Numfashi shi ne tsarin da halittu, musamman ɗan Adam, ke shaƙar iska mai ɗauke da oxygen zuwa cikin jiki sannan ya fitar da iska mai ɗauke da carbon dioxide zuwa waje. Wannan aiki yana faruwa kai tsaye ba tare da sai mutum ya yi niyya ba, domin yana daga cikin ayyukan jiki na ɗabi’a da ƙwaƙwalwa ke sarrafawa kai tsaye.
A ilimin kimiyya, ana kallon numfashi ta hanyoyi biyu masu alaƙa da juna. Na farko shi ne numfashin waje, wato shaƙar iska da fitar da ita ta hanci ko baki zuwa cikin huhu. Na biyu kuma shi ne numfashin cikin jiki, wato yadda ƙwayoyin halitta ke amfani da iskar oxygen domin samar da makamashi daga abinci. Wannan yana bayyana cewa numfashi bai taƙaita ga motsin iska ba kaɗai ba, yana da alaƙa da muhimman ayyuka da ke faruwa a cikin ƙwayoyin halittar jiki. Misali, idan mutum ya rike numfashinsa na wani lokaci, zai fara jin matsanancin bukatar iska, kuma idan ya ci gaba da hana iska shiga, zai iya suma ko ma ya rasa rai. Kenan numfashi shi ne ginshiƙin rayuwa.
Muhimmanci numfashi ga rayuwa
Rayuwar ɗan Adam da sauran halittu masu tsarin numfashi ba za ta yiwu ba idan ba tare da wannan tsari ba. Dukkan gaɓoɓin jiki, musamman ƙwaƙwalwa da zuciya, suna buƙatar isasshiyar iskar oxygen domin su yi aikinsu yadda ya kamata. Idan iskar oxygen ta ragu ko ta ɗauke gabaɗaya, ayyukan jiki za su fara lalacewa cikin sauri.
Numfashi yana ba jiki damar samun oxygen da yake bukata, sannan yana taimakawa wajen fitar da carbon dioxide, wadda ita ce sharar da jiki ke fitarwa bayan amfani da oxygen. Idan carbon dioxide ta taru a jiki, tana iya zama guba kuma ta jawo matsaloli kamar jiri, kasala, ko ma mantuwa.
A rayuwar yau da kullum, ana iya fahimtar muhimmancin numfashi a lokacin da mutum ke yin aiki mai wahala ko motsa jiki. A irin wannan lokaci, numfashi yana sauri kuma yana zurfi saboda jiki yana bukatar karin iskar oxygen domin samar da makamashin kuzari. Haka kuma, mutumin da ya nutse a ruwa ko wanda aka toshe masa hanyoyin numfashi yana cikin hadarin rasa rai cikin ‘yan mintoci, domin ƙwaƙwalwa ba ta jure rashin oxygen na dogon lokaci.
Alaƙar numfashi da makamashin kuzari
Numfashi yana da dangantaka kai tsaye da samuwar makamashin kuzari a jiki. Abincin da mutum yake ci yana ɗauke da sinadaran da ke ba jiki kuzari, amma wannan kuzarin ba zai yi amfani ba sai an haɗa shi da oxygen a cikin ƙwayoyin halitta. Wannan tsari akeashin cikin jiki.
A cikin ƙwayoyin halitta, oxygen tana taimakawa wajen narkar da sinadaran abinci, musamman sukari, domin samar da makamashin da ake kira ATP. Wannan makamashi shi ne jiki ke amfani da shi wajen motsi, tunani, harbawar zuciya, da sauran ayyuka. A lokaci guda kuma, ana samar da carbon dioxide da ruwa a matsayin sharar wannan tsari, wanda daga bisani ake fitar da carbon dioxide ta numfashi.
Misali, lokacin da mutum ke gudu, tsokar jikinsa na bukatar ƙarin makamashin kuzari, shi ya sa numfashinsa ke sauri domin a samu ƙarin oxygen. Idan babu isasshiyar oxygen, jiki zai gaji da sauri kuma aikin tsokoki zai ragu.
Ma’anar tsarin numfashi a ilimin kimiyya
Tsarin numfashi shi ne jerin gaɓoɓi da hanyoyi a jikin ɗan Adam da ke kula da shigar iska, sarrafa ta, da kuma musayar oxygen da carbon dioxide tsakanin jiki da muhalli. Wannan tsarin ya haɗa sassa kamar hanci, maƙogwaro, bututun iska, da huhu, tare da tsokar diaphragm wadda ke taimakawa motsin numfashi.

Babban aikin tsarin numfashi shi ne tabbatar da cewa jiki yana samun oxygen ɗin yake bukata domin rayuwa, kuma yana fitar da carbon dioxide domin kare jiki daga guba. Idan wani ɓangare na wannan tsarin ya samu matsala, kamar kamuwa da cuta a huhu, numfashi zai zama da wahala kuma hakan na iya jawo barazana ga rayuwa.
Rawar oxygen da carbon dioxide yayin numfashi
Oxygen
Oxygen ita ce ginshikin numfashi domin ita jiki ke bukata wajen samar da makamashin kuzari ga kwayoyin halitta. Bayan shiga huhu, oxygen tana shiga jini, sannan jini ya rarraba ta zuwa dukkan sassan jiki. Rashin oxygen na iya jawo matsaloli masu tsanani kamar suma, lalacewar ƙwaƙwalwa, ko mutuwa.
Carbon dioxide
Carbon dioxide kuwa ita ce gurɓatacciyar iskar da jiki ke fitarwa bayan amfani da oxygen wajen samar da makamashin kuzari. Idan ta taru a jiki, tana iya zama guba. Saboda haka, tsarin numfashi yana da muhimmiyar rawa wajen fitar da ita domin kiyaye daidaiton jiki.
Misali, mutumin da ke cikin ɗaki marar isasshiyar iska na iya fara jin jiri ko kasala saboda ƙaruwar carbon dioxide a cikin iskar ɗakin. Haka kuma, yawan carbon dioxide a jini yana sa mutum ya ji bukatar yin numfashi cikin sauri domin ya fitar da ita.
Sassan tsarin numfashi
Tsarin numfashi na ɗan Adam ya ƙunshi wasu muhimman gaɓoɓi da hanyoyi da suke aiki tare domin tabbatar da shigar iska mai ɗauke da oxygen zuwa jiki da kuma fitar da carbon dioxide. Waɗannan sassa suna da tsari na musamman wanda ya dace da aikin da suke yi, kuma kowanne ɓangare yana da rawar da ba za a iya maye gurbinsa da wani ba.
Hanci da kogon hanci
Hanci shi ne kofar shigar iska zuwa tsarin numfashi. Lokacin da mutum ya shaƙi iska, ta fara shiga ta hanci kafin ta wuce zuwa sauran sassan numfashi. Cikin hanci akwai wasu ƙananan gashi masu laushi da kuma wani abu mai kama da ruwan majina wanda ke taimakawa wajen tace datti daga cikin iska.
Manyan ayyukan hanci sun haɗa da karɓar iska, tace ƙura da ƙwayoyin cuta, da kuma shirya iska kafin ta kai huhu. Wannan yana da matuƙar muhimmanci domin huhu na buƙatar iska mai tsafta da kuma yanayin zafin da ya dace.
Hanci yana kuma ɗumama iska idan ta yi sanyi, sannan yana ƙara mata danshi idan ta bushe. Wannan yana kare huhu daga lalacewa ko bushewa. Misali, a lokacin sanyi mai tsanani, idan mutum ya shaƙi iska ta baki kai tsaye, yana iya jin ƙaiƙayi ko zafi a ƙirji, amma idan ta hanci ne, hancin yana rage tasirin sanyi kafin iska ta isa huhu.
Maƙogwaro
Bayan iska ta shiga hanci, tana wucewa ta maƙogwaro. Maƙogwaro ya kasu gida biyu a ilimin kimiyya, wato pharynx da larynx. Pharynx wata hanya ce da iska ke bi daga hanci ko baki zuwa bututun iska, yayin da larynx kuma yake ɗauke da murya.
Rawar maƙogwaro ita ce samar da hanyar wucewar iska zuwa huhu ba tare da tangarɗa ba. A lokaci guda kuma yana taka muhimmiyar rawa wajen hana abinci shiga hanyoyin numfashi. Wannan yana faruwa ne ta wani ɓangare da ake kira epiglottis, wanda ke rufe hanyar iska lokacin haɗiyar abinci.
Larynx yana da alaka kai tsaye da magana, domin a cikinsa ne ake samun jijiyoyin murya. Lokacin da iska ta wuce ta wurin, jijiyoyin murya suna rawar jiki su samar da sauti, wanda daga bisani harshe da baki ke sarrafawa ya zama magana. Misali, idan mutum ya kamu da mura mai tsanani, muryarsa na iya sauyawa saboda kumburin da ke shafar larynx.
Bututun iska (trachea)
Bututun iska wata doguwar hanya ce da ke haɗa maƙogwaro da huhu. An gina shi da wani tsari na kashi mai kama da zobe wanda ke taimakawa ya kasance a buɗe domin iska ta riƙa wucewa cikin sauƙi. Cikin bututun iska akwai wani nau’in gashi mai matukar kankanta da ke motsawa domin tura datti ko ƙura zuwa sama inda za a iya fitar da shi ta tari ko haɗiyewa.
Babban aikin bututun iska shi ne jigilar iska daga maƙogwaro zuwa huhu da kuma mayar da ita lokacin fitar da numfashi. Idan bututun iska ya toshe ko ya samu rauni, numfashi zai zama da wahala sosai. Misali, idan wani abu ya maƙale a bututun iska, mutum na iya kasa numfashi har sai an cire shi.
Huhu
Huhu su ne manyan gaɓoɓin numfashi da ke cikin ƙirji. Ɗan Adam yana da huhu biyu, na dama da na hagu. Huhun dama ya fi girma kaɗan saboda ɓangaren hagu na ƙirji yana ɗauke da zuciya. Huhu suna da laushi kuma suna cike da ƙananan jakunkuna na iska da ake kira alveoli.
Alveoli su ne wurin da muhimmin aikin numfashi ke faruwa, wato musayar oxygen da carbon dioxide tsakanin iska da jini. Bangon alveoli yana da matukar siranta kuma yana ɗauke da ƙananan jijiyoyin jini, wanda ke ba da dama oxygen ta shiga jini cikin sauƙi, yayin da carbon dioxide ke fita daga jini zuwa cikin alveoli domin a fitar da ita.
Misali, idan alveoli sun lalace sakamakon shan taba ko wata cuta, jiki ba zai iya samun isasshiyar oxygen ba, wanda ke jawo wahalar numfashi da gajiya.
Tsokar diaphragm
Diaphragm wata babbar tsoka ce da ke ƙarƙashin huhu, tana raba ƙirji da ciki. Ita ce babbar tsoka da ke taimakawa motsin numfashi. Lokacin da mutum ya shaƙi iska, diaphragm tana matsewa ta sauka ƙasa, hakan yana faɗada ƙirji ya ba huhu sarari su cika da iska. Lokacin fitar da iska kuma, tana komawa sama ta rage girman ƙirji, iska ta fita daga huhu.
Ayyukan diaphragm suna faruwa ne kai tsaye ba tare da niyyar mutum ba, amma mutum na iya sarrafa numfashinsa na dan lokaci, misali lokacin magana, waka, ko nutsewa cikin ruwa.
Misali, idan mutum ya yi dariya sosai ko ya yi kuka, motsin diaphragm yana canjawa, wanda ke sa numfashi ya rikice na wani lokaci. Haka kuma, idan diaphragm ta samu rauni, numfashi zai zama mai wahala domin huhu ba za su iya faɗaɗa yadda ya kamata ba.
Yadda numfashi ke aiki
Numfashi tsari ne mai cike da daidaito wanda ke faruwa ta hanyar haɗin gwiwar huhu, tsokar diaphragm, jijiyoyin jini da kuma wasu sassan jiki. Wannan tsari yana gudana ne ba tare da niyyar mutum ba, kuma yana maimaituwa sau da dama a minti guda domin tabbatar da cewa jiki yana samun iskar oxygen ɗin da yake bukata tare da fitar da carbon dioxide.
Shaƙar iska
Shakar iska ita ce matakin farko na numfashi, inda iska mai dauke da oxygen ke shiga cikin huhu. Wannan yana faruwa ne lokacin da tsokar diaphragm ta matse ta sauka ƙasa, sannan tsokokin ƙirji su ja su faɗaɗa ƙirji. Sakamakon haka, sararin cikin ƙirji yana ƙaruwa, huhu su faɗaɗa su cika da iska.
Lokacin da iska ta shiga ta hanci ko baki, tana wucewa ta maƙogwaro da bututun iska har ta isa huhu. A wannan mataki, iska tana shiga cikin ƙananan jakunkunan iska da ake kira alveoli. Misali, idan mutum ya ja numfashi mai zurfi kafin ya nutse cikin ruwa ko kafin ya ɗaga wani abu mai nauyi, yana ƙoƙarin cika huhunsa da iska domin ya samu ƙarin oxygen.
Fitar da iska
Fitar da iska shi ne matakin da ke biye da shaƙar iska, inda iska mai ɗauke da carbon dioxide ke fita daga huhu zuwa waje. Wannan yana faruwa ne lokacin da diaphragm ta saki ta koma sama, ƙirji ya matse, sararin cikin ƙirji ya ragu, huhu su matse su tura iska waje.
Wannan tsari yana taimakawa wajen cire sharar da jiki ya samar bayan amfani da oxygen. Fitar da iska na iya zama a hankali lokacin da mutum yake hutawa, ko kuma cikin sauri lokacin da yake gudu ko yin aiki mai nauyi. Misali, lokacin da mutum ya hura iska domin kashe kyandir ko ya yi ajiyar zuciya, yana fitar da iska mai ɗauke da carbon dioxide ne daga huhu.
Musayar iskar oxygen da carbon dioxide a jini
Muhimmin aikin numfashi yana faruwa ne a cikin alveoli na huhu, inda ake musayar oxygen da carbon dioxide tsakanin iska da jini. Bangon alveoli yana da matukar siranta kuma yana kewaye da ƙananan jijiyoyin jini, wanda ke ba da damar iskar ta ratsa cikin sauƙi.
Oxygen daga iska tana shiga cikin jini ta bangon alveoli, sannan jajayen ƙwayoyin jini su ɗauke ta su kai ta ga dukkan sassan jiki. A lokaci guda kuma, carbon dioxide daga jini tana shiga cikin alveoli domin a fitar da ita ta numfashi. Misali, idan wannan musayar ta samu tangarɗa, kamar yadda yake faruwa a wasu cututtukan huhu, mutum zai iya jin wahalar numfashi ko kasala saboda jiki ba ya samun isasshiyar oxygen.
Kula da tsarin numfashi
Tsarin numfashi ba ya aiki shi kadai, yana da alaka da wasu manyan tsare-tsare a jiki, musamman tsarin jini da zuciya da kuma ƙwaƙwalwa. Waɗannan sassa suna aiki tare domin tabbatar da cewa numfashi yana gudana yadda ya kamata.
Rawar jini da zuciya ga numfashi
Jini shi ne ke ɗaukar oxygen daga huhu ya kai ta ga ƙwayoyin jiki, sannan ya dawo da carbon dioxide zuwa huhu domin a fitar da ita. Zuciya kuwa ita ce ke harbawa ta tura jini cikin jijiyoyi zuwa dukkan sassan jiki.
Lokacin da jini ya iso huhu, yana ɗaukar oxygen daga alveoli, sannan ya mayar da carbon dioxide. Daga nan zuciya ta tura wannan jini mai dauke da oxygen zuwa ƙwaƙwalwa, tsoka, da sauran gaɓoɓin jiki.
Misali, lokacin da mutum ke motsa jiki, zuciya tana harbawa da sauri domin ta rarraba ƙarin oxygen zuwa jiki, shi ya sa numfashi ma ke sauri. Idan zuciya ko jini ba su yi aiki yadda ya kamata ba, numfashi ma zai samu matsala domin jiki ba zai samu isasshiyar oxygen ba.
Yadda ƙwaƙwalwa ke sarrafa numfashi
Ƙwaƙwalwa ce ke sarrafa numfashi ta tsarin atomatik, musamman wani ɓangare da ake kira medulla oblongata. Wannan ɓangare yana lura da yawan carbon dioxide da oxygen a cikin jini, sannan ya aika saƙonni ga tsokar diaphragm da sauran tsokokin numfashi domin su ƙara ko rage saurin numfashi.
Idan carbon dioxide ta ƙaru a jini, ƙwaƙwalwa tana sa numfashi ya zama da sauri domin a fitar da ita. Idan kuma jiki yana samun hutu da wani aiki, saurin numfashi yana raguwa domin buƙatar oxygen ta ragu. Misali, lokacin da mutum yake barci, numfashinsa yana tafiya a hankali cikin daidaito. Amma idan ya ji tsoro ko firgita, ƙwaƙwalwa na sa numfashi ya yi sauri saboda jiki yana cikin shirin fuskantar wani yanayi.
Cututtukan tsarin numfashi
Tsarin numfashi na iya kamuwa da cututtuka daban-daban da ke shafar hanyoyin iska ko huhu kai tsaye. Waɗannan cututtuka na iya zama masu sauƙi ko masu tsanani, wasu kuma na iya zama masu yaɗuwa daga mutum zuwa mutum. Illolinsu sun haɗa da wahalar numfashi, tari, zafi a ƙirji, da raguwar iskar oxygen da jiki ke samu.
Cutar asma
Asma cuta ce ta dindindin wadda ke sa hanyoyin iska su kumbura su kuma matse, hakan yana hana iska shiga da fita yadda ya kamata. Mutanen da ke fama da asma kan riƙa fuskantar matsaloli na wahalar numfashi, tari, da wani sauti na daban yayin numfashi.
Matsalolin asma na iya tashi ne sakamakon wasu abubuwa kamar ƙura, hayaƙi, sanyi, ko kamuwa da mura. Misali, yaro mai asma na iya fara jin wahalar numfashi idan ya yi wasa a wuri mai ƙura ko lokacin sanyi mai tsanani.
Tarin fuka
Tarin fuka cuta ce mai tsanani da ƙwayar cuta ke haifarwa, wadda galibi tana shafar huhu. Ana iya kamuwa da ita ta iska idan mutum ya yi hulda da mai ɗauke da cutar, musamman idan yana tari ko atishawa.
Alamomin cutar sun hada da tari mai ɗauke da jini a wasu lokuta, zazzaɓi, gajiya, da rama. Idan ba a gano cutar da wuri ba kuma ba a yi magani ba, tana iya lalata huhu har ta kai ga mutuwa. Misali, a wasu yankuna masu cunkoso, yaɗuwar tarin fuka na iya ƙaruwa saboda mutane na shaƙar iska guda a wurare marasa kyau.
Cutar pneumonia
Pneumonia cuta ce da ke haifar da kumburi a huhu sakamakon ƙwayoyin bakteriya, kwayoyin cuta, ko wasu ƙwayoyin halitta. Wannan kumburin na sa alveoli su cika da ruwa ko datti, wanda ke hana musayar oxygen da carbon dioxide yadda ya kamata.
Mutum mai pneumonia kan ji zazzaɓi, tari mai kaki, wahalar numfashi, da zafi a ƙirji. Cutar na iya zama mai haɗari musamman ga yara ƙanana da tsofaffi. Misali, yaron da ya kamu da pneumonia na iya yin numfashi cikin sauri kuma ƙirjinsa yana motsi fiye da kima saboda ƙoƙarin samun iskar oxygen.
Cutar mashaƙo
Mashaƙo cuta ce da ke shafar bututun da ke kai iska zuwa huhu, wanda ake kira bronchi. Idan waɗannan hanyoyi suka kumbura, iska ba ta wucewa yadda ya kamata, kuma mutum yana fama da tari mai zafi da wahalar numfashi.

Akwai mashaƙo ta gajeren lokaci wadda yawanci ke biyo bayan mura, da kuma ta dindindin wadda galibi ke faruwa ga masu shan taba ko waɗanda ke rayuwa a wurare masu gurɓatacciyar iska. Misali, mutumin da ya daɗe yana shan taba na tsawon lokaci na iya kamuwa da mashaƙo ta dindindin saboda hayaƙin taba yana lalata hanyoyin numfashi.
COVID-19 da sauran cututtukan numfashi
COVID-19 cuta ce da ƙwayar cutar coronavirus ke haifarwa, wadda take shafar tsarin numfashi sosai. Cutar na yaɗuwa ta iska daga mutum zuwa mutum, kuma tana iya haifar da tari, zazzaɓi, wahalar numfashi, da rashin jin ɗanɗano ko kamshi. A lokuta masu tsanani, tana iya jawo lalacewar huhu.
Baya ga COVID-19, akwai sauran cututtukan numfashi masu yaɗuwa kamar mura da influenza, waɗanda ke shafar hanci, maƙogwaro, da huhu. Misali, a lokacin ɓarkewar cututtukan mura, mutane da yawa kan kamu da tari da atishawa saboda ƙwayoyin cutar na yaɗuwa cikin sauƙi ta iska.
Hanyoyin kare lafiyar numfashi
Kare lafiyar numfashi yana da muhimmanci domin hana kamuwa da cututtuka da kuma tabbatar da cewa huhu suna aiki yadda ya kamata. Wannan yana bukatar kula da muhalli da kuma tsarin rayuwa na yau da kullum.
Guje wa hayaƙi da gurɓatacciyar iska
Hayaƙi kamar na taba, ƙone-ƙone, ko masana’antu na ɗauke da sinadarai masu cutarwa da ke lalata huhu. Guje wa shan taba da zama a wurare masu hayaki na taimakawa wajen kare tsarin numfashi. Misali, yara da ke rayuwa tare da masu shan taba na iya samun matsalolin numfashi saboda shaƙar hayaƙin da ke yawo a gida.
Motsa jiki
Motsa jiki na taimaka wa huhu su ƙara ƙarfi da inganta yadda jiki ke amfani da oxygen. Yana kuma taimakawa wajen buɗe hanyoyin iska da inganta aikin zuciya da jini. Misali, mutane da ke yawan tafiya ko gudu suna da karfin numfashi fiye da waɗanda ba sa motsa jiki.
Tsabtace muhalli
Tsabtace muhalli yana rage kura da datti da ke iya shiga hanyoyin numfashi. Haka kuma, samar da isasshen sarari da iska za ta wadata a gidaje da wuraren aiki yana taimakawa wajen rage yaɗuwar ƙwayoyin cuta. Misali, buɗe tagogi domin iska ta riƙa shiga na taimakawa wajen sabunta iska a ɗakuna.
Alluran rigakafi
Alluran rigakafi suna taimakawa wajen kare jiki daga wasu cututtukan numfashi masu haɗari, musamman ga yara da tsofaffi. Rigakafi na rage yiwuwar kamuwa da cuta ko tsananta ta. Misali, allurar rigakafin tarin fuka da ta mura suna taimakawa wajen kare huhu daga kamuwa da waɗannan cututtuka.
Numfashi a wasu halittu
Numfashi ba na ɗan Adam kaɗai ba ne, dukkan halittu masu rai suna da hanyoyin da suke amfani da su domin samun oxygen da fitar da carbon dioxide. Duk da haka, hanyoyin numfashi sun bambanta daga halitta zuwa halitta gwargwadon tsarin jikinsu da muhallin da suke rayuwa a ciki.
Bambanci tsakanin numfashin ɗan Adam da na dabbobi
Ɗan Adam da yawancin dabbobi masu shayarwa suna numfashi ne ta huhu, wato suna shaƙar iska daga sararin samaniya su kai ta cikin huhu inda ake musayar iskar oxygen da carbon dioxide. Amma ba dukkan dabbobi ba ne ke da wannan tsarin.
Wasu dabbobi suna da hanyoyi daban, misali ƙwari suna numfashi ta ƙananan ramuka a jikinsu da ake kira spiracles, waɗanda ke kai iska kai tsaye zuwa cikin jikinsu. Haka kuma, wasu dabbobin ruwa suna amfani da gills maimakon huhu.
Misali, kare da saniya suna numfashi kamar ɗan Adam ta huhu, amma kwaɗi na iya numfashi ta huhu da kuma ta fata, musamman lokacin da yake cikin ruwa. Wannan yana nuna cewa tsarin numfashi yana daidaituwa da yanayin rayuwar kowace halitta.
Numfashi a kifi da tsirrai
Kifi
Kifi suna rayuwa ne a cikin ruwa, don haka ba za su iya amfani da huhu kamar ɗan Adam ba. Suna da wani tsari na musamman da ake kira gills, wanda ke ba su damar ɗaukar oxygen daga ruwa. Lokacin da ruwa ya shiga bakin kifi ya wuce ta gills, oxygen da ke cikin ruwa yana shiga jinin kifi, yayin da carbon dioxide ke fita.
Tsirrai
Tsirrai kuwa ba su da huhu ko gills, amma su ma suna numfashi ta wata hanya. A jikin tsirrai akwai kananan ramuka a ganye da ake kira stomata. Ta waɗannan ramuka ne suke karɓar carbon dioxide daga iska su fitar da oxygen a lokacin aikin photosynthesis, sannan su ma suna amfani da oxygen domin samar da makamashi a cikin ƙwayoyinsu. Misali, idan aka toshe ganyen tsiro ko aka hana shi samun iska, zai iya lalacewa domin ba zai iya gudanar da muhimman ayyukan numfashi ba.
Ingantaccen numfashi yana taimaka wa lafiyar zuciya, ƙwaƙwalwa, da sauran gaɓoɓin jiki. Idan numfashi yana tafiya yadda ya kamata, jini yana samun isasshiyar iskar oxygen, wadda ke taimaka wa jiki ya kasance cikin koshin lafiya. Akasin haka, matsalolin numfashi na iya jawo gajiya, jiri, raguwar ƙarfin jiki, da matsaloli ga ƙwaƙwalwa.
Manazarta
Canadian Lung Association. (n.d.). Respiratory system | Canadian Lung Association.
Dezube, R. (2025, July 9). Overview of the respiratory system. MSD Manual Consumer Version.
Libretexts. (2022, May 7). 16.2: Structure and Function of the Respiratory System. Biology LibreTexts. ry_System
Professional, C. C. M. (2026, January 8). Respiratory system. Cleveland Clinic.
Sharuɗɗan Editoci
Duk maƙalun da ku ka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta tare da sa idon kwamitin ba da shawara na ƙwararru. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.
Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.
