Sinadarin neon, yana da alama Ne, sinadarin iskar gas ce mai kyau da ke da launi marar wari a ƙarƙashin ingantaccen yanayi. A gaban makamashin lantarki, sinadarin iskar na neon yana haskaka wani launin ja-ruwan lemo mai haske.
Yana da ƙarfin sanyayawa fiye da helium a amfani da yawa. Ƙarfin sanyayawarsa ya kai sau 40 fiye da helium a nau’in ruwa-ruwa da kuma hydrogen sau uku shi a nau’in ruwa-ruwa. Iskar gas ce da ba kasafai ke samuwa ba, kuma ƙwayoyin halittarsa sun ƙunshi kwayar zarra ta Neon guda ɗaya. Yana da iskar gas marar guba kuma ba ta da illa ga yanayi. Babu wata barazana ga muhalli. Wannan sinadari ba ya haifar da lalacewar muhalli.
Yana iya haifar da wani sinadarin tare da fluorine a cikin ɗakunan gwaje-gwaje. Haka nan yana samar da hydrate marar ƙarfi.
Tarihin gano sinadarin Neon
Masana ilmin sinadarai ɗan Burtaniya William Ramsay da Morris Travers ne suka gano sinadarin neon a shekarar 1898. A cikin gwajinsa, Ramsay ya dafa wani samfurin iska mai ruwa-ruwa ya kuma kama iskar gas yayin da suke fita, a wani tsari da ake kira fractional distillation. Bayan ganowa da yanke hukuncin fitar da nitrogen, oxygen, da argon, Ramsay ya gano krypton. Daga baya, ya gano wata iskar gas wanda ke fitar da haske mai ja-ruwan lemo a ƙarƙashin fitarwar na’urar spectroscopic. Wannan sinadari ya juya ya zama neon. An ba shi suna ne daga kalmar Girkanci ”neos”, wacce ke nufin”sabo.”
Neon a kan teburin periodic
Sinadarin Neon, wanda ke da alamar Ne, iskar gas ne mai daraja a rukuni na 18 a kan teburin sunadarai wanda ake kira da periodic table a Turance. Kamar sauran sunadarai na iskar gas masu daraja, tana da cikakken harsashi na waje tare da (8 valence electrons) kuma tsarinsa na lantarki shi ne [He]2s22p6. Tana cikin p-block a cikin lokaci na biyu. Lambar sinadarai ta Neon ita ce 10.
Sinadarin sanyi daga Neon
A cikin nau’in ruwa-ruwa, ana amfani da neon a matsayin sinadarin refrigerant na cryogenic, ma’ana cewa ruwa ne da ake amfani da shi a wajen aiwatar da sanyaya abubuwa da ke ƙasa da 150 K. Ƙarfin sanyayawa na Neon yana da girma sosai. Yana da ƙarfin sanyaya sau 40 na (kowane girma) na helium nau’in ruwa-ruwa kuma sama da sau 3 na sinadarin hydrogen. Abubuwan da Neon ya ƙunsa a matsayin iskar gas mai daraja suna ba shi damar ba da haɗuwa da wasu abubuwa. Wadannan abubuwa, da kuma madaidaicin yanayin tafasar shi, suna sa ya yi tasiri wajen amfani da shi a matsayin sinadarin refrigerant.
Ƙarancin sinadarin Neon
A cikin nau’ikansa na ruwa-ruwa da kuma iska, neon yana da wuyar samu sosai, don haka yake da tsada a Duniya. Yana da ƙarancin nauyi sosai, yana da matsanancin tiriri a ƙarancin yanayin zafi, kuma ba shi da ƙarfi. Neon yana da kashi 0.00182% na iskar sararin duniya. Akasin haka, neon shi ne kashi na huɗu mafi yawan sinadarai a sararin samaniya.
Amfanin sinadarin neon
Baya ga amfani da shi a matsayin refrigerant na cryogenic, neon galibi ana amfani da shi a wurare daban-daban na haske, wanda suka haɗa da alamomi.
Ana amfani da fitilun neon masu launin ja-ruwan lemo wajen yin alamomin tallace-tallace. Haka nan ana amfani da shi a cikin wasu nau’ikan fitilu lokacin da ake buƙatar sauran iskar gas da yawa don samar da haske masu launi daban-daban.
Ma’aikatar lantarki tana amfani da neon guda ɗaya ko a haɗe tare da sauran iskar gas a cikin nau’ikan bututun lantarki masu cike da iskar gas.
Ana amfani da cakuɗaɗɗun sinadaran helium da neon wajen yin numfashi ta yayin nutsewa a ruwa a cikin teku tunda helium ba ya narkewa a cikin jini fiye da nitrogen a matsanancin yanayin matsin lamba.
Hasken Neon da alamomi
Mafi shaharar amfanin Neon, shi ne samar da alamomin haske masu launin ja-ruwan lemo, an ƙirƙiro wannan a cikin shekarar 1910. Bututun gilashin da ke ɗauke da atom ɗin neon na zana siffofi da alamomi daban-daban. Wucewar makamashin lantarki ta cikin bututun yana faranta wa na’urorin lantarki, yana sa su tsalle matakin makamashi ɗaya. Lokacin da atom ɗin ƙarshe ya koma ƙasa zuwa matakin ƙarfinsa na asali, yana fitar da makamashin kuzari ta hanyar haske launin ja-ruwan lemo.
Helium-Neon Laser
A cikin wani tsari mai kama da alamomin neon, igiyoyin lantarki suna tinzira helium da atom ɗin neon a cikin bututun fitarwa. Haɗuwa tsakanin ƙwayoyin zarra (atoms) suna canjawa tare da sakin makamashin kuzari. Wannan yana haɓaka haske a cikin bututu kuma yana samar da hasken laser. Laser na He-Ne suna fitar da haske ja tare da tsawon nanometer 632.8 (nm).
Wasu muhimman abubuwa game da Neon
- Neon yana da mafi ƙarancin nau’i na ruwa-ruwa. Yana wanzuwa a mafi ƙarancin nau’in ruwa-ruwa a cikin yanayin 2.5 ℃.
- Shi ne sinadarin iska mafi rashin nauyi na biyu, yayin da helium shi ne na farko.
- Kodayake yana da wuya samuwa a duniya, neon shi ne nau’i na huɗu mafi yawa a cikin sararin samaniya. Yana samar da sassa 18 a cikin kowace miliyan ɗaya ta iska.
- Alamar sinadarin neon ita ce mafi sanuwa a cikin dukkan sinadarai. Idan ka ga alamar Neon wanda ba launin ja-ruwan lemo ba, iskar gas ɗin ba neon ba ce.
- Helium da neon su ne kawai sinadarai da ba sa samar da sinadaran mahaɗi tare da wasu sinadaran, kodayake ions da ligands sun kasance haka.
- Neon yana da tabbatattun isotopes 3 waɗanda ke faruwa a zahiri, da ƙarin isotopes 17 na rediyoaktif.
Manazarta
Admin. (2022, August 3). Neon. BYJUS.
Neon – Element information, properties and uses | Periodic Table. (n.d.).
The Editors of Encyclopaedia Britannica. (2025, May 23). Neon | Definition, Uses, melting Point, & Facts. Encyclopedia Britannica.
*****
Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.
Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.