PowerPoint na ɗaya daga cikin manhajoji masu mahimmanci na kamfanin Microsoft, wacce ake amfani da ita don tsara lakcoci kuma a gabatar da su ta hanyar amfani da kwamfuta. PowerPoint wani ɓangare na kudin Microsoft Office Suite, tana ƙunshe da kayan aiki don tsara lakcoci ta hanyar amfani da abubuwa daban-daban don su zama masu kyan gani da ƙayatarwa. MS PowerPoint tana ba da damar yin rubutu mai kyau, yin zane-zane, da saka hotuna da sauti, a haɗa su wuri guda don bai wa mutane damar gabatar da lakcoci da bayanai ta hanya mafi inganci.
Yadda ake buɗe Microsoft PowerPoint
- Click Start Bottom
- Click All Programs
- Select Microsoft Office
- Select Microsoft PowerPoint
Siffofin PowerPoint
Manhajar PowerPoint tana da sauƙin amfani wajen tsarawa da sabunta lakcoci. Yana da mahimmanci mai amfani da wannan manhaja ya san siffofinta da kayan aikin da ke cikinta don shirya lakcoci masu inganci da kuma nagarta. A nan ga wasu muhimman siffofin Microsoft PowerPoint:
Slide layout
Akwai ire-iren layout (wato tsarin yadda shafi yake a PowerPoint) da yawa a cikin slide layout. Ya danganta da irin nau’in lakcar da ake son shiryawa, ana samun waɗannan layouts a cikin sashin Home Tab, kuma ana iya zaɓar dukkan wanda ake ra’ayi a tsara lakca a kai.
Insert Tab
A ƙarƙashin wannan bangare akwai abubuwa da yawa inda mutum zai iya zaɓar abin da yake son sakawa a cikin lakcarsa da yake tsarawa. Wannan na iya haɗawa da hotuna, sauti, bidiyo, alamomi, siffofi, da sauran su.
Slide Design
Microsoft PowerPoint tana da sashen launukan da ake sauya launin shafi iri-iri da su, ta hanyar amfani da waɗannan launuka na shafi za a iya sauya shafin zuwa duk launin da ake so. Hakan yana sa lakcoci su kasance masu kyakkyawan launi kuma suna jan hankalin mutane sosai. Akwai kuma samfuran slide design da ake da su waɗanda manhajar take zuwa da su, mutum zai iya zaɓar duk wanda yake so.
Animation
Wannan fasali ne da ya ƙunshi wasu kayan aiki wadanda ke ba wa rubutu da sauran abubuwan da lakca ta ƙunsa damar motsawa. A lokacin gabatar da lakcar da aka tsara da na’urar kwamfuta, babi-babi na lakcar suna bayyana a kan gilashin kwamfuta ɗaya bayan ɗaya. Wadannan abubuwa da ke ba rubutu da sauran abubuwa damar yin motsi suna samuwa ne a ƙarƙashin Animation Tab.
Slide pane
Slide pane yana daga ɓangaren hagu a shafin, waje ne da yake ɗaukar jerin adadin shafukan da ake amfani da su a wajen shirya lakca. Sukan bayyana ‘yan ƙananu da lamba daga na ɗaya zuwa kan na ƙarshe.
Slide area
Slide area shi ne gundarin shafin PowerPoint, wato nan ne sararin da ake shirya abubuwan da lakcar ta ƙunsa kamar rubutu, hotuna, zane-zane, sauti, bidiyo da sauran su.
Task pane
Task pane sashe ne a cikin manhajar PowerPoint da ke ɓangaren damar shafin, wanda ke ba da damar amfani da kayan aiki irin su animation da sauran su. Baya ga animation akwai nau’ikan abubuwa da dama a task pane.
Presenter view
Presenter view ɓangare ne da ke ba wa mutane damar duba lasifika, rubutun da aka yi, adadin lokaci da kuma samfurin yadda lakcar za ta riƙa bayyana a kan gilashin kwamfuta ko jikin allon haskawa.
Waɗannan siffofin gabaɗaya suna ba da gudummawa ga bunƙasar PowerPoint, kuma sun mayar da ita na’urar shirya lakcoci mai ƙarfi kuma mafi amfani a faɗin duniya.
Amfanin PowerPoint
Wannan manhaja ta PowerPoint tana da matuƙar muhimmanci da amfani ga a fannonin da dama, ga wasu daga cikin bangarorin da ake amfani da PowerPoint:
Ilimi
A tsarin koyo da koyarwa na zamani ta hanyar e-learing da sauran hanyoyin karatu na na’urori, PowerPoint tana taimakawa wajen mayar da ilimi ya zama mai ban sha’awa da jawo hankalin ɗalibai zuwa ga ingantacciyar sigar karatu mai sauƙi.
Talla
A fagen tallace-tallace, PowerPoint na da muhimmanci sosai. Ana amfani da zane-zane, ana iya nuna lambobi a bayyane kuma a sarari waɗanda mai kallo zai iya mantawa da su idan ya kasance karantawa ne zai yi.
Kasuwanci
Ana amfani da PowerPoint a fagen kasuwanci don gayyatar masu saka hannun jari ta hanyar haska ƙaruwa raguwar riba.
Fa’idojin amfani da PowerPoint
PowerPoint dai sananniyar manhaja ce ta shirya lakcoci don gabatarwa ta hanyar amfani da na’urar kwamfuta. Tana da wasu fa’idoji masu yawa ga masu amfani da ita. Ga wasu mahimmai daga ciki;
Visual appeal
Microsoft PowerPoint tana ba da damar ƙirƙirar lakca mai ban sha’awa ta hanyar amfani da kayan aiki da siffofi masu yawa. Ana iya amfani da samfuri, launuka, da layout don ƙawata lakcocin su zama masu ban sha’awa da jan hankali.
Easy to use
PowerPoint tana da tsare-tsaren da mai amfani kan bi su cikin sauƙi, wannan ya mayar da manhajar mai amfani ga kowa a kowane matsw. Akwai kayan aiki da manhajar kan gabatarwa mai amfani su a yayin da yake shirya lakcarsa ko kuma yake gyarawa. Tana ba da damar shiryawa da gabatar da lakca mai kyau.
Flexibility
PowerPoint tana da sauƙi matuƙa ta fuskar ƙirƙirar lakca. Ana iya haɗa nau’ikan abubuwan da lakca za ta ƙunsa daban-daban, kamar rubutu, hotuna, jadawali, bidiyo, da sautuka don jan hankalin mutane yadda ya kamata.
Organization structure
PowerPoint tana da tsarin abubuwa da kan taimaka wajen tsara lakcoci. Ana iya kirkirar lakca mai shakufa da yawa kuma kowane shafi za a iya tsara shi da duk launin da tarin da ake bukata domin lakcar ta zama mai armashi da jan hankalin masu kallo.
Presentation tool
PowerPoint ta haɗa cikakkun kayan aikin shirya kowace irin lakca waɗanda ke taimakawa wajen isar da lakcar cikin sauƙi ga mutane. Mutum na iya amfani da wani ɓangare da ake kira presenter view, don gani da kula da abubuwan da lakca ta ƙunsa, yayin da masu sauraro ke ganin gabatarwar kawai. Misali kamar sauya salon shafin lakca ko animation duk suna yiyuwa ta hanyar amfani da wannan kayan aikin.
Collaboration and sharing
PowerPoint na ba da damar yin haɗin gwiwa cikin sauƙi da raba lakca. Yawanci mutane za su iya aiki lokaci guda a kan lakca iri ɗaya, hakan yana inganta ayyukan haɗaka. Hakazalika za a iya tura kammalalliyar lakca ta imel ko ajiyewa a ma’ajiyar sararin samaniya, ko kuma a shafukan yanar gizo.
Integration with other tools
PowerPoint na ba da damar haɗa sauran aikace-aikacen manhajojin Microsoft Office, kamar Word da Excel. Ana iya shigo da data da charts daga Excel ko a kwafi wani abin tsakanin manhajojin Microsoft Office daban-daban, don rage bata lokaci.
Presenter-audience interaction
PowerPoint na ba da hanyoyi waɗanda ke sauƙaƙe hulɗa tsakanin mai gabatarwa da masu sauraro. Ana iya haɗa hanyoyin mu’amala kamar saka hyperlinks ko buttoms har da tambayoyin kacici-kacici don jan hankalin masu kallo da bibiya.
Portable and accessible
Ana iya adana lakcar da aka tsara a manhajar PowerPoint ta nau’o’i daban-daban, kamar .pptx ko .pdf, don su kasance cikin sauƙi a kan na’urori daban-daban. Wannan tsari yana ba da damar isar da lakcocin a kan kwamfutar tafi-da-gidan ko na’urorin kan tebur ko na’urar projector ba tare da matsalolin rashin dacewa ba.
Time and effort savings
PowerPoint tana sauƙaƙa aikin ƙirƙirar lakcoci, tana rage yawan wahala da bata lokaci. Samfuran shafukan da aka riga aka tsara waɗanda suke zuwa a cikin manhajar da launukan layout da sauran kayan aikin tsara lakca suna ba da damar ƙirƙirar lakcoci masu kyan gani da inganci.
Wasu muhimman bayanai game da PowerPoint
Ga jerin wasu bayanai masu mahimmanci waɗanda ya kamata a sani game da manhajar PowerPoint:
- An fara kirkirar wannan manhaja ne a karkashin wani kamfani mai suna Forethought, Inc. na Robert Gaskins da Dennis Austin.
- An sake ta a ranar 20 ga Afrilu, 1987, kuma bayan watanni 3 da ƙirƙirar ta, sai kamfanin Microsoft ya saye ta.
- Zangon farko na wannan manhaja, lokacin da Microsoft ya gabatar shi ne MS PowerPoint 2.0 (1990).
- Manhaja ce da ta ginu don shiryawa da tsara lakcoci, wadda ke amfani da zane-zane, bidiyo, da sauransu don sanya lakcocin su zama masu ban sha’awa.
- Tsarin file extension na Powerpoint da ake adana aiki da shi a kwamfuta shi ne “.ppt”.
Manazarta
Admin. (2022b, December 22). What is MS PowerPoint? – Introduction, Features & Uses. BYJUS.
TheKnowledgeAcademy. (n.d.). What is PowerPoint Presentation for Students & Professionals? TheKnowledgeAcademy
Vedantu. (n.d.). Introduction to PowerPoint VEDANTU.