Skip to content

Nelson Mandela

Idan aka ambaci sunan Nelson Mandela, ba a kallon sunan a matsayin suna daga jerin shuwagabannin siyasa na duniya kawai, shi ɗin alama ce ta sauyin tunanin bil’adama game da iko da adalci da darajar mutum. Rayuwarsa ta zama wata doguwar tafiya ta gwaje-gwaje da jarabawa wadda ta haɗa ƙuncin rayuwa, asarar kai tsaye da nauyin yanke manyan ƙudurce-ƙudurce a lokutan da kuskure ƙalilan zai iya jefa al’umma gabaɗaya cikin bala’i. A wannan fage, tarihin Mandela ya wuce tarihin mutum guda, ya koma tarihin yadda al’umma ke iya sauya makomarta ta hanyar hankali da ɗabi’a, ba kawai ta ƙarfin iko ba.

nelson mandela hd background
Marigayi Shugaba Mandela.

Abin da ya bambanta Mandela da wasu shi ne yadda ya tinkari zalunci ba tare da ya bar zaluncin ya yi tasiri a tunaninsa ba. Tsawon shekarun da ya shafe a ƙarƙashin mulkin danniya, ba su gina masa zuciyar ramuwar gayya ba, sai dai ma suka ƙarfafa masa fahimtar cewa ’yanci na gaskiya ba ya cika idan ya ta’allaka ne da wulakanta wani ɓangare na al’umma. Wannan fahimta ta sa rayuwarsa ta zama gwaji na zahiri game da yiwuwar gina adalci ba tare da lalata ginshiƙan zaman tare ba.

Haka kuma, Mandela ya kasance mutum da rayuwarsa ta kasu gida-gida: akwai Mandela a gida da iyali, Mandela a matsayin ɗalibi mai neman ilimi, Mandela ɗan gwagwarmaya, Mandela fursuna, da Mandela shugaba. Kowanne daga cikin waɗannan matakai ba wai tsayawa kawai ya yi ba, sai dai ya bar tasiri mai zurfi a cikin tunaninsa da matakan da ya ɗauka a gaba. Saboda haka, fahimtar tarihinsa na buƙatar kallon rayuwarsa a matsayin jerin sauye-sauye masu ma’ana, ba jerin abubuwan da suka faru ba kawai.

A mahangar tarihi da siyasa, rayuwar Mandela ta zama madubi da ke nuna yadda tsarin wariyar launin fata ya lalata ɗabi’ar ƙasa baki ɗaya, ba baƙar fata kaɗai ba. A lokaci guda kuma, ta nuna cewa rushe tsarin zalunci ba lallai sai da rusa ƙasa ko zubar da jini mai yawa ba, muddin an samu jagoranci mai hangen nesa da kyakkyawar ɗabi’a. Wannan ne ya sa tarihin Mandela ya zama darasi mai ɗorewa ga ƙasashe da al’umma da ke fama da rikici, mulkin danniya, ko rabuwar kai.

Saboda haka, wannan bayani da ya gabata shimfiɗa ce kuma  tubalin fahimtar yadda halin mutum ɗaya zai iya zama ginshiƙin sauyin tarihi. Dukkan sassan rayuwar Mandela da za a bi a karanta a gaba sun ginu ne a kan wannan fahimta: cewa jarumta ba ta ta’allaka ga ƙarfin jiki ko makami ba, tana ta’allaka ne ga jajircewar mutum da tsayawa kan gaskiya duk irin tsananin da za a fuskanta.

Haihuwa da asalin Mandela

An haifi Nelson Mandela a ranar 18 ga Yuli 1918 a ƙauyen Mvezo, wani ƙaramin muhalli da ke gefen kogin Mbashe a yankin Eastern Cape. Wannan muhalli na karkara, mai cike da al’adu, dokokin gargajiya, da tsarin girmamawa ga manya, ya taka muhimmiyar rawa wajen gina tunaninsa tun daga ƙuruciya. Ba a haife shi a cikin yanayin birni ko na zamani ba, face cikin al’ummar da ke kallon shugabanci a matsayin nauyi da hidima, ba gata ba.

Sunan Rolihlahla na gargajiya da aka ba shi a haihuwa ba suna ne na ado kawai ba, kalma ce mai ɗauke da nauyi a harshen Xhosa, wadda ke nuni da mutum mai karya tsari ko mai ja da abu daga tushensa. A al’adance, irin wannan suna yana iya zama gargaɗi ko hasashe game da irin rawar da mutum zai taka a rayuwa. A yanayin Mandela, sunan ya dace da makomarsa, domin rayuwarsa ta kai matakin da ta rushe tsarin danniya da ya daɗe yana ɗaure ƙasa baki ɗaya.

Mandela ya fito ne daga dangin sarauta na Thembu, reshe na kabilar Xhosa, inda shugabanci ba ya samuwa kan ƙarfin makami, sai kan mutunci, hikima, da iya sasanta rikici. Mahaifinsa, Gadla Henry Mphakanyiswa, ba sarki ba ne, amma yana cikin manyan masu ba da shawara ga sarkin gargajiya, matsayin da ke buƙatar gaskiya, ƙarfin hali, da iya tsayawa kan ra’ayi ko da yana da illa ga kai. Wannan matsayi ya sa Mandela ya taso yana kallon shugabanci a matsayin alhakin da ake iya sadaukar da kai.

Rasuwar mahaifinsa tun yana ƙarami ta zama babban sauyi a rayuwarsa. Wannan rashin ya kai shi gidan Sarkin Thembu, inda aka ɗauke shi a matsayin ɗan gida, ba baƙo ba. A can, Mandela ya fahimci yadda ake tafiyar da harkokin mulkin gargajiya, yadda ake sauraron ƙorafe-ƙorafe, da yadda ake yanke hukunci bayan doguwar tattaunawa. Wannan tsarin sauraro da jinkirin yanke hukunci ya zauna cikin tunaninsa, ya zama ginshiƙin fahimtarsa game da adalci da shugabanci tun kafin ya san siyasar zamani.

Ilimi da farkon fahimtar zalunci

Mandela ya fara samun ilimin boko ne a makarantar mishan, wurin da ya haɗa ilimi da koyarwar addini, amma kuma ya kasance wani ɓangare na tsarin mulkin mallaka. A nan ne aka ba shi sunan Nelson, suna da ba daga al’adarsa ya fito ba, sai daga tsarin da ke ƙoƙarin maye gurbin asalin Afirka da sunaye da dabi’un Turai. Wannan sauyin suna, kodayake ya yi kama da abu mai sauƙi, ya kasance farkon hulɗarsa kai tsaye da yadda mulkin mallaka ke rage darajar asalin baƙar fata.

Cigaban karatunsa ya kai shi University of Fort Hare, jami’ar da ta zama cibiyar taruwar matasan Afirka masu hangen nesa daga sassa daban-daban na nahiyar. A nan ne Mandela ya fara fuskantar ra’ayoyi masu zurfi game da ’yanci, adalci, da rawar da ilimi ke takawa wajen canja al’umma. Ba wai kawai karatun aji ya buɗe masa ido ba, mu’amala da sauran ɗalibai masu tunani iri ɗaya ta sa ya fahimci cewa matsalar zalunci ba ta shafi mutum ɗaya ba, matsala ce ta tsari.

Korarsa daga jami’a sakamakon shiga zanga-zangar ɗalibai ba wani hatsari ba ne a tarihin rayuwarsa, face alamar farko ta tsayawa kan gaskiya. Wannan lamari ya koya masa cewa ilimi ba ya rabuwa da ɗabi’a, kuma cewa samun digiri ba shi ne babban buri ba idan tsarin da ke bayar da shi yana tauye mutuncin mutane. Wannan fahimta ta sa ilimi a wajensa ya zama kayan aikin ƙwatar ’yanci, ba hanyar neman matsayi kawai ba.

Hijirarsa zuwa Johannesburg ta buɗe masa wani sabon babi na rayuwa. Birnin ya nuna masa fuskar Afirka ta Kudu ta zahiri, inda talauci, wariya, da arziki ke rayuwa a gefe ɗaya. A nan ne Mandela ya haɗa aiki da karatu, yana fuskantar wahalhalu na rayuwar baƙar fata a birni mai tsarin wariyar launin fata. Wannan kwarewa ta zahiri ta ƙarfafa masa fahimtar cewa zalunci ba ra’ayi ba ne na littafi, abu ne da ake rayuwa da shi kullum.

A ƙarshe, zama lauya tare da Oliver Tambo ya kasance mataki mai zurfi a rayuwarsa, domin ya ba shi damar ganin yadda doka ake amfani da ita wajen danniya, amma a lokaci guda yadda za a iya amfani da ita wajen kare waɗanda aka zalunta. Wannan haɗuwar ilimi, aiki, da kwarewar rayuwa ta kafa tubalin tunanin Mandela na gaba, inda ya fahimci cewa gwagwarmaya ta gaskiya dole ne ta haɗa hankali, tsari, da juriyar zuciya.

Shiga gwagwarmayar siyasa

Shigar Nelson Mandela jam’iyyar African National Congress a shekarar 1944 ba lamari ne na dare ɗaya kawai ba, sakamako ne na dogon nazari da kwarewar rayuwa da ya tara tun daga ƙuruciya. A wancan lokaci, ANC ta kasance ƙungiya mai bin hanyoyin lumana, tana dogara da roƙo, koke, da tattaunawa domin samun sauyi daga gwamnatin fararen fata. Wannan salo ya dace da yanayin siyasar lokacin, amma ga matasa irin Mandela, yana tafiya a hankali fiye da yadda tsananin zalunci ke ƙaruwa.

Kafuwar ANC Youth League ta zama wani muhimmin juyi a tarihin gwagwarmayar siyasa a Afirka ta Kudu. Mandela da abokan tafiyarsa sun fahimci cewa tsohon tsarin ANC na bukatar sabon kuzari, sabon tunani, da sabon salo na aiki. Youth League ba wai ta ƙi shugabancin manya ba ne, sai dai ta nemi sake fasalin dabaru, ta mayar da gwagwarmaya daga tsattsauran bin doka zuwa motsin jama’a mai faɗi. A nan ne Mandela ya fara bayyana a matsayin jagora mai iya haɗa tunani da aiki, ba mai surutu kawai ba.

Bayan kafa tsarin apartheid a 1948, gwagwarmayar Mandela ta ɗauki sabon salo. Tsarin wariyar launin fata ya kasance tsari ne da aka tsara da gangan domin cire baƙar fata daga kowane irin iko na siyasa, tattalin arziki, da zamantakewa. A wannan yanayi, Mandela ya fahimci cewa shiru ko jinkiri na nufin amincewa da zaluncin. Saboda haka, ya tsunduma cikin shirya gangami, motsa jama’a, da amfani da ilimi da doka wajen kalubalantar tsarin.

Rawar da Mandela ya taka a kotuna ta nuna wani muhimmin ɓangare na gwagwarmayarsa. A matsayin lauya, ya ga yadda dokoki ke zama makamin danniya, amma kuma ya fahimci cewa fallasa rashin adalcin dokokin a bainar jama’a na iya raunana halaccinsu. Wannan haɗin gwiwar aiki da kuma fafutuka a gaban doka ya sa Mandela ya zama barazana ga gwamnati, domin yana iya magana da jama’a da kuma kalubalantar tsarin a harshensa na shari’a.

Duk da haka, tsauraran matakan da gwamnati ta ɗauka, ciki har da haramta ƙungiyoyi, kama jagorori, da murƙushe zanga-zanga, sun fara rufe dukkan hanyoyin lumana. A wannan mataki, Mandela ya fara fuskantar tambaya mai nauyi: shin ci gaba da bin hanyoyin da gwamnati ta riga ta toshe yana da ma’ana, ko kuwa dole ne a sake tunani gaba ɗaya?

Sauyin salo da fara yaƙin ƙasa

Lamarin Sharpeville a 1960 ya zama wani layi a tarihin gwagwarmayar Afirka ta Kudu. Harbin fararen hula baƙar fata ba tare da makami ba ya fallasa a fili cewa gwamnatin apartheid ba za ta yi jinkiri wajen amfani da ƙarfi domin kare tsarinta ba. A wannan yanayi, Mandela ya fahimci cewa matsalar ba rashin haƙuri ba ce daga ɓangaren masu fafutuka, sai dai rashin niyyar gwamnati ta saurara.

Canja salon gwagwarmaya da Mandela ya runguma bai zo da sauƙi ba. Ya kasance yanke hukunci mai cike da ƙalubale, domin ya san cewa ɗaukar kowane irin matakin ƙarfi na iya haifar da sakamako mai muni. Amma a fahimtarsa, gwagwarmayar da ba ta da wani nau’in matsin lamba na iya zama marar tasiri. Wannan ne ya kai shi da wasu jagorori ga kafa Umkhonto we Sizwe, rundunar da aka tsara domin kai hare-haren lalata kayayyakin gwamnati, ba tare da kai hari ga fararen hula ba.

Muhimmin abu a wannan mataki shi ne Mandela bai rungumi tashin hankali a matsayin manufa ba. A maimakon haka, ya ɗauke shi a matsayin wata hanya ta ƙarshe bayan an rufe dukkan ƙofofin lumana. Tsarin ayyukan Umkhonto we Sizwe ya nuna wannan fahimta, domin an fi mayar da hankali kan abubuwa da gine-ginen gwamnati, da nufin aika saƙo na siyasa, ba tayar da firgici tsakanin jama’a ba.

mandela inauguration 1994
Marigayi Mandela a yayin rantsar da shia matsayin shugaban kasar Afrika ta Kudu, a shekarar 1994.

A jawaban da ya yi a wancan lokaci, Mandela ya jaddada cewa manufar gwagwarmayar ba ta canja ba: ’yanci, adalci, da mutunci. Abin da ya canja shi ne tsarin danniya ba ya rushewa da furuci kaɗai idan waɗanda ke cin gajiyarsa ba sa fuskantar wani nau’i na matsin lamba. Wannan mataki ya ƙara tsananta rikici tsakaninsa da gwamnati, amma kuma ya ɗaga gwagwarmayar Afirka ta Kudu zuwa wani mataki na duniya, inda ƙasashe da ƙungiyoyi suka fara kallon lamarin a matsayin babbar matsalar siyasa.

Mandela da Shari’ar Rivonia

Kama Nelson Mandela a shekarar 1962 ya kasance sakamakon dogon aikin sa ido da gwamnati ta yi a kansa, ba wani lamari na bazata ba. A wannan lokaci, Mandela ya riga ya zama mutum mai haɗari ga tsarin apartheid, ba wai saboda kalamansa kaɗai ba, sai don saboda dabaru da kwarewa da yake da su wajen shirya gwagwarmaya. An kama shi a asirce, an gurfanar da shi, aka yanke masa hukuncin daurin shekaru biyar, hukunci da gwamnati ta ɗauka a matsayin hanyar katse jagorancinsa daga jama’a.

Sai dai wannan hukunci bai zama ƙarshen shari’arsa ba. Binciken da jami’an tsaro suka yi ya kai su wata gona a Rivonia, inda aka gano takardu da tsare-tsaren gwagwarmaya. Wannan ne ya haifar da abin da ake kira da Rivonia Trial, shari’a mai zafi wadda ta ɗauki hankalin duniya. A wannan shari’a, ba a tuhumi Mandela da laifin aikata tashin hankali kai tsaye ba, sai dai da niyyar rusa tsarin gwamnati, laifi da hukuncinsa zai iya zama kisa.

Jawabin da Mandela ya gabatar a gaban kotu ba kariya ta shari’a ba ce kawai, bayani ne na ɗabi’a da tarihi. Ya gina jawabin nasa ne kan hujjar cewa gwagwarmayarsa ta samo asali ne daga tauye mutuncin baƙar fata, ba daga ƙiyayya ga fararen fata ba. Kalaman da ya bayyana cewa ya sadaukar da rayuwarsa domin neman ’yanci, kuma a shirye yake ya mutu saboda wannan buri, sun sauya shari’ar daga takaddama ta doka zuwa hukunci a kan tsarin wariya gabaɗaya. A wannan lokaci, Mandela ya rungumi mutuwa, yana nuna cewa manufarsa ta fi rayuwarsa muhimmanci.

A shekarar 1964, kotu ta yanke masa hukuncin daurin rai da rai, hukunci da aka ɗauka a matsayin hanyar binne gwagwarmayar ’yanci. Amma a maimakon haka, wannan hukunci ya fara gina Mandela a matsayin alamar juriyar ɗan Adam, domin an rufe shi a jiki, amma aka buɗe shi a zukatan jama’a a cikin gida da wajen ƙasa.

Rayuwa Mandela a kurkuku (shekaru 27)

Shiga kurkuku ta kai Mandela wani mataki na gwaji mafi tsanani a rayuwarsa. Mafi yawan shekarunsa ya shafe su ne a Robben Island, wuri mai tsananin sanyi, keɓantuwa, da tsauraran dokoki. An tilasta masa aikin wahala ba wai don amfanin tattalin arziki ba, sai don karyar da zuciya da mutunci. Hanyoyin sadarwa da iyali sun kasance masu ƙuntatawa ƙwarai, lamarin da ya ninka raɗaɗin zaman kurkuku fiye da wahalar jiki.

Abin lura shi ne cewa gwamnatin ba ta ɗaure Mandela kawai don hana shi aiki ba, har ma don murƙushe tunaninsa. Duk da haka, kurkuku ya kasa cim ma wannan buri. A maimakon haka, Mandela ya sauya kurkuku zuwa wata irin makaranta ta rayuwa. Ta hanyar tattaunawa, karatu, da muhawara, ya taimaka wajen gina fahimta da ɗabi’a a tsakanin fursunoni, yana nuna cewa shugabanci ba ya buƙatar ofishi ko muƙami.

A tsawon shekarun da ya yi a kurkuku, Mandela ya gina wata zuciya mai juriya da natsuwa. Bai bar fushin da halin da yake ciki ya mallaki tunaninsa ba. A hankali, ya fara fahimtar cewa idan wata rana aka buɗe ƙofofin kurkuku, ƙasar da zai tarar ba za ta buƙaci jagoran ramuwar gayya ba, sai jagoran sulhu. Wannan tunani ya sa ya fara aikin gina kansa a matsayin jagoran da zai iya magana da abokan gaba ba tare da raini ko tsoro ba.

A waje guda, tsawon ɗaurin da aka yi wa Mandela ya jawo hankalin duniya. Sunansa ya fara zama taken kamfen na ƙungiyoyi, gwamnatoci, da ɗalibai a sassa daban-daban na duniya. Matsin lambar ƙasashen waje, haɗe da rikice-rikicen cikin gida, suka fara raunana tsarin apartheid. A wannan yanayi, kurkukun da aka yi nufin ta zama makabarta, ta koma cibiyar faɗaɗa gwagwarmayar zuwa matakin duniya.

A taƙaice, shekarun kurkuku sun sauya Mandela daga jagoran gwagwarmaya zuwa jagoran tunani da ɗabi’a. Ba wai sun karya gwiwarsa ba ne, sun ƙara gina shi, ta fuskar ikon sarrafa fushi, hangen nesa na dogon lokaci, da fahimtar cewa nasarar gaskiya ita ce wadda ta kuɓutar da mai zalunci da wanda aka zalunta gabaɗaya.

Sakin shi da sulhu

Sakin Nelson Mandela a ranar 11 Fabrairu 1990 ya zo ne bayan haɗuwar manyan dalilai masu nauyi: matsin lambar cikin gida daga al’ummar da ba za ta ƙara yarda da danniya ba, da kuma matsin lambar ƙasashen waje da suka fara ɗaukar tsarin wariya a matsayin abin kunya a idon duniya. Duk da haka, muhimmancin wannan rana bai ta’allaka ga buɗe ƙofar kurkuku kaɗai ba, sai ga irin tunanin da Mandela ya fito da shi zuwa fili.

Abin da ya fi ba duniya mamaki shi ne yadda Mandela ya fassara ’yanci bayan shekaru masu tsawo na ƙuncin rayuwa. Bai ɗauki sakin nasa a matsayin damar ramuwar gayya ko nasarar da za a yi amfani da ita wajen wulaƙanta abokan gaba ba. A maimakon haka, ya ɗauke ta a matsayin alhakin da ke rataye a wuyansa: alhakin hana ƙasa faɗawa cikin rikici. Kiran da ya yi na sulhu, zaman lafiya, da haɗin kan ƙasa ba kalmomi ne na siyasa kawai ba, sakamakon tunani ne da ya ginu tsawon shekaru na lura da halayen ɗan Adam a yanayin tsanani.

Shigar Mandela tattaunawa da gwamnatin fararen fata ya buƙaci jarumta ta daban, domin tattaunawa ba ta nufin mantawa da abin da ya faru, face yarda da cewa maakomar ƙasa ta fi muhimmanci fiye da raɗaɗin da ya wuce. Wannan tsari ya buɗe hanyar rusa tsarin apartheid a hankali, ba ta hanyar rushewar ƙasa ba, sai ta hanyar sauya ginshiƙanta na doka da siyasa. Shirye-shiryen zaɓe na gaskiya da aka fara a wannan lokaci sun kasance sakamakon wannan fahimta, inda aka fifita tsari mai ɗorewa fiye da gaggawar cin nasara.

Mandela a matsayin shugaban ƙasa

Zaɓen shekarar 1994 ya buɗe wani sabon babi a tarihin Afirka ta Kudu, ba sauyin shugabanci kawai ba, har ma da sauyin ma’anar ƙasa da ’yan ƙasa. Zama shugaban ƙasa na farko baƙar fata ya ɗora wa Mandela nauyin da ya wuce aikin gwamnati na yau da kullum. Ya zama dole ya gina yarda a tsakanin al’ummomin da suka daɗe suna kallon juna da tsoro da shakku.

A mulkinsa, Mandela ya fifita gina harsashin ɗabi’a da gaskiya fiye da nuna iko. Kafa hukumar Truth and Reconciliation Commission ta nuna wannan tunani a sarari. Manufar wannan tsari ba hukunta kowa kawai ba ce, illa bayyanar da gaskiya domin al’umma ta san abin da ya faru, ta yadda za a iya gina makoma ba tare da ƙaryar da ke ɓoye a ƙasa ba. Wannan tsari ya nuna cewa adalci ba lallai sai ya kasance na ramuwar gayya ba, zai iya zama na warkarwa.

mandella
Mandela shugaba ne ba na Afirka ta Kudu kadai ba har ma da Afrika baki daya. Hoto: Black History Month

Mandela ya kuma yi aiki tuƙuru wajen rage tsoron fararen fata game da sabuwar ƙasa, yana nuna musu cewa canji ba yana nufin maye gurbin zalunci da wani zalunci ba. A lokaci guda, ya tabbatar wa baƙar fata cewa nasarar siyasa ba za ta zama ta suna kawai ba, sai an juya ta zuwa gina ƙasa da inganta rayuwa. Zaɓinsa na yin wa’adi guda ɗaya kawai ya ƙarfafa wannan saƙo, domin ya nuna cewa mulki ba gado ba ne, amana ce da ake bayarwa na ɗan lokaci.

Rayuwar iyali

Rayuwar iyalin Mandela ta kasance ɗaya daga cikin sassan rayuwarsa da suka fi shan wahala, amma ba su fi bayyana a idon jama’a ba. Siyasa da kurkuku sun cinye masa shekaru da dama da ya kamata ya shafe su tare da iyalinsa, abin da ya haifar da giɓi da ba  za a iya cikewa gabaɗaya ba. Aure sau uku da ya yi ba wai kawai alamar canjin yanayin rayuwa ba ne, shaida ce ta irin tasirin da gwagwarmaya ke yi wa dangantakar ɗan Adam.

A matsayinsa na uba kuma kaka, Mandela ya kasance yana ɗauke da nauyin rashin kasancewa a lokutan da suka fi muhimmanci ga ’ya’yansa. Wannan ba rashin kulawa ba ne, sai sakamakon zaɓin rayuwa da ya yi, inda ya fifita abin da ya ɗauka a matsayin alhakin ƙasa. Duk da haka, a rubuce-rubucensa da kalamansa, ana iya ganin yadda wannan rashi ya kasance masa nauyi, kuma yadda ya fahimci cewa ’yanci na siyasa yakan zo ne da sadaukarwa ta kai tsaye a rayuwar mutum.

A ƙarshe, rayuwar iyalin Mandela ta ƙara cika hoton tarihinsa, domin ta nuna shi ba a matsayin gumaka marar kuskure ba, sai a matsayin mutum na gaske, mai jin raɗaɗi, da ke ɗaukar sakamakon zaɓinsa. Wannan ɓangare na rayuwarsa yana ƙarfafa fahimtar cewa manyan sauye-sauyen tarihi sau da yawa ana biyan su ne da farashi a matakin mutum, ba ƙasa kaɗai ba.

Lambobin yabo da girmamawa

A ƙarshen gwagwarmayar siyasa da shugabanci, Nelson Mandela ya samu irin girmamawar da ba ta taƙaitu ga ƙasa ɗaya ko nahiya ɗaya ba. Lambobin yabon da aka ba shi, fiye da 250, ba wai sakamakon muƙami ko nasarar siyasa kawai ba ne, face amincewar duniya da irin rawar da ya taka wajen sauya tunanin bil’adama game da adalci, iko, da sulhu. Waɗannan karramawa sun nuna cewa aikinsa ya wuce iyakar Afirka ta Kudu, ya zama abin koyi ga al’umma masu fama da danniya a ko’ina.

Lambar yabo ta Nobel Peace Prize da ya samu a 1993 ta kasance mafi fice daga cikin dukkan girmamawar da aka yi masa. Muhimmancin wannan lambar yabo ba ya ta’allaka ne ga sunanta kaɗai ba, sai ga dalilin da ya sa aka ba shi: yadda ya zaɓi hanyar sulhu da tattaunawa maimakon tashin hankali a lokacin da ƙasa ke kan gaɓar rikici. Wannan karramawa ta tabbatar da cewa zaman lafiya ba rauni ba ne, illa wata dabara ce mai buƙatar ƙarfin hali da natsuwa.

Girmamawar da United Nations ta yi wa Mandela ta nuna yadda aka ɗauke shi a matsayin wakilin ‘yancin ɗan Adam a matakin duniya. Ba a Kallon shi kawai a matsayin tsohon shugaban ƙasa, shi ɗin yana a matsayin murya da ke wakiltar waɗanda aka danne, aka ware, ko aka hana damar faɗar ra’ayinsu. Jami’o’i da ƙasashe da dama sun ba shi digirin girmamawa da lambar yabo, ba domin ƙara masa daraja ba kawai, sai domin haɗa sunayensu da irin darajarsa ta ɗabi’a.

A taƙaice, lambobin yabo da girmamawar da Mandela ya samu sun zama wata hanya ta rubuta tarihinsa a zukatan al’umma. Sun tabbatar da cewa nasarar da ta fi ɗorewa ita ce wadda take barin darasi, ba kawai wadda take samar da iko ko suna ba.

Mutuwa da gadon tarihi

Rasuwar Mandela a ranar 5 Disamba 2013, yana da shekaru 95, ta haifar da wani yanayi na tunani da nazari a duniya baki ɗaya. Mutuwarsa ba ta zama labarin baƙinciki kaɗai ba, ta zama wata dama ta duba irin tasirin da mutum guda zai iya yi a tarihin bil’adama. Daga shugabannin ƙasashe zuwa talakawa, martanin da aka bayar ya nuna cewa Mandela ya riga ya wuce matsayin ɗan ƙasa, ya zama mallakar duniya.

Abin da ya fi bayyana a bayan mutuwarsa shi ne yadda mutane suka fassara rayuwarsa a matsayin darasi, ba tarihin nasara kawai ba. An tuna shi a matsayin gwarzon adalci, ba domin ya ci gaba da yaƙi ba, sai domin ya san lokacin da ya kamata a dakata a tattauna. An tuna shi a matsayin alamar sulhu, ba domin ya manta abin da ya faru ba, sai domin ya fahimci cewa makomar al’umma ba ta ginuwa kan tsananin fushi. A wannan yanayi, mutuwarsa ta zama kammaluwar wani babi na tunanin ɗan Adam game da rikici da zaman lafiya.

Gadon da ya bari

Gadon da Mandela ya bari ba dukiya ba ce, ba kuma gado na jini ko iko ba. Gado ne na tunani da ɗabi’a, wanda ya haɗa hakuri mai zurfi da iya jure wahala ba tare da rasa mutunci ba. Hakurin nasa bai kasance na rauni ba, sai na fahimtar cewa lokaci da natsuwa na iya cim ma abin da ƙarfi ya kasa cimmawa.

Yafiyar da ya nuna ba mantuwa ba ce, sai dabarar warkarwa. Ta hanyar yafiya, Mandela ya koyar da cewa al’umma za ta iya ficewa daga duhun tarihi ba tare da ta ɗauki duhun tare da ita zuwa gaba ba. Jarumtarsa kuma ba ta tsaya ga tsayawa kan ra’ayi ba, ta haɗa da jarumtar sauya ra’ayi idan yanayi ya bukata. Gaskiyar da ya tsaya a kai ita ce cewa ’yanci na gaskiya ba ya cika idan bai haɗa da adalci da mutuncin kowa ba.

A ƙarshe, rayuwar Mandela ta kafa wani ma’auni mai tsauri ga shugabanci: cewa iko ba shi ne gwada ƙarfin mutum ba, face gwada halinsa. Wannan gado ne da ke ci gaba da rayuwa, domin ba ya buƙatar hoton mutum ko suna domin ya dore, face mutanen da ke ɗaukar darasinsa su aiwatar da su a rayuwarsu da al’ummarsu.

Manazarta

South African History Online. (n.d.). Nelson Mandela.

The Nelson Mandela Foundation. (n.d.). Nelson Mandela biography.

United Nations. (n.d.). Nelson Mandela Day, 18 July | United Nations

Nelson Mandela Foundation. (n.d.). Biography of Nelson Mandela – Nelson Mandela Foundation

Sharuɗɗan Editoci

Duk maƙalun da ku ka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta tare da sa idon kwamitin ba da shawara na ƙwararru. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.

Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.

Maƙalar ta amfanar?
EAa

You cannot copy content of this page

×