An haifi Malam Aminu Kano ne a gidan Malamai a shekarar 1920. Ya kuma yi karatu a Kwalejin nan ta Katsina kafin ya tafi Landan karo ilmi. A wajen karatu ya haɗu da irin su Firayim Minista (daga baya) Sir Abubakar Tafawa-Balewa. Bayan ya dawo ne ya fara karantarwa a Arewacin Najeriya.
Malam Aminu Kano ya yi makaranta ne a jahar Kano ya yi makarantar Shahuci Primary School da Kano Middle School a tsakanin shekara ta 1930 zuwa 1937, a lokacin yana ɗan shekara goma, kuma ya yi karatu a Kaduna college (Katsina College wanda yanzu Takoma Barewa College) a shekara ta 1937. Bayan ya gama ya karantar a Bauchi Middle School a shekarar 1942, a lokacin Abubakar Tafawa Balewa shi ne shugaban makarantar, daga nan sai aka mayar da shi zuwa Maru Teacher’s College, Sokoto.
A cikin watan Satumban shekara ta 1946 an ba shi tallafin karatu zuwa Jami’ar Institute of Education da take a Landan tare da Prime minister na farko a Najeriya wato Alhaji Sir Abubakar Tafawa Balewa. Dawowarsa ke da wuya, aka kafa kungiyar malamai ta Arewa wato (Northern Teachers Association) a Kano, a watan Mayun shekara ta 1948, wadda wannan kungiya ita ce kungiya ta farko da aka fara kafawa a arewacin Najeriya kuma a Kano a matsayin cibiyar kungiyar malamai.
Siyasa da gwagwarmaya
Malam Aminu Kano ya fara siyasa ne tare da Sa’adu Zungur a tsakanin shekara ta 1943 – 1946, inda suka fara kafa General Improvement Union. Su biyun sun yi hoɓɓasa wajen kafa Nothern Elements Progressive Association (NEPA). Malam Aminu Kano ya kasance ɗan adawa ne kwarai ga Turawan mulkin mallaka. Yana sukar su da ɓarna da dukiyar ƙasa, da kuma ‘yan siyasa da ke biya wa Turawa buƙatunsu na kansu. Hakan ya jawo masa cutarwa matuƙa daga Turawa don su rufe masa baki.
A farkon shekara ta 1950 sun kafa jam’iyyun arewa guda biyu, Northern People’s Congress (NPC) wacce aka kafa a kan tsarin MacPherson Constitution na shekarar 1951 da kuma jam’iyyar Northern Elements Progressive Union (NEPU)
Malam Aminu Kano mutum ne tsayayye a duk furucinsa ya na faɗa wa magoya bayansa zallar maganace ta gaskiya. Ɗabi’arsa kawai shi ne faɗar gaskiya kai tsaye ba tare da yi mata wani kwalliya ba. Fahimta da daukar hakan ya rage ga mai sauraro.
Aminu Kano ya shiga rubuce-rubuce da wayar da kai dangane da karɓar ‘yanci daga Turawan mulkin mallaka da kuma sarakuna.
An ce ya zama sakataren kungiyar malamai da Tafawa Balewa ya kafa kuma yake jagoranta mai suna ‘Bauchi Discussion Circle’.
A shekarar 1948, mallam Aminu Kano ya zamo shugaban Makarantar horas da malamai ta Maru da ke sokoto, haka kuma ya zamo sakataren kungiyar malamai ta Arewacin Nigeria.
A wancan lokaci, ya yi ƙoƙarin ɗaukaka darajar makarantun Allo na arewa don karantar da Alƙur’ani ga ɗalibai.
Haka kuma yana Sakkwato, ya shiga kungiyar siyasa ta Jamiyyar Mutanen Arewa, wadda daga baya ta sauya zuwa NPC.
A shekarar 1950, mallam Aminu kano ya jagoranci wasu jama’a suka sauya sheka daga Jamiyyar Mutanen Arewa zuwa kafa sabuwar jamiyyar siyasa mai suna Northern Elements Progressive Union (NEPU). Wannan jam’iyya ta Mallam Aminu Kano, tana ƙunshe da malamai da sauran mutane masu ra’ayin kawo sauyi a Arewa, irin su Magaji Ɗambatta, Abba Maikwaru da Bello Ijumu.
A zaɓen shekarar 1951, jamiyyar NEPU ta mallam Aminu Kano ta tsaya takara a Kano, kuma ta samu gagarumar nasara.
A shekara ta 1954, mallam Aminu Kano ya tsaya takarar ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Kano amma bai yi nasara ba, inda Marigayi Maitama Sule Ɗanmasanin Kano ya kayar da shi zaɓe.
Amma a Zaɓen shekara ta 1959, mallam Aminu Kano ya sake yin takara kuma ya ci, Inda ya zamo ɗan majalisar ƙasa mai wakiltar gabashin Kano, har kuma a majalisar ya samu muƙamin mataimakin bulaliyar majalisa, a lokacin jamiyyar NEPU da NCNC sun samar da haɗin kai ga juna.
Bayan an yi juyin mulkin shekarar 1966, mallam Aminu Kano ya ci gaba da koyarwarsa da kuma gwagwarmaya kamar yadda ya saba, kuma bai sake riƙe muƙamin gwamnati ba har sai da aka karɓe iko da gwamnatin Aguiy Ironsi, Janar Yakubu Gowon ya zama shugaban ƙasa da kakin soja, gabannin soma yaƙin Basasa ke nan, sai aka naɗa Malla Aminu Kano kwamishinan Lafiya.
Daga nan kuma ba a sake sahale damar yin jam’iyyun siyasa ba sai bayan shekaru 12, inda gwamnatin Soja ta ba da damar kafa jamiyyu a shekar 1978, a nan ne Mallam Aminu Kano da Sam Ikoku, da Edward Ikem Okeke suka kafa jamiyar ‘People Redemtion Party’ PRP.
A shekara ta 1979, jamiyyar PRP ta tsayar da Mallam Aminu Kano takarar shugaban ƙasa amma bai yi nasara ba, sai dai jamiyyar ta tsira da kujerar gwamnoni biyu.
Tun a zamanin Jamhuriya ta farko, Mallam Aminu Kano, a matsayinsa na jagoran NEPU, shi ne ya jajirce wajen yaƙi da takurar sarakuna ga talakawa. Domin kuwa ada, kowanne talaka sai ya biya haraji nasa, da na ‘ya’yansa maza, da kuɗin kan ɗaki, da kuɗin sana’ar duk da yake yi, sannan kuma duk da cewa an daina cinikin bayi, amma akwai duddugen bautar da talakawa a lokacin daga sarakuna.
Saboda haka, Mallam Aminu Kano da gudunmuwar da Tafawa Balewa da Sa’adu Zungur da wasunsu, ya shiga ya fita har aka hana sarakuna yin waɗannan aikace-aikace duk kuwa da irin tsana da tsangwama da mabiyansa yan NEPU suka sha.
Haƙiƙa ba za a taɓa mancewa da mallam Aminu Kano ba matsawar ana batun bai wa mata ‘yanci, da hana sarakunan mulki nuna karfi ga talakawansu da kuma kawar da bambancin ƙabilu tsakanin ‘yan Arewa da ma mutanen Nigeria baki ɗaya.
Mallam Aminu Kano shi ne ya tsaya kai da fata don ganin Jihar Kwara ta faɗo yankin Arewa, bisa yadda ya gamsar da al’umma cewar tarihin asalin tafkin kwara na Arewa ne duba daular da Shehu Usmanu Ɗanfodio ya kafa wadda ta tsallaka har tafkin Kwara.
Daga nan kuma ya hori mabiyansa su zamo masu taskance tarihi don gudun asara a ragowar rayuwarsu, kamar yadda aka jiyo shi yana cewa:
“Matuƙar ba mu yi tarihi ba matuƙar ba mu rubuta tarihi ba, matuƙar ba mu zaƙulo mutanenmu na baya da suka yi aiki nagari ba, za mu kasance muna liƙa lambar LENIN data MAO TETUNG”.
(Lenin shugaban Rasha ne na lokacin, Mao kuma shugaban China. Don haka Mallam Aminu Kano na nufin idan har mutum bai kiyaye tarihin ingantattun mutane a cikin al’ummarsa ba, da sannu zai zamo yana ƙaunar shugabannin wasu al’ummar da ba tasa ba).
Wasu wurare da aka sa sunansa
1. Aminu Kano International Airport, Kano State
2. Aminu Kano Teaching Hospital, Kano State
3. Aminu Kano College Of Islamic and Legal Studies, Kano State
4. Aminu Kano Way, Kano State
5. Aminu Kano Village Of Education, Kano State
Malam Aminu Kano ya rasu ne a ranar Lahadi 17 ga watan Afrilun shekara ta 1983, wacce uwargidansa Shatu ta sami gawarsa sanadiyar shanyewar ɓarin jiki da ya samu bayan ya yi jinyar cerebral malaria.
Janar Abdulsalam Abubakar shi ne shugaban mulkin soja na takwas a Najeriya (bayan Ironsi, Gowon, Murtala, Obasanjo, Buhari, Babangida da… Read More »Abdulsalami Abubakar