Skip to content

Tazarar haihuwa

Ma’anar tazarar haihuwa

Na nufin yin amfani da wasu hanyoyi don hana haɗuwar ƙwayayen haihuwar mace da na namiji, amma na wucin gadi ba na dindindin ba, don samar da tazara tsakanin wannan haihuwa zuwa ta gaba.

A wata mahangar tazarar haihuwa na nufin ƙayade iyali, ko kuma ba da damar walwala tsakanin iyali na wani lokaci domin tabbatuwar lafiyar su da kuma samar musu da nutsuwar da ta kamata. Mata da yawa na tsoron ba da tazara tsakanin haihuwa, wasu kuma suna ganin kamar hakan yi wa ubangiji shishigi ne, wasu kuma daga mazajansu ne matsalar take ba sa buƙatar hakan. Likitoci da dama sun yi bayani kan tazarar haihuwa wanda ta fuskoki da yawa alfanunsa yake a buɗe ba tare da ƙudunduno ba.

Sai dai ra’ayoyi da dama sun bambanta, kamar yadda na taɓa sauraron hirar wata baiwar Allah inda take bayyana cewa, komai wahalar da za ta sha ba za ta iya yin tazarar haihuwa ba. Idan muka duba ta kowace fuska za mu ga akwai alfanu cikin hakan. Haka kuma ko addinni za mu koma za mu fuskanci hikimar hakan, domin shi addinin musulunci kan sa nasiha ne, haka kuma cikinsa akwai sharaɗin kulawa da yara bayan haihuwarsu kama daga kan karatunsu zuwa sutura da cigaban goben rayuwar su. Bari mu bi abin daki-daki domin samar da gamsuwa ga zuƙatan da suke cikin tsoro ko shaku da kuma ruɗani.

Maganin haɗiya don tazarar haihuwa

Dalilan da ke halatta tazarar haihuwa:

1. Don Kare Lafiyar Uwa Da Ɗa: ɗawainiyar daukar ciki da haihuwa na jigata wasu matan, har hakan ya kai ga raunata lafiyarsu. A irin wannan yanayi idan wani cikin ya kara ɓullowa zai zama babbar barazana ga rayuwarsu da kuma lafiyar dan da ake goyo da kuma lafiyar sabon cikin da ke tsirowa; ko kuma in ya kasance matar tana da wani ciwo mai tsanani, wanda bullowar ciki na iya zama barazana ga rayuwarta, kamar mace mai ciwon sikila, asma, ciwon zuciya da makamantansu, ko mai wata cuta, wacce aka iya gadar da ita ga abin da za a haifa; to a nan ya halatta a tsaida haihuwa na tsawon lokacin da zai isa har matar ta samu lafiya da karfin da za ta iya jure daukar wani cikin da shayar da shi.

2. Don Mahaifa Ta Huta: Idan ya tabbata mace mai yawan ɗaukar ciki ce akai akai, wato mai yin ciki da goyo; to ya halatta a dakatar da haihuwa na wani lokaci, don mahaifa ta huta kuma ta koma daidai ta yadda za ta samu karfin daukar wani sabon cikin ba tare da matsala ba. Domin takura mahaifa irin haka na iya haifar da matsala ga lafiyar mai cikin ko a samu wata tangarɗa yayin ɗaukar cikin da haihuwa.

3. Don Cika Lokacin Raino: Kamar yadda ya zo a cikin Alƙur’ani Mai Girma, tsawon lokacin shayar da yaro shi ne wata 24; don haka kowane jariri yana bukatar wannan tsawon lokacin yana shan nonon mahaifiyarsa; wanda bullowar wani sabon ciki na iya sa a katse yaro daga shayarwa ba tare da ya cika lokacin shayarwarsa ba. Don haka ya halatta a dakatar da haihuwa na wucin gadi don tabbatar da cewa jariri ya cika lokacin shayarwarsa.

4. Kasawa Ga Tarbiyya: Haka ma ya halatta a yi tazarar haihuwa don a guji kasawa wajen ba ’ya’ya kyakkyawar tarbiyya idan an tara su da yawa, domin rashin ba su kyakkyawar tarbiyya babbar illa ce ga rayuwar duniyarsu da lahirarsu da kuma barazana ce ga ci gaban al’umma.

Hanyoyin tazarar haihuwa na zamani

Kaɗan daga matsolin da mata kan fuskanta yayin guje wa ba da tazara tsakanin haihuwa sun haɗar da:

1- Ciki da kuma goyo.
2- Yanƙwanewar yaron da ya sha ciki
3- Jigitar uwa yayin ɗaukar ciki da kuma raino.
4- Raunin kulawa ga yaran da ake goyo.
5- Raunin kulawa daga maigida
6- Haifar da ƙazanta
7- Samuwar rashin fahimta tsakanin wasu ma’auratan.
8- Rashin sakewa acikin ‘yan uwa mata
9- Ƙaracin lafiya
10- Samuwar ɓacin rai mara dalili.

Ƙaɗan ke nan daga abin da mata suke fuskanta, wanda muka samu ji ta bakin waɗansu da hakan ya faru a garesu. Don haka dabara ta rage ga mai shiga rijiya. Da wannan hujojin nake ganin, idan likita ya ba da damar yin tazara tsakanin haihuwa da haihuwa a ding ƙoƙarin kwatanta hakan. Haka kuma idan ance mace ta nemi ta huta saboda dalilan sama ba zai iya zama aibu ba. Sai dai ita rayuwa kowa da zaɓin sa, haka kuma ba ya nufin cewar dole sai koya ya ɗauki masalahar da kowa ya bi, domin duk wanda rai ya yi wa daɗi ba kamar mai shi ba. Haka kuma masu iya magana kan ce don tuwon gobe ake wanke tukunya.

Was this article helpful?
YesNo

You cannot copy content of this page

×