Nicolás Maduro Moros ɗan siyasa ne a ƙasar Venezuela wanda ya shahara a duniya saboda jagorantar ƙasar cikin wani lokaci mai cike da rikice-rikicen siyasa, tattalin arziki, da muhawarar demokradiyyar duniya. Ya hau karagar mulki bayan mutuwar Hugo Chávez a shekarar 2013, kuma tun daga lokacin ya kasance ɗaya daga cikin shuwagabannin da aka fi muhawara a kansu a nahiyar Latin America. Wasu na kallon shi a matsayin magajin juyin juya halin Bolivaria, yayin da wasu ke ganin shi a matsayin shugaban da ya gaza kula da ƙasa. Mulkinsa ya jawo cece-ku-ce da ra’ayoyi masu ƙarfi a tsakanin masu goyon baya da masu adawa.
Haihuwa da tashi
Nicolás Maduro Moros an haife shi ne a ranar 23 ga Nuwamba, 1962 a Caracas, babban birnin Venezuela, cikin dangi masu ƙaramin ƙarfi da ke da alaƙa da ƙungiyoyin ƙwadago da siyasa mai sassaucin ra’ayi. Mahaifinsa, Nicolás Maduro García, ya kasance jagoran ‘yan ƙwadago ne mai tasiri, wanda hakan ya sa Maduro tun yana ƙarami ya koyi mahimmancin zama tare da ma’aikata da kare haƙƙinsu a harkokin zamantakewa da siyasa. Mahaifiyarsa, Teresa de Jesús Moros, ta fito ne daga garin Cúcuta a gefen iyaka tsakanin Venezuela da Colombia, lamarin da ya sa shi zama mai gambizar al’adu daga ƙasashen biyu.

A gida, ya taso a unguwar Los Jardines, El Valle, wadda aka sani a matsayin unguwar talakawa da kuma yawan jama’a masu neman hanyar fita daga talauci da rashin dama. Shi ne kaɗai namiji daga cikin ’ya’ya huɗu da iyayensa suka haifa, yana da ’yan’uwansa mata uku — María Teresa, Josefina, da Anita — waɗanda suka girma tare da shi a cikin wannan yanayi mai cike da ƙalubale. Maduro ya kuma taso ne cikin addinin Kiristanci mabiyin ɗariƙar Katolika, wanda ya kasance addini ga yawancin al’ummar Venezuela a wancan lokacin.
Rayuwarsa ta ƙuruciya
A lokacin ƙuruciyarsa, Maduro ya sha fama da matsalolin rayuwa na birni, musamman a unguwannin da ake fama da talauci, rashin aikin yi, da rashin damar aiki ga matasa. A irin wannan muhalli na Caracas, yake ganin yadda bambancin arziki ke shafar al’ummomi daban-daban, inda wasu ke fama da yaƙi da yunwa yayin da wasu ke rayuwa cikin wadata. Wani muhimmin abu a rayuwarsa shi ne cewa al’ummar da suka kewaye shi suna da tasiri mai zurfi a kan tunaninsa, inda ya fara ganin cewa ana buƙatar canji wajen ƙarfafar ‘yan talakawa da kare haƙƙin ma’aikata. A unguwar inda ya taso, mutane da yawa suna amfani da motocin sufuri na jama’a don halartar ayyukansu na yau da kullum, lamarin da ya sa Maduro ya fahimci muhimmancin tsarin sufuri da ƙarin damar samun aiki ga talakawa a matsayin babban ɓangare na cigaban ƙasa.
Karatu da neman ilimi
Maduro bai kammala karatun jami’a ba ko samun digiri na ƙarshe, kuma ba a sami shaidar cewa ya gama makarantar sakandare ba duk da cewa ya halarci Liceo José Ávalos, wata makarantar gwamnati a El Valle. A wannan makaranta ne ya fara sha’awar siyasa, inda ya shiga cikin kungiyar ɗalibai kuma ya zama shugaban ƙungiyar ɗalibai, lamarin da ya ƙara masa ƙarfin gwiwa wajen shiga cikin harkokin ƙungiyoyi da gwagwarmayar siyasa tun yana matashi. Bayan barin makaranta ba tare da takardar kammalawa ba, Maduro ya nemi ilimi ta hanyar kai‑tsaye, inda ya yi nazarin falsafar siyasa, tarihin juyin juya hali, da kuma tsarin Marxism, wanda ya zama babban ginshiƙi a tunaninsa na siyasa da ayyukan jama’a daga baya.
Bugu da ƙari, a cikin shekarar 1986, a matsayin wani mataki na horo a cikin gwagwarmayar siyasa, ya tafi Cuba domin samun horon shugabanci da ƙwarewa a siyasa a Escuela Nacional de Cuadros Julio Antonio Mella, wata cibiyar horo ta siyasa ƙarƙashin Young Communists Union a Cuba. An koya masa abubuwa masu yawa game da Marxism, jagoranci, da tarihin juyin juya hali, sannan ya dawo gida domin amfani da wannan ilimi wajen taimakawa ƙungiyoyin ma’aikata da jama’a. Wannan tafiya zuwa Cuba ta kara masa fahimta game da tsarin juyin juya hali da mahimmancin yaƙar wariyar ƙasa da ƙarfafar talakawa a cikin al’umma.
Ayyukansa na farko
Nicolás Maduro ya fara aikinsa ne daga matakin ƙasa, inda ya yi aiki a matsayin direban bas a tsarin sufuri na Metrobus a Caracas. Wannan aiki ya ba shi damar fahimtar rayuwar talakawa kai tsaye musamman yadda suke fuskantar tsadar rayuwa, ƙarancin albashi, da rashin tsaro, saboda shi kansa yana hulɗa da ma’aikata da fasinjoji a kowace rana.

Nicolás Maduro Moros mutum ne da ya taso cikin rayuwa irin ta masu karamin karfi
Aikin tuƙi ya ba shi damar ganin yadda rasuwar tattalin arziki da rashin tsari ke shafar talakawa a matakin yau da kullum, kuma ya taimaka wajen gina masa tunani kan bukatar kare haƙƙin ma’aikata da al’umma. Daga baya, ya ƙara himma wajen haɗa kansa da mawuyacin halin rayuwar talakawa, wanda ya zama tushen gogewa a harkar jagoranci da siyasa.
Shigar shi ƙungiyoyin ma’aikata
Bayan haka, Maduro ya shiga cikin ƙungiyoyin ma’aikata, inda ya zama ɗaya daga cikin jagororin ƙungiyar direbobin bas da ma’aikatan sufuri. A wannan matsayi, ya fara yin jawabi ga jama’a, shirya zanga-zanga, da jagorantar taron ma’aikata domin neman haƙƙoƙinsu.
Wannan ya sa ya zama sananne a tsakanin ma’aikata kuma ya ba shi damar shiga cikin ayyukan ƙungiyar ma’aikata na siyasa. Wannan ƙwarewa a cikin ƙungiyoyin ma’aikata ta kasance matattakala zuwa siyasar ƙasa, inda mutane suka fara lura da ƙwarewarsa wajen jagoranci da sadarwa.
Shigar shi siyasa
A cikin shekarun 1990s, Nicolás Maduro ya haɗu da Hugo Chávez, wani soja da ya jagoranci ƙungiyar juyin juya hali a Venezuela, wanda ya fito fili wajen sukar tsohuwar jam’iyya da tsarin siyasa na wancan lokaci. Chávez ya yi suna wajen ƙoƙarin kawo canjin siyasa da tattalin arziki a Venezuela ta hanyar ra’ayin Bolivarianismo, inda ya jaddada ƙarfafar talakawa, ƙarfafar ikon gwamnati, da madadin tsarin siyasa na zamani.
Maduro ya rungumi wannan tunani gabaɗaya, ya zama mai aminci ga Chávez, kuma ya fara jin cewa manufar juyin juya hali da taimakon talakawa ita ce hanyar da ƙasa za ta samu ɗorewar zaman lafiya da adalci. Wannan alaƙa ta siyasa da Chávez ta sa Maduro ya zama ɗaya daga cikin amintattun mabiyan Chávez a harkokin siyasa.
Zaɓensa zuwa majalisar ƙasa
Bayan Chávez ya zama shugaban ƙasa a shekarar 1999, Maduro ya samu damar shiga cikin siyasar a hukumance. A shekarar 2000, aka zaɓe shi a matsayin ɗan majalisar ƙasa, inda ya fara bayyana a idon jama’a a matsayin ɗan siyasa mai tsananin biyayya ga manufofin Bolivaria. A Majalisar Ƙasa, Maduro ya fara taka rawa wajen tsayar da manufofin jam’iyya da goyon bayan talakawa, lamarin da ya ƙara masa sanin jama’a a siyasar ƙasa. Wannan muƙami ya zama tubalin farko na siyasa a hukumance da ya ba shi damar ganin yadda tsarin siyasa ke aiki, da yadda ake ƙulla haɗin kai a matakin ƙasa.
Shugabanci a majalisar ƙasa
A tsakanin shekarun 2005 zuwa 2006, Nicolás Maduro ya zama Shugaban Majalisar Ƙasa ta Venezuela, wani babban matsayi a tsarin siyasar ƙasar. A wannan matsayi, ya taka rawa wajen ƙarfafa ikon gwamnatin Chávez, inda ya goyi bayan sauye‑sauyen dokoki da suka ba fadar shugaban ƙasa ƙarin iko wajen tsara manufofi da aiwatar da su. A wannan lokaci, Maduro ya kasance mai jayayya da jam’iyyun adawa, kuma ya jagoranci majalisa wajen tsara dokoki da suka ƙarfafa manufofin Bolivaria da tsarin mulki da ƙa’idojin Chávez ya kafa. Wannan muƙami ya ƙara masa kusanci da cibiyar iko ta ƙasar, ya kuma ƙara masa girma a cikin jam’iyyar da kuma kusanci da shuwagabannin ƙasa.
Matsayin ministan harkokin waje
Daga shekarar 2006 har zuwa 2013, Nicolás Maduro ya shugabanci Ma’aikatar Harkokin Waje ta Venezuela a matsayin Ministan Harkokin Waje. A wannan matsayi, ya yi amfani da damar wajen ƙarfafa alaƙa mai zurfi da ƙasashen da ke goyon bayan manufofin Bolivaria da juyin juya hali, musamman haɓaka manufofi da haɗin gwiwa tare da Cuba, Bolivia, Iran, Rasha, da China. Wannan ya haɗa da ƙirƙirar yarjejeniyoyi na tattalin arziki, tallafi da musayar albarkatu, haɗin gwiwar siyasa, da haɗin kai wajen jayayya da tasirin manyan ƙasashen yamma, musamman Amurka, a yankin Latin America.
Ta wannan hanyar, Maduro ya yi ƙoƙarin tabbatar da cewa Venezuela ba ta kasance ƙarƙashin takunkumin Amurka ba, kuma ta samu goyon bayan ƙasashen duniya masu ra’ayi iri ɗaya. Wannan tsarin diflomasiyya ya taimaka masa wajen samun goyon baya a tarukan ƙasa da ƙasa, duk da cewa ya kuma janyo sukar wasu ƙasashen da suka yi la’akari da manufofinsa a matsayin saɓa wa dokokin demokraɗiyya da sanadin rarrabuwar ra’ayoyi a duniya.
Salon diflomasiyya
Salon diflomasiyyar Nicolás Maduro ya bambanta da yadda aka saba gani a shuwagabannin ƙasashen Latin America. Ya kasance mai amfani da harshe mai tauri da furuci mai zafi a duk lokacin da yake magana a tarukan ƙasa da ƙasa, musamman wajen bayyana goyon bayansa ga akidar Bolivaria da biyayya ga tunanin Chávez. A lokuta da dama, ya yi amfani da irin waɗannan kalmomi don nuna adawa ga manufofin ƙasashen yamma, musamman ƙasashen Turai da Amurka, inda ya riƙa musu kallon masu tsoma baki a harkokin cikin gida na Venezuela. Wannan salon ya sanya Maduro ya zama wakili mai tsattsauran ra’ayi a wasu taruka na duniya, inda ya yi ƙoƙarin kare muradun waɗanda ke adawa da tsarin siyasa na gargajiya, da kuma ƙarfafa haɗin kai tsakanin ƙasashen da ke goyon bayan manufofinsa.
Naɗa shi a matsayin mataimakin shugaban ƙasa
A shekarar 2012, a yayin da Hugo Chávez ke fama da rashin lafiya mai tsanani, ya naɗa Nicolás Maduro a matsayin mataimakin shugaban ƙasa. Wannan naɗi ya nuna cewa Chávez ya ɗauki Maduro a matsayin magajinsa a siyasa, kuma ya amincewa da shi wajen tsayawa a matsayin jagora idan abubuwa suka taɓarɓare. A wannan lokaci, Chávez yana ta gwagwarmaya da ciwon da ke damun shu, wanda ya sa Maduro ya fara jagorantar gwamnati a lokuta da dama, musamman wajen tarurruka da tattaunawa da masu ruwa da tsaki, da kuma kulawa da harkokin yau da kullum na gwamnati. Wannan aikin da ya yi ya ba shi ƙwarewa mai muhimmanci wajen fahimtar manyan al’amuran ƙasa da siyasa kafin ya hau mulki bayan mutuwar Chávez.
Zaman shi shugaban ƙasa
Bayan mutuwar Hugo Chávez a Maris 2013, Nicolás Maduro ya zama shugaban riƙon ƙwarya bisa tsarin mulkin Venezuela. Wannan ya ba shi damar jagorantar ƙasar yayin da aka shirya gudanar da zaɓe na musamman don cika ragowar lokacin mulkin Chávez. A zaɓen Afrilu 2013, Maduro ya lashe zaɓen da ƙaramar tazara, wanda ya haifar da cece‑ku-ce, inda jam’iyyun adawa suka zargi cewa an samu maguɗi a zaɓen, kuma suka ƙalubalanci sakamakon. Wannan ya sa aka samu zanga‑zangar adawa a sassan ƙasar, da kuma ra’ayoyi mabanbanta tsakanin jama’a kan halaccin sakamakon.
Manufofin siyasa a mulkinsa
A matsayin shugaban ƙasa, Maduro ya ci gaba da aiwatar da manyan manufofin Bolivaria da Hugo Chávez ya kafa, inda ya mayar da hankali kan ƙarfafa rawar gwamnati a tsarin tattalin arziki, tallafa wa talakawa ta hanyar shirye‑shiryen jin‑ƙai, da rage tasirin kamfanoni masu zaman kansu. Wannan ya haɗa da ƙoƙarin amfani da albarkatun ƙasa, musamman man fetur, wajen samar da kudade don tallafin abinci, aikin yi, da shirye‑shiryen jin‑ƙai ga talakawa. Duk da haka, manufofin suna ci gaba da haifar da muhawara saboda yadda suka yi tasiri ga yanayin tattalin arzikin ƙasar da damar jawo zuba jari na waje.
Tattalin arziki a lokacin mulkinsa
A ƙarƙashin mulkinsa, tattalin arzikin Venezuela ya shiga cikin mawuyacin hali mai tsanani, wanda ya ƙara jefa ƙasar cikin rikici da Ƙalubalen rayuwar talakawa. An samu ƙaruwa mai yawa a farashin kayayyaki, yawaitar ƙarancin abinci, magunguna, da sauran kayan masarufi, tare da faɗuwar darajar kuɗin ƙasar, bolívar, wanda ya haifar da tsananin hauhawar farashi a fadin ƙasar.

Nicolás Maduro Moros yana da goyon baya sosai a cikin al’ummar kasar musamman talakawa.
Masu suka suna danganta wannan babban koma baya ga dogaro da man fetur kaɗai, rashin tsari a gudanar da tsarin tattalin arziki, da tasirin takunkumin ƙasashen waje, musamman daga Amurka da wasu ƙasashen yamma, wanda ya taƙaita damar fitar da kayayyaki da samun kuɗaɗen shiga. Wannan ya shafi miliyoyin mutane, ya haifar da yin ƙaura mai yawa, da ƙarancin damar samun abinci mai gina jiki da magunguna.
Siyasar cikin gida da rikice-rikice
A cikin harkokin siyasar cikin gida, Maduro ya fuskanci ƙalubale masu yawa daga ƙungiyoyin adawa, waɗanda suka yi ta ƙoƙarin kalubalantar mulkinsa ta hanyoyi daban‑daban kamar yin zanga‑zanga da shigar da ƙorafe-ƙorafe a kotu kan halaccin wasu zaɓuka. A wasu lokuta, an kame ko an hana wasu ‘yan siyasa shiga zaɓe, kuma an samu rahotannin amfani da kotuna da hukumomin tsaro wajen ƙarfafa ikon gwamnati da hana ‘yan adawa samu damar bayyana ra’ayinsu.
Wannan ya sa ƙasashe da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam suka yi ta sukar matakan gwamnati, suna danganta su da take hakkin ɗan Adam, hana ‘yancin faɗar albarkacin baki, da raunana tsarin demokraɗiyya. Rahotannin sun nuna cewa gwamnatinsa ta yi amfani da ikonta wajen taken tsaro don rugujewar ‘yanci da matakan kariya ga masu adawa kuma akwai ƙorafe‑ƙorafen ɗaure ‘yan adawa da cin zarafi a wasu lokuta.
Alaƙa da ƙasashen waje
Maduro ya ci gaba da ƙarfafa alaƙa mai ƙarfi da Cuba, Rasha, China, da Iran, inda ya samu tallafi a harkokin tattalin arziki, siyasa, da diflomasiyya. A lokaci guda, ya kasance mai tsananin adawa da Amurka da wasu ƙasashen Turai, inda ya yi zargin cewa matsalolin tattalin arziki da siyasa da Venezuela ke fuskanta suna da alaƙa da tsoma bakin waje da takunkumin ƙasashen waje. Ta wannan hanyar, ya yi ƙoƙarin kare Venezuela daga tasirin waje, ya mayar da hankali ga ‘yancin kai da ikon mulkin ƙasa.
Rayuwarsa da iyali
Maduro yana auren Cilia Flores, wadda ita ma ‘yar siyasa ce mai tasiri a Venezuela. Aurensu ya haɗa shugabanci da siyasa, inda Cilia Flores ta taka rawa a cikin jam’iyya da manufofin Bolivaria. Ɗansu, Nicolás Maduro Guerra, ya shiga harkokin siyasa, wanda ya haifar da muhawara a tsakanin al’umma kan batun fifiko ga iyali da yiwuwar tasirinsu a siyasar ƙasar. Wannan lamari ya jawo cece-ku-ce kan gadon siyasa da fifita iyali a matsayin ɓangare na tsarin shugabancin Maduro.
Masu goyon baya
Masu goyon bayan Maduro suna kallon shi a matsayin mai kare gadon Chávez, wanda ke ci gaba da aiwatar da manufofin Bolivaria. Suna ganin shi a matsayin mai yaƙi da mulkin mallaka na zamani, wanda ke tsaya wa talakawa da kare hakkinsu a harkokin siyasa da tattalin arziki.
Masu adawa
A gefe guda, masu adawa suna kallon shi a matsayin shugaban kama-karya, mai haddasa rushewar tattalin arziki, mai raunana tsarin demokradiyya. Sun yi zargin cewa mulkinsa ya kawo tsanani ga talakawa, ya rage yancin ‘yan siyasa masu adawa, kuma ya haifar da rarrabuwar ra’ayoyi a cikin al’umma.
Kama Nicolás Maduro da matarsa
A ranar 3 ga Janairu, 2026, sojojin Amurka suka ƙaddamar da wani babban samame da ake kira Operation Absolute Resolve, inda suka kai hari a yankin Caracas da wasu muhimman wurare na soja a Venezuela domin samun shugaban ƙasa Nicolás Maduro da matarsa, Cilia Flores. Wannan samame ya haɗa da na’urorin musamman na soja da manyan jiragen yaƙi don murƙushe kariya da sauran tsarin tsaro kafin a kama su cikin gida.
Bayan kama su, an wuce da su zuwa New York, Amurka, inda suka fara fuskantar tuhuma a gaban kotun tarayya kan zarge‑zargen da suka haɗa da narco‑terrorism da fataucin miyagun ƙwayoyi. Wannan lamari ya jawo babban cece‑ku-ce a duniya kuma ya buɗe sabon babi a tarihin siyasar Venezuela da dangantakar tsakiyar Amurka da Latin America.
Shugabancin wucin gadi a Venezuela
Bayan kama Maduro, Aliƙalin shugaban ƙasa Delcy Rodríguez, wacce ta kasance mataimakiyar shugaban ƙasa a lokacin mulkinsa, ta zama shugabar wucin gadi ta Venezuela bisa umarnin Kotun Koli. A yayin da take rike da wannan mukami, ta ɗauki matakai don tattara jami’an gwamnati da haɗa kan shugabannin siyasa domin tabbatar da tsaro a fadin ƙasa, tare da fara sakin wasu ‘yan siyasa da fursunoni da ake ɗauka a matsayin masu adawa ga tsohuwar gwamnati.

Maduro ya zama shugaban kasa a zaɓen Afrilun 2013 da ƙaramar tazara.
Wannan sabon tsarin siyasa na wucin gadi an kafa shi ne domin rage rikicin siyasa da tashe‑tashen hankula da suka biyo bayan kame shugaban ƙasa na baya. Rodríguez ta kuma kafa wasu manufofi don samar da damar tattaunawa tsakanin jam’iyyun siyasa a cikin ƙasar, lamarin da ke nuni da cewa ana ƙoƙarin samar da tsarin shugabanci mai ɗorewa bayan abin da ya faru.
Tasirin tattalin arziki bayan kama Maduro
Bayan kama Maduro da sauya shugabanci, tattalin arzikin Venezuela ya shiga wani sabon mataki na rashin tabbas da matsi. A cikin wannan yanayi, an samu faduwar darajar kuɗin ƙasa, bolívar, yayin da farashin kayayyaki da abinci ya ci gaba da tashi, wanda hakan ya ƙara matsi ga al’umma musamman masu ƙaramin ƙarfi. Tasirin takunkumin ƙasashen waje ya ci gaba da zama takura ga gwamnatin wucin gadi wajen samun kuɗaɗe, musamman ma wajen fitar da albarkatun ƙasa kamar man fetur, wanda yake ɗaya daga cikin manyan tushen kudaden shiga na ƙasar.
Hukumar IMF ta bayyana cewa idan za a dawo da dangantakarta da ƙasar, dole ne a sami goyon bayan yawancin ƙasashe su amince da gwamnatin da ta biyo baya, bayan kame shugaban ƙasa; in ba haka ba, za ta ci gaba da kasancewa a cikin mawuyacin hali tattalin arziki.
Dangantaka da ƙasashen waje
Bayan kama Nicolás Maduro da Cilia Flores, dangantakar Venezuela da wasu ƙasashen duniya ta shiga wani sabon yanayi mai ɗauke da rikice‑rikice da sabbin dabaru a fagen diflomasiyya. Amurka, karkashin shugabancin Donald Trump, ta fara tsara harkokin tattalin arzikin Venezuela, musamman wajen sayar da man fetur da sauran albarkatun ƙasa, inda aka fara shirya fitar da mai ga kasuwannin duniya da kuma yuwuwar zuba jari daga kasashen waje. Wannan mataki na tattalin arziki yana wani ɓangare ne na dabarar Amurka ta sarrafa albarkatun Venezuela da sake kafa alaƙar tattalin arziki da sabuwar gwamnatin wucin gadi, musamman ta hanyar yarjejeniyoyi da manyan kamfanonin ƙetare.
A gefe guda, martanin duniya ya bambanta sosai. Wasu ƙasashe sun yi suka mai tsanani kan aikin sojojin Amurka a Venezuela, suna bayyana cewa amfani da ƙarfi a cikin ƙasa mai cin ƙashin kanta ya saɓa wa Dokar Majalisar Ɗinkin Duniya da ka’idojin ƙasa da ƙasa. Misali, China ta bayyana cewa tana jin “tsananin kaɗuwa” kuma tana ƙin amfani da ƙarfi a kan wata ƙasa, tana ganin hakan ya saɓa wa ɗabi’un zaman lafiya da ƙa’idojin dokar duniya.
Wataƙila wannan martani ya haɗa da ra’ayoyin manyan ƙasashe irin su Rasha da Iran, waɗanda suke kallon matakin Amurka a matsayin ƙarin haɗari ga zaman lafiya da ‘yancin ƙasa. Wasu ƙasashen Turai da Afirka sun yi kira ga girmama ‘yancin kai da ikon ƙasa, suna masu ƙarfafa tattaunawa tsakanin ‘yan siyasa a cikin Venezuela domin magance rikicin siyasa.
Cece‑ku-ce da ra’ayoyi a duniya
Kamun shugaban ƙasar Venezuela ya jawo mummunan cece‑ku-ce a duniya, inda ra’ayoyi suka bambanta sosai bisa matsayin ƙasashen duniya da ƙungiyoyi game da halaccin wannan aiki. Masu suka sun bayyana cewa kama shugaban ƙasar da Amurka ta yi ya saɓa wa dokar kasa da ƙasa saboda amfani da ƙarfi ba tare da izini daga Majalisar Ɗinkin Duniya ba, lamarin da masu sukar ke ganin ya saɓa wa manufar girmama ‘yancin ƙasa da tsare‑tsaren UN. Wasu masana da ƙungiyoyi masu kare haƙƙin ɗan Adam sun yi kira a tabbatar cewa duk wani mataki na siyasa da aka ɗauka ya bi ka’idojin kare haƙƙin ɗan Adam da ƙa’idojin duniya game da tafiyar da rikice‑rikice.

A gefe guda, masu goyon baya ga matakin Amurka suna ganin tsarin cire Maduro daga mulki zai iya haifar da sauyi mai kyau ga talakawa da kuma ƙoƙarin magance matsalolin siyasa da tattalin arziki da suka addabi Venezuela tsawon shekaru. Wannan fahimta tana ganin cewa cire shuwagabannin da ake zargi da rashin gaskiya da wasu laifuka na iya kawo sauyi a jagoranci da kuma buɗe ƙofa ga sabbin hannu a dimokuradiyya da cigaba. Duk da haka, waɗannan ra’ayoyi na goyon baya suna da damuwa kan yadda ƙarshen wannan lamari zai kasance a cikin dogon lokaci, musamman idan ba a bi hanyar tattaunawa da zaman lafiya ba.
Tasirin siyasa a yankin Latin America
Abin da ya faru a Venezuela ya haifar da babban tasiri a siyasar Latin America baki ɗaya. A wannan yanki, mafi yawancin ƙasashe sun yi kira ga girmama ‘yancin kai da zaman lafiya yayin magance rikicin Venezuela, suna ƙin amfani da ƙarfi a harkokin cikin gida na wata ƙasa. Misali, shuwagabannin wasu ƙasashen sun bayyana damuwa cewa matakin Amurka ya ƙirƙiri mummunan misali da zai iya rinjayar sauran ƙasashe a yankin, lamarin da ke ƙara tayar da hankula tsakanin ƙasashen maƙwabta na Venezuela.
Wasu jam’iyyun adawa da gwamnati a ƙasashen kusa da Venezuela suna ƙoƙarin haɗa kai wajen shawo kan rikicin tattalin arziki da siyasa, suna amfani da hanyoyin diflomasiyya da tattaunawa domin neman mafita.
Manazarta
Norden, D. L. (2026, January 5). A review of Authoritarian Consolidation in Times of Crisis: Venezuela under Nicolás Maduro. ReVista: Harvard Review of Latin America.
Arana Araya, I. (2024, June). Chavismo in Venezuela (in A. Baturo, L. Anceschi, & F. Cavatorta, Eds.), in Personalism and Personalist Regimes. Oxford University Press.
Garoupa, N., Rosales, V., & Spruk, R. (2025, November 11). Assaults on judicial independence under the pretense of modernization: Evidence from Venezuela. arXiv.
Sharuɗɗan Editoci
Duk maƙalun da ku ka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta tare da sa idon kwamitin ba da shawara na ƙwararru. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.
Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.