Skip to content

Sidra chain

Sidra Chain wani tsari ne na fasahar blockchain wanda aka tsara musamman don tallafawa hada-hadar kuɗaɗe waɗanda suka dace da ka’idojin kuɗi na Shari’ar Muslunci.

Screenshot 20250304 1816402
Tambarin kuɗin crypto na Sidra.

Wannan tsari yana samar da mafita wajen tabbatar da cewa an gudanar da kowace hada-hada cikin aminci, a bayyane, kuma daidai da dokokin Shari’ar Muslunci, tare da samar da amana da tsaro ga masu amfani da ke bin ƙa’idojin hada-hadar kuɗi ta Musulunci. Ta hanyar wannan sabuwar fasaha, Sidra Chain na da burin sauƙaƙe hada-hadar kuɗaɗe ta duniya da ta dace kuma mafi inganci.

Sidra Coin wani nau’in kuɗi ne na dijital da ake amfani da shi don sauƙaƙe hada-hadar da mu’amala tsakanin masu amfani da tsarin kuɗin. Wannan nau’in kuɗin yana aiki a matsayin hanyar musanya a cikin manhajar wanda ke ba masu amfani damar yin hada-hada, samun tukuici, da shiga ayyuka daban-daban a cikin manhajar.

Sidra Chain fasaha ce ta blockchain wacce aka ƙera don sauƙaƙe hada-hadar kuɗi waɗanda suka dace da ƙa’idodin Shari’ar Muslunci. Sidra Chain fasaha ce ta blockchain wacce aka gina a kan tsarin Proof of Work (PoW).

Ba kamar tsarin hada-hadar kudi na gargajiya wanda cibiyoyi na tsakiya (bankuna) ke sarrafawa ba, Sidra Chain yana ƙarfafa gwiwar masu amfani ta hanya mai aminci. Wannan yana ba da damar yin sauri, samun ƙarin haske, da tabbatar da hada-hadar kuɗi a sauƙaƙe.

Siffofin tsarin Sidra Chain

Sidra Chain ta bambanta kanta ta hanyar mayar da hankali kan hanyoyin warware matsalar kuɗaɗe masu bin tsarin Shari’ar Muslunci. Wannan yana nuna cewa an tsara siffofi da ayyukan manhajar don yin riƙo da ka’idojin kuɗi na Musulunci, kamar haramcin hada-hadar riba (usary). Akwai wasu mahimman abubuwan da suka keɓance Sidra Chain waɗanda ke da mahimmanci a san su:

Sharia financial instruments

Sidra Chain tana ƙoƙarin samar da tsarin samfuran kuɗade masu dacewa da Shari’ar Muslunci kamar su Sukuk (haɗin gwiwar Islama) da Murabaha (kuɗi-da-riba).

Mining

Sidra Chain na da tsarin mining na musamman, inda ake ba masu amfani da manhajar lada don tabbatar da hada-hada. An tsara tsarin mining don zama mai sauƙi ga masu amfani da ita.

Alfanun Sidra chain

Amfani da tsarin Sidra Chain ya wuce aiwatar da aikace-aikacen kuɗi na gargajiya. Ga wasu misalai.

Cross-Border Payments

Sidra Chain na sauƙaƙe hanyoyi hada-hadar kuɗaɗe cikin aminci. Hanya ce mai kyau don haɗa kasuwanci a cikin ƙasashe, tana ba da damar yin hada-hada cikin inganci kuma a bayyane.

Supply chain management

Ana iya amfani da manhajar don bin diddigin motsin kayayyaki da tabbatar da gaskiya a harkokin kasuwanci. Sidra Chain tana ba da ingantacciyar mafita ga halattattun masana’antu tare da samar da kayayyaki waɗanda ake buƙata da kuma tabbatar da cewa kowane mataki na bisa tsarin da ya dace da ƙa’idodin da ake so.

Sharia fundraising

Sidra Chain na samar da wani ɓangare don tallafawa kasuwancin da suka dace da ƙa’idodin Shari’ar Muslunci. Tsarin yana goyon bayan tara kuɗaɗen da suka dace da ka’idojin kuɗi na Shari’a, tare da tabbatar da cewa an gudanar da kowace hada-hadar kudi bisa ka’idojin da suka dace da tsarin kudi na Musulunci.

Masana’antun waɗanda ke amfana da Sidra

Ana iya amfani da fasahar Sidra Chain a sassa daban-daban. Ga wasu misalan masana’antu waɗanda ke amfani da nau’in kuɗin Sidra:

Islamic banking and finance

Cibiyoyi na iya yin amfani da kuɗaɗen Sidra don samar kayayyaki da ayyuka na kuɗi waɗanda suka dace da ƙa’idodin Sharia. Tsarin yana taimakawa wajen magance kalubalen shigar kudi a cikin tattalin arzikin Musulunci, tare da bai wa mutane da dama damar samun hidimomin kuɗi wadanda suka dace da tsarin Musulunci.

Logistics and supply chain

Manhajar tana ƙara bayyana gaskiya tare da bin diddigi a tarin samar da kuɗaɗen, wanda ke da mahimmanci don ganowa da bibiyar kayayyakin halal. Haka nan tana taimaka wa kamfanoni wajen tabbatar da cewa an cika ka’idojin halal, ta yadda za su ƙara ƙwarin gwiwa ga masu amfani da kayayyakin da suke samarwa.

Non-profit organization

Sidra Chain na samar da amintaccen tsarin na gaskiya don tara kuɗade da sarrafa gudummawa. Fasahar Sidrabna tabbatar da gaskiya da riƙon amana a harkokin amfani da kudade, ta yadda za a samar da masu ba da gudummawa da ƙarin ƙwarin gwiwar cewa ana amfani da gudummawarsu yadda ya kamata kuma daidai da manufar da aka yi niyya.

Manufofin Sidra

Sidra ya fahimci cewa, da yawa daga cikin Musulmai suna shan wahalar shiga duniyar kasuwancin crypto saboda tambayoyi kan ko sayan kadarorin dijital halal ne ko kuma haramun ne, shin ya halatta a yi hasashe a cikinsu, da kuma wane kuɗaɗe aka halatta ko aka haramta.

Sidra yana da manufar inganta tsarin cinikayya a wannan fage ta hanyar ƙirƙirar tsarin kasuwanci na tushen fasaha da kuma samar da wasu hanyoyin da doka ta halatta maimakon haramci ko shakku, kamar ribar kuɗi, ciniki mai gefe, jinginar gida, lamuni da sauran hanyoyin.

Sidra ya ƙunshi ƙwararrun masana fasaha, da hada-hadar kuɗi, da ƙwararrun masana shari’ar Musulunci. Shugaban bankin Sidra ɗan kasuwar ƙasar Qatar ne kuma masani kan harkokin kasuwanci, kuma mai ba da shawara kan kasuwanci sama da shekaru goma.

Masu gina manhajar Sidra suna da gogewa a fannin ilimin gina shafukan yanar gizo da manhajoji bisa fasaha daban-daban, kamar Python, Linux, IBM, nazarin bayanai. Sidra yana samar da ayyuka daban-daban kamar tsarin hada-hadar kuɗi a Musulunci, ayyukan wallet, damar aika kuɗaɗe, tallace-tallace da yarda da tallafi mai tsari, da shawarwari da sauran su.

An tsara manhajar Sidra don zama mai sauƙin amfani ta yadda kowa zai iya shiga kuma ya amfana daga ayyuka daban-daban. Bugu da ƙari, tsarin Sidra ya himmatu wajen kiyaye mafi girman matsayin mutunci da yin aiki tuƙuru don tabbatar da hada-hada ta gaskiya da amana.

Manazarta

Utami, S. (2024, January 11). Sidra Bank: a unique Sharia Digital Asset platform.  | Indodax Academy.

Bittime. (2024, August 1). Sidra Chain: Sharia Blockchain for Decentralized Finance. Bittime.

Sidra start (n.d). Sidra Chain. Sidrastart.com

*****

Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.

Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.

Maƙalar ta amfanar?
EAa

You cannot copy content of this page