Printer na’ura ce da ke karɓar bayanai ko kuma saƙwanni rubutattu ko fayal ko kuma hotuna daga na’ura mai ƙwaƙwalwa ta sarrafa su ta hanyar mayar da su a takarda ko kuma fim. Ta kan iya karɓar saƙon kai tsaye daga na’ura mai ƙwaƙwalwa ko kuma ta hanyar amfani da hanyar isar da sako wato (network). A wani bayanin kuma masana sukan ce; Printer na’ura ce da take fitar da bayanai daga cikin masarrafar na’ura zuwa zahiri. Ta hanyar fitar da rubutun da yake a kwanfuta, ko zane ko hoto zuwa bugagge a takarda ko a wani wajen da za a iya ganin shi a zahiri.
Printer ta farko da aka samar an samar da ita ne ta hanyar wani ƙwararren masani mai suna Charles Babbage wanda ya samar da ita hanyar injina mabanbanta a ƙarni na sha tara (19th Century). Wannan printer da aka samar ana amfani da ita ne, amma kuma da taimakon hannu yayin gudanar da aikin, aikinta bai zamo cikakken ba kuma kamallale sai a shekarar 2000.
Tarihi ya bayyana samuwar printer tun shekaru ɗari da hamsin baya. Sai dai kuma wani bayani ya tabbata kan cewar Charles Babbage ya tabbatar da cikar aikinta a shekarar 2000 da taimakon wani gidan kimiyyar tarihi dake a ƙasar London. A yanzu a zamanin da muke ciki, za mu iya cewa printar ta zagaye ko’ina na duniya ta fuskar cuɗanya da kuma amfani.
Ire-iren Printer
Akwai ire-iren printer da yawa kamar yadda Team, A. (2023), ya kawo su kamar haka,
• 3D Printer
Printer ce da take aiwatar da ayyuka uku lokaci ɗaya, ta hanyar fitar da tsarin takardu ɗaya bayan ɗaya bi sa yadda aka shirya su.
• AII In One Printer
Printer ce da ke haɗa ayyuka masu yawa, kuma ta gudanar da su lokaci ɗaya. Kamar: fitar da hoto da fitar da rubutu da kwafar wani abu.
• Dot Matrix Printer
Printer ce da take yin aiki kamar ba saura ba, aikinta bai wuce fitar da ‘yar ƙaramar da ba kamar invoices na rasiti.
• Plotter Printer
Printer ce da ake amfani da ita wurin ƙirƙirar zane mafi girma da kuma ƙayatarwa takarda.
• Multifunction Printer
Aikinta kamar aikin All in one printer ne. Takan ninka aikinta sama da aiki guda ɗaya.
Wasu ɓangarori na Printer
Printer na da ɓangarori da dama, kamar Pedamkar, P. (2023) ya bayyana, waɗanda suka ƙunshi tassarufin gudanar da ayyukan da ke tattare da ita, ta fuskar bayyanannu da kuma waɗanda suka kasance ɓoyayyu wato waɗanda idanunmu ba sa iya gani. Ɓangararin nata sun ƙunshi:
• Paper support: Ya ƙushi abin da ya shafi wani keɓantacen wuri da ake zura takarda a jikin printer. Shi ne mai alhakin danne takarda, tare da ba ta kariya domin kada ta faɗi.
• Sheet feeder: Ya ƙushi abin da ya shafi duk wani abu da yake ba wa takarda damar shiga cikin printer yayin da aka danne ta da papper support.
• Printer cover: Shi ne abin da ya shafi duk wani abu da ya ba Printer kariya, wanda ya lulluɓe injinan cikinta suka kasance ba a ganinsu.
• Output tray: Ya ƙushi abin da ya shafi wuri da takarda take tsayuwa idan ta fito daga cikin printer bayan kammaluwar aiki. Output tray kala-kala ne, wani dogo ne wani kuma gajere ne.
• Connected: Su ne wayoyin da ke isar da sako cikin printer din kai tsaye. Ana kiran su da (source cables)
• Edge guides: Ya ƙushi abin da yake ba da alhakin riƙe takarda tare da tabbatar da tsayuwar ta a wuri ɗaya, ta gefe da gefe ba tare da ta yi yawo a cikin printer ɗin ba.
• Control buttons: Ya ƙushi abin da ya shafi madanai da ake amfani da su na jikin printer.
• Print head: Ya ƙushi abin da ya shafi ruwan da yake tabbatar da rubutun jikin printer. Kai tsaye za mu iya kiransa da tawadar printer domin shi yake tantance kalar rubutun da za a yi.
Muhimmancin Printer
Printer tana da amfani daban-daban kuma ta hanyoyi daban-daban. Ga kaɗan daga cikin amfaninta kamar haka:
- Takan yi scanning na abu wato ta daukar hoton abu kuma a tantance kafin ta fitar da shi.
- Ɗaukar wani abu daga wani wuri zuwa wani wuri, ko kuma ƙara yawan wani abu daga wani mataki zuwa wani mataki, ko kuna ninka yawan abu. Kaɗan daga aikinta ne wannan, idan kana da takarda guda ɗaya cikin ƙanƙanin lokaci za ta iya ninka ta ta hanyar yin amfani da copy ta kaita adadin da ake buƙata. Misali za a iya fitar da takarda guda ɗari iri ɗaya kuma a lokaci ɗaya.
- Takan tantace rubutu da ya kasance a tattare wuri ɗaya kamar (decuments) ta hanyar amfani da (disk) ta tura shi wani wuri na musamman da ake buƙatar isar da shi.
- Printer kan bayar da copy na wasu dunƙulallun abubuwa, ta hanyar gajarta hanyar da za a yaɗa su cikin sauƙi.
- Printer kan taimaka ƙwarai wurin adana muhimman abubuwa, musamman abin da ya shafi kamfanoni ko kuma kasuwanci.
- Printer takan iya fitar da wasu abubuwa masu muhimmanci, kamar poster, flayers, domin gudanar da wasu muhimman abubuwa kuma masu armashi.
- Printer kan taimaka wurin haɓaka tafiyar ilmi ta fanni daban-daban ta fuskar sauƙaƙa ɗalibai hanyoyin fitar aikin jinga da aka ba su (assignments) ko kuma (project).
- Printer kan taimaka wurin fitar da wasu tsare-tsare wanda aka shirya ta hanyar fasahar ƙirƙira ko kuma wani aiki na musamman domin zama ƙayatace.
Matsalolin Printer
A duniya duk abin da ya kasance yana da a doran ƙasa to yana da amfani da rashinsa to haka ma printer. Ga masu daga cikin matsalolinta:
- Tafiya a hankali wato rashin yin aiki cikin sauri. A wasu lokutan akan samu wannan matsalar a tare da ita.
- Printer ta kan yi kuskure ta hanyar fitar da wasu takardun rabi da rabi ma’ana wani rubutun bai cika ba.
- Fitar da wata takardar babu komai a ciki, wanda ba za a fahimci hakan ba sai bayan abin da aka fitar ya fita.
- Fitar da wani rubutun cikin hatsa-hatsa ko kuma wani wurin ya yi baƙi-baƙi.
- Fitar da wani sashi a koɗe wani kuma a turrare ma’ana bambanta kalar dake aihinin jikin abin.
- Fitar da wani sashin takardar da haske sosai wanda zai ita kawo matsala a idon mai karatun takardar.
- Wasu lokutan takardar kan maƙale taƙi fita kwata-kwata daga ainihin jikinta.
- Na’urar printer na da tsada, kuma tana buƙatar ilimin sarrafawa.
- Hakazalika, na’urar tana iyakar amfanin ta, wato ta taƙaita ga wurin da ake da makamashin lantarki.
Manazarta
Pedamkar, P. (2023, April 14). What is Printer? EDUCBA.
Team, A. (2023, March 14). What are the Different Types of Printers? Adorama.