A baya na yi magana a kan bangarori daban-daban da ilimin noma da kiwo ya kunsa. A yau zan dora ba tare da bata lokaciba.
Abubuwan da ake yi game da noma wadanda ake samun ayyukan yi da su:
1. Shuka
2. Sarrafawa (production)
3. Rarrabawa (distribution)
4. Sayarwa (marketing)
5. Ajiya (storage)
Hanyoyin daza a bunkasa domin samun ayyuka ta bangaren noma
1. Neman ilimin noma da kuma yin noman
2. Sana’o’in aikin gona da kula dasu
3. Saye da sayarwa na amfanin gona.
4. Kiwon kifi
5. Kiwon kaji
6. Kiwon dabbobi
Idan aka bi wadannan hanyoyi za a samu saukin wadannan matsalolin kamar haka:
- Yawan barayi
- Rashin zaman lafiya
- Samun ci gaban tattalin arzikin kasa
- Rage hijira daga wani gari zuwa wani gari
- Rage ‘yan zauna gari banza
Shi wannan bangare na ilimin noma da kiwo ya na da bangarori daban daban da su ka hada da sannin nau’oin dabbobi da kuma yadda za’a kula da kasar noma ita kanta har izuwa noman da za a kaiwa kasuwa don sayarwa.
Idan muka kula da neman ilimin noma da kiwon dabbobi za a samu ayyukan yi da kuma karuwar arziki kasarnan.