Tsawa ɗaya ce daga cikin muhimman al’amuran yanayi waɗanda ke haifar da ruwan sama mai ƙarfi da iska mai ƙarfi da ƙanƙara da walƙiya har ma da guguwa. Tsawa na afkuwa dalilin rashin daidaituwar yanayi da kaɗawar iska wanda ke janyo haɗuwar mabanbantan yanayi da yawa, ciki har da iska mai ɗumi ta riƙa tashi da sauri zuwa cikin yanayi; isasshen danshi don samar da gajimare da ruwan sama; da kuma ɗaga igiyoyin iskar da ke haifar da sauyin yanayi (sanyi da ɗumi), daga iskar teku ko tsaunuka.
Ana bayyana tsawa a matsayin mai tsanani kuma mai haɗari idan ƙarfinta ya kai ko ya wuce adadin 58 hph, takan haifar da guguwa ko kuma zubar ƙanƙara aƙalla inci 1 a tsarin awon diamita. Tsawa na iya faruwa a matsayin guda ɗaya, ko a cikin gungu, ko cikin layuka. Don haka, yana yiwuwa tsawa da yawa su yi tasiri a wuri ɗaya cikin sa’o’i kaɗan. Waɗannan al’amuran suna haddasa ɓarna musamman lokacin da tsawa ɗaya ta shafi wuri ɗaya na tsawon lokaci. Irin waɗannan yanayi suna haifar da sakwarkwacewar ƙasa da kuma ambaliya da zaizayar ƙasa.
Walƙiya babbar barazana ce ta biyu da ke da alaƙa da tsawa. A Amurka, tsakanin Amurkawa 75 zuwa 100 ne walkiya ke kashewa a kowace shekara. Yawancin bala’o’in iska ana danganta su da tsawa saboda yanayi ne da ba a iya hango tashin hankali da suke haddasawa da kuma barazanar gazawar na’ura ko hanyar hasaso faruwar su. Lokacin da walƙiya da tsawa suka afka wa mutane ko sassa, tasirinta yana da muni ga duka biyun.
Tsawa yanayi ne mai tsanani da ke da alaƙa da yawan walƙiya, yawan iska, da ruwan sama mai yawa. Tana iya faruwa a kowane lokaci na shekara, amma galibi tana faruwa a lokacin rana da sa’o’in yamma da lokacin bazara da rani. Ana kiran ta tsawa saboda ƙarar da ke tashi. Kasancewar tsawa na wanzuwa da sauti, don haka tana fitowa daga walƙiya, dukan tsawa suna faruwa da walƙiya.
Nau’ikan tsawa
Single-cell
Wannan nau’in tsawar ƙarama ce, mai rauni kuma gajeriya, yawanci ba ta wuce minti 30 zuwa 60, misali guguwar da ke tasowa a unguwanni a lokacin rani da rana.
Multi-cell
Wannan ita ce tsawa ta gama gari da ake kallo a matsayin tsawa, takan yi tafiyar mil da yawa, tana daɗewa har tsawon sa’o’i, kuma tana iya haifar da ƙanƙara da iska mai ƙarfi da gajeriyar guguwa da ambaliya a wasu lokutan.
Supercell
Wannan ma tsawa ce mai daɗewa wadda ke haifar da haɓakar abubuwa kamar tashin igiyoyin iska wanda kan iya haddasa aukuwar guguwa mai ƙarfi da ɓarna.
Mesoscale Convective Systems (MCS)
Waɗannan tarin tsawa ne waɗanda ke aukuwa a matsayin guda ɗaya. Suna iya bazuwa ko’ina cikin ƙasa ko yanki, kuma suna wanzuwa fiye da sa’o’i 12.
Ayyukan tsawa
Tsawa ginshiƙai ne masu samar da wutar lantarki, waɗanda ke fitar da igiyoyi zuwa sama a cikin da’irar wutar lantarki ta duniya. Sararin makamashin lantarki da aka samar ta hanyar tsawa da ke motsawa a yanzu na iya shafar E×B plasma drift, wanda yake haifar da sake rarraba yawan plasma a cikin sashen ionosphere. An ba da rahoton cewa ayyukan lantarki da ke da alaƙa da koda ƙaramar tsawa ne yana shafar sashen ta hanyar ɗumama makamashin electrons sannan daga baya ya rage yawan electron ɗin.
Baya ga tasiri a fannin wutar lantarki, ayyukan tsawa na haifar da haɓakar igiyar ruwa daga saman girgijen da ya mamaye sama. Kaɗawar nauyin da aka samar daga ayyukan tsawa yana yaɗuwa zuwa sama kuma yana tura makamashi zuwa sashen ionosphere wanda za a iya gani a cikin TEC na ionosphere ɗin kuma a wasu lokuta ayyukan tsawa na iya haifar da kumfar ionospheric plasma da aikin scintillation.
Tattaruwar tsawa
Tsawa ba koyaushe take faruwa a matsayin keɓaɓɓen abu guda ɗaya ba. A maimakon haka, takan zama rukuni-rukuni, a cikin layuka ko gungu guda ɗaya. Mafi akasarin tsawar da aka fi sani ita ce mai afkuwa a cikin layuka, wani lokaci ana kiran ta da squall liines. Lokacin da ƙwayoyin sinadaran samuwar tsawa masu yawa suka haɗu suka taru, to tarin tsawa na iya daɗewa na tsawon lokaci fiye da ƙwayar sinadarin guda ɗaya (wanda tsawon rayuwarsa bai wuce mintuna 20 zuwa 30 ba. Wannan yana nufin cewa ƙanƙara da abubuwan da ke faruwa na iska da irin waɗannan rukunonin tsawa ke haifarwa ba sa daɗewa, maimakon tsawaitawa kamar yadda suke a manyan ƙwayoyin sinadaran samuwar tsawa, kamar yadda ƙwayar sinadarin ke tasowa kuma ta ruɓe a cikin rukunin. Yanayi mai tsanani na iya ci gaba a cikin irin wannan hali har tsawon sa’o’i da yawa a lokacin da aka fuskanci irin wannan tsawa. Hulɗa tsakanin ƙwaya guda ɗaya samuwar tsawa a cikin tsarin layuka da kuma gungu na ƙwayoyin sinadaran tsawa galibi suna da rikitarwa kuma suna da wuya a iya tsinkaye ko hasashe, sannan irin wannan hulɗar na iya zama silar haifar da gurɓataccen yanayi.
Wani nau’i mai haɗari musamman na haɗuwar tsawa yana tasowa lokacin da sababbin kwayoyin sinadaran samuwar tsawa ke tasowa a kowane lokaci, da kuma bin diddigin yanki ɗaya akai-akai, wannan yanayi shi ake kira ‘training’ saboda ƙwayoyin sinadaran kamar motoci ne a cikin jirgin ƙasa. Wannan yana nufin cewa wani yanki na fuskantar ruwan sama daga jerin tsawa da ƙwayoyin sinadaran, wanda zai iya haifar da ruwan sama mai tsananin gaske. Wannan shi ne tsarin da ke da alaƙa da yawancin abubuwan da suke faru na ambaliya, a duk duniya.
A Amurka, ba a ɗaukar ruwan sama mai yawa a matsayin ma’auni ga abin da a hukumance ake ɗauka a matsayin ‘mai tsanani’ duk da mahimmancin irin wannan ruwan sama a cikin abubuwa masu haddasa ambaliya. A ɗaya bangaren kuma, wasu ƙasashe da dama na duniya suna ɗaukar ruwan sama mai karfi a matsayin muhimmin nau’i na haɗari mai tsanani da tsawa ke haddasawa.
Tasirin tsawa ga lafiya
Cutar asma
Masana sun bayyana wani nau’i na cutar asma da ke faruwa sakamakon tsawa wanda ake kira da “Thunderstorm asthma.” Wannan yanayi yana nufin ƙaruwar tsananin ciwo ga masu fama da asma bayan aukuwar tsawa. An fara samun rahoton irin wannan nau’in asma mai alaƙa da tsawa a cikin shekarun 1980s. A lokacin an bayar da rahoton samuwar ta a duniya a ƙasashe irin su; Biritaniya, Australia, Kanada, Amurka, Italiya, da sauran su.
Cumulonimbus cloud convection
Baya ga duba na’urar radar don hasashen yanayin tsawa, wata hanyar gano tsawa mai girma ita ce duba yanayin gajimare da ake kira da cumulonimbus. Tsawa na aukuwa a lokacin da iska a kusa da ƙasa ta yi zafi kuma ta tashi sama zuwa cikin sararin iska (atmosphere), irin wannan tsari ana bayyana shi da “convection.” Tunda giza-gizai na cumulonimbus giza-gizai ne da ke shimfiɗe a tsaye zuwa sararin samaniya, sau da yawa hakan alama ce tabbatacciya da ke nuna haɗari mai ƙarfi zai iya faruwa. Kuma inda akwai convection (wanzuwar iska mai zafi a kusa da ƙasa, hadari tabbas zai biyo baya.
Wani batu da za a lura shi ne cewa mafi girman saman gajimare na cumulonimbus, mafi tsananin guguwar da za a fuskanta.
Yadda tsawa take zama mai haɗari
Saɓanin abin da mutane ke tunani, ba duk tsawa ba ce take zama mai haɗari ko mai tsanani ba. National Weather Service ba ta kiran tsawa mai haɗari sai dai idan ta haifar da ɗaya ko fiye na waɗannan sharuɗɗan:
- Ƙanƙara ta kai 1 inch ko mafi girma a diamita, dalilin tsawar
- Ƙarfin iskar ya kai 58 mph ko fin haka ta sanadiyyar tsawar
- Gajimare ko guguwa ƙasa da kashi 1% na tsawar yahaifar da guguwa.
Tsawa mai haɗari takan tashi a gaban, gaban sanyi, yankin da iska mai ɗumi da sanyi ba sa jituwa. Tashin tsawar mai ƙarfi yana faruwa a wannan matakin rashin jituwa kuma yana haifar da rashin tabbas ga yanayi mai ƙarfi, saboda haka mafi tsananin yanayi fiye da dagawar yau da kullun na samuwa wanda kan wadatar da tsawa.
Yanayin nisan tsawa
Tsawa (sautin da walƙiya ke yi) yana tafiya kusan mil ɗaya a cikin daƙiƙa 5. Ana iya amfani da wannan adadin don ƙididdige mil nawa nesa da tsawa zai iya kasancewa.
Manazarta
Earth Networks. (2019, July 23). Thunderstorms: Everything you need to know – Earth Networks. Earth Networks -.
Krider, & Philip, E. (2025, June 22). Thunderstorm | Definition, Types, Structure, & Facts. Encyclopedia Britannica.
NOAA National Severe Storms Laboratory. (n.d.). Thunderstorm Basics.
*****
Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.
Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.