Microsoft Word manhaja ce a kwamfuta da manyan wayoyin salula na zamani da ake amfani da ita don yin rubutu kamar rahoto, maƙala da sauran su. Microsoft Word na’urar yin rubutu ce da kuma sarrafa shi wacce shahararren kamfanin samar da manhajoji nan wato Microsoft ya samar. Tana da abubuwan ci gaba waɗanda ke ba da damar tsarawa da gyara rubutu ya fita ta hanya mafi kyau.
Wani lokaci ana kiran manhajar da sunaye kamar Winword, MS Word, ko Word. Tana ɗaya daga cikin manhajojin da ke tallafa wa aikin ofis da ke cikin kundin Microsoft Office. Charles Simonyi da Richard Brodie ne suka kirkire ta a cikin shekara ta 1983.
Akwai Microsoft Word ta na’urorin kwamfuta masu amfani da manhajar Microsoft Windows, Apple macOS, Android, da Apple iOS. Haka nan tana iya aiki a kan manhajar operating system ta Linux ta hanyar amfani da Wine (WINE ba emulator ba ne).
Yadda za buɗe MS Word akan kwamfuta
Donin buɗe manhajar rubutu ta Microsoft Word, bi waɗannan matakai masu sauƙi;
Start menu → All programs → Microsoft Office → Microsoft Word.
Yadda ake rubutu a MS Word
Don yin rubutu da manhajar MS Word, a bi matakan da aka ambata a sama don buɗe Microsoft Word din. Sa’an nan da zarar an bude manhajar, sai danna “File” sannan kuma “New“. Wannan zai buɗe sabon shafi inda za a yi rubutun da sauran aikace-aikacen da manhajar kan ba da damar yi.
Kasancewar mutane a kowane matakin shekaru suna iya amfani da Microsoft Word, walau a makarantu, a kwalejoji da kuma ɓangaren hukumomi da ma’aikatu, samun sahihin ilimin amfani da manhajar ya zama dole.
Siffar Microsoft Word
Hoton da ke ƙasa yana nuna abubuwa daban-daban da ke ƙunshe a cikin MS Word.
Home Tab
Wannan ɓangare yana da abubuwan da kan taimaka wajen gyara rubutu ya zama mai ban sha’awa kamar launin rubutu, girman harufan, salon rubutu, daidaitawa, tazarar tsakanin layukan rubutun, da sauransu. Duk ainihin abubuwan da mutum zai buƙata don sarrafa rubutun da gyara shi suna samuwa ƙarƙashin home tab.
Insert Tab
Abubuwa kamar tables, siffofi, hotuna, zane-zane, lambar shafi, da sauran su duk ana iya shigar da su a cikin rubutu ta hanyar dakko su a cikin insert tab.
Design Tab
Wannan sashe ne a cikin wannan manhaja wanda mutane za su iya zaɓar samfurin shafin da za su aiki a ciki ko ƙirƙirar daftarin aikin yin aikin da kanku. Zaɓin shafin da ya dace zai ƙarawa aikin da za a yi kyau da nagarta.
Page Layout
A ƙarƙashin Layout akwai da abubuwa kamar margins, page orientation, columns, lines spacing, da sauransu.
Reference Tab
Wannan sashe shi ne mafi amfani ga waɗanda ke rubuta project ko rubutun littattafai ko makalu masu tsayi. Akwai abubuwan amfanin wannan ɓangare kamar citation, footnote, table of contents, caption, bibliography, da sauransu a duk suna ƙarƙashin reference tab.
Review Tab
Nazartar haruffan da aka rubuta don a tabbatar an rubuta su daidai babu kuskure da duba ƙa’idojin nahawu da sanin yawan kalmomin da aka rubuta da zaɓar harshe ko fassarar da sharhi da sauranvsu duk ana iya samun su a ƙarƙashin shafin review tab. Wannan dama ce ga waɗanda suke rubuta rubutunsu a kan MS Word.
Baya ga duk abubuwan da aka ambata a sama, ana iya ƙara saita tsarin shafin a cikin view da layout tabs daban-daban, waɗanda za a iya ƙarawa da inganta su ta amfani da View Tab.
Idan aka kwatanta da Microsoft PowerPoint, Microsoft Word ta fi ba da damar yin rubutu, yayin da PPT ta fi mayar da hankali wajen tsara hotuna da bayanai.
Amfanin MS Word
MS Word tana ba wa mutane damar yin rubuce-rubuce, ƙirƙira takardu kamar projects da reports, da sauransu. Wannan manhaja ɗaya ce daga cikin waɗanda aka fi amfani da su a ƙarƙashin kundin Microsoft Office.
Akwai fannoni daban-daban da yawa waɗanda ake amfani da MS Word don sauƙaƙa aiki ga mutane:
Ɓangaren ilimi
Microsoft Word na ɗaya daga cikin mafi sauƙin manhajar da malamai da ɗalibai suke amfani da ita. Ƙirƙirar darasi da rubuta shi yana da sauƙi ta amfani da MS Word kamar yadda za a iya inganta shi ta hanyar saka alamomi da hotuna don sauƙaƙa fahimta. Haka nan ta dace don yin ayyukan assignment kuma a tura wa malami ta yanar gizo.
Ma’aikatu
Rubuta wasiku da lissafin kuɗi da ƙirƙirar rahotanni da takardun samfuri duk ana iya yin su cikin sauƙi ta amfani da MS Word.
Ƙirƙirar da sabunta CV
Microsoft Word daga cikin manhajoji mafi kyawun kayan aikin da ke ba da damar ƙirƙirar CV, da kuma gyarawa da yin canje-canje a ciki gwargwadon bukata.
Marubuta
Mafi soyuwa ga marubuta kasancewar akwai abubuwa daban-daban dangane da rubutun littafi, kamar tsarin abubuwan da ke cikin littafin, da sauransu, ita ce manhaja mafi kyawun kayan aiki wadda marubuta za su iya amfani da su don rubuta littattafai da daidaita su yadda za su ƙayatar.
Haka nan, ana iya ƙirƙirar fayil ɗin Doc da canja shi zuwa tsarin PDF, wannan hanya ce mai sauƙi kuma mafi dacewa.
Adadin layukan rubutu a shafin Microsoft Word
Ba tare an yi sauye-sauye ba, akwai layukan rubutu har guda ashirin da tara (29) a cikin shafi ɗaya na manhajar Microsoft Word.
Nau’ikan fayil ɗin Microsoft Word
Samfuran farko na Microsoft Word an yi amfani da file extension ɗin .doc , yayin da sabbin samfuran Microsoft Word kan fito da file extension na .docx.
Har ila yau akwai sabbin samfuran Microsoft Word na kwanan nan da suke ba damar yin amfani da nau’ikan file extension da dama kamar:
- .doc, .docm, .docx
- .dot, .dotm, .dotx
- .htm, .html
- .mht, .mhtml
- .odt
- rtf
- .txt
- .wps
- .xps
- .xml
Samfuran Microsoft Word
Microsoft Word tana da samfura da yawa a tsawon tarihin samuwar manhajar. An riƙa samun cigaba ta hanayar sabunta ta a shekaru daban-daban.
- Word 1.1, wanda aka saki a 1990
- Word 2.0, wanda aka saki a 1991
- Word 6.0, wanda aka saki a 1993
- Word 95, wanda aka saki a 1995
- Word 97, an fito da ita a 1997
- Word 98, an fito da ita a 1998
- Word 2000, wanda aka saki a 1999
- Word 2002, wanda aka saki a 2001
- Word 2003, wanda aka saki a 2003
- Word 2007, wanda aka saki a 2006
- Word 2010, wanda aka saki a cikin 2010
- Word 2013, wanda aka saki a 2013
- Office 365 da Word 2016, wanda aka saki a 2016
- Word 2019, wanda aka saki a cikin 2018
Manazarta
Admin. (2022, December 21). What is MS Word? – Basics, Uses, Features & Questions. BYJUS.
MyEducator – (n.d.). Introduction to Microsoft Word MyEducator
The Editors of Encyclopaedia Britannica. (2024, July 31). Microsoft Word | Definition, History, Versions, & Facts. Encyclopedia Britannica.