OKX ita ce manhajar musayar kuɗaɗen cryptocurrency ta uku mafi girma a duniya ta fuskar yawan hada-hadar yau da kullun. Miliyoyin masu amfani da ita daga ƙasashe sama da 100 na iya saya, sayarwa, zuba hannun jari da kasuwanci cryptocurrencies da sauran kadarori masu alaƙa.

An ƙaddamar da manhajar OKX a matsayin OKEX a cikin shekarar 2017 kuma mallakin kamfanin OK Group ce, wanda Mingxing Star Xu ya kafa a cikin shekarar 2013. Star Xu a halin yanzu yana aiki a matsayin Babban Darakta na kamfanin. OKX manhajar musayar cryptocurrency ce ta duniya wacce ke da hedikwata a Seychelles.
Ayyuka da OKX ke samarwa
OKX tana samar da cikakkiyar fasahar hada-hadar kuɗaɗen yanar gizo wato cryptocurrencies wanda aka keɓance don dillalai da manufofin masu saka hannun jari a cikin kasuwar cryptocurrency.
Manhajar tana da zaɓuɓɓukan cinikayya iri-iri, da suka haɗa da tsarin cinikayyar spot trading, inda masu amfani da ita za su iya saye da sayar da kuɗaɗen cryptocurrencies, da tsarin margin trading, wanda ke ba da damarmakin amfani har zuwa 125x a kan wasu kadarori. Sashen cinikayya na manhajar OKX yana bayyana hada-hada ta gaba (future trading) tare da kwanakin ƙarewa daban-daban da tsarin swaps na dindindin waɗanda ba sa ƙarewa. Hakazalika yana ba wa ‘yan kasuwa damar yin hasashe a kan farashi na gaba ko iyakance matsayinsu na yanzu. OKX tana ba da zaɓin cinikayya ga masu amfani da ita.
OKX ta haɗa wasu siffofi da zaɓuka na tsarin DeFi waɗanda ke ba masu amfani da manhajar damar samun kuɗin shiga ta hanyar saka hannun jari a ƙarƙashin sashi na musamman. Masu amfani da manhajar za su iya tura kuɗaɗen cryptocurrencies ɗinsu kai tsaye a kan manhajar, samun tukuicin shiga cikin jerin masu amfani da manhajar, ko shiga aikin mining ta hanyar samar da kuɗi wasu ka’idojin DeFi. Masu amfani da ita za su iya amfani da kadarorinsu na crypto wajen ba da lamuni don samun tabbatacciyar riba.
Tsarin ƙirƙirar asusun OKX
Idan ana bukatar ƙirƙirar asusun OKX, masu amfani da tsarin crypto dole ne su yi rajista kamar yadda ake yi a sauran manhajojin musayar crypto. Da farko, za a samu adireshin imel da kalmar sirri. (Email and password).
Dole ne mutum ya kammala tantancewar (KYC) don samun damar abubuwa masu yawa da kuma ƙarin fasaloli da ɓangarori a fagen hada-hadar cinikayyar cryptocurrency. Wannan ya ƙunshi bayar da bayanan sirri, kamar cikakken suna, ranar haihuwa, da kuma ID card na gwamnati. Dangane da dokokin gida, buƙatun za su bambanta daga ƙasa zuwa ƙasa.
Adadin kuɗaɗen da OKX ke caji
OKX tana da tsari mai sauƙi dangane da yawan cinikayyar kowane mutum da nau’in kasuwancin da yake ciki.
A tsarin spot trading, kuɗaɗen da ake caji yayin hada-hada ba su da yawa ga manyan ‘yan kasuwa masu babban jari, inda masu aikawa ke biyan daga kashi 0.14% zuwa 0.010% yayin da ake cajin masu karɓa daga kashi 0.23% zuwa 0.03%.
A tsarin margin trading ya ƙunshi ƙarin kuɗin ruwa dangane da adadin kuɗin da aka ara da kuma tsawon lokaci.
OKX tana cajin cirar kudi, wanda ya bambanta dangane da nau’in cryptocurrency ɗin da aka cire. Shafin lokaci-lokaci yana kawo tallace-tallace da rangwamen kuɗi don ƙarfafa ayyukan cinikayya. Mallakar asusun manhajar OKX kyauta ne.
Me OKB ke nufi?
OKB ita ce alama ko tambarin kuɗin crypto mallakin kamfanin OKX, wanda ke nuna haɓaka da bunƙasar ayyukan manhajar. Gidauniyar OK Blockchain ta bayyana cewa, OKB alama ce ta ERC-20 wacce ke sauƙaƙe ayyuka daban-daban a cikin manhajar musaya ta OKX. Ɗaya daga cikin manyan abubuwan da ake amfani da shi shi ne ba wa masu riƙe da kuɗaɗe rangwame a kan kuɗaɗen caji, wanda zai iya rage farashin hada-hada a cikin manhajar.
Bugu da ƙari, ana iya amfani da kuɗin OKB don shiga cikin kasuwar saye da sayarwa wadda ke cikin manhajar OKX a wani ɓangare mai suna ‘Jumpstart’, wanda ke ba da dama ga ayyukan fasahar blockchain. Masu riƙe da kuɗin OKB suna fa’idanta da wasu damarmaki, kamar haƙƙin yin zaɓi a kan batutuwan da suka shafi manhajar da damar riƙe kuɗaɗe domin samun ƙarin riba da sauran su.
Tarihin bunƙasar OKX a tsawon shekaru
Tun lokacin da aka ƙaddamar da ita a cikin shekarar 2017, OKX ta haɓaka cikin sauri zuwa babbar manhajar cinikayyar cryptocurrency. A cikin shekararta ta farko, OKX ta gabatar da tsarin cinikin future trading, ta kuma bunƙasa bangaren masu amfani da ita da kuma ƙimar cinikayya ta hanyar samar da cigaba.
A shekarar 2018, manhajar ta faɗaɗa a duniya, ta kafa ofisoshi a ƙasashe daban-daban. A cikin shekarar 2019, OKX ta ƙaddamar da nau’in kuɗinta ga masu amfani da ita, wato OKB, wanda ke ba da rangwame a kan kuɗaɗen cajin hada-hada kamar yadda aka ambata a baya, kuma ta fara samar da fasalin DeFi, tana ba wa masu amfani da manhajar damar yin amfani da nau’ikan kuɗaɗen cryptocurrencies, kuma su shiga tsarin mining. A cikin shekarar 2020, OKX ta sauya suna daga sunanta na asali wato OKEx zuwa OKX.
A cikin shekarar 2021, OKX ta gabatar da sabbin tsare-tsare kamar zaɓin saka hannun jari guda biyu da asusun ajiyar kuɗi mai sauƙi, kuma ta ƙarfafa matakan tsaro. A shekarar 2023, OKX ta sami babban cigaban mai amfani, tare da adadin kasuwancinta akai-akai a matsayi mafi girma a cikin masana’antar hada-hadar kuɗaɗen crypto. Manhajar ta aiwatar da kayan aikin kasuwanci na zamani da cigaba, tana ba da dama ga sabbi da ƙwararrun ‘yan kasuwa.
A shekarar 2024, OKX ta ƙara ci gaba da haɓaka ta hanyar ƙirƙirar sabbin fasahohin blockchain da faɗaɗa tsarin DeFi, ta riƙe matsayinta na jagora a cikin kasuwar hada-hadar cryptocurrency.
Ƙalubalen manhajar OKX
Kamar sauran manhajojin musanya da dama, OKX ta gwada tsare-tsare da yawa kuma ta fuskanci ƙalubale tun lokacin da aka kafa ta. A cikin shekarar 2018, manhajar ta fara cin karo da binciken tsari yayin da hukumomin duniya suka tsaurara sa ido kan manhajojin musayar cryptocurrency. Wannan ya tsananta a cikin watan Oktobar 2019 lokacin da China ta murkushe kasuwancin cryptocurrency da ICOs, wanda hakan ya shafi manhajoji da yawa ciki har da OKX.
A watan Satumbar 2020, OKX ta dakatar da duk wani tsarin cire kuɗaɗe saboda rashin aminta da ɗaya daga cikin masu ruwa da tsakinta mai zaman kansa da ke yin aiki tare da ofishin tsaro na gwamnatin China. Wannan lamarin ya ta’azzara ne a watan Oktobar 2020 lokacin da Star Xu, wanda ya kafa OKX, ya ba da rahoton cewa hukumomin ƙasar Sin sun yi masa tambayoyi game da ayyukan manhajar da bin ka’idoji. OKX ta janye takunkumin cirar kuɗi a watan Nuwamba.
Duk da kasancewar hedikwatar kamfanin ta farko a birnin Beijing, a shekarar 2021, OKX ta sanar da shirinta na dakatar da ayyukanta a kasar Sin gabaɗaya saboda matsin lamba na yau da kullun kan kasuwancin crypto.
Manazarta
CoinMarketCap (n.d.). OKX trade volume and market listings. CoinMarketCap.
McCracken, T. (2024a, March 26). Uncovering pros & cons of OKX App: A comprehensive review. Coin Bureau.
Crypto news (n.d.). OKX: a Crypto-to-Crypto and fiat exchange. crypto.news.
*****
Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.
Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.