Saratu Gidado (Daso)
An haifi fitacciyar ‘yar wasan kwaikwayon Kannywood, Saratu Gidado da ake yi wa laƙabi da Daso, a ranar 17 ga watan Janairu 1968, a birnin Kano.
Saratu Gidado ta yi makarantunta na firamare da sankandare a cikin birnin Kano, daga nan kuma ta wuce kwalejin fasaha ta Kaduna wato Kaduna Polytechnic, inda ta yi karatun babbar Diploma.
Shigarta harkar fim
Jarumar Saratu Gidado, ta shiga masana’antar fina-finan Hausa wato Kannywood ne a shekarar 2000. Fim na farko da ta fara fitowa wani fim ne mai suna Linzami da Wuta.
Daso ta yi fice a masana’antar fina-finan Hausa sama da shekaru 18. Ta fito a cikin fitattun wasanni da dama da kuma muhimmiyar rawar da ta taka a masana’antar. Kafin ta shiga harkar wasan kwaikwayo, Saratu ta yi aiki a matsayin malamar makaranta mai ƙwazo.
Duk da nasarar da ta samu a harkar fim, ta kasance mace mai son soyayya kuma uwa. Jajircewarta da sadaukarwarta ga sana’arta ya zame mata kwarin gwuiwa ga dimbin jarumai da mata masu kishin masana’antar Kannywood.
A wata hira da ta yi da gidan rediyon Bbc Hausa, jarumar ta bayyana dalilin da yake sawa ba ta rawar fitowa a matsayin muguwa.
“An fi ba ni damar taka rawar mai mugunta. Kuma mu mun san duk wani loko na mugunta amma fa a fim. Zan iya taka kowace irin rawa amma dai na fi jin daɗin wannan ɗin. Amma kowacce aka ba ni zan yi”. Cewar Daso.
Daga baya Saratu ta sauya akalar rawar da take takawa q finafinai inda ta yanke shawarar daina taka rawa ta faɗace-faɗace da guje-guje ko kuma fitowa a masifaffiya.
Ga abin da ta faɗa a wani ɓangare na hirar tata, “yanzu gaskiya na koma taka rawar girma. Yanzu ba zan yi guje-gujen nan ba ko kuma na yi ta masifa saboda a kullum mutum girma yake yi.”
Adadin finafinanta
Abu ne mai matuƙar wahala a iya haƙiƙance yawan fina-finan da ta yi kasancewar suna da yawa kuma ba abu ba ne da aka yi a lokaci guda ba.
Amma ga wasu daga cikin fina-finan jarumar da suka fi yin fice wanda suka haɗa da:
- Fil’azal
- Labarina
- Sansani
- Nagari
- Gidauniya
- Mashi
- Gidan Iko
- Cudanya
- ‘Yar Maiganye
- Sarauniya
- Daham
- Alaƙa
- Mazan fama
Haka nan kuma Saratu Gidado tana taka muhimmiyar rawa a wani fim mai dogon zango mai suna Umarni, Kodayake ba a kai ga fara sakin shi.
A shekarar 2016, an naɗa jaruma Saratu Gidado a matsayin jakadiyar sarkin Kano Muhammad Sanusi II.
Haka nan jaruma Saratu Gidado tana aiki da Taj Bank a matsayin ambassador.
Rasuwarta
Hajiya Saratu Gidado ta rasu ne a ranar Talata 9, ga watan Afrilu, 2024 wanda ya yi daidai da 30 ga watan Ramadan, 1445 A.H. Ta rasu tana da shekaru 56 a duniya.
‘Yan uwanta sun ce Daso ta rasu ne a cikin barcin da take yi da sanyin safiyar Talata bayan an ci abincin Sahur kafin gari ya ƙarasa wayewa. Sanarwar mutuwar ta sa magoya baya da abokan aikinta nuna jimamin rashinta.
Manazarta
Matazu, Hafsah Abubakar (23 March 2019). “5 Kannywood veterans still on screen”. Daily Trust.
“I’m the only married woman that is still into acting – Daso”. Blueprint. Blueprint.
“TOP 10 NORTHERN ACTRESSES” Modern Ghana. Modern Ghana.
Blueprint (2021-08-27). “Why I like playing role of wicked women – Daso”. Blueprint Newspapers.
Bahara, Hafsat Bello (2024-04-09). “JUST-IN: Veteran Kannywood Actress Saratu Daso Is Dead”.