abubuwan da ke motsi.
Bisa tsarin tafiya
Ballistic missile
Ballistic missile wani nau’in makami mai linzami ne da ke tashi zuwa sararin sama cikin sauri mai ƙarfi sannan ya ci gaba da tafiya bisa hanyar da ƙa’idoji motsi suka tsara har sai ya faɗo kan wurin da aka nufa. Bayan matakin farko na tashi da injin ke tura shi, makamin yana shiga wani yanayi inda yake ci gaba da tafiya ba tare da ƙarin turawa ba, yana kama da yadda dutsen da aka jefa sama ke tafiya kafin ya faɗo ƙasa. Wannan tsarin tafiya yana ba shi damar kaiwa nesa sosai cikin ɗan lokaci kaɗan.
Saboda tsayin da yake kaiwa a sararin sama da kuma saurin da yake samu yayin dawowa ƙasa, yana da wahala a dakatar da shi bayan an harba shi. Wannan ya sa ake amfani da irin wannan makami domin kai hari a nesa sosai, har ma daga wata nahiya zuwa wata. Yayin da yake dawowa cikin sararin duniya, sashin da ke ɗauke da abin fashewa yana fuskantar zafi mai tsanani saboda gogayya da iska, don haka ana ƙera shi da kayan da za su iya jure wannan yanayi.
Cruise missile
Cruise missile kuma wani nau’in makami ne da ke tafiya kusa da doron ƙasa ko saman ruwa yayin da yake bin hanya zuwa wurin da aka aika shi. Ba kamar ballistic missile ba, wannan makami yana amfani da injin da ke ci gaba da tura shi har zuwa lokacin da zai kai hari. Yana iya sauya hanya, kauce wa kariya, ko bin wani tsari mai rikitarwa domin kada a gano shi.
Wannan nau’i yana da daidaito sosai wajen kai hari, domin yana iya amfani da taswira da na’urorin gano wuri domin gyara tafiyarsa. Haka kuma, kasancewarsa kusa da doron ƙasa yana sa ya fi wahalar ganowa da na’urorin kariya. Saboda haka, ana amfani da shi wajen kai hari kan muhimman wurare da ake son a buge su a daidai sosai.
Bisa wurin harbawa
Surface-to-surface
Surface-to-surface missile makami ne da ake harbawa daga doron ƙasa ko wani wuri a ƙasa zuwa wani wuri da aka nufata da ke kan doron ƙasa. Ana amfani da shi domin kai hari kan sansanonin soja, gine-gine, ko wasu wurare na abokan gaba daga nesa. Wannan nau’i na iya kasancewa mai nisa ko gajere gwargwadon yadda aka ƙera shi.
Surface-to-air
Surface-to-air missile an ƙera shi ne domin harba jiragen sama ko wasu makamai da ke sama daga ƙasa. Wannan makami yana da matuƙar muhimmanci wajen kare sararin samaniya na ƙasa daga hare-haren jiragen yaƙi ko makamai masu linzami. Yana amfani da na’urorin gano wurare domin bin jirgin da ke motsi a sama har sai ya same shi.
Air-to-air
Air-to-air missile makami ne da jirgin sama ke harbawa zuwa wani jirgin saman a sararin samaniya. Ana amfani da shi a yaƙin sama tsakanin jiragen yaƙi, inda ake buƙatar makami mai sauri da iya bin abu mai motsi. Wannan nau’i yana da tsarin jagoranci da zai iya bibiyar jirgin da ake hari a kai ko da yana canja hanya cikin sauri.
Air-to-surface
Air-to-surface missile makami ne da ake harbawa daga jirgin sama zuwa wurin da aka nufata a doron ƙasa ko a saman ruwa. Wannan nau’i yana ba jirgin sama damar kai hari daga nesa ba tare da kusantar wurin da ake hari ba. Ana amfani da shi wajen lalata tankuna, gine-gine, ko jiragen ruwa.
Sea-launched missiles
Sea-launched missiles su ne makamai masu linzami da ake harbawa daga jiragen ruwa ko jiragen ruwa na ƙarƙashin teku. Wannan yana ba ƙasa damar kai hari daga cikin teku zuwa wurare a ƙasa ko sama. Irin wannan tsari yana da muhimmanci a yaƙin ruwa, domin yana ba da damar kai hari daga wurin da abokin gaba ba ya tsammani.
Bisa nisan tafiya
Wata muhimmiyar hanya ta rarrabe makamai masu linzami ita ce ta la’akari da nisan da za su iya kaiwa daga wurin da aka harba su zuwa wurin da aka nufata. Wannan rarrabewa yana da tasiri sosai a fannin tsaro da dabarun soja, domin nisan makami yana nuna irin yankin da zai iya kai hari da kuma irin barazanar da yake haifarwa. Makamai masu linzami na iya kasancewa na gajeren zango ko masu nisan zango ƙwarai, gwargwadon irin ƙirar da aka yi musu da ƙarfin injin da suke da shi.
Short-range missiles
Makami mai linzami na gajeren zango shi ne wanda aka ƙera domin kai hari nesa amma ba sosai ba idan aka kwatanta da sauran nau’o’i. Ana amfani da irin wannan makami ne a filin daga ko a yankunan da ke kusa da juna, domin kai hari cikin sauri ba tare da buƙatar makami mai nisa ba. Saboda gajeren nisan da yake kaiwa, shirya shi da harba shi na iya kasancewa cikin sauƙi, kuma yana iya zama wani ɓangare na makaman da ake amfani da su kai tsaye a yaƙi.
Irin wannan makami yana da amfani wajen kai hari kan sansanonin soja, tankuna, ko wuraren da ke cikin iyakar ƙasa ko yankin da ake fafatawa. Duk da cewa ƙarfinsa na yin ɓarna na iya zama mai girma, tasirinsa yana taƙaita ne ga yankin da yake iya kaiwa kawai.
Medium-range missiles
Makami mai linzami na matsakaicin zango yana iya kai hari nesa fiye da na gajeren zango, yana ba da damar kai hari daga cikin ƙasa zuwa wata ƙasa da ke kusa ko yankuna masu nisa kaɗan. Wannan nau’i yana da muhimmanci a dabarun soja domin yana ba ƙasa damar kare kanta ko kai hari ba tare da kusantar maƙiyi ba.
Ana amfani da makamai masu matsakaicin zango a lokutan rikici tsakanin ƙasashe da ke cikin yanki ɗaya, domin suna iya kai hari cikin sauri kuma da ƙarfi. Haka kuma, suna iya zama wani ɓangare na tsarin kariya domin hana maƙiyi kusantar iyaka.
Intermediate-range missiles
Makami mai linzami na matsakaicin zango mai tsawo, wanda ake kira intermediate-range, yana tsakanin matsakaicin zango da na nesa mai tsawo sosai. Wannan nau’i yana iya kai hari nesa mai faɗi wanda ya zarce iyakar yankin ƙasa guda, har ma ya ratsa nahiyoyi idan aka kwatanta da na matsakaicin zango.
Irin wannan makami yana da muhimmanci a tsarin tsaron ƙasa, domin yana ba da damar kai hari daga nesa sosai cikin ɗan lokaci. Saboda haka, yana taka rawa a daidaiton ƙarfin soja tsakanin ƙasashe, musamman a lokutan da ake takun-saka a siyasa ko tsaro.
Intercontinental ballistic missile (ICBM)
Intercontinental Ballistic Missile, wanda ake kira ICBM a taƙaice, shi ne makami mai linzami mafi nisa da aka taɓa ƙirƙira. An ƙera shi domin ya iya tashi daga nahiya ɗaya ya kai hari a wata nahiya mai nisa sosai, yana ketare manyan tekuna da sararin samaniya kafin ya faɗo kan wurin da aka nufata. Wannan makami yana amfani da tsarin ballistic missile, inda yake tashi zuwa sararin sama mai tsayi sannan ya dawo cikin sauri mai tsanani.
Saboda nisan da yake iya kaiwa da kuma saurin da yake samu, ICBM yana daga cikin manyan makaman da ke da tasiri a tsarin tsaron duniya. Yawanci ana haɗa shi da manyan makamai masu ƙarfi, wanda ke sa ya zama wata babbar barazana idan aka yi amfani da shi. Saboda haka, mallakar irin wannan makami yana nuna ƙarfin soja da fasaha na ƙasa, kuma yana taka muhimmiyar rawa a daidaiton iko tsakanin manyan ƙasashe.
Yadda makami mai linzami ke aiki
Aikin makami mai linzami yana gudana ne ta wasu matakai da ke a jere, waɗanda aka tsara su domin tabbatar da cewa makamin ya tashi daga wurin da aka harba shi, ya bi hanyar da aka tsara masa, sannan ya kai hari kan wuraren da aka nufata cikin daidaito. Wannan aiki ya haɗa fasahohi masu yawa, daga injinan turawa zuwa na’urorin sarrafawa da gano wuri, waɗanda duk suna aiki cikin daƙilewa domin kada makamin ya kauce hanya ko ya kasa kaiwa ga inda aka nufa. Kowanne mataki yana da muhimmanci, domin gazawar wani na iya hana makamin cika aikinsa gabaɗaya.
Matakin harbawa
Matakin harbawa shi ne farkon mataki da makami mai linzami ke bi bayan an ba da umarnin kai hari. A wannan lokaci ne injin tura makamin ke kunnuwa, ya haifar da ƙarfi mai yawa da ke ɗaga makamin daga doron ƙasa, jirgin sama, ko jirgin ruwa gwargwadon inda aka harba shi. Wannan mataki yana da matuƙar muhimmanci domin dole ne makamin ya samu daidaiton tashi da kuma alƙiblar da za ta kai shi ga hanyar da aka tsara.
Yayin tashi, na’urorin sarrafawa suna tabbatar da cewa makamin bai karkata ba, domin ƙaramin kuskure a wannan lokaci na iya jawo babbar matsala daga baya. Haka kuma, a wasu nau’o’in makamai masu linzami, sassan farko na injin na iya rabuwa bayan sun gama aikinsu domin rage nauyi, wanda hakan ke taimaka wa makamin ya ci gaba da tafiya cikin sauri da sauƙi.
Matakin tafiya
Bayan makamin ya bar wurin harbawa, yana shiga matakin tafiya inda yake ci gaba da motsi zuwa inda aka nufa. A wannan lokaci, injin turawa da tsarin jagoranci suna aiki tare domin kiyaye hanyar da makamin ke bi. Gwargwadon nau’in makamin, zai iya tashi sama sosai zuwa sararin sama ko kuma ya bi kusa da doron ƙasa domin kauce wa ganowa.
A wannan mataki ne na’urorin da ke auna wuri da sauri suke ci gaba da aika bayanai zuwa kwamfutar da ke cikin makamin, wadda ke gyara tafiya idan akwai karkacewa. Idan makamin yana amfani da sigina daga waje, kamar na tauraron dan Adam ko radar, a nan ne ake amfani da su domin ƙara daidaito. Wannan mataki yana iya ɗaukar lokaci mai tsawo idan makamin na nesa ne, kuma yana buƙatar ingantaccen tsarin sarrafawa domin kada ya ɓace a hanya.
Matakin kai hari
Lokacin da makamin ya kusanci wurin ko abin da aka nufata, yana shiga matakin kai hari wanda shi ne mafi muhimmanci a aikinsa. A wannan lokaci, makamin yana rage tazara tsakaninsa da wuri ko abu cikin sauri, yana kuma yin gyare-gyare na ƙarshe domin tabbatar da cewa zai bugi wurin da aka nufa kai tsaye. A wasu nau’o’in makamai, sashin da ke ɗauke da abin fashewa na iya rabuwa da sauran jikin makamin domin sauƙaƙa kai hari cikin sauri.
A wannan mataki, makamin na iya amfani da na’urorin gano daidai wuri ko abin da aka nufa domin tabbatar da daidaito, musamman idan abin da aka nufa yana motsi. Bayan isa ga tazara mai dacewa, warhead ɗin yana aiki, zai haifar da fashewa ko wani tasiri gwargwadon irin makamin da aka saka.
Tsarin gano wuri ko abin da aka nufa
Tsarin gano wurin ko abin da aka nufata shi ne abin da ke ba makami mai linzami damar gane inda zai kai hari da kuma tabbatar da cewa bai kuskure ba. Wannan tsarin na iya aiki tun kafin harbawa, inda ake saka bayanan wurin da ake son kai hari a cikin makamin, ko kuma yana iya aiki yayin tafiya ta hanyar gano manufa kai tsaye.
A wasu lokuta, makamin yana amfani da na’urorin gano zafi, haske, ko motsi domin bambance manufa daga sauran abubuwa. A wasu kuma, ana iya jagorantar shi daga waje ta hanyar radar ko wasu na’urori. Wannan tsari yana da muhimmanci musamman idan ana kai hari kan abubuwan da ke motsi, domin yana ba makamin damar gyara tafiyarsa har zuwa lokacin da zai kai ga manufa.
Amfanin makami mai linzami
Makami mai linzami yana daga cikin manyan kayan aikin soja da fasaha na zamani da ke taka muhimmiyar rawa a fannoni daban-daban na tsaro, yaƙi, da binciken kimiyya. Duk da cewa an fi sanin shi a matsayin makamin yaƙi, amfani da shi ya wuce hakan, domin fasahar da aka gina shi da ita ta taimaka wajen bunƙasa wasu muhimman fannoni kamar kariyar sararin samaniya da kuma binciken sararin samaniya. Wannan ya sa makami mai linzami ya zama wani ɓangare na tsarin tsaro da cigaban fasaha na ƙasashe masu ƙarfin kimiyya.
Tsaron ƙasa
A fannin tsaron ƙasa, makami mai linzami yana aiki a matsayin kariya da kuma hanyar hana maƙiyi kai hari. Mallakar irin wannan makami na nuna cewa ƙasa na da ikon kare kanta daga barazanar waje, domin tana iya mayar da martani cikin gaggawa daga nesa mai tsawo. Wannan yana taimakawa wajen hana yiwuwar farmaki, saboda maƙiyi zai yi la’akari da irin lalacewar da zai iya fuskanta idan ya kai hari.
Haka kuma, wasu makamai masu linzami ana girke su ne a wurare daban-daban domin su zama wani ɓangare na tsarin kariya, musamman a lokutan da ake fargabar hari. Wannan tsari yana ba ƙasa damar sa ido a kan duk wani motsi da ka iya zama barazana, tare da shirye-shiryen mayar da martani idan an buƙata.
Yaƙi
A lokacin yaƙi, makami mai linzami yana taka muhimmiyar rawa wajen kai hari kan muhimman wuraren abokan gaba daga nesa. Wannan yana rage haɗarin da sojoji za su fuskanta idan suka kusanci wurin da ake yaƙi. Ana iya amfani da shi wajen lalata sansanonin soja, hanyoyin sadarwa, wuraren adana makamai, da sauran muhimman ababen more rayuwa na abokin gaba.
Saboda saurinsa da kuma wahalar dakatar da shi bayan an harba shi, makami mai linzami yana iya sauya yanayin yaƙi cikin ɗan lokaci. Yana ba da damar kai hari ba tare da gargaɗi ba, wanda hakan kan jawo rikicewa ga abokin gaba. Haka kuma, yana iya zama wata hanya ta nuna ƙarfin soja domin tilasta abokin gaba ya janye ko ya shiga tattaunawa.
Kariya ga sararin samaniya (air defense)
A ɓangaren kariyar iska, makami mai linzami yana amfani wajen kare sararin samaniya daga hare-haren jiragen sama, drones, ko wasu makamai masu linzami. Wannan tsari yana haɗa na’urorin gano hari da kuma makamai masu linzami da aka ƙera domin harbo abin da ke sama kafin ya kai hari.
Kariya ga iska tana da matuƙar muhimmanci a wannan zamani, domin hare-haren sama na iya lalata birane da muhimman wurare cikin sauri. Saboda haka, makamai masu linzami na ba da kariya ga iska, suna zama wata garkuwa da ke kare ƙasa daga irin wannan barazana, suna kuma ba da damar daƙile hari kafin ya haifar da mummunar illa.
Binciken sararin samaniya
Fasahar makami mai linzami ta taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa binciken sararin samaniya, domin rokoki da ake amfani da su wajen harba tauraron dan Adam da jiragen bincike suna aiki da irin wannan tsarin turawa da aka samo daga fasahar makamai masu linzami. Duk da cewa manufarsu ta bambanta, asalin kimiyya da injiniyanci iri ɗaya ne.
Rokoki masu kama da makami mai linzami suna ba da damar aika kayan bincike zuwa sararin samaniya domin nazarin taurari, duniyoyi, da sauran abubuwan da ke sama. Haka kuma, suna taimaka wa sadarwa, hasashen yanayi, da tsarin taswira a duniya. Wannan ya nuna cewa fasahar da aka fara domin yaƙi ta zama wata muhimmiyar hanya ta cigaban kimiyya da rayuwar ɗan Adam gabaɗaya.
Ƙasashen da suka fi mallakar makami mai linzami
Mallakar makamai masu linzami na zamani yana da alaƙa kai tsaye da ƙarfin fasaha, tattalin arziki, da tsarin soja na ƙasa. Ba kowace ƙasa ce ke da ikon ƙera irin waɗannan makamai ba, domin suna buƙatar manyan masana’antu, ƙwararrun masana kimiyya, da kuɗaɗen bincike masu yawa. Saboda haka, ƙasashen da suka fi mallakar makamai masu linzami su ne waɗanda suka daɗe suna zuba jari a fannin tsaro da kimiyya.
-
Amurka
Amurka tana daga cikin ƙasashen da suka fi kowa mallakar makamai masu linzami iri daban-daban, tun daga na kariyar iska zuwa manyan makamai masu iya kai hari nesa sosai. Wannan ya samo asali ne daga cigaban fasahar soja da binciken kimiyya da ƙasar ta yi tun bayan Yaƙin Duniya na Biyu.
-
Rasha
Haka kuma, Rasha, wadda ita ce magajiyar Tarayyar Soviet, tana ɗaya daga cikin manyan ƙasashe masu tarin makamai masu linzami a duniya, musamman waɗanda aka ƙera domin kai hari nesa mai matuƙar nisa.
-
Sin
Sin ma ta bunƙasa sosai a wannan fanni, inda take ƙera sabbin makamai masu linzami na zamani domin ƙarfafa tsaronta da tasirinta a duniya.
-
Birtaniya da Faransa
A nahiyar Turai kuma, Birtaniya da Faransa suna daga cikin ƙasashen da suka mallaki makamai masu linzami masu ƙarfi, musamman waɗanda ke iya ɗaukar manyan makamai na musamman.
-
Nahiyar Asiya
A nahiyar Asiya, Indiya da Pakistan sun haɓaka shirye-shiryen makamai masu linzami a sakamakon gasa ta tsaro tsakaninsu. Haka kuma, Koriya ta Arewa ta jawo hankalin duniya saboda gwaje-gwajen makamai masu linzami da take yi, waɗanda ke nuna ƙoƙarinta na nuna ƙarfin soja duk da takunkumin da aka saka mata.
Mallakar irin waɗannan makamai yana tasiri sosai a siyasar duniya, domin yana ƙara ƙarfin tasiri da kariya ga ƙasa, amma a lokaci guda yana haifar da fargaba da takun-saka tsakanin ƙasashe.
Haɗarin makami mai linzami
Duk da muhimmancin makamai masu linzami a fannin tsaro da kariya, suna kuma ɗauke da manyan haɗura ga rayuwar ɗan Adam da muhalli. Amfani da su a lokacin yaƙi na iya haifar da mummunar asara da tasiri na dogon lokaci wanda ba a iya gyarawa cikin sauƙi.
Asarar rayuka da dukiya
Lokacin da aka yi amfani da makami mai linzami, musamman a yankunan da mutane ke rayuwa, sakamakon na iya zama asarar rayuka da dukiya mai yawa cikin ɗan lokaci. Fashewar makamin na iya rusa gine-gine, lalata hanyoyi, da haddasa gobara mai tsanani. Haka kuma, mutane da dama na iya rasa matsugunansu, abin da ke jawo matsalolin jin ƙai da hijira.
Barazanar yaƙin duniya
Yawaitar mallakar makamai masu linzami, musamman masu nisan zango da ƙarfin gaske, yana ƙara yiwuwar ɓarkewar babban yaƙi tsakanin ƙasashe. Saboda saurin da makamin ke yi na kai hari da wahalar dakatar da shi, kuskure ko rashin fahimta tsakanin ƙasashe na iya haifar da rikici mai girma cikin gaggawa. Wannan ne ya sa ake kallon makamai masu linzami a matsayin ɗaya daga cikin abubuwan da ke barazana ga zaman lafiyar duniya.
Tasiri ga muhalli
Fashewar makamai masu linzami na iya haifar da gurbatar muhalli, musamman idan aka yi amfani da su a wuraren da ke da albarkatun halitta ko wuraren zama. Hayaki, tarkace, da sinadarai da ke fita daga fashewar na iya gurɓata iska, ruwa, da ƙasa. Wannan na iya shafar dabbobi, tsirrai, da lafiyar mutane na dogon lokaci.
Haɗarin makaman nukiliya idan an ɗora su kan makami mai linzami
Mafi girman haɗari yana tasowa ne idan makami mai linzami yana ɗauke da makamin nukiliya. Fashewar irin wannan makami na iya haifar da ɓarna mai faɗi wadda kan wuce iyakar wurin da aka kai harin. Baya ga zafi da ƙarfin fashewa, tiririn iskar makamin na iya shafar rayuwa ta tsawon shekaru masu yawa, yana haddasa cututtuka da lalacewar muhalli. Saboda irin wannan haɗari, duniya ta samar da yarjejeniyoyi da dokoki domin takaita yaɗuwar makamai masu linzami masu ɗauke da makaman nukiliya, domin rage yiwuwar amfani da su.
Tarihin ɓarnar makami mai linzami
Yaƙin Gulf, 1991
A lokacin yaƙin Gulf, musamman daga Janairu zuwa Fabrairu 1991, Iraki ta harba makamai masu linzami na Scud zuwa Isra’ila da Saudiyya. A Isra’ila, an harba kusan makamai 39. Rahotannin gwamnatin Isra’ila sun nuna cewa mutane 2 sun mutu kai tsaye sakamakon harin, yayin da fiye da 200 suka jikkata. Daruruwan gine-gine, ciki har da gidaje da ofisoshi, sun lalace musamman a Tel Aviv da Haifa. Asarar dukiya ta kai miliyoyin daloli.
A Dhahran, Saudiyya, a ranar 25 Fabrairu 1991, makami mai linzami ya bugi sansanin sojojin Amurka. Sojoji 28 sun mutu, kusan 100 kuma sun jikkata. Wannan shi ne mafi muni cikin hare-haren makamai masu linzami a wancan yaƙi.
Yaƙin Iraki, 2003
A farkon mamayar Iraki a shekarar 2003, a cikin rikicin da aka fi sani da Iraq War, an yi amfani da makamai masu linzami wajen kai hare-hare kan Bagadaza da wasu manyan birane.
Rahotanni daga Human Rights Watch da wasu kafafe sun nuna cewa a matakan farko na hare-haren “shock and awe”, ɗaruruwan fararen hula sun mutu ko jikkata sakamakon fashewar makamai masu linzami da rokokin soji. Gine-ginen gwamnati, tashoshin sadarwa, da wasu wuraren more rayuwa sun lalace sosai. Duk da cewa ba a fitar da takamaiman adadin gine-ginen da suka rushe gabaɗaya ba, rahotanni sun nuna lalacewar ɗaruruwan gine-gine a Bagadaza kaɗai.
Yaƙin Rasha da Ukraine, 2022 zuwa yanzu
Tun daga Fabrairu 2022 a rikicin Rasha-Ukraine War, an yi amfani da makamai masu linzami masu nisan zango daban-daban wajen kai hare-hare kan birane da muhimman wuraren more rayuwa.
Rahotannin Majalisar Ɗinkin Duniya sun nuna cewa daga 2022 zuwa ƙarshen 2024, dubban fararen hula sun mutu, yayin da dubban mutane suka jikkata sakamakon hare-haren makamai masu linzami da rokokin soji. An lalata dubban gine-gine, ciki har da gidaje, makarantu, asibitoci, da tashoshin wutar lantarki.
A wasu lokuta, hare-haren sun haddasa katsewar wutar lantarki ga miliyoyin mutane a lokacin sanyi, lamarin da ya ƙara tsananta matsalar jin kai. Bankin Duniya ya kiyasta cewa asarar dukiya da ababen more rayuwa da gine-gine ta kai biliyoyin daloli masu yawa tun farkon rikicin.
Rikicin Isra’ila da Iran, 2026
A shekarar 2026, an samu musayar harba makamai masu linzami tsakanin Israel da Iran.
Rahotannin farko daga kafafen labarai na ƙasa da ƙasa sun nuna cewa fiye da mutane 50 ne suka mutu a ɓangarorin biyun gabaɗaya, yayin da daruruwa suka jikkata. Wasu makaman sun kai hari kan wuraren soja, amma wasu sun faɗa kusa da yankunan fararen hula, inda gidaje da cibiyoyin kasuwanci suka lalace. Hukumomi sun ruwaito lalacewar gine-gine da ababen more rayuwa, duk da cewa alƙaluma sun ci gaba da sauyawa yayin da ake tattara bayanai.
Matakan kariya daga harin makami mai linzami
Yayin da makamai masu linzami suke ƙara ƙarfi da sauri a zamanin yau, ƙasashe da dama sun mayar da hankali wajen gina hanyoyin kariya domin rage haɗarin da irin waɗannan hare-hare za su iya haifarwa. Kariyar daga harin makami mai linzami ba ta dogara da makami guda ɗaya ba, illa dai tsari ne mai haɗa fasahohi daban-daban da ke aiki tare domin gano hari tun kafin ya iso, bibiyar shi yayin tafiya, da kuma ƙoƙarin dakatar da shi kafin ya kai ga wurin da aka nufata. Wannan tsarin yana buƙatar haɗin kai tsakanin na’urorin lura, kwamfutoci masu sarrafa bayanai cikin sauri, da makamai na musamman da aka ƙera domin kakkaɓo makami mai linzami a sararin samaniya ko a kusa da ƙasa.
Tsarin kariyar iska
Tsarin kariyar iska shi ne ginshiƙin kariya daga makamai masu linzami. Wannan tsari yana ƙunshe da na’urori da makamai da aka girke a wurare daban-daban domin kare sararin samaniya na ƙasa daga duk wani hari da zai zo ta sama. Ana tsara shi ne domin ya iya gano makami tun daga nesa, ya bibiyi tafiyarsa, sannan ya ɗauki matakin daƙile shi kafin ya kai ga inda ake so.
Wasu ƙasashe suna girke irin wannan tsarin a kusa da manyan birane, sansanonin soja, da wuraren da suke da muhimmanci ga tattalin arziki. Wannan yana taimakawa wajen rage yiwuwar ɓarna idan aka kai hari. Tsarin kariyar iska yana aiki ne a matakai daban-daban, domin wasu makamai ana kakkaɓo su tun suna nesa, wasu kuma a kusa da ƙasa idan sun tsallake matakin farko.
Radar da na’urorin gano hari
Radar da sauran na’urorin gano hari su ne idanu da kunnuwa na tsarin kariya. Su ne ke gano motsin makami mai linzami tun daga lokacin da aka harba shi, suna kuma bibiyar shi yayin tafiya domin a san inda zai faɗo. Waɗannan na’urori suna amfani da siginar ko wasu fasahohi domin gano abubuwan da ke motsi a sararin samaniya ko sama da doron ƙasa.
Da zarar an gano makami, bayanan da aka samu suna shiga cikin kwamfutoci masu sarrafa tsarin kariya, waɗanda ke nazarin hanyar da makamin ke bi da kuma hasashen inda zai iya kaiwa. Wannan yana ba da damar ɗaukar matakin kariya cikin lokaci kafin hari ya kai ga wurin da aka nufata. Ingancin radar da na’urorin gano hari yana da matuƙar muhimmanci, domin jinkiri ko kuskure na iya sa makamin ya tsallake kariya.
Interceptor missiles
Interceptor missiles su ne makamai na musamman da aka ƙera domin su tashi su tare ko su lalata makami mai linzami kafin ya kai ga inda aka nufata. Ana harba su ne bayan an gano hari, kuma suna amfani da tsarin jagoranci domin bin makamin da ake son dakatarwa. A wasu lokuta suna lalata shi ta hanyar fashewa kusa da shi, a wasu kuma suna bugun shi kai tsaye domin rushe shi.
Wannan tsari yana da wahala matuƙa, domin dole ne interceptor ya isa wurin cikin lokaci kuma ya yi daidai sosai, saboda makamai masu linzami na tafiya da sauri ƙwarai. Duk da haka, cigaban fasaha ya sa ƙasashe da dama suka samu nasarar ƙirƙirar tsarin da zai iya kare muhimman wurare daga irin wannan hari.
Makami mai linzami ya kasance ɗaya daga cikin manyan fasahohin soja da suka sauya yadda ake gudanar da yaƙi da tsaro a duniya. Yana ba da damar kai hari daga nesa cikin sauri da daidaito, amma a lokaci guda yana haifar da manyan haɗura ga rayuwar ɗan Adam da zaman lafiyar duniya. Saboda haka, ƙasashe suna ci gaba da ƙera hanyoyin kariya domin rage barazanar da irin wannan makami ke haifarwa.
A lokaci guda, fasahar da aka samo daga ƙirƙirar makamai masu linzami ta taimaka wajen bunƙasa binciken sararin samaniya da wasu fannoni na kimiyya. Wannan ya nuna cewa fasaha guda ɗaya na iya kasancewa da amfani da illa gwargwadon yadda aka yi amfani da ita. Saboda haka, tattaunawa da yarjejeniyoyi tsakanin ƙasashe suna da muhimmanci domin tabbatar da cewa an sarrafa wannan fasaha cikin hikima domin kare rayuwa da zaman lafiya a duniya.
Manazarta
An wallafa wannan makalar 1 March, 2026, sannan an sabunta ta 4 March, 2026.
Sharuɗɗan Editoci
Duk maƙalun da ku ka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta tare da sa idon kwamitin ba da shawara na ƙwararru. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.
Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.