Barci wani ginshiƙi ne na rayuwa kamar abinci da ruwa, domin yana ba da dama ga ƙwaƙwalwa da jiki su huta, su sake sabuntuwa da kuma ƙarfafa garkuwar jiki. Rashin samun wannan hutu na iya jawo matsaloli da dama ga lafiyar ɗan’adam. Rashin barci wata babbar matsalar lafiya ce da ake fuskanta idan mutum ya kasa yin barci yadda ya kamata, ko kuma barcin bai wadatar da shi ba. A turance ana kiran wannan matsala da insomnia. Rashin barci na iya kasancewa na ɗan lokaci (na wucin gadi) ko kuma ya zama mai tsawo (na dindindin).
Ma’anar rashin barci
Rashin barci na nufin yanayin da mutum ke samun matsala wajen yin barci, ko yana tashi sau da yawa cikin dare, ko kuma yana farkawa da wuri fiye da ƙima ba tare da samun damar komawa barci ba. Wannan yanayi yana shafar lafiyar jiki da ta ƙwaƙwalwa, yana rage kuzari, da kuma iya shafar aikace-aikacen yau da kullum.
A fannin likitanci, rashin barci na nufin yanayin da mutum yake samun matsala wajen yin barcin a lokacin da ya dace, ko kuma duk da cewa an yi barci na tsawon lokaci, mutum baya jin cewa ya huta. Wannan matsala tana iya kasancewa ta ɗan lokaci kawai, ko kuma ta dore har ta zama cuta mai illa.
Ire-iren rashin barci
Masana sun rarraba rashin barci zuwa rukuni biyu:
- Rashin barcin na ɗan lokaci (Acute insomnia): Wannan shi ne rashin barcin da yake faruwa a wasu lokuta na musamman, misali idan mutum yana cikin tashin hankali, damuwa, ko canjin muhalli. Yakan ɗauki kwana ɗaya zuwa makonni biyu, kuma yawanci yakan wuce da kansa idan an shawo kan dalilin da ya jawo shi.
- Rashin barcin dindindin (Chronic insomnia): Idan matsalar barci ta wuce aƙalla makonni uku, ana kiran ta da (chronic insomnia.) Wannan na da alaƙa da wasu matsalolin lafiya kamar cututtukan zuciya, ciwon suga, hawan jini, ko matsalolin ƙwaƙwalwa. Wannan nau’in ne mafi hatsari, domin yana iya jawo matsaloli masu tsanani a jiki da tunani.
Abubuwan da ke haifar da rashin barci
- Damuwa (stress da anxiety)
- Ciwon hauka
- Shan magunguna da ke hana barci
- Shan abubuwan motsa jiki na sinadarai (irin su caffeine da nicotine)
- Cututtuka kamar ciwon asma, ciwon suga, ciwon hawan jini da sauransu.
- Sauyin muhalli ko yanayin aiki, musamman masu aikin dare.
Alamomin rashin barci
Daga cikin alamomin rashin barci akwai:
- Wahalar yin barci da dare
- Tashi a cikin dare sau da yawa
- Tashi da wuri fiye da ƙima
- Gajiya da raunin jiki da safe
- Wahalar mayar da hankali da yin aiki
- Yin fishi
Illolin rashin barci
Illolin da rashin barci ke haddasawa suna da yawa, amma ga manya daga cikinsu:
- Rage ƙarfin tunani da ƙarfin aiki
- Barazanar samun haɗurra musamman a wurin aiki ko tuƙi
- Ciwon zuciya da hawan jini
- Rage ƙarfin garkuwar jiki
- Jawo cututtuka na ƙwaƙwalwa kamar damuwa da tsananin bacin rai.
Magani da hanyoyin guje wa rashin barci
Maganin rashin barci ya dogara da gano dalilin da ya jawo shi. Ana iya bi ta hanyoyi kamar haka:
- Bin tsarin barci mai kyau, kamar yin barci a kan lokaci
- Guje wa shan shayi, coffee da taba sigari kafin lokacin barci
- Rage amfani da waya ko talabijin kafin barci
- Motsa jiki a rana, amma fa kafin lokacin barci
- Tuntuɓar likita idan rashin barcin ya zama na dogon lokaci, domin samun cikakken bincike da magani
- Ƙirƙirar yanayi mai natsuwa a ɗakin barcin (haske kaɗan, iska mai kyau da tsafta).
Ta bangaren magani kuma, a wasu lokutan, likita na iya ba da magungunan kwantar da hankali ko maganin barci, amma ba a so a yi amfani da su na dogon lokaci saboda illa.
Sannan akwai magungunan inganta yanayin zuciya (Cognitive Behavioral Therapy for Insomnia CBT-I), wannan kuma hanya ce ta magani inda ake koyar da mutum yadda zai shawo kan damuwa, tsoro ko halayen da ke hana shi barci. Sannan ana ganin wannan hanyar ta fi tasiri fiye da magunguna a lokuta da dama.
A addinace kuma yin addu’o’i da azkar kafin kwanciya, na taimakawa mutum ya samu isasshen barci. Shan ruwan zafi ko shayi mai ɗumama jiki. Ana kuma amfani da zuma da madara kafin kwanciyar barci, wanda masana suka tabbatar yana taimakawa wajen samun natsuwa.
Matsayin barci a musulunci
A Musulunci, barci yana da muhimmanci domin, ayoyin Alkur’ani mai girma sun yi magana a kansa, kuma Hadisan Manzon Allah sun koya mana yadda ya kamata mu yi shi saboda muhimmancinsa ga rayuwa baki ɗaya. Sannan a addinace ma barci hutu ne mai cike da ni’ima da yake samar da ƙarfi a wajen yin ibada, tare da ƙarfafa zuciya don kasancewa cikin ƙoshin lafiya.
Al-Qur’ani
- Suratul Rum (30:23): Barci da neman arziki daga falalar Allah na daga cikin ayoyinsa.
- Suratul Furqan (25:47): Dare an sanya shi tufafi, barci hutawa, da yini aiki.
- Suratun Naba’i (78:9): Allah ya sanya bacci a matsayin hutunmu.
Hadisai
- Annabi (SAW) yana yin addu’a kafin barci: “Bismika Allahumma amuutu wa ahyaa.”
- Idan ya farka, yana cewa: “Alhamdulillahil-ladhi ahyaanaa ba’da maa amaatanaa…”
Wannan yana nuna cewa barci ba kawai hutawa ba ne, ibada ce idan aka yi shi da niyya da addu’o’i. Sannan waɗannan ayoyi suna tabbatar mana da rashinsa babbar illah ce, domin duk abin da aka ce hutu ne, ni’ima ce, lafiya ce, toh da zaran an rasa shi an shiga damuwa, don haka waɗannan ayoyi duk da akan barcin suka yi magana, toh ta wani ɓangaren suna bayyanar da illar rashin barcin.
Don haka, a addinace da fannin likitanci, rashin samun barci mai kyau (wanda ake kira insomnia) yana da illa ga lafiyar mutum ta ɓangaren ƙwaƙwalwa, jiki da kuma rayuwa ta yau da kullum.
Manazarta
Office on Women’s Health. (n.d.). Insomnia. Office on Women’s Health.
Lamoreux, K. (2025, April 18). Everything you need to know about insomnia. Healthline.
Suni, E., & Suni, E. (2025, July 4). Insomnia: symptoms, causes, and treatments. Sleep Foundation.
Website, N. (2025, May 22). Insomnia. nhs.uk.
*** Tarihin Wallafa Maƙalar ***
An wallafa maƙalar 27 March, 2019
An kuma sabunta ta 26 August, 2025
*** Sharuɗɗan Editoci ***
Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.
Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.