Skip to content

Tsibiri

An rarraba tsibirai a matsayin ko dai na teku ko na nahiya. Tsibirin teku yana tasowa ne sama daga ƙasan teku. Irin waɗannan tsibiran gabaɗaya dutse mai aman wuta ne. Narkakken dutse yana taruwa, yawanci na tsawon lokaci, yakan yi kauri sosai har sai ya buntsiro sama. Ta irin wannan hanya ce aka kafa tsibiran Hawai.

Tsibiri mafi girma a Tekun Bahar Rum shi ne Sicily.

Tsakanin watan Nuwamba 1963 da Yuni 1967, aikin volcanic ya haifar da sabon tsibiri, wato Surtsey, kusa da bakin tekun Iceland. Sabon tsibirin ya kasance mai faɗin murabba’in mil ɗaya (kilomita 2.6) a cikin yankin kuma ya tashi sama da ƙafa 560 (mita 170) sama da matakin teku, jimullar ƙafa 950 (mita 290) daga ƙasan teku. Tarin dutsen da ya samar da tsibirin Hawaii ya tashi sama da ƙafa 32,000 (mita 9,750) daga ƙarƙashin teku.

Tsibiran Continental suna kusa da ko kuma cikin nahiyoyi. Sun wanzu ne daga cikin ɓangarorin nahiyoyin duniya, waɗanda yawancinsu suna ƙarƙashin tekuna; a ɓangaren tafki ko kogi, tsibirai na tasowa ne daga sassan da ruwa ya lullube, na cikin nahiyar. Greenland, mai faɗin murabba’in mil 840,000 (kilomita 2,175,600) tsibiri mafi girma a duniya, ya ƙunshi abubuwa iri ɗaya da nahiyoyin Arewacin Amurka, wanda ke nuni da cewa su biyun suna haɗe ne a ƙarƙashin teku. Hakazalika, tsibiri na biyu mafi girma, wato New Guinea, yana da alaƙa da Austiraliya. Sauran manyan tsibiran nahiyoyi su ne Great Britain, Newfoundland, da Falklands. Florida Keys, waɗanda suka wuce kudu daga Florida, amma wannan faɗi ne kawai na jihar.

Tsibirin Padre, kusa da bakin tekun Texas, da jerin tsibiran da ke da alaƙa da gaɓar gabas na Florida, tsibiran shinge ne. Wannan nau’in tsibiri na nahiyoyi yana samuwa ne lokacin da kaɗawar iska da igiyoyin ruwa suka nutsar da yankunan da ke daf da ruwa daga baya kuma su bayyana.

Daga cikin tsibiran kogi, mafi shahara shi ne Manhattan, wani yanki na birnin New York. Ya yi iyaka ta yamma da kogin Hudson, a gabas da kogin Gabas, a arewa maso gabas da kogin Harlem da Spuyten Duyvil Creek, sannan daga kudu ya yi iyaka da New York Bay. Manhattan yana da jimullar faɗin mil 22 (murabba’in kilomita 57). Tsibirin kogi mafi girma shi ne Ilha de Marajo a cikin kogin Amazon a Brazil. Yana da nisan mil 183 (kilomita 295) da faɗin mil 124 (kilomita 200), tare da faɗin murabba’in mil 18,900 (kilomita 49,000).

Hanyoyin tsibiri dogaye ne masu lanƙwasa. Suna cikin ɓangaren girgizar ƙasa mafi yawa a wuraren da ke da dutse mai aman wuta a duniya. Ban da East Indies, akwai West Indies (Caribbean) arcs, da Scotia arc a Kudancin Atlantic, duk tsibiran sun yi iyaka da Tafkin Pacific. Wasu daga cikin waɗannan manyan hanyoyin tsibiran su ne Aleutians, Japan, Ryukyus, da Marianas, Philippines, New Britain–New Guinea, Solomons, da New Zealand. Saboda irin wannan tsari na yanayin ƙasa, wasu sassan duniya waɗanda ba na tsibiri ba galibi ana haɗa su cikin ma’anar tsibiri, misali; Amurka ta tsakiya, Italiya, da gaban kudancin Himalayas.

Bugu da ƙari ga yanayin fili da ke bambanta, sauran siffofi na tsibirai sun haɗa da dogayen ramuka masu zurfi, zurfin teku tare da madaidaiciyar gaɓa; hanyoyin dutsen mai aman wuta waɗanda ke samar da yawancin tsibirai masu karkata; tashin rairayin bakin teku da kuma ɗagawa, naɗewa, da sauran su.

Kusan 1 cikin mutane 6 na duniya suna rayuwa a tsibiri. Manazarta

Rayuwar tsirrai da dabbobi a tsibiran da ke cikin ko kusa da wata nahiya yawanci alama ce da ke nuna irin nau’in tsirrai da dabbobin da ke rayuwa a nahiyar. Keɓantattun tsibiran teku, yawanci wasu nau’ikan dabbobi ne kawai ke mamaye su. Sau da yawa ana lulluɓe su da ciyayi masu armashi, waɗanda irinsu ke fara zuwa lokacin da iska, igiyoyin ruwa, ko tsuntsaye suka ɗauke su.

Nau’ikan tsibiri

1. Tsibirin Volcanic

Tsibirin volcanic suna samuwa ne ta hanyar volcanic actions, inda narkakken dutsen magma ke fitowa daga ƙarƙashin ƙasa, wanda ke haifar da sabbin wurare a doron ƙasa daga ƙarkashin teku. A tsawon lokaci, fashewar dutsen akai-akai tana haɓaka samuwar lava, wato sabo dutsen da ke samuwa a sakamakon narkewar dutse mai aman wuta, a hankali sai ya kafa tsibirai a saman teku. Waɗannan tsibiran yawanci ana siffanta su da ƙaƙƙarfar ƙasa, tuddai, da kololuwar tsaunuka. Misalai: Tsibirin Hawaii (Amurka), Tsibirin Galapagos (Ecuador), Tsibirin Canary (Spain).

2. Coral Islands (Atolls)

Tsibirin Coral, ana kuma kiran wannan tsibiri da atolls. Yana wanzuwa ne daga tarin tarkace da matattun halittun ruwa. Yayin da waɗannan tarkace ke haɓaka da kuma faɗaɗa, suna ƙirƙirar iyakoki da shingaye a cikin ruwa. Tsibiran Coral yawanci ƙanƙara ne kuma sun haɗa da calcium carbonate. Misalai: Maldives, Seychelles, Tsibirin Marshall.

3. Continental Islands

Tsibiran nahiyoyi yanki ne na ƙasa waɗanda a da sun kasance ɓangare na babban nahiya amma sun rabu saboda yanayin ƙasa kamar motsin tectonic, canjin yanayin teku, ko zazzagewa. Waɗannan tsibiran yawanci suna kusa da kantunan nahiyoyi kuma suna iya bayyana siffofin yanayin ƙasa da yanayin halittu kamar nahiyoyin da suka fito. Tsibirin Nahiya na iya bambanta ta kowace fuska kamar girma, tsayi, da kuma yanayi, yana nuna bambancin shimfidar doron ƙasar nahiyoyi. Misalai: Great Britain, Tasmania (Ostiraliya), Newfoundland (Kanada).

4. Tsibirin Oceanic

Tsibirin Oceanic, wannan tsibirai ne masu tsayi, keɓaɓɓun yankun ne waɗanda ke tashi daga ƙarkashin teku, galibi suna samuwa ta hanyar ayyukan volcanic ko hanyoyin tectonic. Ba kamar tsibiran nahiyoyi ba, tsibiran teku ba su da alaƙa da nahiyoyin ƙasa kuma yawanci suna nesa da iyakokin nahiya. Waɗannan tsibiran na iya haɗawa da ɓangarorin bakin tekuna, kololuwar tsaunuka, da dazuzzukan wurare masu zafi, suna samar da wuraren zama na musamman ga nau’ikan da ba su da yawa. Misalai: Easter Island (Chile), Madeira (Portugal), Fiji.

5. Barrier Islands

Tsibirai masu shinge suna da tsayi da siffofi masu kama da bakin tekuna. Waɗannan tsibirai suna samuwa ne ta hanyar danƙarewar laka, yashi, da tarkace da matattun halittun ruwa. Tsibirai masu shinge suna ba da muhimmiyar kariya a bakin teku, suna kare yankin daga guguwa, zaizayar ƙasa, da ayyukan igiyar ruwa, yayin da kuma suke zama mazaunin tsuntsaye da namun daji. Misalai: Bakunan Waje (Amurka), Tsibirin Fraser (Australia), Tsibirin Padre (Amurka).

6. Tsibirin Kogi (Fluvial Islands)

Tsibirin kogin, ana kiran shi da fluvial island, manyan filaye ne da ke tasowa a cikin magudanan kogin ko filayen ambaliyar ruwa sakamakon laka. Tsibirin kogin na iya bambanta da girma da siffa, kama daga tarin yashi zuwa manyan filayen tuddai, da kuma samar da muhimman wurare ga ciyayi na rafuka da halittun ruwa. Misalai:  Thousand Islands (Kanada/Amurka), Île de la Cité (Faransa), Tsibirin Kogin Brahmaputra (Indiya/Bangladesh).

Misalan tsibiran da ke faɗin duniya

Tsibiran yankunan kasa ne da ba su da alaka da wata nahiya da ke kewaye da ruwa. Akwai manyan nau’ikan tsibirai guda biyu; tsibiran nahiyoyi da tsibiran teku. Tsibirin nahiya wani yanki ne na nahiyar. Ɗaya daga cikin misalin wannan shi ne Great Britain, tsibiri ne da ke zaune a kan gabar tekun Turai. Oceanic Islands, tsibirai ne waɗanda ba sa zaune a kan shimfidar nahiya. Yawancin tsibiran teku suna samuwa ta hanyar tsaunuka na ƙarƙashin teku kamar Hawaii a cikin Tekun Pacific. A ƙasa akwai wasu manyan tsibiran duniya:

Greenland

Greenland shi ne tsibirin mafi girma a duniya wanda ba nahiya ba. Yana da fadin murabba’in mil 822,706 wanda ya ninka fiye da ninki biyu na tsibiri mafi girma na biyu, wato New Guinea. Saboda irin wannan babban tsibiri, Greenland kawai yana da yawan jama’a kusan 56,000 wanda hakan ya sa ya zama wuri mafi ƙarancin yawan jama’a a duniya. Wannan ya faru saboda yawancin Greenland na rufe da  ƙanƙara. Greenland yanki ne na nahiyar Arewacin Amurka, amma a siyasance gabaɗaya ya kasance yanki na Turai ta ƙasar Denmark.

Great Britain

Great Britain shi ne tsibiri na tara mafi girma a duniya kuma shi ne tsibiri mafi girma a tsibiran Burtaniya. Shi ne tsibiri na uku mafi yawan jama’a a duniya. Daular Burtaniya ta kasance a tsakiya a kololuwar ta a karni na 18 zuwa na 20, ita ce daula mafi girma a tarihin duniya. Wani yanki ne na Turai kuma yana bakin tekun arewa maso yammacin Faransa.

Madagascar

Madagascar shi ne tsibiri na hudu mafi girma a duniya. Yana kusa da gaɓar tekun kudu maso gabashin Afirka. Madagaskar gida ne ga nau’ikan dabbobi da tsirrai da yawa waɗanda ba za a iya samun su a ko’ina a duniya ba. Kusan kashi 80% na tsirrai da dabbobi a tsibirin ana iya samun su a Madagascar ne kawai. Yana da ban mamaki wasu masana kimiyya suna kiran shi a matsayin nahiya ta takwas.

Honshu

Honshu shi ne tsibiri mafi girma da ya ƙunshi ƙasar Japan. Shi ne tsibiri na bakwai mafi girma kuma yana a matsayi na biyu mafi yawan mutane bayan tsibirin Java mai yawan jama’a sama da miliyan 100. Dutsen mafi girma a kan Honshu shi ne sanannen dutsen na mai suna Fuji, mai aman wuta kuma birni mafi girma shi ne Tokyo.

Luzon

Luzon babban tsibiri ne na tsibiran da suka ƙunshi ƙasar Philippines. Shi ne tsibiri na biyar mafi yawan jama’a a duniya kuma gida ne ga birnin Manila. Ana ɗaukar Manila Bay a matsayin ɗaya daga cikin mafi kyawun tashar jiragen ruwa ta yanayi a duniya saboda girmanta da wurinta.

Wasu muhimman bayanai game da tsibiran duniya

  • Java shi ne tsibiri mafi yawan jama’a a duniya tare da sama da mutane miliyan 130.
  • Dutsen mafi tsayi a tsibiri shi ne Puncak Jaya da ke tsibirin New Guinea.
  • Wasu tsibiran ƙirƙirarru ne. Misali ɗaya na wannan shi ne filin jirgin sama na Kansai a Japan wanda ke zaune a tsibirin da mutun ne ya ƙirƙira.
  • Kalmar tsibirin hamada tsibiri ne da babu mutane a cikinsa. Wannan ba yana nufin cewa tsibiri hamada ne ba, sai dai a ce babu kowa.
  • An haifi Napoleon Bonaparte a tsibirin Corsica.
  • Tsibiri mafi girma a Tekun Bahar Rum shi ne Sicily.
  • Kusan 1 cikin mutane 6 na duniya suna rayuwa a tsibiri.

Manazarta

Decoding Biosphere. (2024, February 2).  An overview of 6 major types of islands and their characteristics and examples.  Decoding Biosphere.

Geography for Kids: Islands. (n.d.).

Britannica  island. (n.d.). Britannica Kids.

Was this article helpful?
YesNo

You cannot copy content of this page

×