Maulidi ya kasance ɗaya daga cikin manyan bukukuwa da Musulmi ke gudanarwa a duniya domin tunawa da haihuwar Annabi Muhammadu (SAW). Duk da kasancewar akwai saɓani tsakanin malamai game da halaccinsa, ya zama al’ada da ake gudanarwa a matsayin tunawa, girmamawa da ƙaunar Annabi (SAW), tare da yin addu’o’i da ilmantar da jama’a.
Ma’anar Maulidi
Maulidi ko Mawlud kalma ce da ta samo asali daga harshen Larabci wadda ma’anarta ita ce haihuwa. Amma a addinin Musulmi ana amfani da ita musamman wajen nuni da rana ko biki na tunawa da haihuwar Annabi Muhammadu (SAW), wanda aka haifa a ranar 12 ga watan Rabi’ul Awwal a shekara ta 570 Miladiyya, wadda ake kira Shekarar Giwaye.
Tarihin asalin Maulidi
Bikin Maulidi bai kasance a lokacin Annabi (SAW) da Sahabbai ba. Amma an fara aiwatar da shi ne a ƙarni na 7 zuwa 8 bayan hijira, musamman a ƙasar Masar, lokacin mulkin daular Fatimiyyun (wani rukuni na Shi’a). Daga baya bikin ya yaɗu zuwa ƙasashen Musulmi daban-daban, ciki har da ƙasar Sham, Bagadaza, Turai ta Musulunci, har ta zo Afirka da Asiya.
A Najeriya, Maulidi ya samu karɓuwa tun lokacin da addinin Musulunci ya shiga ƙasar Hausa da sauran yankuna. Malamai da sun riƙa shirya bukukuwan Maulidi domin koyarwa da tunatar da jama’a game da tarihin Annabi (SAW).
Manufar yin Maulidi
Soyayya ga Annabi (SAW)
Maulidi hanya ce da Musulmi ke amfani da ita wajen nuna ƙauna da girmamawa ga Annabi Muhammadu (SAW). Tunawa da haihuwarsa yana ƙara cusa soyayya cikin zukatan mutane, domin wannan soyayya ita ce ginshiƙin imani. A yayin bikin, ana rera waƙoƙin yabon Annabi da salati a gare shi, wanda hakan ke ƙarfafa haɗin kai tsakanin Musulmi da kuma ƙara nutsuwa ga zukata.
Wa’azi da ilmantarwa
Bikin Maulidi wata babbar dama ce ga malamai su ilmantar da jama’a game da tarihin Annabi (SAW), halayensa da koyarwarsa. Ana karanta littattafan tarihin Maulidi kamar Mawlud Barzanji, ana bayyana mu’ujizai, da kuma labaran da suka shafi addinin Musulunci. Wannan ilmantarwa na taimaka wa jama’a wajen fahimtar muhimmancin bin tafarkin Annabi a rayuwarsu ta yau da kullum.
Addu’a da neman albarka
A yayin Maulidi, ana gudanar da addu’o’i na musamman domin neman rahma da albarka daga Allah. Ana yin istigfari, roƙon lafiya, zaman lafiya, da ci gaban al’umma. Haka kuma, ana raba sadaka da abinci ga talakawa domin taimakon juna. Wannan na ƙarfafa zumunci da taimakon addini.
Haɗin kan al’umma
Maulidi na haɗa mutane wuri guda daga ƙabilu, ƙauyuka, da mazhabobi daban-daban. Wannan taro na zama wata dama ta nuna haɗin kai da haɗa zumunci. Ana samun tattaunawa tsakanin malamai, shuwagabanni, da talakawa, wanda hakan na jawo fahimtar juna da ƙarfafa zaman lafiya.
Ƙarfafa ibada da salati
A lokacin Maulidi, ana ƙara yawaita yin salati ga Annabi (SAW), wanda shi kansa ibada ce mai girma. Haka kuma, ana yawan karatun Qur’ani da zikiri, wanda ke kusantar da musulmi ga Allah. Wannan na ƙarfafa zuciya da ibada da sabo da ayyukan ɗa’a.
Ƙarfafa tarihi da al’adu
Maulidi hanya ce ta ci gaba da adana tarihi da al’adun Musulunci. Ana tunatar da jama’a irin rayuwar Annabi (SAW), da yadda aka samu ci gaban Musulunci daga lokacinsa har zuwa yau. A ƙasashen Hausa, ana rera waƙoƙin Maulidi da salon harshen Hausa na gargajiya, wanda yake sanya jama’a su fi jin daɗin koyon tarihi cikin harshe da al’adarsu.
Yadda ake gudanar da Maulidi
Karanta littattafai
Ɗaya daga cikin manyan abubuwan da ake yi a taron Maulidi shi ne karanta littattafan da suka tattara tarihin haihuwar Annabi (SAW), rayuwarsa, da mu’ujizansa. Littattafan da suka fi shahara a nan sun haɗa da Mawlud al-Barzanji, Simtud-Durar, da Mawlud ad-Dayba’i. Ana karantawa cikin waƙe mai daɗin sauraro ko cikin salo na ƙasida, sannan a yi fassara ga jama’a domin su fahimta. Wannan na sa jama’a su koyi tarihi cikin sauƙi.
Rera waƙoƙin yabo
Waƙoƙin yabon Annabi (SAW) suna taka muhimmiyar rawa a Maulidi. Ana rera su cikin harshen Larabci ko Hausa, ta hanyar ƙasida ko kuma salon waƙar baka. Marubuta irin su Shehu Usmanu Ɗanfodiyo da malaman ɗarikun Sufanci sun yi fice wajen rubuta irin waɗannan waƙoƙi. A wasu wurare kuma, ana amfani da kayan kiɗa na gargajiya kamar ganga da algaita wajen rera su, musamman a ƙasar Hausa.
Wa’azi da tuni
Malamai masu wa’azi suna amfani da damar Maulidi wajen koyar da jama’a darusa na addini da rayuwa. Ana yi wa mutane bayani kan tarihin Annabi (SAW), da irin halayensa kamar gaskiya, amana, adalci, da tausayi. Hakan yana zama darasi ga jama’a su gyara rayuwarsu, su tsarkake zukatansu, su kuma ƙarfafa bin koyarwar Musulunci.
Addu’o’i da zikirai
Wani ginshiƙi a taron Maulidi shi ne yin addu’o’i da zikiri. Ana tuba da istigfari, ana roƙon Allah ya kawo zaman lafiya, ya ba da albarka da ci gaban ƙasa, ya kuma gafarta zunuban al’umma. Ɗarikun Sufaye musamman suna gudanar da zikiri da haɗin kai, inda ake ambaton sunayen Allah da yin salati ga Annabi (SAW).
Al’ada da zamani
A wasu ƙasashe, musamman a Afirka da Asiya, ana haɗa Maulidi da wasu al’adu na gargajiya. A Najeriya misali, ana yin raye-raye, kiɗan mandiri, da kuma liyafar cin abinci. A wasu wurare kuma, shuwagabanni da sarakuna suna amfani da taron wajen raba kayan abinci ga talakawa da ba da kyaututtuka. Wannan ya sanya Maulidi ya kasance ba wai taron addini kaɗai ba, har ma da na zamantakewa da al’adu.
Ra’ayoyin malamai
Akwai manyan ra’ayoyi biyu game da taron bikin Maulidi, rukunin da ke goyon bayan yin Maulidin da kuma waɗanda ba sa goyon baya.
- Malamai masu goyon baya: Suna ganin Maulidi bidi’a ce kyakkyawa (bid’a hasana), tana kyau abar so. Domin tana ƙarfafa soyayya ga Annabi (SAW) da kuma ilmantar da Musulmi.
- Malamai marasa goyon baya: Wasu malaman kuma suna ganin ba a yi shi a zamanin Annabi (SAW) ba, don haka ba wajibi ba ne, maimakon haka ya fi kyau a karanta Qur’ani, yin salati da kuma bin koyarwar Annabi kai tsaye.
Muhimmancin Maulidi
- Ƙarfafa soyayya ga Annabi (SAW): Yana jawo hankalin jama’a kan muhimmancin yin salati a gare shi da bin koyarwarsa.
- Hadin kai: Yana tara jama’a daga ƙabilu daban-daban, yana haifar da haɗin kai da zaman lafiya.
- Ƙarfafa ilimi: Yana zama dama ta koyon tarihi, harshe, waƙoƙin yabon Annabi da kuma ilimin addini.
Bikin Maulidi a Najeriya
A Najeriya, musamman a arewacin ƙasar inda Musulunci ya fi ƙarfi, Maulidi ya kasance ɗaya daga cikin manyan bukukuwa na addini. An shigo da shi ne tun lokacin da Musulunci ya shigo ƙasar Hausa, tare da tasirin malamai daga ƙasar Mali, Sudan da Masar.
A arewacin Najeriya, musamman a Sokoto, Kano, da Katsina, ana karanta littattafan Maulidi kamar Mawlud al-Barzanji da Simtud-Durar a masallatai da gidajen malamai. Malamai suna karanta littattafan cikin salo mai daɗin sauraro, suna fassara wasu sassa cikin Hausa don jama’a su fahimta. Wannan na sa jama’a su koyi tarihin Annabi (SAW) cikin sauƙi.
Waƙoƙin yabo a Najeriya ana rerawa ne da Larabci da Hausa. Misali, a Sokoto, mawakan Tijjaniyya da Qadiriyya suna rera waƙoƙi da ƙasida a gidajen taro. A Kano da Katsina kuma, waƙoƙin Hausa na Maulidi ana amfani da kayan kiɗa na gargajiya kamar ganga, kalangu da algaita da mandiri, wanda ke kawo nishaɗi ga jama’a yayin tunawa da haihuwar Annabi (SAW).
A wasu manyan garuruwa kamar Kano da Sokoto, Maulidi na haɗa al’adu da zamanin yau. Misali, a gidajen sarauta, sarakuna suna tarbar jama’a, suna raba kayan abinci da kyaututtuka ga talakawa. A wasu ƙauyuka, ana gudanar da raye-raye da kaɗe-kaɗen gargajiya, wanda ke ƙara nishaɗi ga Maulidi. Wannan haɗin addini da al’adu ya sa Maulidi ya zama taro na musamman a Najeriya.
Misalan shahararrun tarukan Maulidi a Najeriya
Maulidin Shehu Usmanu Ɗanfodiyo (Sakkwato)
A fadar Sultan na Sakkwato, ana gudanar da ɗaya daga cikin manyan bukukuwan Maulidi a Najeriya. Wannan Maulidi na da tarihi tun daga zamanin Shehu Usmanu Ɗanfodiyo, wanda ya yi amfani da bikin wajen karantar da jama’a tarihin Annabi (SAW) da koyarwarsa. A yau, ana ci gaba da gudanar da shi a matsayin biki na addini da tarihi, inda malamai, sarakuna, da al’umma ke halarta daga sassa daban-daban na Najeriya da ƙasashen waje.
Maulidin Ɗariƙun Sufanci
Ɗariƙun Sufaye irin su Tijjaniyya da Qadiriyya suna gudanar da Maulidi a manyan masallatai da majalisu. A Kano misali, ana yin gagarumin taro a gidajen malamai kamar na Sheikh Nasiru Kabara da sauran fitattun malamai. Wannan Maulidi na haɗa karatun littattafan Maulidi, zikirai, waƙoƙin yabo, da addu’o’i. A Katsina da Bauchi kuma, irin waɗannan taruka na zama wata hanya ta ilmantarwa da kuma nishaɗi ga al’umma.
Maulidi a gidajen sarauta
A gidajen sarakunan Musulmi, musamman a Kano, Zazzau, Katsina, da Sokoto, Maulidi na kasancewa biki na gargajiya da addini. Ana yin karatun littattafan Maulidi a fada, ana rera waƙoƙin yabon Annabi (SAW), sannan a yi addu’o’i da wa’azi. Haka kuma, sarakuna kan raba abinci da kyaututtuka ga jama’a domin nuna karamci da taimakon al’umma.
Maulidin makarantu da ƙungiyoyi
A makarantu da ƙungiyoyin Musulmi, ana shirya Maulidi domin ilmantar da ɗalibai game da tarihin Annabi (SAW). Wannan na haɗawa da wa’azi, karatun Qur’ani, da rera waƙoƙin Hausa na yabo. Ƙungiyoyin al’umma mabiya Ɗariƙar Tijjaniyya da Qadiriyya da Shi’a suna gudanar da shi a kai a kai.
Maulidin ƙauyuka da ƙananan unguwanni
A ƙauyuka da ƙananan al’umma, Maulidi na zama lokaci na musamman na haɗuwa. Ana gudanar da karatuttuka a cikin masallaci, sannan a yi waƙoƙi cikin Hausa da Larabci. Bayan haka kuma, ana raba abinci da kayan ciye-ciye ga jama’a, wanda hakan na ƙara zumunci da haɗin kai tsakanin al’umma.
Tasirin Maulidi ga siyasa da zamantakewa a Najeriya
Haɗin kan jama’a
Maulidi na taka muhimmiyar rawa wajen tara mutane daga ƙabilu, mazhabobi, da al’ummomi daban-daban. Wannan taro na zama wata hanya ta ƙarfafa zumunci da haɗin kai. A Najeriya, inda akwai bambance-bambancen addini da ƙabilu, Maulidi na taimakawa wajen kawar da husuma da samar da zaman lafiya.
Ƙarfafa sarauta da shugabanci
Sarakunan Musulmi da shuwagabannin siyasa suna amfani da Maulidi a matsayin wata dama ta nuna jagoranci da shugabanci nagari. Lokacin Maulidi, ana iya samun sarakuna suna jawabi kan muhimmancin zaman lafiya, adalci, da haɗin kai, wanda hakan ke ƙara musu karɓuwa a idon jama’a. Haka kuma, shuwagabannin siyasa kan halarci Maulidi don nuna kusanci da al’umma.
Hanyar yaɗa saƙon zamantakewa
Malamai da shuwagabanni na amfani da Maulidi wajen isar da saƙonni na musamman da suka shafi al’umma. Ana tattauna batutuwa irin su zaman lafiya, ilimi, taimakon marasa ƙarfi, da guje wa ɓarna. Wannan na sa Maulidi ya zama wata hanya ta ilimantarwa da faɗakarwa ta zamantakewa.
Ƙarfafa zaman lafiya
A Najeriya, inda ake fuskantar matsalolin tsaro da rikice-rikice, Maulidi na zama dama ta yin addu’o’i na musamman domin samun zaman lafiya da kariya daga fitinu. Malamai kan yi kira ga shuwagabanni da jama’a su rungumi adalci da gaskiya. Wannan ya sa Maulidi ya kasance abin da ke taimakawa wajen rage fitintinu a al’umma.
Ƙarfafa al’adu da tattalin arziki
A lokacin Maulidi, ana gudanar da shagulgula, raye-raye, da kasuwanci a wasu wurare. ‘Yan kasuwa kan samu damar sayar da kayayyaki kamar littattafai, turare, tufafi, da kayan abinci. Wannan na sa Maulidi ya zama abin da ke motsa tattalin arziki, musamman a manyan birane kamar Kano da Sokoto.
Ƙarfafa siyasa ta addini
A wasu lokuta, shuwagabannin siyasa kan yi amfani da halartar Maulidi domin jawo hankalin jama’a da samun goyon baya. Duk da haka, malamai kan yi gargaɗi cewa kada a juya Maulidi zuwa hanyar yaƙin neman zaɓe. Amma ba za a iya musanta tasirinsa wajen ƙara kusanci tsakanin shuwagabanni da jama’a ba.
Ƙalubalen Maulidi a Najeriya
Saɓanin ra’ayin addini
Babbar matsala da ake fuskanta game da Maulidi ita ce saɓani tsakanin malamai da mazhabobi. Wasu suna ganin Maulidi ibada ce mai kyau domin tana ƙarfafa soyayya ga Annabi (SAW), wasu kuma suna ganin ba ta da asali a zamaninsa, don haka ba wajibi ba ce. Wannan saɓani na iya jawo muhawara mai tsanani da rarrabuwar kawuna tsakanin Musulmi.
Rabuwar kai a wasu lokuta
Duk da cewa manufar Maulidi ita ce haɗin kai, a wasu wurare yakan haifar da rarrabuwa. Wasu al’umma suna gudanar da Maulidi, wasu kuma suna ƙin shiga, wanda hakan ke kawo rabuwar kai da rashin fahimtar juna tsakanin jama’a.
Shigar al’adun da ba na addini ba
A wasu lokuta, ana haɗa Maulidi da shagulgulan da suka haɗa da kiɗa, raye-raye, ko kuma abubuwan da ba su da tushe a addini. Wannan yana haifar da muhawara tsakanin malamai, wasu na ganin hakan ya lalata ainihin manufar bikin.
Amfani da siyasa
A Najeriya, an sha ganin ana amfani da taron Maulidi a matsayin wajen siyasa. ‘Yan siyasa kan halarci Maulidi domin su jawo hankalin jama’a ko neman goyon baya. Wannan na iya rage darajar kimar taron da kuma karkatar da hankali daga manufar asali.
Tasirin tattalin arziki
Kodayake Maulidi na kawo cigaban kasuwanci a wasu wurare, a wani ɓangare kuma yana jawo kashe kuɗi masu yawa wajen shirya shagulgula da bukukuwa, wanda hakan kan yi nauyi ga wasu jama’a, musamman masu ƙaramin ƙarfi.
Tashin hankali da tsaro
A wasu lokuta, musamman a wuraren da ake da saɓani tsakanin mazhabobi, gudanar da Maulidi na iya jawo tashin hankali. Akwai rahotanni na arangama tsakanin masu goyon bayan Maulidi da masu adawa da shi, wanda ke barazana ga zaman lafiya da tsaro.
Rashin mayar da hankali kan asalin ma’anarsa
Yawancin jama’a sukan ɗauki Maulidi a matsayin lokacin shagali kawai, ba tare da sun mayar da hankali kan karatu, wa’azi, da koyarwar Annabi (SAW) ba. Wannan na rage muhimmancin ilimi da darasin da ya kamata a samu daga Maulidi.
Shawarwarin inganta Maulidi a Najeriya
Samar da fahimtar juna tsakanin mazhabobi
Malamai daga mazhabobi daban-daban su riƙa tattaunawa cikin lumana don fahimtar juna kan Maulidi. Wannan zai rage muhawara da rikici, ya kuma ƙarfafa haɗin kai tsakanin Musulmi.
Mayar da hankali ga manufar asali
Ya kamata a mayar da hankali wajen karantar da tarihin Annabi (SAW), wa’azi, addu’a, da ilmantarwa. Idan aka tsaya kan waɗannan, Maulidi zai kasance abin amfani, ba kuma abin shagali kawai ba.
Guje wa abubuwan da ba addini ba
A guji haɗa Maulidi da abubuwan da ba su dace ba kamar raye-raye, kiɗa na zamani ko kuma shagulgulan da ke ɗauke hankali daga ibada. Wannan zai taimaka wajen tsaftace Maulidi daga abubuwan da ake muhawara a kansu.
Kawar da siyasa daga Maulidi
Ya kamata a guji amfani da Maulidi a matsayin hanyar neman goyon bayan siyasa. Shuwagabanni idan suka halarta, su yi hakan don neman albarka da haɗin kai, ba don nuna siyasa ba. Wannan zai tabbatar da cewa addini ya zauna tsantsar ibada.
Ƙarfafa ilimantarwa
A lokacin Maulidi, malamai su fi ba da muhimmanci wajen faɗakar da jama’a kan ilimi, zaman lafiya, taimakon marasa ƙarfi, da koyarwar Annabi (SAW). Wannan zai taimaka wajen ganin jama’a sun amfana da taron a zahiri.
Gudanar da maulidi cikin tsari da natsuwa
A tabbatar da cewa taron Maulidi yana gudana cikin tsari da kulawa da tsaro, domin kauce wa arangama ko rikici. Hakan na buƙatar haɗin kai tsakanin malamai, sarakuna, da hukumomin tsaro.
Manazarta
Ibrahim, M., & Katz, S. (2022). Remapping the study of Islam and Muslim cultures in postcolonial Nigeria. Africa, 92(5), 755–776. Cambridge University Press.
International Centre for Investigative Reporting. (2021, October 19). Why Muslims celebrate Eid-il-Mawlid – Scholars. ICIR Nigeria.
Wikipedia contributors. (2025, August 31). Mawlid. Wikipedia.
Yusha’u, M. J. (2019). Religious diversity in Sharia-compliant cities in Northern Nigeria. ResearchGate.
Suleiman, I. (2020). The celebration of Prophet Muhammad’s birthday (Mawlid al-Nabiyy) in Nigeria: Unity or disunity? Unity or disunity? International Journal of Humanities and Social Science Research, 6(2), 45–53.
*** Tarihin Wallafa Maƙalar ***
An wallafa maƙalar 5 September, 2025
An kuma sabunta ta 5 September, 2025
*** Sharuɗɗan Editoci ***
Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.
Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.