Skip to content

Sheikh Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo

Farfesa Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo, shahararren malamin addinin Musulunci ne ɗan Najeriya, wanda ya ƙware a fannin ilimin Hadisi da Tafsirin Alƙur’ani mai girma. Shugaban ƙasa Muhammad Buhari ya karrama shi da babbar lambar karramawa ta ƙasa wato (OON) a watan Oktobar shekarar 2022 bisa kokarinsa na ilmantarwa da wanzar da zaman lafiya a tsakanin al’umma.

Farfesa Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo, shahararren malamin addinin Muslunci.

Haihuwarsa da kuma tashi

An haife Farfesa Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo a ranar 1 ga watan Yuli na shekarar 1970, a birnin Makka na ƙasar Saudiyya. Ya tashi a unguwar Rijiyar Lemo da ke birnin Kano, Nijeriya.

Karatu da neman iliminsa

Muhammad Sani Umar ya halarci makarantar firamare ta Khairul Bariyya Islamic Primary School da ke Kano a tsakanin (1978-1983). Ya ɗora da karatu a ƙaramar sakandire ta (H.I.S) a sakandiren Shahuci Kano (1987), kuma ya wuce Makarantar Ilimi mai zurfi ta addinin Musulunci, a Gwale, in da ya kammala babbar sakandiren (Senior Islamic Studies) da mafi kyawun sakamako wato (Distinction) a shekarar 1989.

Tafiyarsa zuwa jami’ar Madina

Shehin malamin ya samu gurbin karatu a tsangayar ilmin hadisai ta jami’ar Musulunci da ke birnin Madina in da ya ya yi digirinsa na farko a fannin ilimin hadisai da nazarin Addinin Musulunci wato (B.A. in Hadith Science and Islamic Studies,1994) hallau da kuma digiri na biyu a fannin ilimin hadisai da nazarin Addinin Musulunci, a shekarar 2000. A dukkan waɗannan digiri guda ya fita da kyakkyawan sakamako mafi girma (First Class da Distinction). Kasancewar shi mai sha’awar ilmi mai zurfi da bincike, sai ya sake ɗorawa da karatun digirin digirgir wato digiri na uku (PhD) a dai wannan jami’ar ta Musulunci da ke birnin Madina inda Allah ya ba shi damar kammalawa a shekarar 2005, da daraja mafi girma (Distinction)

Malaman da suka karantar da shi

Shehin malamin ya yi karatun litattafai masu yawa a wajen malamai da dama a nan gida Nijeriya da kuma ƙasar Saudiyya, waɗanda suka haɗa da:

Malamansa na gida Najeriya

  • Malam Hamza Adakawa (Akhdari, Arbauna hadisan, Ishriniya, Hamziyya da sauransu)
  • Dr. Bashir Hasan (Adabin Larabci da Tarjama)
  • Malam Sani Inuwa (Nahwu da Sarfu)
  • Malam Aminu Mahe (Tarihi)
  • Malam Mahbub Abdulkadir Sumaly (Balaga ta Tarjamar)

Malamansa na ƙasar Saudiyya

  • Sheikh Dr. Hafiz Alhakami (Musdalahul hadis)
  • Sheikh Dr.Muhammad Nur Saif (Musdalahul hadis)
  • Sheikh Abdulmuhsin Al-Abbad (Tauhid)
  • Sheikh Ali Abdurrahman Alhuzaifi limamin Madina (Tauhid)
  • Sheikh Muhammad Matar (Tadwin and Ruwat)
  • Sheikh Dr. Umar Hawiyya (Tafsir)
  • Dr. Abdulaziz Al-Abdullatif (Jarh Wattaadil)
  • Sheikh Dr.Abdussamad Abid (Musdalahul hadis)
  • Sheikh Dr. Faihan Almudairi (Fiqh)

Karantarwarsa a nan gida Najeriya

Malam ya fara harkokin koyarwa tun shekarar 1985 da darasin littafin Fathul Majid sharhin Kitafut-Tauhid  na Abdurrahman ibn Hassan Aali Sheikh ga taron talibai da littafin Bulugul Maram a unguwar Rijiyar Lemo har Allah ya yi masa tafiya zuwa jami’ar Musulunci ta Madina.

Karantarwarsa a ƙasar Saudiyya

Shehin malamin ya kuma koyar da darusa da dama a ƙasar Saudiyya ciki har da takaitaccen littafin Minhajjus Sunnah da littafin Risaala na Imam Al- Shafi’ da kuma Littafin Bulugul Maram. Dalibai da dama sun halarci waɗannan darusa, mafi shahara daga cikin su ne:

  • Sheikh Dr. Abubakar Muhammad Sani Birnin Kudu – Federal University Dutse
  • Sheikh Muhammad Sani Bala Jos
  • Sheikh Dr. Munir Abdallah Jos
  • Sheikh Nasir Yahaya – Malami a Aminu Kano School for Shari’a and legal Studies
  • Sheikh Dr. Muhammad Muslim Ibrahim – Associate Professor Al-Qalam University Katsina
  • Sheikh Alhassan Sa’id Jos
  • Professor AbdulRashid Abdulqaniy – Gombe State University
  • Sheikh Dr. Abdallah Getso Kano – Sa’adatu Rimi Collage of Education Kano
  • Sheikh Abubakar Abbas Kano yana cikin daliban masu himma
  • Sheikh Muhammad Rabi’u Umar Rijiyar Lemo Kano – Collage of Education Gumel
  • Sheikh Dr. Ibrahim Abdullahi Sani Rijiyar Lemo – Bayero University Kano
  • Sheikh Muhammad Kabiru Maru Zamfara – Director Ibn Uthaimin Islamic Centre Zamfara
  • Sheikh Dr. Muhammad Kabiru Goje Kebbi
  • Sheikh Dr. Abdallah Usman Kano – School of Continue Education, Bayero University Kano
  • Sheikh Dr. Umar Garba Dokaji Gombe
  • Sheikh Dr. Ibrahim Disina Bauchi – MD Sunnah TV

Rubuce-rubucen da malamin ya yi

  • Bita da tahkikin Littafin At-Tamyiz Fi Talkhis Takhrij Ahdith Sharh Al-Wajeez, na Al-Hafiz Ibn Hajar Al-Athqalaani, wanda aka wallafa by Adhwa’ As-Salaf, Riyadh, K.S.A a shekarar 2005.
  • Makarantar Hadith a garin Makkah da Madinah a karni na farko da na biyu da kuma tasirinta a kan ilimin hadisi. (Wanda aka wallafa cikin harshen larabci) (An buga a Darul Minhaj, Riyadh a shekarar 2005)
  • Dhawabit al-Jarh wat Ta’dil inda Al-Hafiz Az-Zahabi, (M.A thesis, an wallafa a kasar London, U.K 1995)
  • Bita da tahkikin Littafin Al-Ighrab na Al-Imam An-Nasa’i, wanda aka wallafa a Al-Ma’athir, Madina, K.S.A. a shekarar 1995.
  • Littafin Ayyami Ma’a Daa’iyatil Jeel, An Wallafa a kasar Masar a shekarar  2011. Ya kunshi bayanin rayuwarsa tare da marigayi Sheikh Jafar Mahmud Adam
  • Littafin Bughyatul Mushtaq Fi Sharhi Risalati Shaikhil Islam Ibn Taimiyya Ila Ahlil Iraq, wanda aka wallafa a kasar Masar a skekarar 2013.
  • Littafin Ramadaniyyat (Takaitattun rubuce-rubuce da ake gabatarwa a kowace rana a Watan Ramadan ) wanda aka wallafa a Nigeria a Shekarar 2021
  • Littafin Addibajah Fi hukmi Ta’adudil Masaajid min gairi haajah – Littafin dake jan hankali kan yawaitar Masallatan Juma’a ba tare ta bukata ba (Ba a kai ga buga shi ba zuwa yanzu)
  • Littafin Nabiyyur-Rahmah, (Sirar Annabi Muhammad S.A.W) (a Wallafa a kasar Masar a shekarar, 2012, 2013 da kuma 2014).
  • Littafin At-Tabseer Li Majaalisit  Tafseer, (Egypt, 2012, 2013).
  • Littafin Asheikh Usman bn Fodiye: Qiraa’tun Fee Turathihil Elmi an buga a kasar Masar a shekarar 2015.
  • Littafin Tamamu Attahfiq Fi Siratus Saddiq, (Tarihin Sayyadina Abubakar AS-Siddiq R.A ) (An buga a Kasar Masar, 2015)
  • Littafin Al Al-maniyyah wa Atharuha fil Mujtama’atul Islamiyya (An buga a kasar Masar a shekarar, 2015).
  • Littafin Al Bina’ Al- Ilmi Liddaa’iya (An Buga a kasar Masar a shekarar 2015).
  • Ithafus Sami’ Wal Qari’ Fi Khatm Saheehul Bukhari, (An wallafa a Nigeria a shekarar 2018).
  • Ra’ayoyi biyu masu hannun riga, na Abul Hasan Ali An-Nadwy (an rubuta da harshen Hausa). (Kano, Nigeria 1999). An sa ke bugashi a shekarar 2022
  • Mahimmancin Sunnah a yaren Hausa. (An rubuta a harshen larabci) (An Wallafa a King Fahd Qur’an Complex, K.S.A.  a shekarar 2004.
  • Littafin Bughyatul Muhtaj Fee Khatmi Saheehi Muslim bn Al-Haj, (An wallafa a Nigeria a shekarar 2019).
  • Fayyataccen Bayani Na Ma’anoni Da Shiriyar Al’Kur’ani, (Tafsirin AlQur’ani a harshen Hausa ) (An Buga a Bairut Lebanon 2020).
  • Littaffin Fatawoyin Rahama (Wanda aka buga a Nigeria a Shekarar 2021

Ayyukan karantarwa

  • Babban Malami a sashen addinin musulunci na Jami’ar Bayero dake Kano daga shekarar 2013 zuwa yanzu
  • Shugaban kwamitin daukar sababbin mambobi na hadaddiyar kungiyar malamai ta Afrika
  • Babban Daraktan Cibiyar Fassara da Bincike ta Imamul Bukhari, (Al-Imamul Bukhari Centre For Research and Translation) Kano
  • Babban Malami a sashen addinin musulunci na Jami’ar musulunci ta Alkalam dake Katsina daga shekarar 2006 zuwa shekarar 2012
  • Karantarwa a daurar da jami’ar madina take gabatarwa ga malaman Arabiya da darusan addinin Musulunci. (Maiduguri, Kano da Bauchi)
  • Shugaban Cibiyar Tarihin Cigaban addinin Musulunci da kuma tattaunawa tsakanin addinai dake Jami’ar Bayero, Kano (Centre For Islamic Civilization and Interfaith Dialogue (CICID))
  • Limamin Babban Masallacin Juma’a na Dorayi, Kano
  • Shugaban Cibiyar Tattara Karatuttukan Sheikh Ja’afar (Sheikh Ja’afar Islamic Documentation Centre (SJIDC))

Karatuttukan da yake gabatarwa a yanzu

Har kawo yanzu Shehin malamin yana gabatarda darusan da Karatuttuka da dama a garuruwan Kano, Katsina da kuma Bauchi wanda suka hadar da:

  • Karatun Tafsirin Al-Qur’ani a watan Ramadan a Masallacin Gwallaga na Jahar Bauchi
  • Karatun Tafsirin Al-Qur’ani a Masallacin Usman Bin Affan, Kano
  • Darasin Adda’u Waddawa’  a Masallacin Modibbo Jihar Katsina
  • Darasin sharhin littafin Kalimatul Ikhlas a masallacin Kerau dake Jihar Katsina
  • Sharhin Takaitaccen Littafin Sahihul Bukhari duk ranar Asabar a Masallacin Usman bin Affan Gadon Kaya
  • Darasin Littafin Akida duk ranar Litinin a Masallacin Usman Bin Affan Gadon Kaya
  • Darasin sharhin Manzumar Imam Suyudi ta Ilimin Hadisi a Jihar Bauchi
  • Shirin Fatawoyin a gidan Talabijin da Rediyo a Jihohin Kano (Rahama Radio), Kaduna (DITV) da Jigawa (Radio Jigawa)

Tarurrukan da bitocin da ya halarta

  1. Farfesa Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo, ya halarci tarurrukan ƙara wa juna ilmi da kwasa-kwasai da dama a nan gida Nijeriya da ƙasashen Saudi Arabiya, Sudan, Mali da sauransu. wanda suka haɗa da:
  2. The regional Conference on Da’awa in Sudan under the theme of “Adda’iya Al-Mutamayyiz” Khartum, 19th – 23rd October 2014, presented a topic titled: “Al-Bina’ul Ilmi Lidda’iya” (i.e. making a solid Academic background for Islamic Preacher”.
  3. International Islamic Conference of Security Stability in the Face of Contemporary Challenges organized by Muslim World League with Cooperation of J.I.B.W.I.S Nigeria Held in Abuja Between 16th to 19th March 2016, Presented Paper Titled (Al-Ghuluw: Asbabuhu wa Ilajuhu “Extremism: Factors and Wayout”).
  4. International Conference on Sunnah and Sirah, organized by the Ministry of Islamic Affairs, K.S.A. presented a topic titled (The Importance attached to Sunnah In Hausa Literature) ( Madinah, 2004).
  5. The Conference on the Protection of Societies organized the International Union of Muslim Preachers held in Doha Qatar between 2nd to 4th March 2016, Presented Paper Titled (Tahsinul Mujtama’ Minal Makhadir Al-Aqadiyya: At-Tashayyu’ Fi Nigeria “ The Protection of the Society from the Dread Beliefs: Shi’a in Nigeria”).
  6. International Conference on Supporting the Holy Prophet (S.A.W), organized by the International University Of Khartum, and Al-Muntada Organization, Al-Khartum, Sudan, presented a topic titled (The Position of the holy Prophet within his companions and the rest of Ummah. (Sudan, 2007)
  7. Conference on leadership organized by Al-Muntada Al-Islamiy, Held in Khartoum Sudan between 10th to 14th April 2016, (At-Taurisul Qiyadiy fi Garb Ifriqiyyah: Tajarub wa Tahadiyyat “The Leadership in west Africa: Examples and Challenges”).
  8. International Conference on Islam in Africa: Combating Extremism and Terrorism organized by International Moderation Forum in Hashimite kingdom of Jordan, in Cooperation with the Islamic peace Society and the Nigerian Centre for Arabic Research, Paper Presented Titled: “Advancing peace by establishing the Al-Wasatiyya and avoiding the extremism”, Held between 8th to 9th August 2015.
  9. Bamako Conference For The Importance of the media in Da’awah, which took place on 20th – 24th July, 2010 presented a paper titled (Media participation: Its importance and Criteria).
  10. International Conference on Islamic and Challenges of Development in the 21st Century Organized by Departmrnt of Islamic Studies and Sharian in Collaboration with Centre for  Qur’anic Studies Bayero University Kano Nigeria, Presented Paper Titled (Al Al-maniyyah wa Atharuha fil Mujtama’atul Islamiyya “Secularism and its Impact on the Muslim Societies”).
  11. Farfesa Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo, yana da mata huɗu da ‘ya’ya goma sha tara. A yanzu haka yana zaune a birnin Kano da iyalinsa yana ci gaba da karantarwa da wa’azantarwa da bayar da fatawowi a addinin Musulunci.

Manazarta

Daily Chronicle. (2022, April 15). Renowned Islamic scholar authored 5 chapters of the Qur’an in tafseer format. 

Dr Sani Rijiyar Lemo – The Daily Reality. (n.d.).

Was this article helpful?
YesNo

You cannot copy content of this page