Skip to content

Rabilu Musa Ibro

Rabilu Musa, wanda aka fi sani da Ibro ko ‘Ɗan Ibro’ shahararren ɗan wasan barkwanci ne kuma jarumin fim ne da aka taɓa yi a ƙasar Hausa wanda ke fitowa a cikin fina-finan Kannywood. Bayan fitowa a matsayin jarumin fim, yana kuma shiryawa da kuma ba da umurni. Ƙwarewarsa, salonsa da kuma irin yanayin da yake yawan fitowa a cikin fina-finai na daga cikin abubuwan da suka kawo masa ɗaukaka a tsakanin Hausawa. Ɗaya daga cikin salon da Ibro ya shahara da su shi ne ƙwarewarsa wajen iya sarrafa harshen Hausa, da irin yadda yake magana da salon da ‘yan kallo ke iya alaƙantuwa da shi.

Marigayi, Rabilu Musa Ibro

Haihuwarsa

An haifi Rabilu Musa Ibro ne a ranar Juma’a 12 ga watan Disamba 1971 a Wudil, Kano. Ana kallonsa a matsayin jagoran ci gaban masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood, ya ciyar da masana’antar gaba sosai har zuwa lokacin rasuwar sa a shekarar 2014.

Tasowarsa da karatunsa

Ɗan Ibro ya yi karatunsa na firamare a Ɗanlasan Primary School da ke Wudil, ƙaramar hukumar Warawa da ke Kano. Sannan kuma ya yi Sakandare a Kwalejin horon malamai ta Wudil (Teachers College) duka a jahar Kano. Ya kuma yi karatun addinin Musulunci duk a cikin jahar Kano.

Daga nan kuma sai ya shiga aikin jami’in tsaro na gidan yari, wato Nigerian Prison Service a shekarar 1991, inda ya kai matakin insfekto, baya ga haka kuma ya yi ayyukan sa kai da dama. Bayan ya yi aikin jami’in tsaron gidan yari na shekaru takwas ne sai ya ajiye aikin ya koma harkar fim.

Karatun da ya yi tun yana yaro da kuma ayyukan da ya yi sun ba da gudummawa mai girma a cikin sana’arsa ta fim.

Aiki da gwagwarmayarsa

Kafin Rabilu Musa ya fara fitowa a cikin fina-finai sai da ya fara taɓa harkar waƙa tukunna, wadda ita ce ta zama sanadin fara fitowarsa a cikin fina-finan Kannywood. Fim na farko da ya fara fitowa a ciki shi ne ‘Yar Mai Ganye wanda ya fita a shekarar 1977, wanda ya zamo tubalin karɓuwa da shahararsa a harkar fim.

A tsawon lokacin da ya ɗauka yana fitowa a fina-finan Hausa, Ibro ya fito a cikin fina-finai sama da 300, wanda hakan ya ba shi damar bayyana baiwarsa ta iya kwaikwayo da fitowa a salo da yanayi iri daban daban. Duk kuwa fim ɗin da aka kalla daga ciki za a ga irin yadda tauraruwarsa ke haskawa a ciki.

Gudummawar da Ibro ya bayar a masana’antar fina-finan Nijeriya, musamman na Kannywood da ke fitar da fina-finai a harshen Hausa ya taimaka ƙwarai wajen yaɗawa da kuma adana al’adun Hausawa da ma yankin arewa baki ɗaya.

Ƙwarewarsa wajen iya bayyana abubuwan da ke jan hankalin masu kallo cike da barkwanci ya sa ya samu miliyoyin masoya a yankin arewa. Fina-finan Ibro ba nishaɗantarwa kawai suke yi ba, face har da haɗa kan jama’a tare da jan hankali wajen tabbatar da zaman lafiya tare da yin dariya da juna.

Daɗewar da ya yi a harkar fim ne ya ba shi damar buɗe kamfanin shirya fina-finai na kansa mai suna Ibro Drama Group, wanda a ƙarƙashinsa ya fitar da fina-finai da dama, na ƙarshensu shi ne ‘Andamali’. Baya ga shiryawa kuma, ya kasance mai ba da umurni.

Ibro ya yi fina-finai da sauran jaruman masana’antar Kannywood da dama, amma waɗanda ya fi fitowa tare da su su ne Ƙulu, Ɗan Wanzam, Ciroki, Tsigai, Daushe, Sa’adu Ado Gano (Ɓawo), Dumɓaru, Gatari, Suleiman Bosho, Rabi’u Ibrahim, Mustapha Naburaska, Musa Mai Sana’a, da kuma Ɗan Dolo.

Marigayi Rabilu Musa Ibro, a lokacin ɗaukar shirin wani fim

Ibro ya ƙware wajen iya juya kowane irin yanayi ko batu ya koma barkwanci, wannan dalili ne ma ya sa ake yi masa laƙabi da ‘Sarkin Barkwanci’, kuma shi ne dalilin da ya sa ya samu wani shahararren suna a masana’antar fina-finai wato ‘Ciyaman’.

Rabilu Musa ya shahara wajen hawa fitattun waƙoƙin da suka zamo kamar wata al’ada ce ta fina-finansa. A cikin irin waɗannan waƙoƙi, yakan bayyana ra’ayoyinsa da kuma barkwanci a haɗe, wanda ya sa nan da nan suke karɓuwa a wurin jama’a. Sai dai yawancin waƙoƙin ba shi ne ke rera su ba, Sadi Sidi Sharifai ne ke rerawa domin shi ya iya sauya muryoyi iri-iri, shi kuma Ibro sai ya hau. Daga cikin irin waɗannan waƙoƙi akwai irin su Bayanin Naira, Idi Wanzami, Direba Makaho da sauransu.

Ga wasu daga cikin fina-finan da Ibro ya fito a ciki:

  • Bodari
  • A Cuci Maza
  • A Kasa A tsare
  • Ibro Usama
  • Ibro Liman
  • Bita Zai Zai
  • Borin Ibro
  • Namaliya
  • Ibro Ƙala Ƙato
  • Dan Gatan Ibro
  • Dawa Dai
  • Gabar Ibro
  • Ibro Alkali
  • Ibro Aloko
  • Kuturu Na Jogana
  • Ibro Ɗan Almajiri
  • Ibro Ɗan Chacha
  • Ibro Ɗan Daudu
  • Ibro Ɗan Fulani
  • Ibro Ɗan Najeriya

Kyautuka da nasarori

Rabilu Musa Ibro ya samu nasarori da dama a harkar fina-finan Hausa, babba daga cikinsu kuwa ita ce ɗaukaka. Ibro ya samu ɗaukakar da a yankin arewa babu wanda bai san shi ba, ko da bai san shi a fuska ba, to ya san sunan shi. Sannan yana da masoyan da ba su da adadi, wanda hakan ya sa fina-finansa ke samun kasuwa a duk lokacin da suka fita.

A shekarar 2014, ya samu damar shiga gasar Nigeria Entertainment Awards Best Supporting Actor Special Recognition, wanda bai yi nasara ba. Sai kuma kyautar 2nd Kannywood/MTN Awards Best Comedian na 2015 (Jurors Choice Awards) wacce ya lashe bayan mutuwarsa.

Mutuwarsa

Rabilu Musa ya rasu ne a ranar Talata, 9 ga watan Disamba 2014 bayan ya sha jinyar cutar ƙoda, ya mutu ne yana da shekaru 43 a duniya, ya bar mata uku yara 19. Daga cikin yaransa akwai Faisal, Jawahid, Lawiza, Abdul-Mummuni, Asma’u, Sa’adiyya, Akwai wani yaro kuma da ya haifa ya sa sunan mai gidansa wato Baba Yaro.

Mutuwarsa ta haifar da giɓi babba a masana’antar fina-finan Hausa sakamakon irin karɓuwa da ya samu. Fim ɗinsa na ƙarshe da ya fita shi ne ‘Karfen Nasara’ wanda ya fita a 2015 bayan rasuwarsa. Kafin Rasuwarsa Ya bayyana Ciroki a matsayin dan wasan hausa abokin sana’ar sa da ya fi burgeshi.

A ɗaya daga cikin wata tattaunawar da yi da FIM Magazine a cikin watan Maris 2008, da aka tambaye shi sana’ar da zai iya yi bayan sana’ar fim, duk da ya kawo sunayen wasu sana’o’i da dama, sai kuma ya ƙara da cewa:

“In ka ji an ce an daina yi da Ibro, to sai dai in Ibro ya mutu.”

Daga cikin dubunnan fina-finansa Ibro ya bayyana cewa ya fi son waɗannan fina-finan; Ƙauran Mata, Kowa Ya Ɗebo Da Zafi, da kuma Mai Dawa.

Ibro ya bayyana ya fi son tuwon dawa a ɓangaren abincinsa, fannin sutura kuma sai ya ce, “Na fi son yadi wanda zan shekara da shi ina gurzawa, ba in sa shadda ba kwana biyu in ga tana koɗewa.”

Da aka tambayi Marigayi Ibro a lokacin ya na raye me ya fi baƙanta masa rai a kan harkar sana’arsa sai ya ce, “Ni abinda yake ɓata mani rai kawai a wannan sana’a bai wuce rashin haɗin kan ‘yan wasa ba.”

Kammalawa

Har bayan mutuwarsa, ayyukan Ibro na ci gaba da samun karɓuwa kuma mutane na ci gaba da riƙe su a matsayin abubuwan tunawa da mamacin. Gudummuwar da ya bayar a masana’antar fina-finan Kannywood kuwa, abu ne da ba za a taɓa mantawa da shi ba. Za a ci gaba da tunawa da Rabilu Musa Ibro a matsayin ɗaya daga cikin jaruman fim ɗin da Najeriya ba ta taɓa samun irinsu ba.

Manazarta

Lere, Mohammed (1 February 2015). “Late Ibro honoured at MTN Kannywood Awards 2015″. Nigeria: Premium Times.

BBC News Hausa. (2014, December 10).  Dan wasan Hausa, Rabilu Dan Ibro ya rasu.Bbchausa.com

Was this article helpful?
YesNo

You cannot copy content of this page

×