Syphilis, wanda a Hausance ake kira ciwon sanyi, wata cuta ce mai yaɗuwa ta hanyar jima’i wadda ƙwayar cuta mai suna Treponema pallidum ke haifar da ita. Cutar tana iya kama mace da namiji, kuma tana ɗaya daga cikin tsofaffin cututtukan da ake ɗauka ta hanyar jima’i a duniya. Syphilis cuta ce mai matakai da dama, kuma idan ba a yi maganinta da wuri ba, tana iya shafar zuciya, ƙwaƙwalwa, idanu, da sauran gaɓoɓin jiki, har ta kai ga mutuwa.

Syphilis tana ɗaya daga cikin cututtukan da ake ɗauka ta hanyar jima’i (sexually transmitted infections: STI) waɗanda suka fi daɗewa suna damun ɗan Adam. Duk da cewa ana iya magance ta da ƙwayoyin antibiotics musamman penicillin, idan ba a gano ta da wuri ba tana iya rikiɗewa zuwa matakai masu haɗari. A wasu lokuta, cutar na iya ɓoyuwa a jiki tsawon shekaru ba tare da alamominta sun bayyana ba, amma daga baya ta dawo da tsanani.
Asalin cutar syphilis
An daɗe da sanin syphilis a tarihi, domin masana tarihi da na kimiyyar lafiya sun tabbatar cewa ta wanzu tun ƙarni na 15 zuwa na 16, lokacin da aka fara lura da kamuwarta a Turai bayan cuɗanyar kasuwanci da wasu sassan duniya. A wancan lokaci, ta zama wata babbar annoba da ta addabi bil’adama, kafin a gano dalilinta da kuma maganinta. Daga baya, a ƙarni na 20, likitoci suka gano cewa ƙwayar Treponema pallidum ce ke haifar da cutar, kuma wannan ganowa ta zama babbar nasara a tarihin likitanci.
Cutar syphilis tana faruwa ne sakamakon shiga jikin mutum da wata ƙwayar cuta mai suna Treponema pallidum ke yi, wadda take daga cikin nau’in bakteriya. Haka kuma, ta na da alaƙa da sauƙin kamuwa da wasu cututtuka masu haɗari kamar HIV/AIDS, saboda tana rage ƙarfi da kariya ta garkuwar jiki.
Yadda cutar syphilis ke yaɗuwa
Cutar Syphilis tana daga cikin cututtuka masu yaɗuwa ta hanyar jima’i (Sexually Transmitted Infections – STIs), kuma tana da hanyoyi kaɗan amma masu matuƙar haɗari na yaɗuwa daga mutum zuwa mutum. Babban tushen yaɗuwarta shi ne mu’amalar jima’i da wanda ke ɗauke da ƙwayar cutar Treponema pallidum, amma akwai wasu hanyoyi na musamman da ke taimakawa wajen yaɗuwar cutar a cikin jama’a.
Hanyar jima’i (sexual transmission)
Wannan ita ce hanya mafi yawan haddasa kamuwa da syphilis. Ana iya kamuwa da cutar ta hanyar:
- Saduwa ta farji (vaginal intercourse)
- Saduwa ta dubura (anal intercourse)
- Saduwa ta baki (oral sex).
A lokacin irin waɗannan saduwa, idan ɗaya daga cikin abokan hulɗa yana ɗauke da rauni mai ɗauke da ƙwayar cutar (chancre), ƙwayoyin Treponema pallidum na iya shiga jikin wanda ba shi da ita ta hanyar ƙananan raunuka a fata ko mucous membrane. Wannan na iya faruwa ko da mutum bai ga raunin ba, domin a wasu lokuta, chancre ɗin yana iya zama ƙarami ko a ɓoye a cikin farji, dubura, ko baki.
Daga uwa zuwa jariri (congenital transmission)
Syphilis tana iya watsuwa daga uwa zuwa jariri yayin da uwar take ɗauke da ciki ko a lokacin haihuwa. Idan uwa ba ta sami magani da wuri ba, ƙwayar Treponema pallidum na iya shiga jinin jariri ta hanyar mahaifa. Wannan yanayi ana kiran shi da Congenital Syphilis, kuma yana da tsanani sosai saboda yana iya haddasa:
- Haihuwar jariri a mace (stillbirth)
- Mutuwar jariri bayan haihuwa
- Lalacewar kwakwalwa, ƙuruciya mai rauni, kurma, ko makanta.
Saboda haka, yana da matuƙar muhimmanci a duba uwa a lokacin renon ciki don tabbatar da cewa ba ta ɗauke da cutar.
Hanyar ƙarin jini (blood transmission)
Kodayake wannan ba ya faruwa da yawa a wannan zamani saboda tsauraran matakan gwajin jini da ake ɗauka, mutum na iya kamuwa da Syphilis idan aka yi masa ƙarin jini (blood transfusion) daga wanda ke ɗauke da cutar. Haka kuma, yin amfani da allura ɗaya ko kayan shan magunguna da mai cutar, na iya zama hanyar yaɗuwa, musamman a wuraren da ake amfani da allura ba tare da tsafta ba.
Rashin tsafta yayin aikin jinya ko aiki da rauni
A cikin asibitoci, ma’aikatan jinya ko likitoci na iya kamuwa da cutar ta hanyar buɗaɗɗen rauni, idan jinin mai cuta ya taɓa fatarsu kai tsaye. Wannan yana da wuya, amma yana nuna muhimmancin amfani da safar hannu da kayan kariya a wuraren kiwon lafiya.
Hanyoyin da cutar ba ta yaɗuwa
Akwai wasu hanyoyi da mutane da dama ke zargin suna haddasa syphilis, amma a zahiri ba haka ba ne. Ba a iya kamuwa da syphilis ta hanyar:
- Cin abinci ko shan ruwa tare da wanda ke ɗauke da cutar
- Yin wanka a cikin ruwa ɗaya
- Amfani da kofi, cokali, ko kwano ɗaya
- Ko ta hanyar runguma, gaisuwa, ko zama tare da mai cutar.
Wannan saboda ƙwayar Treponema pallidum ba ta iya rayuwa tsawon lokaci a wajen jikin mutum. Da zarar ta fita daga jiki, tana mutuwa cikin mintuna kaɗan saboda rashin isasshen zafi da danshi.
Mataƙan cutar syphilis
Syphilis tana da matakai huɗu masu muhimmanci, kowanne da nasa alamomi da haɗari.
Matakin farko (primary syphilis)
A wannan mataki, cutar tana bayyana ne da ƙurji ɗaya ko fiye da haka a wajen da ƙwayar cutar ta shiga jiki. Wannan ƙurji, wanda ake kira chancre, ba ya zafi ko zubar da ruwa. Yana iya fitowa a kan al’aurar mace ko namiji, a baki, ko a dubura. Yana fitowa tsakanin kwanaki 10 zuwa 90 bayan kamuwa da cutar, yawanci kwanaki 21. Ko da ba a yi magani ba, ƙurjin yana iya warkewa da kansa cikin makonni biyu zuwa shida, amma ƙwayar cutar na ci gaba da yawo a jikin mutum.
Mataki na biyu (secondary syphilis)
Idan ba a yi magani ba a mataki na farko, cutar na bazuwa cikin jini ta haifar da ƙuraje masu launin ja ko ruwan kasa a fata, musamman a tafin hannu da tafin ƙafa. Alamomi sun haɗa da zazzaɓi, ciwon kai, ciwon ƙashi, zubewar gashi, da kumburin ƙwayoyin jini. Waɗannan alamomi kan ɓace da kansu, amma hakan ba yana nufin cutar ta gushe ba.
Ɓoyayyen mataki (latent syphilis)
A wannan mataki, babu wata alama da ake gani da ido, amma ƙwayar cutar tana ci gaba da yawo a jikin mutum. Wannan yanayin na iya ɗaukar shekaru da dama, kafin ta rikiɗe zuwa mataki mafi haɗari.
Babban mataki (tertiary syphilis)
Idan har ba a magance cutar ba, tana iya kaiwa ga matakin da ake kira tertiary syphilis. A wannan lokaci, cutar na iya lalata ƙasusuwa, ƙwaƙwalwa, idanu, zuciya, da jijiyoyi. Mutum zai iya kamuwa da Neurosyphilis (Syphilis ta ƙwaƙwalwa) ko Cardiovascular Syphilis (Syphilis ta zuciya). Waɗannan su ne matakai mafi haɗari, kuma suna iya haifar da lalura ta dindindin ko mutuwa.
Alamomin cutar syphilis
Alamomin Syphilis suna bambanta bisa ga matakin da cutar ke ciki, amma mafi yawan alamomin sun haɗa da:
- Ƙurji a wajen jima’i, baki, ko dubura.
- Ƙuraje masu launin ja ko fari a fata.
- Ciwon kai da zazzaɓi.
- Ciwon ƙashi da haɗin gwiwa.
- Zubewar gashi.
- Kasala da rashin ƙarfi.
- Matsalar gani ko taɓuwar ƙwaƙwalwa a matakin ƙarshe.
Hanyoyin gwaje-gwaje
Gano cutar syphilis da wuri yana da matuƙar muhimmanci domin yana taimakawa wajen samun nasarar magani da kuma hana yaɗuwar ta ga wasu mutane. Likitoci da masana kimiyya suna amfani da nau’o’in gwaje-gwaje daban-daban don tabbatar da kasancewar ƙwayar Treponema pallidum a jikin mutum. Gwaje-gwajen nan suna taimakawa wajen gano ko mutum ya taɓa kamuwa da cutar, ko har yanzu ƙwayar tana aiki a jikinsa.
A asibitoci, ana iya gano syphilis ta hanyoyi biyu masu muhimmanci: gwajin jini da ruwan jiki (cerebrospinal fluid), musamman idan ana zargin cewa cutar ta kai ga ƙwaƙwalwa ko jijiyoyi.
Gwajin jini (blood test)
Shi ne mafi sauƙi kuma mafi yawan amfani wajen gano cutar syphilis. Ana ɗaukar jinin mutum don a bincika ko jikinsa yana ɗauke da ƙwayoyin kariya (antibodies) da yake samarwa don yaƙar ƙwayar Treponema pallidum. Akwai manyan rukunan gwaje-gwajen jini guda biyu da ake amfani da su:
Gwaje-gwajen da ba su da alaƙa kai tsaye da ƙwayar cutar (Non-treponemal tests)
Waɗannan gwaje-gwajen suna gano ƙwayoyin kariya da jiki ke samarwa saboda harin da cutar ke yi, ba wai ƙwayar cutar kanta ba. Ana amfani da su wajen:
- Gano cutar a farkon lokaci
- Bibiyar yadda magani ke aiki
- Da lura da cigaban cutar.
Misalan irin waɗannan gwaje-gwajen sun haɗa da:
- Rapid Plasma Reagin (RPR) test,
- Venereal Disease Research Laboratory (VDRL) test.
Sakamakon waɗannan gwaje-gwaje kan nuna ko akwai ƙwayoyin kariya a jini da kuma adadinsu. Idan bayan magani adadin ƙwayoyin kariya ya ragu, hakan na nuna cewa magani yana aiki yadda ya kamata.
Gwaje-gwajen da ke gano ƙwayar cutar kai tsaye (Treponemal tests)
Waɗannan su kuma suna tabbatar da kasancewar ƙwayar Treponema pallidum kanta a jiki. Ana amfani da su wajen tabbatar da sakamakon da aka samu daga gwaje-gwajen farko. Misalan su sun haɗa da:
- Fluorescent Treponemal Antibody Absorption (FTA-ABS)
- Treponema Pallidum Particle Agglutination (TP-PA)
- Enzyme Immunoassay (EIA) ko Chemiluminescence Immunoassay (CIA).
Gwaje-gwajen treponemal suna kasancewa masu ɗorewa. Wato, ko da bayan an warke daga cutar, sakamakonsu kan ci gaba da nuna alamomin cewa mutum ya taɓa kamuwa da syphilis a baya.
Gwajin ruwan jijiyoyi (cerebrospinal fluid test)
A wasu lokuta, musamman idan likita ya yi zargin cewa cutar ta kai ga ƙwaƙwalwa ko jijiyoyi (neurosyphilis), ana yin lumbar puncture don ɗaukar ruwan cerebrospinal fluid (CSF) daga ƙashin baya. Ana yin wannan gwaji ne don bincikar alamomin ƙwayar Treponema pallidum a cikin tsarin jijiyoyi. Wannan na taimakawa wajen tabbatar da nau’in cutar da kuma zaɓen maganin da ya dace.
Gwajin uwa mai ciki da jarirai (prenatal and infant testing)
Domin daƙile congenital syphilis, ana shawartar kowace mace mai ciki da ta je gwajin jini don gano syphilis a farkon watannin cikinta. Idan an gano cutar da wuri, ana iya ba da magani wanda zai kare jariri daga kamuwa da ita kafin haihuwa. Jariran da aka haifa daga uwa mai ɗauke da syphilis su ma ana yi musu gwaji domin tabbatar da lafiyarsu.
Muhimmancin gwaje-gwaje
Gano syphilis da wuri yana da matuƙar tasiri wajen:
- Hana lalacewar gaɓoɓin jiki kamar zuciya, ƙwaƙwalwa, da ido
- Tabbatar da cewa mutum ya warke gabaɗaya
- Da kuma daƙile yaɗuwar cutar ga abokan jima’i da jarirai.
- Magani da kariya daga cutar syphilis
Magani
Magance cutar syphilis yana da sauƙi idan an gano cutar da wuri. Maganin da ya fi tasiri a yanzu shi ne penicillin, wani nau’in ƙwayar magani mai kashe ƙwayoyin Treponema pallidum kai tsaye. Wannan magani na daga cikin antibiotics mafi ƙarfi da ake amfani da su wajen kawar da ƙwayoyin cutar da ke haifar da Syphilis tun daga shekarun farko na gano ta.
Amfani da penicillin
- Benzathine Penicillin G shi ne mafi yawan amfani. Ana yi wa mutum allura guda ɗaya ko fiye, gwargwadon matakin da cutar ta kai.
- A matakan farko (primary da secondary syphilis), allura guda ɗaya ta isa ta kawar da cutar gabaɗaya.
- Amma idan cutar ta kai ɓoyayyen mataki ko babban mataki, ana iya buƙatar yin allura sau uku ko fiye, a makonni daban-daban, domin tabbatar da cewa ƙwayoyin cutar sun mutu gabaɗaya.
Masu cuta mai karya garkuwar jiki (HIV/AIDS)
Mutanen da suke da cutar da ke karya garkuwar jiki (HIV/AIDS) sukan buƙaci kulawa ta musamman, saboda yadda Syphilis ke iya sa ƙwayoyin HIV su yi ƙarfi cikin jiki. Saboda haka, ana lura da irin waɗannan marasa lafiya sosai, tare da yin gwaje-gwaje a kai a kai don tabbatar da cewa magani yana aiki yadda ya kamata.
Mata masu ciki
- Mata masu ciki da aka gano suna da syphilis dole ne su fara amfani da magani da wuri don guje wa yaɗa cutar ga jariran da ke cikinsu.
- Idan ba a yi magani ba, jariran na iya mutuwa a cikin mahaifa, haihuwa da naƙasa, ko kamuwa da congenital syphilis bayan haihuwa.
- Penicillin shi ne maganin da ake amfani da shi wajen magance cutar ga mata masu ciki, domin ba shi da illa ga jariri.
Bayan magani
Bayan an kammala shan magani, ana buƙatar a ci gaba da zuwa asibiti akai-akai don yin gwajin jini domin tabbatar da cewa ƙwayar cutar ta gushe gabaɗaya daga jiki. Likita na iya bayar da shawarar yin gwaji a bayan watanni uku, shida, da shekara guda bayan magani. Idan sakamakon gwaje-gwajen bai nuna raguwar ƙwayoyin kariya ba, hakan na iya nuna cewa cutar ba ta gushe gabaɗaya ba, kuma dole ne a sake magani.
Rigakafin cutar syphilis
Rigakafi da kariya daga syphilis suna da matuƙar muhimmanci domin hana kamuwa da cutar da kuma daƙile yaɗuwar ta a cikin al’umma. Ana iya ɗaukar matakan kariya kamar haka:
Guje wa jima’i da mutane da yawa
Hanya mafi inganci ta kariya daga syphilis ita ce guje wa jima’i da mutanen da ba a tabbatar da lafiyarsu ba. Tsayawa ga abokin jima’i guda ɗaya yana rage haɗarin kamuwa da cututtuka masu yaɗuwa ta jima’i.
Amfani da kwaroron roba (condom)
Amfani da kwaroron roba a duk lokacin da ake yin jima’i yana taimakawa wajen rage yiwuwar kamuwa da syphilis, musamman idan ana yin jima’i da wanda ba a san lafiyarsa ba. Duk da haka, kwaroron roba ba ya kare mutum gabaɗaya, domin ƙwayar cutar na iya shiga ta wasu ɓangarori na fata da kwaroron roba ba ya rufewa.
Gwaji akai-akai
Yin gwaji na syphilis akai-akai, musamman ga mutanen da ke da abokan jima’i da dama da mata masu ciki. Mutanen da suka taɓa kamuwa da wasu cututtukan jima’i, yana taimaka wa wajen gano cutar da wuri kafin ta haifar da illa.
Guje wa amfani da allura ɗaya
Duk da cewa yphilis ba ta yaɗuwa ta wannan hanya sosai, ya kamata a guje wa amfani da allura ɗaya ko kayan aikin jini ga mutum fiye da ɗaya, domin kare kai daga kamuwa da kowace irin cuta, ciki har da Hepatitis da HIV.
Ilmantarwa da wayar da kai
Wayar da kan jama’a game da hanyoyin yaɗa syphilis da illolinta na da matuƙar muhimmanci. A makarantu, asibitoci, da gidajen rediyo, ya kamata a riƙa koyar da yadda ake kariya da muhimmancin yin gwaji kafin aure.
Syphilis cuta ce mai haɗari wadda za a iya daƙile ta cikin sauƙi idan an kiyaye dokokin tsafta da rigakafi. Gwaji da wuri, magani na antibiotics, da nisantar jima’i da mutane da dama suna daga cikin muhimman matakan da ke daƙile yaɗuwarta. Kula da lafiyar jiki da bin shawarwarin likitoci yana taimakawa wajen rage mace-mace da cututtuka masu kama da syphilis a al’umma.
Manazarta
Centers for Disease Control and Prevention. (2023, 19 Disamba). Syphilis – CDC fact sheet (detailed).
Mayo Clinic. (2024, 10 Satumba). Syphilis: Symptoms and causes.
National Health Service (NHS). (2024, 13 Mayu). Syphilis overview.
Workowski, K. A., & Bachmann, L. H., et al. (2021, 23 Yuli). Sexually transmitted infections treatment guidelines, 2021. MMWR Recommendations and Reports, 70(4), 1–187.
World Health Organization. (2025, 29 Mayu). Syphilis: Key facts.
Sharuɗɗan Editoci
Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.
Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.
