Skip to content

Norovirus

    Aika

    Norovirus wata ƙwayar cuta ce mai matuƙar saurin yaɗuwa wadda ke haddasa ciwon ciki da amai, wanda masana kimiyya ke kira da acute gastroenteritis. Ana yawan kiran wannan cuta da suna “stomach flu”, amma wannan suna ba daidai ba ne, domin ba ta da wata alaƙa da cutar influenza wadda ke kama huhu.

    Cutar Norovirus tana daga cikin mafi yawan sanadin gudawa da amai a duniya, tana iya kama kowane rukuni na mutane, sawa’un yara, manya, da tsofaffi. An kiyasta cewa miliyoyin mutane a kowace shekara suna kamuwa da ita a sassan duniya daban-daban, kuma tana haifar da mutuwa musamman a ƙasashen da ba su da ingantaccen tsarin tsafta da kiwon lafiya.

    shutterstock 1103078720 1
    Norovirus, ƙwayar cuta mai haddasa amai da gudawa.

    Wannan ƙwayar cuta tana da ƙarfin yaɗuwa sosai ta hanyoyi da dama, har ta zama ɗaya daga cikin manyan matsalolin lafiya na jama’a a duniya. A wuraren da ake da cunkoson jama’a kamar makarantu, asibitoci, gidajen marayu, sansanonin soja, gidajen yari, sansanonin ‘yan gudun hijira, da jiragen ruwa masu yawon shakatawa, norovirus kan haifar da ɓarkewar cuta cikin lokaci kaɗan, inda mutum ɗaya kaɗai zai iya yaɗa cutar ga mutane da dama.

    Ƙwayar Norovirus tana da ƙarfin jurewa sinadarai masu kashe ƙwayoyin cuta, tana kuma iya rayuwa a kan abubuwa da mutum ke taɓawa kamar tebura, ƙofa, kayan abinci na tsawon kwanaki ko ma makonni. Saboda wannan ƙarfi, cutar na yaɗuwa cikin sauƙi, musamman idan ba a kula da tsafta da wanke hannu da sabulu da ruwa ba.

    Cutar ba ta bambanta tsakanin ƙasashe masu ci gaba da marasa ci gaba ba, domin ta kan iya bayyana a ko’ina, musamman idan akwai cunkoso, rashin tsafta, ko hulɗa mai yawa tsakanin mutane. Saboda haka, norovirus tana daga cikin manyan ƙwayoyin cuta da ƙungiyoyin lafiya kamar WHO da CDC suke bai wa kulawa ta musamman wajen riga-kafi da gano hanyoyin yaɗuwarta.

    Tarihin ƙwayar cutar norovirus

    An fara gano norovirus ne a shekarar 1968 a garin Norwalk, Jihar Ohio na Amurka, lokacin da aka samu ɓarkewar cutar amai da gudawa a makarantar firamare. Daga wannan wuri aka fara kiran shi da “Norwalk virus”. Daga baya aka tabbatar da cewa ƙwayar cutar na daga cikin manyan rukuni na Caliciviridae, kuma tana da matuƙar sauƙin bazuwa.

    A duniya, Norovirus ta kasance sanadiyyar kusan kashi 18% na dukkan cututtukan gudawa. Ta yawaita musamman a wuraren da ake da cunkoso, kamar makarantu, gidajen jinya, sansanonin soja da na’yan gudun hijira, da jiragen ruwa. Tana haifar da sama da ɓarkewar cututtuka dubu dari uku (300,000) a  kowace shekara, lamarin da ke janyo asarar kuɗaɗe da kuma koma baya ga tattalin arziki.

    A Najeriya, bincike ya nuna cewa Norovirus tana yaɗuwa musamman tsakanin yara ƙanana da marasa lafiya masu raunin garkuwar jiki. An samu rahotanni daga jihohi da dama, ciki har da Ogun, inda aka gano bambancin kwayoyin cutar a cikin yara masu fama da gudawa. A Abuja kuma, an samu binciken da ya nuna yawan kamuwa da cutar a tsakanin masu ɗauke da cutar HIV. Wannan ya nuna cewa Norovirus ba sabon abu ba ne a Najeriya, sai dai ba a yawan gano shi saboda ƙarancin gwaje-gwaje na musamman.

    Siffar ƙwayar cutar

    Norovirus ƙwayar cuta ce mai ƙanƙanta ƙwarai, wadda ke da diamita kusan nanometer 27 zuwa 38 kacal, abin da ya sa ta zama ɗaya daga cikin ƙwayoyin cuta mafi ƙanƙanta a duniya. Tsarinta ya ƙunshi RNA guda ɗaya (single-stranded RNA), wanda ke cikin rufin capsid da aka gina da sinadaran protein. Wannan tsarin capsid yana da siffar icosahedral, wato yana kama da ƙwallon ƙafa mai fuskoki 20.

    Ƙwayar norovirus ba ta da ɓawo ko kwanso (wanda ake kira “envelope”) kamar yadda ake samu a wasu ƙwayoyin cuta kamar influenza. Rashin wannan rufin lipid yana ba ta ƙarfin jure sinadaran tsafta kamar alcohol-based sanitizers, detergents, da wasu magungunan kashe ƙwayoyin cuta. Saboda haka, sabulu da ruwa mai zafi ne kawai ke da tasiri sosai wajen lalata ta idan aka yi amfani da su da kyau.

    Ƙwayar na da ƙarfin jure rayuwa mai tsawo a waje, musamman a wuraren da ba su da tsafta. A cikin yanayi mai matsakaicin zafi, norovirus na iya rayuwa har zuwa makonni biyu, yayin da a yanayin sanyi take iya rayuwa har fiye da wata ɗaya. Haka kuma tana iya rayuwa a cikin ruwa, ruwa mai sanyi ko daskararre, da kayan abinci da aka adana a firiji.

    A dalilin ƙanƙanta da juriya mai ƙarfi, norovirus na iya shiga cikin jikin mutum cikin sauƙi ta hanyar abinci ko ruwa da aka gurɓata, ko kuma ta hanyar taɓa wani abin da ke ɗauke da da hannu. Bayan ta shiga jiki, tana ninka kanta cikin sauri a cikin hanji, tana lalata ƙwayoyin epithelial da ke shimfiɗe a bangon hanji, wanda hakan ke haifar da gudawa, amai, da sauran alamomin ciwon ciki.

    Saboda waɗannan siffofi, norovirus ta zama ɗaya daga cikin ƙwayoyin cuta mafi wuya a kawar da su, tana buƙatar tsabtace muhalli da kulawa ta musamman wajen magance ɓarkewar cuta.

    Yadda norovirus ke yaɗuwa

    Norovirus tana yaɗuwa ta hanyoyi da dama. Babbar hanyar yaɗuwarta ita ce ta cin abinci ko shan ruwa da suka gurɓace da ƙwayar cutar. Mutum na iya kamuwa da ita ta hanyar taɓa abubuwa da suka gurɓace da ƙwayar, irin su ƙofofi, tebura, ko kayan kicin, sannan ya kai hannu baki.

    Hulɗa kai tsaye da wanda ya kamu da cutar, musamman ta hanyar taɓa najasa ko kasancewa kusa da amai. Duka na daga cikin manyan hanyoyin yaɗuwar ƙwayar cutar. Cutar na yawan bazuwa a wuraren cunkoson jama’a, kamar makarantu, gidajen jinya, gidajen marayu, sansanonin soja, da kuma cikin jiragen ruwa. Wannan shi ya sa ake ɗaukar ta a matsayin cuta mai saurin bazuwa wadda ke iya haddasa ɓarkewar annoba cikin gaggawa.

    Alamomin ƙwayar cutar norovirus

    Alamomin ƙwayar cutar norovirus sukan bayyana bayan awanni 12 zuwa 48 da kamuwa da cutar. Babban abin da ke bayyana shi ne amai mai yawa da kuma gudawa mai ruwa, wanda ke iya haddasa rashin ruwa a jiki cikin sauri.

    Marasa lafiya sukan ji ciwo ko tsami a ciki, wani lokaci tare da tsananin gurɓatar ciki. Haka kuma ana samun zazzaɓi mai sauƙi, jin jiri, ciwon kai da gajiya. Yawanci cutar tana ɗaukar kwanaki biyu zuwa uku kafin ta wuce, amma ga yara, tsofaffi da masu raunin garkuwar jiki, tana iya tsananta kuma ta haifar da matsananciyar rashin ruwa a jiki. Wasu daga cikin alamomin sun haɗa da:

    • Amai mai yawa.
    • Gudawa mai ruwa.
    • Ciwo ko murɗa a ciki.
    • Jin kasala da rauni.
    • Zazzabi mai sauƙi.
    • Jin jiri ko rashin ruwa a jiki.

    Alamomin yawanci suna ɗaukar kwanaki 1 zuwa 3, sannan su wuce da kansu, amma a wasu lokuta cutar na iya zama mai haɗari ga yara ƙanana, tsofaffi, da mutane masu raunin garkuwar jiki.

    Illolin ƙwayar cutar norovirus

    Illar da ta fi girma da norovirus ke haifarwa ita ce rashin ruwa a jiki (dehydration). Wannan na faruwa ne saboda amai da gudawa masu yawa, musamman ga yara ƙanana da tsofaffi. Idan aka yi sakaci ba a maye gurbin ruwan da jiki ya rasa ba, cutar na iya zama mai hatsari duk da cewa a mafi yawan lokuta ba ta kashewa.

    Riga-kafi da hanyoyin kare kai

    Babu maganin allura da aka ƙirƙira domin riga-kafin norovirus. Don haka kariya mafi muhimmanci ita ce kula da tsafta. Wanke hannu da kyau da sabulu da ruwa bayan zuwa banɗaki ko kafin shirya abinci ya zama wajibi.

    Dafa abinci yadda ya kamata da kuma shan ruwa mai tsafta suna rage haɗarin kamuwa da cutar. Haka nan, tsaftace kayan girki, tebura da da sinadarai masu kashe ƙwayoyin cuta yana taimakawa. Idan wani ya kamu da cutar, ya dace a killace shi har sai ya warke don rage yaɗuwar cutar.

    Maganin norovirus

    Babu wani magani na musamman da ke kashe ƙwayar cutar norovirus a jiki. Magani ya fi karkata ga magance alamomin cutar da dawo da ƙarfin jiki. Muhimmiyar hanya ita ce maye gurbin ruwan da aka rasa ta hanyar shan ruwan gishiri da suga (oral rehydration solution).

    A lokuta masu tsanani, musamman ga yara da tsofaffi, ana iya buƙatar kulawar asibiti da bayar da yin ƙarin ruwa (drip). Shan ruwa mai tsafta da cin abinci mai muhimmanci suna taimakawa wajen murmurewa cikin kwanaki kaɗan. Magungunan saukar zazzabi da rage ciwon kai za su iya taimakawa, amma ba a ba za a iya amfani da magungunan dakatar da gudawa ba sai da umarnin likita.

    Norovirus cuta ce da ke bazuwa cikin sauƙi, kuma tana daga cikin manyan dalilan ɓarkewar amai da gudawa a duniya. Duk da cewa ba ta kashewa a mafi yawan lokuta, cutar na iya zama barazana ga rayuwa idan ta haddasa matsananciyar rashin ruwa. Hanyoyin riga-kafi da suka haɗa da tsafta, shan ruwa mai tsafta, da killace masu cutar su ne matakai mafi inganci wajen dakile yaɗuwarta.

    Manazarta

    Arowolo, K. O., Oluwadare, O. O., Afolabi, M. O., & Olowe, O. A. (2023). Genetic diversity of norovirus in children with acute gastroenteritis in Ogun State, Nigeria. Archives of Virology.

    Chigor, V. N., Eze, U. E., Nwiro, C. J., & Iwu, C. (2024). Epidemiology of norovirus infection in Nigeria: A systematic review and meta-analysis. Journal of Medical Virology.

    Osazuwa, F., Johnson, W. O., & Grobler, H. S. (2023). Norovirus infection among HIV-infected patients in Abuja, Nigeria: Impact of combination antiretroviral therapy status. BMC Infectious Diseases, 23, 623.

    Tarihin Wallafa Maƙalar

    An kuma sabunta ta 6 October, 2025

    Sharuɗɗan Editoci

    Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.

    Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.

    Maƙalar ta amfanar?
    EAa

    You cannot copy content of this page

    ×