Makero cutar fata ce mai yaɗuwa wadda kwayoyin cuta dangin ‘Fungai’ suke haddasawa a fatar jiki ko a kai da sauransu. Wata ƙwayar cuta ce mai suna ‘dermatophytes tinea’ ke samun damar maƙalewa a fatar jiki ta haddasa wannan cuta ta makero. Kodayake ƙwayoyin cutar sun kasu kashi-kashi, kuma suna haddasa makero iri-iri. Makero ya fi cutar da yara ƙanana saboda rashin kulawa. Sannan yana kama kai, fatar jiki, akaifa, tafukan kafa da hannu da sauransu.

Makero wani irin ciwon fata ne mai ƙaiƙayi da ke yaɗuwa wanda ke haifar lalacewar fata. Wasu nau’ikan magungunan Over-the-counter na iya hana ƙwayar cutar yaɗuwa zuwa wasu sassan jiki ko ga wasu mutanen.
Ƙwayoyin fungai da ke haifar da ƙwayar cutar suna bunƙasa a wurare masu ɗumi da danshi kamar ɗakunan kwana da banɗakunan da jama’a da yawa ke amfani da su. Wannan ciwon fata yana kama kowa kuma yana yaɗuwa tare da haifar da jajayen ƙuraje a fata, masu ƙaiƙayi a zagaye kamar zobe. Yawanci ƙurjen masu laushi ne. Suna yaɗuwa cikin sauƙi kuma ta hanyar haɗuwa. Ana kamuwa cutar makero sakamakon cuɗanya ko saduwa da mai ɗauke da cutar ko dabba ko wani abin. Makero yana fitowa a sassan jiki daban-daban, yana iya bayyana hannaye da ƙafafu da gaɓoɓi har ma da fuska.
Nau’ikan makero
Makeron kai
Makeron kai yana da alamomi ga yara ƙanana a kai wanda su ne suka fi kamuwa da wannan ciwo mai yaɗuwa. Kamar ganin wasu zagayayyun kuraje ƙanana masu ƙaiƙayi sun yi da’ira ko da’irori a kai. Kaɗewar gashi ba tare da an yi aski ba, wato gashin ya zube. Sannan gashin kai zai riƙa datsewa yana faɗuwa ƙasa. Haka kuma makero yana iya sanya kaluluwa a wuraren da yake fitowa a cikin jiki da dukkan alamominsa kamar masassara da sauransu.
Makeron fata
Irin wannan yana nacewa ne a jikin fatar jiki ya riƙa karuwa ko yaɗuwa a fatar jiki a hankali. Yana da ƙaiƙayi da da’irorin ƙuraje ƙanana, wani lokaci za su iya fashewa, ruwa ya riƙa fita. Za a iya ganin tsakiyar makeron babu komai, kuma babu wata alamar cuta a tsakiyar inda ya gewaye.
Makeron tafukan hannu da ƙafa
Baya ga makeron fata da na kai, akwai wanda ke fitowa bisa tafukan hannu ko ƙafa ko cikin hammata da sauransu. Kusan duk matakan kulawa da waɗannan makeron ɗaya ne. Sai dai ana son yin amfani da shan-shabale (GV paint) ga makeron tafukan hannu ko ƙafafu kafin a fara amfani da man kashe ƙuraje, kamar ‘whitfields’ ko ‘smulphur ointment’ da sauran su.
Hanyoyin kula da makero
Makeron kai
Da farko dai a fara aske gashin kan, a riƙa wanke kan da magungunan kashe ƙwayoyin cuta, kamar sinadarin ‘chlorohexidine, cetrimide, dettol, septol, purit,’ wadanda aka hada da ruwa gwargwadon yadda ka’idar haɗa su take a tsarin asibiti.
Akwai man shafawa na ƙuraje kamar ‘whitfield’s ointment, sulphur lotion’ da sauransu waɗanda ake son yin amfani da su sau biyu aƙalla a yini na tsawon sati biyu zuwa wata guda. Akwai kuma magungunan kashe ƙwayoyin cutar da za a iya samu a asibiti da sauran cututtuka da wannan makero zai iya haddasa wa jiki bakiɗaya.
Makeron fata
Kamar makeron kai, inganta tsafta da wanke wurin da waɗannan sinadaran magani masu kashe ƙwayoyin cutar irin su sinadaran ‘dettol’ da sauransu duk ana buƙatar su a wannan nau’i na makero. Wato a kula da wanke wurin sosai kuma a kai a kai, ana shafa ire-iren waɗannan mayamayai masu kashe ƙwayoyin cutar, kamar ‘whitfields’ da sauransu. Haka kuma idan waɗannan makeron suka yawaita, to lalle suna buƙatar magani ko allurai waɗanda likita ne kawai zai tsara su.
Waɗanda suke kamuwa da makero
Makero yana shafar dukkan mutane a kowane mataki na rayuwa. Sai dai akwai waɗanda suka fi haɗarin kamuwa da cutar idan sun kasance:
- Suna da raunin tsarin garkuwar jiki ko cuta mai saurin yaɗuwa kamar lupus.
- Suna shiga cikin wasanni masu alaƙa da cuɗanya, kamar kokawa.
- Suna yin zufa da yawa (hyperhidrosis).
- Suna yin amfani da ɗakunan taruwar jama’a ko wuraren wanka.
- Suna cuɗanya tare da dabbobi masu iya yaɗa ƙwayar cutar.
Yawaitar cutar makero
Makero yana yaɗuwa kuma yana da yawa a cikin mutane. Yana iya shafar kashi 20% zuwa 25% na yawan mutanen duniya a kowane lokaci.
Alamomin cutar makero
Alamomin cutar yawanci suna bayyana tsakanin kwanaki huɗu zuwa 14 bayan fatar jiki ta haɗu da ƙwayoyin fungi da ke haifar da makero, wasu daga cikin alamomin cutar sun haɗa da:
- Ɗan kumburi a fata jaja-jaja mai siffar zobe ko plaques.
- Ƙuraje ƙananu a zagaye.
- Ƙaiƙayin fata.
- Karyewar gashi ko tabo a yankin da abin ya shafa.
Abin da ke kawo makero
Ƙwayoyin fungai na haifar da cutar makero. Irin wannan ƙwayoyin halittar na fungai a zahiri suna rayuwa a kan fata, gashi da farce. Lokacin da muhallan waɗannan ƙwayoyi ya yi zafi da, fungi sukan fara girman ba tare da kulawa ba. Ana iya kamuwa da cutar a duk lokacin da fata ta haɗu da ƙwayoyin fungai masu haifar da makero a yayin cuɗanya da fatar wani daban.
Hanyoyin yaɗuwar makero
Makero yana yaɗuwa. Yana iya bayyana a kan fata, a sama da ƙasa. Manyan hanyoyin yaɗa makero sune:
- Saduwar fata-da-fata tare da mutumin da ke da cutar.
- Cuɗanya da dabbobi masu ɗauke da cutar, mage ko kare da sauran su.
- Taɓawa ko kasancewa a gurɓataccen wuri, kamar ɗakin kwana ko tufafin ‘yan wasan motsa jiki wanda gumi kan jiƙa.
- Yin amfani da kayayyaki tare da mai cutar ko dabba kamar tawul ko kayan shimfiɗa.
- Gurbatacciyar ƙasa.
Gwajin cutar makero
Likita na iya gwaji tare da tantance cutar makero ta hanyar kallon fata tare da tantance alamomin cutar. Zai iya goge wurin don duba ƙwayoyin fata a ƙarƙashin na’urar hangen nesa. Binciken na’ura yawanci ya fi tabbatar da cutar makero.
Magungunan shafawa
Waɗannan su ne magungunan da ake kira Over-the-counter (OTC) irin su man shafawa (creams antifungal), gels ko hoda yawanci suna aiki mai kyau. Irin waɗannan sun haɗa da:
- Clotrimazole (Lotrimin ko Mycelex).
- Miconazole (Desenex).
- Terbinafine (Lamisil AT).
- Tolnaftate (Tinactin).
Idan yanayi da alamomin cutar sun yi muni ko kuma ba su bayyana ba bayan makonni biyu, ana iya buƙatar maganin sha ko haɗiya ta baki daga ƙwararrun masana kiwon lafiya.
Maganin baka
Masana kiwon lafiya na iya rubuta wa mai ɗauke da cutar maganin fungal na sha ko haɗiya ta baki idan nau’in cutar makeron ta fata ce ko a yawancin sassan jiki. Yawancin magungunan ana rubuta wa marar lafiya ya yi amfani da su tsakanin wata ɗaya zuwa uku. Magungunan antifungal na sha ko haɗiya sun haɗa da:
- Fluconazole (Diflucan).
- Griseofulvin (Griasctin).
- Itraconazole (Sporanox).
- Terbinafine (Lamisil).
Shin cutar makero na dawowa?
Tabbas bayan warkewa daga kamuwa da makero, yakan iya dawowa. Cutar kan tafi idan an bi da ita yadda ya kamata. Tilas a bi tsarin jiyya da ƙa’idojin da likita ya shimfiɗa har sai cutar da alamominta sun ƙare gabaɗaya. Idan aka daina amfani da magani ko maganin ya ƙare da wuri kafin warkewa daga cutar, yiyuwar kamuwa da cuta na iya dawowa.
Maganin makero na gargajiya
Magunguna da dabarun gargajiya kamar ruwan tumatir, zuma, man kwakwa, da aloe vera ba a bayyana suna da tasiri a kimiyyance don
maganin makero ba. Wasu daga ciki na iya kawarwa ko rage ƙaiƙayi da kumburi amma ba sa maganin ƙwayoyin fungai ɗin da ke haifar da makeron. A zahiri ma dai, likitoci sun yi gargaɗi game da amfani da su saboda suna iya haifar da buɗewar raunuka da tabo idan an shafa su kai tsaye zuwa wurin da abin ya shafa.
Hanyoyin riga-kafin makero
Ƙwayoyin da ke haifar da cutar makero suna ko’ina. Amma duk da haka, akwai wasu abubuwa da za a iya yi don rage yiwuwar kamuwa da ciwon ko dakatar da shi daga yaɗuwa:
- Tsaftace fata
- Canja safa da kayan ciki aƙalla sau ɗaya kowace rana.
- A guji yin amfani da tufafi ɗaya ga mutane biyu, ko abin tsifa ko tawul.
- Ga masu wasanni, a kula da kayayyakin wasannin da tsaftarsu, kuma kada a yi amfani da riga ɗaya ga ‘yan wasa biyu ko fiye.
- A kula da wanke hannu da sabulu da ruwa bayan an taɓa dabbobi. Idan dabbobin gida suna ɗauke da makero, a tuntuɓi likitan dabbobi.
- A wanke duk kayan shimfiɗa, tawul, da tufafi a cikin ruwan zafi.
- Idan an taɓa sashin jiki da ke ɗauke da makero, a tabbatar an wanke hannu da sabulu da ruwa kafin a taɓa wani sashin jikin ko wani wajen daban.
Manazarta
Dock, E. (2024, August 27). Everything you want to know about Ringworm. Healthline.
Mayo Clinic. (2022, April 26) .Ringworm (body) – Symptoms & causes – Mayo Clinic. Mayo Clinic.
Mustapha, O. (2018c, May 27). Amsoshin tambayoyi daban-daban. Aminiya.
*****
Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.
Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.