Skip to content

Sankarau

Cutar sankarau cuta ce mai tsanani da ke faruwa a lokacin da ƙwayoyin kariya (meninges) da ke kewaye da kwakwalwa da kashin baya suka yi kumburi. Sanakarau wata cuta ce da ke kama mayafin da ke zagaye da kwakwalwa da lakka. Alamomin cutar sun haɗa da; ciwon kai mai tsanani da zazzaɓi da taurin wuya da yin amai. Cutar sankarau na iya zama barazana ga rayuwa kuma tana buƙatar kulawar gaggawa. Cutar ta sankarau dai ta fi kama kananan yara amma lokacin da ake annoba, tana kama har da manya.

Cutar sankarau na riƙe wuya.

Akwai nau’o’in cutar sanakarau daban-daban, sai dai hukumar dakile cututtuka masu yaduwa ta Nijeriya ta bayyana cewa kwayoyin cutar da suka fi shahara wurin jawo sankarau sun hada da Neisseria da Haemophilus influenzae da kuma Streptococcus.

Haka kuma a cikin ukun nan sankarau din da aka fi kamuwa da ita, ita ce wadda kwayar cutar Neisseria ke jawowa.

Ire-iren sankara

1. Sankarau na kwayar cutar bacteriya

Wannan nau’in yana iya yaɗuwa da sauri kuma wata kwayar cutar bakteriya ce ta musamman ke janyo cutar. Irin wannan na da hatsari sosai ga lafiyar al’umma saboda yana iya kasancewa sanadin mace-mace da dama. Yana iya kasancewa annoba duk da cewa wannan ya danganci nau’in kwayar cutar bacteriya da ta yi sanadin zuwan cutar amma kuma ana iya kare kai daga kamuwa da ita kuma ana iya samun waraka.

2. Virus da bakteriya

Wannan nau’in wanda aka fi sani da Viral bacteria ita ce wadda aka fi yawan kamuwa da ita. Wannan nau’in yakan tafi ba tare da an sha magunguna ba. Sai dai dole a kula da wadansu daga cikin abubuwan da suke janyo cutar.

3. Sankarau na Fungi

Ba kasafai ake samun wannan nau’in na cutar ba. Wannan kwayar cutar ta Fungi takan shiga jinin mutun ne ta yadu har ta kai ƙwaƙwalwa. Mutanen da ba su da garkuwar jiki mai inganci ne ke iya samun wannan nau’in.

4. Sankarau na Parasite

Parasites su ne irin kwayoyin cutar da ba su iya rayuwa da kansu dole sai sun sami wani abu mai rai sun manna kansu a jikinsa domin ci da shan su. Akwai irin waɗannan kwayoyin cutar da yawa waɗanda ke kasancewa sanadin sankarau. Akwai wadanda ake samu daga bayangida, dauda/bola, da kuma wadansu dabbobin da ake ci irin su dodon kodi, danyen kifi, kaji da kuma kayan gona. Sai dai ba kamar sauran nau’o’in cutar ba, da wuya mai ɗauke da cutar iya ba wa wani kai tsaye illa dai ƙwayoyin cutar za su ɓoye cikin abincin da ɗan’adam zai ɗauka ya ci musamman idan ba a tsabtace su ba.

5. Sankarau mai dadewa

Ƙwayar cutar fungi, cututtukan da kan shafi gabobin jiki da kasusuwa da kuma citar daji kan janyo irin wannan sankarau. Magungunan da ake sha don wannan cutar kan mayar da hankali wajen yakar cutar da ta janyo su ne.

Sankarau nau’in fungal.

Yaɗuwar cutar sankarau

Bisa bayanan Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), kwayar cutar bakteriyar da ke sanadin sankarau kan yaɗu ne daga mutun ɗaya zuwa wani ne idan har wanda ke ɗauke da ita ya tofar da miyau ko ya fyace majina ko kuma dai wani abun da ya fito daga makogwaro ko tare da naumfashi. Don haka daɗewa kusa da mai ɗauke da cutar da ma yin ma’amala da su ta hanyar sumbata, atishawa, ko tari a kan wani, ko kuma zama a kusa da wanda ke ɗauke da cutar na taimakwa wajen yaduwar cutar.

Tsawon lokacin da cutar ke dauka ta hayayyafa a jikin mutun shi ne kwanaki hudu amma ya danganta domin wani lokacin yakan dauki tsakanin kwanaki biyu zuwa 10. Kwayar cutar na iya buya a cikin makogwaro ta yadda za ta karya garkuwar jikin mutun ta shiga cikin jini daga nan har ta taɓa ƙwaƙwalwa.

Ganin cewa an fi samun sankarau a lokacin zafi, cunkusuwa a daki daya da babu isasshiyar iska ma na taimakawa wurin kara yaduwar cutar.

Kariya daga kamuwa da cutar sankarau
Fadakar da al’umma dangane da yaduwar sankarau na da mahimmanci ga yakar cutar saboda ana iya shakarta a iska.

A matakin mutun da al’umma, kula da kai na da mahimmanci sosai. Wannan ya hada da samun hutu sosai, kada a sha taba sigari, a guji cudanya da wadanda ke dauke da cutar, wanke hannuwa a kai-a kai duk suna da mahimmanci wajen dakile yaduwar cutar. Allurar rigakafi tana iya kare mutane daga kamuwa daga cutar.

Alamomin cutar sankarau

Hukumar NCDC ta bayyana cewa daga cikin alamomin cutar akwai ciwon kai da zazzabi da sankarewar wuya.

Haka kuma ta ce wanda ya kamu da cutar zai rinka gudun hasken fitila ko hasken rana haka kuma cutar tana kai ga har mutum ya suma.

Hukumar ta NCDC ta ce musamman ga yara kanana wadanda suka kamu da sankarau yana da wuya a ga wadannan alamomin, sai dai akasari yaran suna rashin walwala da kuma rashin cin abinci.

Haka kuma NCDC ta kara da cewa cutar dai tana iya sa mutum ya rinƙa amai da ɗaukewar numfashi da kuma jinin mutum ya sauka.

Matakan kariya

Allurar riga-kafin cutar sankarau.

Hukumar da ke yaki da cututtuka masu yaduwa ta duniya CDC ta bayyana cewa mataki mafi muhimmanci da mutum ya kamata ya soma dauka domin kiyaye kai daga kamuwa da sanakarau shi ne yin rigakafi.

Sauran matakan kariya daga cutar kamar yadda NCDC ta Nijeriya ta bayyana akwai kauce wa cunkoson jama’a sa’annan kuma a rinka tabbatarwa akwai isashen iska a cikin gida.

Hakan na nufin bude tagogi na da amfani domin samun isasshiyar iska musamman da dare idan za a kwanta barci.

Ga wasu daga cikin shawarwari da hukumar CDC ta bayar domin zama cikin koshin lafiya da kuma kare kai daga cututtuka irin sanakarau:

  • A rinka samun isashen hutu.
  • A daina matse wa marasa lafiya
  • Wanke hannu lokaci bayan lokaci da sabulu
  • A kuma rinka rufe baki da hanci da kyalle ko tolifefa idan za a yi tari ko kuma atishawa ( a rinka amfani da gwiwar hannu ko kuma gefen hannu idan babu kyalle).

Maganin cutar sankarau

Maganin sankarau ya danganci irin nau’in da ake dauke da shi. Wanda ke dauke da nau’in bakteriya na bukatar magungunan antibiotics – magungunan da ke hana habaka da kuma kashe kwayoyin cuta. Wadanda kwyar cutar virus ta janyo na iya tafiya cikin mako guda. Wadanda kuma kwayar cutar fungi ta janyo (Wadansu kan kira fungi naman gwari) ana iya amfani da magungunan da ke yaƙi da kwayar cutar wajen kashe su, wadanda ake kira antifungal.

Manazarta

Ude, I. (2023, May 2). Cutar Sankarau: Abubuwan da ya kamata ku sani dangane da alamu, kariya, magunguna da yadda ake kamuwa da ita. Dubawa.

Undefined, U. (2023b, April 23). Cutar Sankarau: Alamomi da hanyoyin magance ta. Cutar Sankarau: Alamomi Da Hanyoyin Magance Ta – TRT Afrika.

Was this article helpful?
YesNo

You cannot copy content of this page

×