Skip to content

Sallar idi

Sallar idi sunna ce mai karfi a kan kowanne namiji baligi da mai hankali, ba matafiyi ba, kuma abar so ce bisa yara maza da bawa da matafiyi da tsohuwar da ba a sha’awarta. Yawan sallar idi raka biyu ce. Babu bambanci tsakanin sallolin idi guda biyu, wato yadda aka yi sallar idin ƙaramar sallah haka ake yin ta babbar sallah.

19379947 440067399707306 4876124277214019584 n

Yadda ake yin sallar idi

  • Da farko mutum zai yi niyyar koyi da liman Ya ce “Na yi niyyar koyi da liman a cikin sallar idin kaza amma a ɓoye a zuciyarsa ba a bayyane ba don faɗa a bayyane ba a samu a shari’a ba.
  • Liman zai ce Allahu Akbar sau bakwai 7 a cikin raka’a ta farko, tun kafin ya fara karatun Fatiha da sura. Kabbarar haramar sallar tana cikin guda bakwai din.
  • Shi kuma mamu (mai bin liman) zai fadi “Alllahu Akbar” bayan fadar liman amma sau ɗaya kawai ake daga hannu sama wato a wajen kabbarar farko.
  • Da zarar an ƙare faɗar kabbarorin nan sai liman ya karanci fatiha da sura a bayyane amma an fi son surar Sabbi a cikin raka’a ta farko.
  • Sai ya yi ruku’u da sujjadai sannan ya mike tsaye don yin raka’a ta biyu. Zai ce Allahu Akbar sau shida kafin ya fara karatun Fatiha da sura.
  • Kabbarar mikewa tsaye tana cikinsu, zai karanta fatiha da sura a bayyane amma an fi son a karanta Suratul Shamsu a cikin raka’a ta biyu.
  • Sannan ya yi ruku’i da sujjadai, ya zauna ya yi tahiya ya yi sallama.

Bayan an ƙare sallah sai liman ya fuskanci jama’a ya yi huɗuba biyu. Zai zauna a farkonsu da tsakiyarsu, zai fara kowace huɗuba da kabbarori kuma ya yawaita faɗarsu a huɗubarsa, wato misali zai dinga cewa “Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allahu Akbar!” Alokacin nan dole ne wajibi ne mutane su yi shiru su saurari abin da yake faɗa a cikin hudubarsa.

Yadda ake gyaran sallar idi

Idan mutum ya samu liman yana tsakiyar karatun a cikin raka’a ta farko ko ta biyu sai ya yi niyya ya bi shi ya faɗi kabbarorin nan bakwai ko shi kaɗai, idan kuwa ya riga ya samu liman ya yi wasu kabbarori sai ya bi shi ga sauran. Bayan liman ya cika nasa, shi kuma mai bin shi sai ya kawo ragowar wanda bai samu yi da liman ba. Idan mutum ya tarar da liman yana ruku’u sai ya yi niyya ya sunkuya ga ruku’u don ya same shi. Shike nan kabbarorin wannan raka’a sun faɗi gare shi, babu komai a kansa, sallah ta yi kyau.

Idan mutum ya samu raka’a ta biyu tare da liman, idan zai rama ta farko zai yi mata kabbarorin nan nata bakwai 7. Idan Imam ya ƙara wasu kabbara a bisa adadin da aka iyakancen bisa mantuwa, mai koyi da shi ba zai fadi karin nan ba, idan liman ya rage kabbara ɗaya ko abin da ya fi ɗaya bai tuna ba sai bayan da ya yi ruku’i to shi ma zai yi sujjadar Kabli, idan kuwa kafin ruku’i ne sai ya faɗi kabbarar sai ya sake karatun Fatiha da sura daga farko to zai yi sujjada ba’adi. Idan mutum bai samu zuwa masallacin idi ba domin wani uzuri ko kuma da gangan to ana so ya yi kabbarorin nan shi kadai.

Sunnonin idi

Sunna ne mutum ya rayar da daren sallah da yawaita ibada ga Ubangiji Allah. Kamar sallar nafila da karatun Alkur’ani da Tasbihi. Kuma a ranar sallah abin so ne ga kowanne musulmi babba da yaro mace da namiji mai zuwa masallacin idi da wanda ba ya zuwa ya yi wanka, an fi so mutum ya yi wanka tun da asuba wato bayan fitowar alfijir, kuma ana iya yinsa ko da bayan fitowar rana.

Haka kuma abin so ne, ya sanya tufafinsa mafi kyau a ranar sallah. An fi son sababbin tufafi idan da hali, kuma abin so ne mutum ya tafi masallacin idi a ƙasa da gaɓoɓinsa, amma a wurin dawowa gida bayan ka gama sallah zai iya hawa duk abin da ya ga dama. Kuma abin so ne mutum ya sake sabuwar hanya a lokacin dawowarsa daga masallacin idi.

Abin so ne ga wanda zai tafi masallacin idi ya yi ta yin kabbara tun daga fitowarsa daga gida har isar sa masallaci kuma ya ci gaba da yin kabbarorin nan har sai lokacin da liman ya tashi yin sallah. Ga yadda kabbarorin suke:

“Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allahu Akbar, La ila ha illallah, Allahu Akbar, Allahu Akbar, Wa lillahil hamdu”.

Idan mutum ba zai iya fadar dukkan wadannan ba sai ya yi ta maimaita Allahu Akbar, Allahu Akbar ya isa. Kuma ba laifi yara su yi wasanni na farinciki a ranar sallah.

Manufofin idi a Musulunci

Idi ya kunshi wasu manufofi na Musulunci manya-manya, da amfani mai yawa. Idi ya kunshi aƙidar Musulunci tsarkakakkiyya tataciyya, wadda take ita ce mafi girman ni’ima da Allah ya yi wa ɗan’adam. Haka kuwa na tabbata ta hanyar girmama Allah da kabbara gare shi, da kuma yabo da kirari a gare shi. Tare da shaidawa cewa, shi ne Ubangijin gaskiya wanda Musulmi yake neman kusanci zuwa gare shi, ta hanyar roƙo da fata, da neman taimako da dukkan nau’o’in ibada, ba tare da tara bautarsa da wani abu ba, kamar yadda Allah Ta’ala ya ce:

”Kuma masallatai na Allah ne, don haka kada ku kira wani tare da Allah.”

Shaidawa da gaskiya cewa Annabi Muhammadu bawansa ne kuma Mazonsa ne, ta hanyar bin umarninsa, da barin haninsa, da gaskanta labarinsa, da bautawa Allah da abin da ya shar’anta. Idi ya kunshi bayanin shari’ar musulunci, ta hanyar bayyana alamomi na idi, da gabatar da sallarsa, da bayyana hukunce-hukuncen musulunci a huɗubarsa.

Idi ya kunshi tsarkake ɗabi’u, da kyautata halaye, ta hanyar kwaɗaitarwa a kan haƙuri da juriya, da sada zumunci a cikin wannan ranar, da afuwa, da tsarkake zukata daga ƙullata da hassada da gaba. Domin Idi yini ne na farinciki da ‘yan’uwantaka ta Musulunci.

Idi ya kunshi alaƙa ta ‘yan uwantaka tsakanin Musulmi, da tallafawa ta zamantakewa ta hanyar ba da zakkar Fid-da-kai kafin sallah, saboda fadin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama:

“Ku wadatar da su ga barin yawon ruqo a wannan yini”. Yana nufin faƙirai. Daru Ƙuɗni ne ya rawaito shi daga Ibn Umar.

Idi ya kunshi sauƙin musulunci da rangwamensa, domin a wannan ranar Allah ya wajabta a sauke azumi, ya halarta daɗaɗan abubuwa, kamar yadda yake gabanin azumi wajen halatta su. Sai dai Musulunci ya ƙulla wannan da babban tushe, wato imani da miƙa wuya ga Ubangijin talilkai, ya buɗe farincikin idi da murnarsa ta hanyar buɗe shi da salla raka’a biyu ga Allah Ta’ala. Don kada Musulmi ya shantake wajen holewa ya manta da Ubangijinsa, wanda ya raine shi da ni’imomisa, ya aje masa bala’i, Allah Ta’ala ya ce:

”Ya ku waɗanda suka yi imani, kada ku haramta daɗaɗan abubuwa da Allah ya halatta muku, kuma kada ku wuce iyaka, haƙiƙa Allah ba ya son masu wuce iyaka. Kuma ku ci daga abin da Allah Ya azurta ku da shi, halak mai daɗi, kuma ku ji tsoron Allah wanda kuka yi imani da shi.” [Suratul Ma’ida]

Hukunce-hukunce kwanakin idi

Allah Ya shar’anta mana kabarbari bayan kammala azumin watan Ramadan, sai ya ce,

‘Kuma domin ku cika adadi, kuma ku girmama Allah saboda shiriyar ku da ya yi, ko kwa godewa Allah.” [Suratul Baƙarah aya ta 185]

Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi umarni da sallar idi ga maza da mata har da kullallun mata waɗanda ba al’adarsu ba ce su fita, da masu haila, domin su halarci addu’ar alheri, da addu’ar Musulmi, su ƙauracewa wajan sallah, kada su zauna cikin filin idin, domin filin idi Masallaci ne, yana da duk hukunce-hukuncen masallaci.

Bukhari da Muslim sun ruwaito hadisi daga Ummu Aɗiyya (R.A) ta ce, “Manzon Allah Sallallahu Alaihi ya umarce mu da fitar da masu haila da kullallun mata, su masu haila su nisanci salla. A wani lafazin: Su nisanci wajen sallah, su halarci alheri da addu’ar Musulmi. Sai na ce, “Ya Ma’aikin Allah idan ɗayarmu ba ta da riga fa.” Sai ya ce, “’’Yar uwarta ta tufatar da ita da rigarta.”

Da yawa alheri da kyaututtuka kan sauka a filin idi daga Ubangiji mai girma, addu’o’i tsarkaka da ake karɓar su suna gudana a wannan guri. Mazaje su fita suna masu tsabta, suna masu sanya turare, suna masu sanya mafi kyawun tufafinsu. Sai dai bai halatta su sa alharini ba, da kowane abu na zinare, domin su haramun ne ga maza. Mata su fita cikin kamun kai, ba tare da sun sa turare ko bayyana ado ba.

Sunna ce mutum ya ci dabino kafin ya fita sallar idi, ya ci wuturi, uku ko biyar ko sama da haka in ya so, ya dai tsaya a kan mara. Anas ɗan Malik (R.A) ya ce, “Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya kasance ba ya fita da safe ranar idi har sai ya ci dabinai, kuma yana cin su mara”

Wasu muhimman bayanai game da sallar idi

Liman da mamu za su tafi filin idi bayan rana ta fito domin suna isa filin idi hantsi ya yi sai a yi salla.

  • Ana yin sallar idi a filin idi ba a masallaci ba sai dai idan akwai lalura, to za a iya yi a masallaci, haka nan waɗanda suke a garin Makka za su yi ta ne a Harami.
  • Za a tafi filin idi ana kabarbari a bayyane har a je filin idi, idan an je ba a yin nafila za a zauna a ci kaba da kabarbari har liman ya ƙaraso, sai a tsaya da kabarbari. Idan liman yana kabarbari , nan ma mamu za su yi kabarbari idan liman ya yi.
  • Ana so a rinƙa kabarbari a bayan kowacce salla ta farilla sau uku bayan salla da kwana uku, kuma ana so a yawaita zikiri a cikinsu.
  • Mustahabbi ne ga mata da yara idan ba za su je sallar idi ba, to su yi wanka da ado da sanya sababbun kaya idan da hali.
  • Mata su guji caba ado da sanya turare idan za su idi saboda gudun fitina.
  • Makruhi ne mutum ya ƙi yin ado da kwalliyya da gayu a ranar idi wai don gudun duniya, idan kuma ya ƙi yi da sunan addini, to ya zama ɗan bidi’a.
  • Allah ya karɓa mana ibadunmu Ya yafe mana amin.

Manazarta

Alkur’ani Mai Tsarki: Surori kamar irin su Baƙarah, Ma’ida, Hajji,Jinni da sauran su.

Hadisan Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama: Musanman Kutubus sitta.

*****

Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.

Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.

Maƙalar ta amfanar?
EAa

You cannot copy content of this page