Skip to content

Telex

Telex wata tsohuwar hanyar sadarwa ce ta aika saƙonnin rubutu kai tsaye daga wata na’ura zuwa wata ta hanyar layin waya. Tsarin yana amfani da na’urorin da ake kira teleprinter ko teletypewriter, waɗanda suke kama da na’urar buga rubutu (typewriter) amma suna da damar aika abin da aka rubuta zuwa wata na’ura a wani wuri mai nisa. Saƙon da aka aika ta Telex yana isa a rubuce a takarda a gefen mai karɓa, ba tare da buƙatar wani ya sake buga shi ba. Wannan ya sa Telex ya zama muhimmin cigaba a sadarwa, domin ya rage jinkiri da kuskuren fassarar saƙonni.

A aikace, Telex yana aiki ne kamar kira ta waya amma maimakon magana, ana aika rubutu. Kowace na’ura tana da lamba ta musamman da ake kira Telex number, wadda ake bugawa domin haɗuwa kai tsaye da na’urar da ake son aika saƙo gare ta a ko’ina cikin duniya. Saboda wannan sauƙi da tabbacin isar saƙo, Telex ya zama ginshiƙi a harkokin kasuwanci, diflomasiyya, banki, da sufuri a zamanin da ya shahara.

Asalin kalmar “Telex” (Teleprinter Exchange)

Kalmar Telex ta samo asali ne daga haɗakar kalmomin Ingilishi guda biyu: Teleprinter (na’urar aika rubutu ta nesa) da Exchange (cibiyar haɗa layukan sadarwa). Ma’anarta ita ce cibiyar sadarwa da ke haɗa na’urorin teleprinter domin su rika aika saƙonni ga juna. Wannan suna ya bayyana a sarari cewa tsarin ba kawai na’ura guda ba ne, illa cikakkiyar hanyar sadarwa ce da ke ba da damar hulɗa tsakanin ofisoshi da ƙasashe.

An fara amfani da wannan suna ne a Turai a farkon ƙarni na 20, lokacin da aka fara gina hanyoyin sadarwa na musamman domin teleprinter. Daga baya sunan ya zama gama-gari a duniya don kiran wannan tsarin gabaɗaya.

Telex ya taka muhimmiyar rawa a tarihin sadarwa kafin zuwan injin fax, intanet, da imel. Shi ne karo na farko da aka samu hanyar da ke ba da damar aika rubutaccen saƙo kai tsaye daga ofis zuwa ofis a duniya cikin sauri. Wannan ya taimaka sosai wajen bunƙasar kasuwancin ƙasa da ƙasa, hulɗar diflomasiyya, da sadarwar gaggawa.

Na'urar telex mai allon nuna rubutu.
Akwai nau’ikan injin telex da dama, ciki har da mai allon nuna rubutu kafin a fitar a takarda.

Haka kuma, Telex ya zama abin dogaro a wuraren da ake buƙatar sahihin rubutaccen bayani, kamar bankuna, kamfanonin jiragen ruwa, jiragen sama, da hukumomin gwamnati. Saboda saƙon yana fitowa a rubuce kai tsaye, ana iya adana shi a matsayin hujja, wanda ya ba shi fifiko a kan tattaunawar waya ta baki kawai.

Tarihin samuwar  injin telex

Farkon na’urorin teleprinter

Asalin Telex ya samo tushe ne daga ƙirƙirar na’urorin teleprinter a ƙarshen ƙarni na 19 da farkon ƙarni na 20. Waɗannan na’urori sun samu cigaba ne daga fasahar telegraph, wadda take aika saƙonni ta hanyar lambobin Morse. Masana sun yi ƙoƙarin sauƙaƙa wannan tsari ta yadda za a iya buga haruffa kai tsaye maimakon koyon lambobin Morse.

Daga cikin muhimman cigaban akwai ƙirƙirar na’urar da za ta iya fassara abin da aka buga a maɓallin zuwa siginar lantarki, sannan ta mayar da siginar zuwa rubutu a gefen mai karɓa. Wannan ya haifar da na’urar teletypewriter, wadda ta zama ginshiƙin tsarin Telex daga baya.

Bunƙasar telex a ƙarni na 20

A shekarun 1920 zuwa 1930, ƙasashe musamman a Turai da Arewacin Amurka suka fara gina hanyoyin sadarwa na Telex a matsayin tsarin hukuma. Kamfanonin sadarwa da hukumomin gwamnati suka rungumi wannan fasaha saboda amincinta da saurin aiki.

Bayan Yaƙin Duniya na Biyu, Telex ya ƙara bunƙasa sosai, domin kasuwanci da hulɗar ƙasa da ƙasa sun ƙaru. A wannan lokaci aka fara samar da cibiyoyin Telex na duniya, inda za a iya aika saƙo daga wata ƙasa zuwa wata cikin mintuna kaɗan.

Yaɗuwarsa a duniya

A tsakiyar ƙarni na 20, Telex ya zama hanyar sadarwa ta duniya. Manyan kamfanoni, bankuna, ofisoshin jakadanci, da kamfanonin sufuri sun mallaki na’urorin Telex domin gudanar da ayyukansu. Haka kuma, an kafa lambobin ƙasa da ƙasa domin sauƙaƙa kira tsakanin ƙasashe, kamar yadda ake yi a tsarin waya.

A wasu lokuta sa suka shuɗe, Telex ya zama hanya mafi aminci wajen aika umarni da bayanan kasuwanci, musamman a lokutan da sadarwar waya ba ta da inganci ko kuma ba a yarda da ita saboda rashin tabbacin rubutacciyar hujja.

Shigowarsa Afirka da Najeriya

Telex ya shiga Afirka ne ta hannun hukumomin sadarwa na mulkin mallaka da kamfanonin kasuwancin Turai. Manyan birane da tashoshin jiragen ruwa su ne wuraren farko da aka kafa shi, domin su ne cibiyoyin kasuwanci da hulɗar ƙasa da ƙasa.

A Najeriya, an fara amfani da Telex ne a lokacin da harkokin kasuwanci da gwamnati ke bunƙasa, musamman a biranen Lagos da sauran manyan cibiyoyi. Hukumar sadarwa ta ƙasa da bankuna da kamfanonin mai sun yi amfani da shi wajen aika saƙonni na gaggawa zuwa ƙasashen waje. Kafin zuwan fax da intanet, Telex ya kasance muhimmin ginshiƙi na sadarwar ofisoshi a Najeriya.

Yadda telex ke aiki

Tsarin haɗa na’urar da layin waya

Tsarin Telex yana aiki ne ta hanyar haɗa na’urar teleprinter da layin waya na musamman da aka tanada domin sadarwa. Wannan layi yana kama da na wayar tarho, amma an keɓe shi domin watsa siginar rubutu maimakon murya. Lokacin da aka haɗa na’urar da wannan layi, tana samun damar shiga cibiyar sadarwar Telex (exchange), wadda ke haɗa dukkan na’urorin da ke cikin tsarin.

A cikin cibiyar Telex, akwai na’urorin sauya layi (switching equipment) da ke ba da damar haɗa mai aikawa da mai karɓa kai tsaye. Wannan tsari yana kama da yadda ake haɗa kira a wayar tarho, sai dai a nan rubutu ake turawa. Saboda haka, dole ne a samu ingantaccen layin waya domin tabbatar da cewa saƙon ya isa ba tare da tangarda ba.

Aika saƙo daga na’ura zuwa na’ura

Lokacin da aka haɗa na’urorin biyu, mai aikawa zai fara buga saƙo a maɓallin rubutu. Duk abin da aka buga yana canjawa zuwa siginar lantarki, sannan siginar ta bi ta cikin layin waya zuwa na’urar mai karɓa. A can, na’urar za ta sake mayar da siginar zuwa haruffa, ta buga su a takarda kai tsaye.

Wannan tsari yana faruwa nan take, wato yayin da ake bugawa a wuri ɗaya, ana ganin sa a ɗaya gefen. Saboda haka Telex ya ba da damar tattaunawa ta rubutu kai tsaye, kamar yadda ake yi ta baki a waya. Haka kuma, ana iya dakatar da rubutu domin ba wa ɗaya bangaren damar amsawa.

Amfani da lambar Telex

Kowace na’urar Telex tana da lamba ta musamman da ake kira Telex number. Wannan lamba ita ce adireshin na’urar a cikin cibiyar sadarwar. Domin aika saƙo, mai aikawa zai buga wannan lamba domin haɗuwa kai tsaye da na’urar da ake son tuntuɓa, ko tana cikin gari, ƙasa, ko wata ƙasa daban.

Lambar Telex tana da matuƙar muhimmanci domin tana hana kuskuren aika saƙo ga wanda ba a nufa ba. A lokuta da dama, bayan an haɗa, na’urorin suna aika wani saƙon tantancewa ta tsarin atomatik domin tabbatar da cewa an haɗa da na’urar da ta dace.

Yadda ake karɓar saƙo

Lokacin da aka aika saƙo, na’urar mai karɓa za ta fara buga rubutun a takarda ko a cikin na’urar adanawa. Idan babu wanda ke kusa da na’urar a lokacin, za ta ci gaba da bugawa har sai saƙon ya ƙare. Wannan ya ba da damar a bar saƙo kamar wasiƙa, wanda za a zo a karanta daga baya.

A wasu na’urori, akwai ƙararrawa ko alamar sanarwa da ke nuna cewa an shigo da saƙo. Bayan karɓa, ana iya cire takardar a adana ta a matsayin hujja, musamman idan saƙon na da muhimmanci ga kasuwanci ko gwamnati.

Sassan na’urar telex

Maɓallan rubutu

Maɓallan rubutu su ne a dunƙule ɓangaren da ake amfani da shi wajen shigar da saƙo. Yana kama da maɓallan na’urar typewriter ko kwamfuta, inda kowanne maɓalli yake wakiltar harafi, lamba, ko alama. Lokacin da aka danna maɓalli, na’urar tana canja shi zuwa siginar lantarki domin aika shi ta layi. Ingancin maɓallin yana da muhimmanci domin yana shafar saurin aiki da sauƙin rubutu.

Na’urar buga saƙo (printer)

Wannan ita ce ɓangaren da ke fitar da saƙon a rubuce. Tana buga duk abin da aka karɓa daga layi a kan takarda, haruffa bayan haruffa. Wannan ya ba da damar a samu kwafin saƙo kai tsaye ba tare da sake bugawa ba. Printer ɗin Telex tana aiki ne da sauri kuma tana nagarta, domin an ƙera ta domin aiki na dogon lokaci a ofisoshi da cibiyoyi masu aiki tuƙuru.

Allon nuna saƙo

Wasu na’urorin Telex na zamani sun ƙunshi allon da ke nuna abin da ake bugawa ko karɓa kafin a buga shi a takarda. Wannan yana taimakawa wajen gyara kuskure kafin aika saƙo. Sai dai, tsofaffin na’urori ba su da wannan fasali, domin suna buga saƙo kai tsaye ba tare da nunawa a allo ba.

Na’urar haɗa layi (modem/line unit)

Wannan ɓangare ne da ke kula da haɗa na’urar da layin waya. Yana canja siginar lantarki zuwa irin wadda za ta iya tafiya ta cikin layin sadarwa, sannan ya mayar da ita zuwa rubutu a gefen karɓa. Shi ne zuciyar tsarin sadarwar Telex, domin idan ba tare da shi ba, na’urar ba za ta iya tuntuɓar wata ba. Haka kuma, line unit yana kula da buɗe sako, rufe shi, da tabbatar da cewa sadarwa tana gudana cikin tsari.

Nau’o’in naurar telex

Point-to-point system

Point-to-point system shi ne tsarin Telex mafi sauƙi, inda ake haɗa na’ura ɗaya kai tsaye da wata na’ura guda ta hanyar layin waya na musamman. A wannan tsari babu wata cibiyar sadarwa ta tsakiya, domin na’urorin biyu suna da layi kai tsaye tsakaninsu. Wannan yana sa sadarwar ta zama mai sauri kuma ba ta da cunkoso daga sauran masu amfani.

An fi amfani da wannan tsari a wuraren da ake buƙatar sadarwa kai tsaye tsakanin ofisoshi biyu masu muhimmanci, kamar hedkwatar kamfani da reshe, ko tsakanin hukumomi biyu na gwamnati. Duk da sauƙinsa, tsarin yana da iyaka, domin ba zai iya haɗa na’urori da yawa ba sai an ƙara wasu layukan daban.

Telex network system

Telex network system shi ne tsarin da ya fi shahara, inda ake haɗa na’urori da dama ta hanyar cibiyar sadarwa guda (exchange). A wannan tsari, kowace na’ura tana da damar tuntuɓar kowace a cikin cibiyar ta hanyar amfani da lambar Telex. Wannan ya ba da damar sadarwa tsakanin wurare da dama ba tare da buƙatar layi kai tsaye ga kowace na’ura ba.

Cibiyar sadarwar tana aiki kamar cibiyar wayar tarho, tana haɗa kira daga mai aikawa zuwa mai karɓa. Wannan tsari ya sauƙaƙa amfani da Telex a duniya, domin kamfanoni da hukumomi na iya hulɗa da juna ba tare da tsadar gina layi na musamman ba.

Automatic telex system

Automatic Telex system wani mataki ne na ci gaba a fasahar Telex, inda tsarin haɗa kira da aika saƙo yake faruwa ta atomatik ba tare da taimakon ma’aikacin cibiyar sadarwa ba. A nan, mai aikawa zai buga lambar Telex kawai, sai tsarin ya nemo na’urar da ake nema ya haɗa kai tsaye.

Wannan tsari ya rage jinkiri da kuskure, ya kuma ba da damar amfani da Telex cikin sauri kamar yadda ake yin kira ta waya. Haka kuma, ya ba da damar sadarwa ta duniya cikin sauƙi, domin ana iya haɗa ƙasashe da yawa a cikin tsarin guda.

Amfanin injin telex

A kasuwanci da bankuna

Telex ya taka muhimmiyar rawa a harkokin kasuwanci da bankuna kafin zuwan intanet. Kamfanoni sun yi amfani da shi wajen aika umarni, bayanan kasuwanci, takardun yarjejeniya, da sanarwar gaggawa. Bankuna kuma sun yi amfani da Telex wajen tabbatar da aika kuɗi, aika bayanan asusun ajiya, da sadarwa tsakanin rassa a ƙasashe daban. Saboda saƙonnin Telex suna fitowa a rubuce, ana iya adana su a matsayin hujja, wanda ya sa bankuna suka fi yarda da shi a kan tattaunawar waya kawai.

A ofisoshin gwamnati

Hukumomin gwamnati sun yi amfani da Telex domin sadarwa tsakanin ma’aikatu, ofishin jakadanci, da ofisoshin gwamnati a ciki da wajen ƙasa. Wannan ya taimaka wajen aika umarni, rahotanni, da bayanan sirri cikin sauri da aminci. A harkokin diflomasiyya ma, Telex ya zama muhimmin kayan aiki, domin ofishin jakadanci na iya aika saƙonni zuwa hedkwata cikin gaggawa, musamman a lokutan rikici ko muhimmiyar tattaunawa.

A harkokin jiragen ruwa da jiragen sama

Kamfanonin jiragen ruwa da jiragen sama sun yi amfani da Telex domin sadarwa tsakanin tashoshi, jirage, da ofisoshin gudanarwa. A harkokin jiragen ruwa, ana amfani da shi wajen aika bayanan jigilar kaya, jadawalin tashi da sauka, da sanarwar gaggawa. Haka kuma, a harkokin jiragen sama, Telex ya taimaka wajen aika bayanan jirage, rajistar fasinjoji, da saƙonnin tsaro tsakanin filayen jiragen sama a ƙasashe daban-daban.

A kafofin watsa labarai

Kafofin watsa labarai kamar gidajen rediyo, talabijin, da kamfanonin dillancin labarai sun yi amfani da Telex wajen karɓar labarai daga sassan duniya. Kamfanonin dillancin labarai suna aika rahotanni ta Telex zuwa ofisoshinsu domin a watsa su cikin gaggawa. Wannan ya ba da damar yaɗa labarai na duniya cikin sauri kafin zuwan intanet, kuma ya taimaka wajen haɗa duniya ta fuskar bayanai.

Fa’idojin telex

Aika saƙo kai tsaye

Daya daga cikin manyan fa’idojin telex shi ne damar aika saƙo kai tsaye daga na’ura zuwa wata ba tare da tangarɗa ba. Da zarar an haɗa na’urorin biyu ta hanyar lambar telex, mai aikawa zai iya fara buga saƙo, kuma a lokaci guda ana karɓarsa a ɗaya gefen. Wannan ya rage jinkiri sosai idan aka kwatanta da wasiƙa ko sauran tsofaffin hanyoyin sadarwa.

Rubuta sako da injin telex.
Injin telex ya shahara wajen aika rubutaccen saƙo daga ofishi zuwa ofishi a bankuna da ma’aikatun gwamnati kafin bayyanar hanyoyin zamani kamar e-mail.

Haka kuma, wannan tsarin kai tsaye ya ba da damar tattaunawa ta hanyar rubutu tsakanin ɓangarori biyu, inda kowane ɓangare zai iya amsawa nan take. Wannan ya sa Telex ya zama kayan aiki mai amfani a lokutan gaggawa ko muhimman harkoki.

Aminci da inganci

Telex ya shahara wajen aminci da daidaito, domin saƙon yana isowa a rubuce kamar yadda aka aika shi. Wannan ya rage yiwuwar kuskure ko rashin fahimta da kan faru a tattaunawar baki. Saboda haka, hukumomi da bankuna sun fi son amfani da Telex wajen aika bayanai masu muhimmanci.

Haka kuma, tsarin yana da tabbacin isar saƙo, domin ana iya tabbatar da cewa an haɗa da na’urar da ta dace kafin a fara aika rubutu. Wannan ya sa an ƙara yarda da shi a harkokin kasuwanci da diflomasiyya.

Sauƙin adana bayanai

Saboda saƙonnin Telex suna fitowa a takarda, ana iya adana su cikin sauƙi a matsayin hujja ko tarihi. Ofisoshi da kamfanoni sun yi amfani da wannan dama wajen ajiyar bayanai na kasuwanci, umarni, da yarjejeniyoyi.

Adana saƙonnin ya taimaka wajen komawa ga bayanai a gaba, musamman idan aka samu saɓani ko buƙatar duba abin da aka tattauna a baya. Wannan ya sa Telex ya zama muhimmin kayan aiki a tsarin gudanarwa.

Rashin buƙatar intanet

Telex ba ya buƙatar intanet ko kwamfuta domin aiki, domin yana amfani ne da layin waya kai tsaye. Wannan ya sa ya dace a zamanin da babu intanet, kuma har ma a wuraren da sadarwar zamani ba ta kai ba. Saboda haka, a lokuta da dama Telex ya kasance hanya mafi tabbaci ta sadarwa a wuraren da sauran hanyoyi ba su da inganci.

Matsaloli da gazawar Telex

Aika rubutu kawai

Babbar gazawar Telex shi ne cewa yana iya aika rubutu ne kawai, ba tare da hotuna, zane, ko wasu nau’ikan bayanai ba. Wannan ya sa ya zama mai gajeren amfani idan aka kwatanta da fax ko imel, waɗanda ke iya aika takardu da hotuna gabaɗaya. Saboda wannan iyaka, aka fara rage amfani da Telex lokacin da aka samu sabbin hanyoyin sadarwa masu ƙarin abubuwa.

Jinkirin yayin aiki

Kodayake Telex ya kasance mai sauri a zamaninsa, idan aka kwatanta da fax, imel, da saƙonnin intanet, yana da jinkiri. Aika saƙo na iya ɗaukar lokaci mai tsawo, musamman idan saƙon yana da tsayi ko kuma layin sadarwa ba shi da ƙarfi. Haka kuma, buƙatar bugawa da hannu ta maɓalli na rage saurin aika bayanai idan aka kwatanta da na’urorin kwamfuta na zamani.

Tsadar kayan aiki

Na’urorin Telex suna da tsada wajen saya, girkawa, da kula da su. Haka kuma, cibiyar sadarwar da ake buƙata domin aiki tana buƙatar manyan kayayyaki da gyare-gyare akai-akai. Wannan ya sa ƙananan kamfanoni ba su iya mallakar tsarin cikin sauƙi ba. Tsadar ta ƙara fitowa fili lokacin da aka samu sabbin fasahohi masu rahusa kamar fax da intanet.

Layin waya na musamman

Domin telex ya yi aiki yadda ya kamata, yana buƙatar layin waya na musamman da aka tanada domin wannan aiki. Ba kowane layi na waya ba ne zai dace da shi. Wannan ya haifar da ƙarin wahala wajen girka tsarin, musamman a wuraren da ba su da ingantaccen tsarin sadarwa. Saboda wannan dalili, ya zama dole a samu cibiyar sadarwa mai ƙarfi kafin a iya amfani da Telex yadda ya kamata.

Bambanci tsakanin telex da sauran hanyoyin sadarwa

Telex da Fax

Telex da Fax duka hanyoyin sadarwa ne da suke amfani da layin waya, amma suna da bambance-bambance masu muhimmanci. Telex yana aika rubutu kawai, inda abin da aka buga a maɓalli yake isa a rubuce a ɗaya gefen. Fax kuwa yana aika kwafin takarda gabaɗaya, wato rubutu, hoto, sa hannu, da zane duk tare, kamar yadda suke a asali.

Haka kuma, Telex yana buƙatar na’urorin teleprinter guda biyu masu tsarin Telex, yayin da Fax zai iya aika kowace takarda da aka saka a na’urar. Saboda wannan damar aika hotuna da takardu gabaɗaya, Fax ya fi dacewa da ofisoshi a lokacin da aka ƙirƙire shi, wanda  hakan ta sa ya fara maye gurbin Telex a wurare da dama.

Telex da Telegram

Telegram wata tsohuwar hanyar sadarwa ce da ta gabaci Telex, wadda ke aika saƙonni ta hanyar telegraph. A tsarin Telegram, ana aika saƙo zuwa cibiyar sadarwa, sannan ma’aikata su sake rubuta shi ko isar da shi ga mai karɓa. Wannan tsari yana ɗaukar lokaci kuma yana iya haifar da kuskure.

Telex ya fi Telegram inganci domin yana ba da damar sadarwa kai tsaye tsakanin na’urori biyu ba tare da wani a tsakiya ba. Haka kuma, Telex yana ba da damar tattaunawa ta rubutu kai tsaye, yayin da Telegram yawanci hanya ce ta aika saƙo guda ɗaya da za a karɓa daga baya.

Telex da Email

Email wata sabuwar hanyar sadarwa ce da ke amfani da intanet domin aika saƙonni cikin sauri a duniya. Idan aka kwatanta da Telex, Email yana da fa’idoji da yawa, kamar damar aika rubutu, hotuna, bidiyo, da takardu iri-iri cikin sauƙi. Haka kuma, Email ba ya buƙatar layin waya na musamman, domin yana aiki ne ta hanyar intanet.

Telex yana da iyaka ga rubutu kawai, kuma yana buƙatar na’ura ta musamman. Saboda haka, Email ya zama mafi sauƙi, sauri, da arha, wanda ya sa ya maye gurbin Telex a yawancin fannoni na sadarwa.

Manazarta

Electro Props Hire. (n.d.). 1960s-1970s practical ASR33 Teletype/teleprinter/telex terminal with ticker tape | Electroprops.

Uys, J. (2025, June 1). The Telex Machine: how it worked, stored messages, and connected the world. LinkedIn

Wikipedia contributors. (2026, February 16). Teleprinter. Wikipedia.

Sharuɗɗan Editoci

Duk maƙalun da ku ka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta tare da sa idon kwamitin ba da shawara na ƙwararru. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.

Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.

Maƙalar ta amfanar?
EAa

You cannot copy content of this page

×