Skip to content

Memory

Memory card wani lokacin ake kiran sa da Flash Memory card, wata na’ura ce da ake amfani da ita wajen ajiye abubuwa, kamar hotuna, bidiyoyi, wakoki, rubutu da sauran su, cikin na’urorin.masu aiki da lantarki. Na’urar da aka fi sanin suna amfani da memory card su ne: cameras, digital camcorders, handled computers, MP3 players, PDA’s, Wayar salula, game consoles, da printers.

Na’urar ajiye bayanai (Memory card)

Ire-iren memory card

Akwai ire-iren memory card da muke da su da yawa a kasuwa, ko wanne da yanayin girmansa da kuma irin device ɗin da ke amfani da shi, da kuma adadin abubuwan da zai iya ɗauka.

  • CF (compactFlash)
  • Micro SD
  • Micro SDHC
  • Mini SDHC
  • MMC
  • SD card
  • SDHC card
  • Smart Media Card
  • Sony Memory Stick
  • x-d Picture card.

Compact Flash (CF)

Wani irin nau’in memory card ne wanda yawanci aka fi sanin cameras ake sawa, ina nufin kyamarori ne ke amfani da shi, amma ana saka wa wasu devices ɗin. compactFlash yana da ɗan girma a kan sauran memory cards ɗin, sannan yana ɗaukar abubuwa da yawa, da sauƙin yin transfer abubuwa. Duk da haka ya danganta da giga nawa yake da shi. Daɗin-daɗawa yana da ƙwari ba ya lalacewa da wuri.

Micro SD

Ana yawan kiran sa da Micro Secure Digital cards, domin ƙaramin memory card ne wanda aka fi yin amfani da shi cikin wayar salula, portables, da sauran su. Shi ne wanda muke amfani da shi. Ana samun sa da storage ɗin GB zuwa TB.

Micro SDHC (Secure Digital High Capacity)

Komai da komai irin Micro SD ne, banbancin kawai shi ne Micro SDHC ya fi Micro SD ɗibar kaya. Yawanci ana amfani da shi cikin devices ɗin da suke buƙatar waje mai yawa ne.

Mini SDHC

Kamar Micro SD, amma sai dai ya ɗan fi shi girma. Tsofaffin wayoyi ne suka yi amfani da shi. Yanzu ba lallai ba ne a samu Mini SDHC a kasuwa ba saboda an fi amfani da Micro SD da Micro SDHC.

2 terabyte memory

MMC (MultiMediaCard)

Nau’i ne na memory card wanda devices da yawa ke amfani da shi kamar Cameras, music players, da PDAs

MMC da SD card girman su ɗaya, sai dai suna da bambancin configuration. MMC bai kai SD card ɗaukar abubuwa ba sannan devices na zamani ba sa amfani da shi. Ya zama tsohon yayi kenan.

SD Card (Secure Digital Card)

Shi ma kamar Micro SD, ana amfani da shi cikin cameras, wayoyi, tablets da sauran su. Aikinsa ɗaya da Micro SD. Sai dai yawanci idan za a saka Micro SD cikin device din da SD Card take amfani da shi, to dole sai an saka Adapter wadda za ta daidaita girman Micro SD card din ya zo ɗaya da girman SD Card tun da SD card ya fi girma.

SDHC card (Secure Digital High capacity)

Wannan a taƙaice SD Card ne ammma ya fi SD Card ɗaukar kaya, kamar dai shi ne babbansa. Girmansu ɗaya, faɗinsu ɗaya, tsayinsu ma ɗaya, sai dai shi yana amfani da FAT32 FILE SYSTEM, yadda zai ɗauki kayan da suka fi wanda SD Card zai ɗauka.

Smart Media Card

Wannan tun kusan 1990 zuwa 2000 aka yi amfani da shi. A lokacin kyamarori ake sakawa da wasu sauran devices. Smart Media Card amma an daina yayin sa kwata-kwata kuma an daina amfani da shi.

Sony Memory Stick

Wannan kuma kamfanin sony ne ya haɗa don kyamarori, camcorders, da wayoyi wanda kamfanin Sony ya haɗa. Sony Memory Stick yana zuwa kala-kala, tun daga kan Memory Stick PRO, Memory Stick Duo, da Memory Stick Micro. Amma zamani ya sa mutane ba su faye amfani da irin wannan ba, sun fi son SD Card da sauran su.

xD Picture

Shi kuma wannan kamfanin Fujifilm da Olympus ne suka haɗa shi. An haɗa shi ne don digital cameras kawai, amma kasancewar rashin bin ƙa’ida a haka ake amfani da shi yadda ake so. Sai dai a hankali aka daina yayin sa mutane suka manta da shi saboda ba ya ɗaukar kayayyaki da yawa, don haka mutane suke amfani da irin na zamani irin su SD card da Micro SD.

Manazarta

David Taylor (2014). The SD Card Book. CreateSpace.

Micheal Miller. (June 22, 2000.) The complete Guide to Memory cards: A Practical Guide to Understanding and Using memory cards.

Shu Lin and Kai Jin. (2017). Flash Memory: Fundamentals and Applications. Cambridge University Press.

Was this article helpful?
YesNo

You cannot copy content of this page

×