Skip to content

Motion (physics)

    Aika

    Ita motion tana karkashin kinematics ne, wanda kuma tana nufin tafiya ko kuwa mu ce canjin guri da abu ke yi ta yadda ake lura da lokacin aukuwan canjin. A harshen Turanci zamu iya cewa motion is the change in position of a body with time with respect to a reference point. Or motion is the movement of a body from one point to the other. Ita motion tana aukuwa a dukkan naukan ‘matter’ (state of matter – solid, liquid and gas), kuma motion na kasancewa a yanayi daban-daban. Misalan motion suna nan kamar haka, movement of the earth round the sun, rotation of the sun about its axis, an aeroplane flying in/on the sky and a man walking or running.

    Rabe-raben motion

    Ita motion an kasa ta ne kamar haka;

    1. Random motion
    2. Translational motion
    3. Rotational motion
    4. Circular motion
    5. Oscillatory or vibratory motion
    6. Relative motion

    Random motion: Wannan nau‘i na motion ba ya da “direction”, wato abun na tafiya ne a ko ta ina kawai, wani lokaci ana kiran wannan nau’in zig-zag motion. A Turance zamu iya kawo shi kamar haka random motion is the movement of a body in a zig-zag or disorderly manner with no specific direction. Misalan irin wannan motion sune; motion of dust particles in air, the motion of smoke particles da motion of butterfly da sauransu.

    Translational motion: Wannan nau’in motion kuma shi ne idan mutum ko abu ya tafi straight babu kaucewa. A Turance zumu iya cewa is the type of motion whereby a body or an object moves in a straight line. It is also called rectilinear motion. Misalan wannan nau’in motion ga su kamar haka; walking from one wall of a class to the other but in a straight line, da kuma dropping of fruit from tree to the ground.

    Rotational motion: Wannan shi ma wani nau’in motion ne dake faruwa idan tafiyan abu ya kasance yana FORMING CIRCLE ta yadda kuma abun zai kasance yana makale a guri guda. Muna iya kawo shi a Turance kamar haka; this type of motion occurs when a body moves in a circular path about its axis. Misalan sa na nan kamar haka; the rotation of the blades of fan, the rotation of a wheel about an axis, the rotation of the earth about its axis da sauransu.

    Circular motion: Shi circular motion yana aukuwa ne idan asali dama akwai CIRCLE sai kuma abu ko mutum yazo ya zagaya shi CIRCLE din. A Turance zamu ce is a type of motion in which an object or a body moves round a circle and in this kind of motion the speed is constant. Misalin irin wannan nau’in motion sune, movevement of the earth round the sun, movement of a car around a round-about da sauransu.

    Oscillatory or vibratory motion: A wannan irin motion kuma abun (wato object) yana tafiya  gaba ne sa’annan sai kuma ya dawo baya, wato to and fro ko kuma abun ya tafi sama ya dawo kasa. A harshen Turanci kuwa zamu iya kawo shi kamar haka ‘this is the motion of a body in a to and fro manner about a fixed point’. When a body moves to and fro about a fixed point we say, the body is oscillating. Misalan su sune, motion of the balanced wheel of a wristwatch, motion of a simple pendulum, motion of a loaded test-tube inside water da sauransu.

    Relative motion: Wannan irin motion yana faruwa ne idan mutum na tafiya a cikin mota sai ya ga kamar itatuwa ma suna tafiya. A Turance muna iya rubuta shi kamar haka, ‘relative motion is the motion of an object with respect to a reference point (mun yi bayani a baya akan reference point)

    Causes and effects of motion

    Sir Isaac Newton (wani masanin physics) ya yi bincike akan motion ta yadda ya gano cewa kowani abu (object) na kasancewa ne a gurin da aka ajjiye shi (wato state of rest –inertia). Idan ka ga ya bar gurin da yake akwai abunda ya sa shi barin gurin, sannan sai ya ce wannan abun kuma shine FORCE.

    Kuna iya duba makalar mu da ta yi bayani akan yadda ake samo equation na motion da misalan yadda ake amfani da shi wajen amsa tambaya a physics.

    *** Tarihin Wallafa Maƙalar ***

    An kuma sabunta ta 19 July, 2025

    *** Sharuɗɗan Editoci ***

    Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.

    Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.

    Maƙalar ta amfanar?
    EAa

    You cannot copy content of this page

    ×