Skip to content

Modem

Modem wani ɓangare ne kuma muhimmiyar na’ura wadda ke canja tsarin siginar dijital zuwa siginar analog da makamancin haka. Wannan wata ingantacciyar hanya ce da ke ba da damar sadarwa tsakanin kwamfutoci da sauran cibiyoyin sadarwa tare da damar canjawa bayanai waje. Akwai nau’ikan Modem iri-iri a yau dangane da ci gaban fasaha kamar dial-up, DSL, cable, fiber optic da satellite modem da sauran su.

51rtkji9jbL
Modem na’ura ce da ke haɗa kwamfuta da yanar gizo (intanet).

Modem, na nufin Modulator/Demodulator, na’urar sadarwa ce mai mahimmanci da ake amfani da ita don taimakawa wajen shiga intanet (yanar gizo) wanda ake canja bayanai daga tsarin analog ɗin zuwa dijital. Yana aiki ne ta hanyar samun siginar analog wanda galibi ake samu ta hanyar layukan tarho tare da canja su zuwa nau’i na biyu na lambobi, wanda ya ƙunshi 0 da 1, ta yadda kwamfutoci da sauran na’urorin dijital za su yi aiki a kai. Wannan na ba da ingantacciyar damar yaɗa bayanai a kan ɗimbin hanyoyin sadarwa, wanda modem na zaman muhimmin abu a cikin tsarin kwamfuta da kuma hanyar sadarwa.

Modem shi ke da alhakin tabbatar da cewa duk bayanan da za a watsa ko karɓa an yi su cikin tsari, ba wannan kaɗai ba ma, modem na taka muhimmiyar rawa wajen inganta saurin canja wa bayanai waje a tsarin dijital daga wannan na’urar zuwa waccan. Cigaban fasaha ya haifar da nau’ikan modem tare da inganta saurin intanet da ka’idoji da yawa waɗanda ke sa ƙwarewar intanet ta fi kyau.

A dunkule, modem shi ne mahimmin ɓangare na hanyoyin sadarwar dijital, yana ba wa masu amfani damar shiga yanar gizo.

Siffofin modem

  • Modem na daidaitawa da inganta sigina lokaci guda.
  • Yana haɗa ƙayyadaddun adadin na’urori zuwa intanet.
  • Farashin modem ya bambanta dangane da fasali da ingancinsa.
  • Ana buƙatar saiti tare da kamfanin ba da sabis na intanet (ISP) don samun damar shiga intanet.
  • Haɗa modem zuwa cibiyar sadarwa yana iya haifar da jinkirin ayyukan yanar gizo.

Yadda modem ke aiki

Domin fahimtar yadda modem ke aiki, ga bayani dall-dalla tare da abubuwan da ke tattare da tsarin:

Data generation

Tsarin moden yana farawa ne daga ƙarshe, wato inda na’urar kwamfuta ke samar da lambobi guda biyu a tsarin binary, wato (0s da 1s) don tabbatarwa ko ana buƙatar aika bayanai.

Modulation

Ana canza bayanan da ke a tsarin dijital zuwa siginar analog ta hanyar modulation (daidaitawa), wanda ya haɗa da gabatar da bayanan tsarin dijital don watsawa a intanet ta hanyar carrier wave.

Transmission

Ana aika waɗannan siginar analog ɗin da aka daidaita a kan layin sadarwa zuwa ɗayan modem wanda shi ne mai karɓar bayanan.

Demodulation

Yayin samar da hanya zuwa modem mai karɓar bayanai, waɗannan hanyoyin sun ƙunshi siginar analog iri ɗaya, waɗanda ke raguwa zuwa nau’ikan siginar da tsarin kwamfuta ke karɓa, wato dijital.

Decoding

Tsari na ƙarshe da na’urar modem ke yi a aikinta shi ne sauya bayanai ta yadda na’urar kwamfuta za ta iya sarrafa bayanan har su zama masu ma’ana a tsarin dijital.

Nau’ikan modem

Modem na da nau’ikansa, suna da fasali daban-daban kuma suna ba da fa’idoji daban-daban. Ga wasu nau’ikan modem da bayanansu daki-daki a ƙasa:

Dial-up modem

Wannan nau’i na modem wani ɓangare ne na kayan aikin kwamfuta da ake amfani da shi don canja bayanan dijital daga kwamfuta zuwa siginar analog wanda ya dace da layukan tarho da mayar da siginar analog zuwa bayanan dijital. Yana ba da damar canja wurin bayanai ta hanyar amfani da daidaitattun hanyoyin haɗin waya domin na’urorin kwamfutoci. Modem ne wanda ke ba da damar haɗa na’urar kwamfuta da layukan tarho, don haka ake samun damar canja wa bayanai6 wuri. Yana iya watsa bayanai a saurin da ya kai 56 Kbps (wato 56 Kilobits a sakan ɗaya).

DSL modem

DSL, ko Digital Subscriber Line, fasahar modem ce da ke ba da damar haɗin intanet mai sauri ta hanyar da amfani da layukan tarho da ake da su. Akwai manyan nau’ikan tsarukan DSL guda biyu:

Asymmetric DSL (ADSL)

Wannan nau’in ya ƙunshi ba da fifikon ƙimar sarrafawa fiye da adadin lodawa; ya fi dacewa ga masu amfanin gida na gama-gari waɗanda ke sarrafa abubuwan da ake da su a cikin yanar gizo maimakon lodawa ko ɗora wasu abubuwan, kamar bidiyo.

Simmetric DSL (SDSL)

Shi ma SDSL yana ba da damar sauri iri ɗaya na duka tsarin ɗorawa da sauke bayanai, wanda ya dace da buƙatun kasuwanci ko masu amfani waɗanda ke buƙatar gudanar bayanai akai-akai, kamar haɗa kiran bidiyo ko loda manyan fayil-fayil zuwa tushen yanar gizo.

modem e87b127f cce9 4070 804d f7c907cc24d7
Modem na amfanin gida ko ofis wanda ba a jona shi da kwamfuta. (Wireless).

DSL fasaha ce ta watsa bayanai wacce ke aiki ta hanyar wayar tarho. Tana da arha sosai fiye da sauran zaɓuɓɓuka masu sauri kamar cable optics, waɗanda ke buƙatar sabbin kayayyakin fasaha. A takaice, modem nau’in DSL hanya ce ta haƙiƙa ta samun haɗin intanet mai kuzari ba tare da kashe kuɗi masu yawa ba.

Cable modem

Cable modem na’urar modem ce ta musamman da ake amfani da ita wajen sadarwa tsakanin kwamfutoci da kamfanonin samar da sabis ɗin intanet wato (ISPs); suna amfani da hanyoyin sadarwar talabijin na USB don haɗa fasahar sadarwar intanet. Wannan modem ɗin yana ɗaukar siginar bayanai a kan layukan kebul na coaxial waɗanda aka ƙera don watsa shirye-shiryen talabijin da juya su zuwa siginar dijital waɗanda kwamfutoci za su iya fassarawa.

Sau da yawa, modem ɗin kebul na’urori ne keɓantattau waɗanda ke maƙale cikin kwamfutar tebur ko na’ura mai ba da hanya tsakanin hanyoyin sadarwa ta amfani da kebul na Ethernet kuma suna fassara tsakanin kayan aikin mallakar mai amfani da wuraren sadarwa mallakar kamfanonin ISP.

Fiber optic modem

Ba kamar tsarin modem na yau da kullun ba, waɗanda ke amfani da kebul na ƙarfe kamar wayar tagulla don watsa bayanai, fiber optic modem na amfani da igiyoyin fiber optic ne. Waɗannan manyan modems suna ɓoye bayanan dijital kafin a haskaka su a tsarin haske. Wannan tsari yana buƙatar amfani da diode mai haske (LED) ko Laser wanda ke fitar da siginonin haske daidai da lambar binary.

Sukan yi kama da wayar na’urar lantarki, tsarin hasken optic light yana ba da damar mafi girman ta watsa bayanai da babban bandwidth fiye da wayoyi na ƙarfe; wannan yana haifar da asarar sigina a yanayi mai nisa. Wannan modem na tabbatar da mafi dacewa ga aikace-aikacen da suka haɗa da bandwidth na intanit, sabis na sadarwa, da sadarwar bayanai, wanda ya haɗa da buƙatun manyan ayyukan canja wurin bayanai.

Satellite modem

Ana amfani da wannan modem don daidaitawa da rage sigina waɗanda ke amfani da tsarin tauraron dan’adam don samar da hanyar haɗa da’irar tauraron dan’adam a duniya (satellite network). Wannan ya bambanta da modem na yau da kullun, wanda dole ne a yi amfani da modem na USB ko na wayar hannu don sada masu amfani da intanet, amma a maimakon haka, satellite modem na watsa bayanai zuwa da kuma daga tauraron dan’adam, inda haɗin intanet ɗin yake da matuƙar mahimmanci a wuraren da ke da ƙanana ko babu wata hanyar haɗawa. Yana farawa ne lokacin da satellite modem ya karɓi bayanai daga kwamfutar mai amfani, ya sanya su cikin siginar rediyo, kuma ya aika zuwa tauraron dan’adam mai kewayawa.

Digital modem

Modem nau’in dijital na’ura ce da ake amfani da ita wajen jujjuya bayanan dijital a cikin tsarin binary ko lambobin da aka yi na 0s da 1s zuwa siginar watsawa. Yana cim ma aikin daidaitawa, wanda ya haɗa da haɗa bayanan dijital cikin siginonin dijital mai ɗaukar hoto don dacewa wajen watsawa ta hanyoyin sadarwa daban-daban. Tun da a cikin digital modem ana iya canja siginar mai ɗaukar hoto, yana da mahimmanci wajen samar da haɗin intanet mai sauri tare da inganta amincin bayanai a cikin tsarin sadarwar dijital.

Alfanun na’urar modem

  • Modem yana zuwa da siffofi da fasali daban-daban har da farashi daban-daban daidai da ƙarfin aljihun jama’a.
  • Wasu modem ɗin suna kan fasahar built-in routers, hanyar sadarwar da ke ba wa na’urori da yawa damar hawa intanet lokaci guda.
  • Modems suna da kuzarin sauri mabanbanta, wanda hakan kan yi tasiri ga ayyukan intanet.
  • Yawancin modem na zamani suna da tsare-tsare na ci gaba kamar saitunan ingancin sabis (QoS), waɗanda ke ba da fifikon wasu nau’ikan zirga-zirga don samun ingantaccen aiki.
  • Modems suna buƙatar sabunta firmware na yau da kullun don haɓaka aiki, tsaro, da dacewa da tsarin kamfanoni masu samar da sabis.

Ƙalubalen da tattare da modem

  • Sauri da kuzarin modem yana raguwa lokacin da aka haɗa shi zuwa cibiyar sadarwa mai na’urori da yawa.
  • Modem ba shi da ƙarfin bin diddigin zirga-zirga tsakanin hanyar sadarwar tsarin (LAN) da intanet ba.
  • Ƙayyadaddun adadin na’urorin ne kawai za a iya haɗa su da intanet yayin amfani da modem.
  • Modems suna da haɗari ga babban haɗarin hare-hare masu alaƙa da tsaro.
  • Modem ba ya ba da kulawar zirga-zirga ko fasalulluka na gudanarwa.

Manazarta

GeeksforGeeks. (2023b, September 12). What is Modem? GeeksforGeeks.

Modem vs Router: What’s the Difference? (n.d.).

*****

Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.

Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.

Maƙalar ta amfanar?
EAa

You cannot copy content of this page

×